Sashe 20
Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A dan kwanciyar da tayi batasan lokacin da bacci ya dauketaba, wasu matasan yara tagani da akalla befi su bata shekaru uku ba, kyawawa dasu sai faman kuka suke , daga gefensu wani farin macijine shima tass dashi, kallan tahee dake gefe sukai sai suka kara fashewa da kuka , suna kuka suna biyota , cikin tsorata tahee ta fara jan baya, girgiza mata kai suka shigayi, cikin daddadan muryarsu “sun kashe mana farin cikin mu , sun cutar damu, bamuyi musu komai ba, laifin me mukai musu, nace laifin me mukai musu” suka karasa cikin data tsawa , firgita tahee tayi da yanayinsu, ganin sun tsaye ne yasa itama tsayawa,cikin rawar murya tahee ta fara magana “su..suwane ku, me nayi muku”, dariya suka saki tare da kara sakin wani saban kukan, “SIF,LOLA,”sai kuma farar magan ciki ta shafa can macijin nan” SUSAN”, tana gama fadar haka suka kara sakin kuka tare da bace bat kamar basu taba wanzuwa ba. A firgice tahee ta farka daga baccin da ya dauketa bakin ta dauke da addua , shafa wuyanta da ya dan rike tayi” me yasa nake yawan mafarkin masu sunannan,su wanene su”ganin babu me bata amsa yasata mikewa , kayan jikinta ta cire tare da shiga wanka , mintuna kadan tafito daga nan dakin, daya daga cikin abayoyin da ammi ta bata ta saka , gaban mudubin dake shake da kaya ta nufa,kurawa fuskarta ido tayi ganin irin sahirtaccen kyan da tayi a cikin kwanaki uku da tayi a cikin gidan , sanye take cikin red Egyptian abaya sai faman walwali stone din jiki ke dauka,asalin farin fatarta ta buzaye ta fito tass a jikinta, yayinda cikakken yalwataccen gashin kanta ya sauko har wajan kugunta, sosai bakin kwantaccen gashin goshinta ya kara kwantawa tare da dogon siririn hancinta , ba make up ne a fuskarta ba amma fadin haduwarta bata lokaci ne musamman dan karamin lips dinta da ya fito tass dashi kamar wacce ta saka janbaki,bakin kwalli ta saka da ya fito da farin kyawawan idanuwanta, sosai kwallin ya fito da asalin kwayar idanunta,cikakkiyar gashin girarta da dogayen eye lashes din idanuwanta su suka kara fito da ainahin kyawun fuskarta , ba ma a bociyar lip gloss bace shiyasa tabar dan karamun lebenta a haka, ribbon dinta ta dauka shima red colour tana kichiniyar daurashi, sosai ta jigata kafun ta daureshi sabida cikowarsa,mayafin abayarta ta dauka tare da yafashi saman kanta, red din takalmin ta ta saka , gaban mudubin ta kara komawa tare da karewa kanta kallo , murmushi ta sakar wa kanta tare da rufe fuska , “ ke din me kyau ce “kalmar da kullum taheer ke fada mata, murmushi kawai ta kara saki , tayi kewarsu sosai, hanyar fita daga dakin ta nufa bayan ta gama feshe jikinta da turaruka, Daidai lokacin da yan matan ke shigowa part din,amrah sai faman dingishi take haryanxu jikinta be dena tsami ba, sakin baki tayi ganin irin kyawun da tahee tayi, bama ita kadai ba hatta su ihsan duk sakin baki sukai suna binta da kallo, gaishe da su tayi babu Wanda ya amsa mata sai ihsan dake faman sakin murmushi, “tubarkallah Masha Allah , gaskiya ke kyakkyawa ce tahee”,sun kuyar da kai kawai tahee tayi tana wasa da yan yatsun hannunta, binta da kallo su sumayya sukai kowa yana hadiye abunda ke ransa, dogon tsaki amrah taja tare da karasa kan daya daga cikin kujerun falon, sosai take bakinci, dama ace Itace take da wannan kyawun, wani dogon tsaki ta kuma ja tare da daukar wayarta suma duk yan matan waje suka samu tare da zama ,ihsan ce ke kokarin magana ,jin sallamar zoya ne ya katse mata zancenta, inda Ihsan take ta nufa “aunty ihsan” rungumeta ihsan tayi “na’am my baby”kallan yarinyar da aka kira da baby tahee tayi , Itace dai yarinyar da ta gani tana bacci,”aunty ihsan wai ina da wata aunty tana ina “murmushi ihsan ta saki, “toh daman bazuwan kowa kikai ba sai na auntyn taki ko”dariya zoya tayi tana rufe fuskarta , itama murmushi ihsan din ta saki “oya kinganta” juya wa zoya tayi tare da kallan Wanda aka nuna mata, zaro fararan idanuwanta irin na king tayi, “aunty ihsan tana kyau, harta fini ma, amma yaya king dina ya fita” dariya ihsan ta saki kawai , sai alokacin tahee taga tsananin kamanninta da Wanda yake zuwa part Dinsu,murmushi kawai tahee ta sakar mata, itama murmushi zoyan ta saki “Aunt ya sunanki” taheera shine kadai abinda tahee tace,kara zaro ido zoya tayi “sunanki me dadi , ni kuma zoya yanxu Kema kinzama aunt dina kinji”girgiza mata kai tahee tayi sosai yarinyar tashiga ranta, duk wannan abun su sumayya na zaune suna kallan ikon Allah musamman amrah dake jin kamar ta samu wuka ta caccakawa tahee..shigowar ammi ne ya katsemata tunanin da ta shiga,”yaude yan mata na sai yanxu nake ganinku” ko wannansu murmushi ya saki sabanin sumayya da amrah da suka saki na yake “Aah ammi kinsan akwai school shiyasa “gyada musu kai ammi alamun gamsuwa kafin ta mike ,”yanxu dai ku Tashi ku kaiwa son abinci sai a dawo a yi hirar”, cikin firgita kowannansu ya zaro idanuwansa tare da furta YAYA KING…..
Comment and share .
💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Ya fita zakka
Jini daya
Sarki sameer
Baby .
MSS LEE💖..
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)
Story & written
By
Mss Lee 💖
PAID BOOK
littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581.
BOOK 1 📕
Free page 17🦋
Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace “zani ammi”jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya” Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata”ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta,”mtswww na tsani shishshigi Wallahi “, kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi, “zaki hanani taka ko ina na gidan mune”, dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu “malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne” tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita, “Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey”tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi “ammi zan bita”murmushi ammi ta sakar mata “toh daughter “kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka.