Sashe 12
Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bin bayan ta da kallo oumma tayi , abun na damunta sosai amma tana boye rauninta ne sabida kar tahee ta karaya, kullum adduar ta Allah ya zaba mata mafi alkairi.
Shigowar tahee dakin ne yasa taheer sakin murmushi dan duk yaji zancensu,kara sakin wani murmushin yayi yana kamo hannun tahee din, be bari tayi magana ba ya dora da “nayi mafarki, nayi mafarki kinyi aure ,kin auri babban mutum da kowa yake san mallakarsa ba wancan dan iskanba, zakiyi rayuwa dasu sosai wasu zasu soki, wasu kuma zaki nuna miki ki”binsa da kallo kawai tayi duk da bata yadda da magan ganun saba amma hakan ya sanyaya mata zuciya .
Karfe biyu na rana wasu manyan motocine suka shigo garin, kowa sai bin motar yake da kallo ana d’aga musu hannu, Daidai kofar gidansu tahee motocin nan sukai parking yara da manya kowa ya cika wajan , cikin gida kuwa har an kawo musu labari, da sauri kaka ta bawa ta shige daki tare da dakko wata farar Leda data cukurkude, bude ledar tayi tare da dakko tsinken turaran wuta, bayan ta kunna turaren wutarne ta koma ta dauko sabuwar tabarmarta ta shinfida a tsakar gidan , komai cikin sauri take yinsa .
A hankali ta fito daga cikin bayan wata tinted prado,bayan uban damin kudin data bawa security su rabawa mutane , ba kowa bace face hajiya kilishi, a hankali cikin takun manyan mutane ta nufi cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, yayinda biyu daga cikin security din suka fara fito da kayan motar suna shigar dasu cikin gidan . Tun daga kan matasan gidan har manya kowa tsugunnawa yake yana gaisheta, cikin sakin fuska take amsawa kowa harta karasa zama akan tabarmar da aka shinfida mata batare da ‘kyan ‘kyanin komai ba. Sosai sukai hirar Yaushe gamo ta bawa kowa tsarabarsa , duk wannan abun da ake su tahee basu sai me ke faruwa ba , sai hayaniyar da suke ji tana tashi sama sama,anan ne suke mata gulmar dawowar oumma da Sanar da tahee, sosai hajiya kilishi ranta ya baci akan rashin sanar da ita da basuyi ba , da Auran da suke san yiwa tahee, ranta ba karamun baci yayi har suka fara dana sanin fada mata , bata nuna musu komai ba sai fadan da tayi musu da Nasiha me ratsa jiki , sun dade suna tattaunawa kafin ta mike ta nufi dakin su tahee, kwankwasa kofa tayi , TAHEE dake tsaye rike da tsintsiya ta bude kofar , cikin waro ido da tsananin farin ciki ta furta “AUNTY” itama aunty tata murmushi ne kwance a fuskarta, budewa tahee hannuwa tayi da sauri kuwa tahee ta nufe ta , ta rungumeta sosai tayi farin ciki da ganin auntyn Tata har hakan ya kasa boyuwa, kallanta hajiya kilishi tayi ganin yadda ta kara ramewa ga bakin da tayi, batace mata komai ba sai girgiza kai kawai da tayi bayan tahee ta bata hanyar wucewa, sallar da hajiya kilishi tayi ne yasa ko wannansu kallan kofa, take ko wannansu ya saki murmushi, TAHEER ne ya tashi daga inda yake ya bawa aunty ta su waje , bayan sun gaisa sun dade suna hira kafun hajiya kilishi tayi wa oumma jajan abin da ya faru , kallan tahee hajiya kilishi tayi kafin ta kira sunanta” taheera “ tagowa tahee tayi tana amsa mata “na’am aunty” cikin dan hade rai hajiya kilishi ta soma magana” naji labarin kince kinaso kiyi aure har ankawo kudin ki , hakane “, fashewa da kuka tahee tayi tana girgiza kanta ni bana san shi aunty”ganin yadda take kuka ne yasa aunty tausaya mata itama tayi mata hakan ne sabida ta san asalin gaskiyar “shikenan share hawayen to” kamar yadda ta satan kuwa share hawayen tayi” yanxu zan baki za’bi zaki bini ko zaki auri tanimu” saurin dago da idanuwan ta tayi da zubawa auntyn tata, murmushi hajiya kilishi tayi tana mikewa “ kuyi shawara toh “, ganin yadda ta mike din zata basu waje oumma ta dakatar da ita “itama yar kice ai wata shawara zatayi , duk yadda kikayi ai Daidai ne”,Murmushin farin ciki hajiya kilishi tayi “nagode sosai yaya, Allah ya bar zumunci, nan da munti 30 zamu tafi “ tana gama fadar hakan ta bar dakin.
Dan kallan oumma tahee tayi cikin damuwa tace “oumma kin yadda na tafi ya barku” yar harara oumma tayi mata kafun ta mike “ idan ba kyaso ki bita sai kitsaya ayi miki auren inyaso sai ki tare” tana gama fadar hakan ta shige dakin. Kallanta TAHEER yayi “ shawarar da oumma tayi miki shine alkairi a gareki dan mutanan nan bazasu kyaleki ba sai sun aura miki shegen mutumin can , me kama da biri “jinjina masa kai tayi cikin damuwar dake fuskar nan, ganin yadda ta damu yasashi fara janta da hira har ta sake. Suna zaune oumma tafi to tare da kallansu, sosai tayi wa tahee fada da nasiha akan ta rike mutuncin ta, ta zama me hakuri da kawaici a duk yadda ta sameta, sosai oumma tayi mata nasiha da nuna mata illar rashin yin azkar, har kuka tahee tayi ganin yadda oumma take Mata nasihan me ratsa jiki, ko wannansu dauriya yake, shima taheer ji yake kamar ya saki kuka amma ya dake tare da sakin murmushi, suna zaune a hakan hajiya kilishi ta dawo , kasan cewar tahee tayi wanka hijabinta kawai tasa tana sharar kwalla, TAHEER ya dauki jakar kayanta tare da fita dasu, oumma bata biyota rakiya ba gudun abinda ze je ya dawo . Cikin sanyin jiki tahee ta fito waje , tsatstsaye ta same mutanan yan gidan kowa sai faman harare Harare suke ba bakin magana , musamman Dije da har kwallar bakin ciki se datayi, bintalo ba sai faman zaginta take ganin ba a tafi da ita . Saida hajiya kilishi ta gama sallamarsu kafun ta kama hannun tahee ta shigar da ita mota, a haka motocin suka fara tafiya, tunda aka fara tafiya tahee tunani take , har aka karaso airport din bata sani ba sai da hajiya kilishi tayi mata magana , wata Hanya sukabi a cikin airport din da ya kaisu wani babban fili, wasu manyan jiragene awajan kusan guda uku, ko wanne da tanbarin AL_NAHYAN a jiki , daya daga cikin jiragen suka nufa jikin tahee sai faman rawa yake,Daidai bakin step din jirgin ta tsaya ta fara rarraba idanu, ruko hannunta hajiya kilishi tayi “karki damu ba abunda zai miki” saurin gyada mata kai tahee tayi zuciyarta sai faman bugawa take , ga hannun hajiya kilishi da ta rike gagam a haka suka shiga cikin jirgin, duk sauran bodyguard din Sara mata sukai tare da tsayawa a wajan jirgin….
Comment and share ✍️.
💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖
💖LITTAFAN SUNE KAMAR HAKA 💖
👇👇👇👇👇
💖DUK KARFIN IZZATA( star lady)💖
💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖
💖SARKI SAMEER (xeenat love )💖
💖YA FITA ZAKKA (maman sayyid)💖
💖JINI DAYA (mrs bbk)💖
Comment and share ✍️.
Mss Lee 💖
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(A heart touching love story )
Story & written
By
Mss Lee 💖
💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖
PAID BOOK
MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581
BOOK 1📕
Free page 11 🦋