← Book details Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 23

Sashe 5

Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana komawa part dinsa , Wanka yayi cikin tsada sun suit dinsa black colour da suka fito da ainayin kalar fatar jikinsa , black hair din sa da ya hade da sajensa sai faman daukan sheki suke , hannunsa sanye yake cikin diamond watches , har yanxu fuskarsa a hade take karamun pink lips dinsa ya kara turuwa sosai , sosai kayan sukai masa kyau danshi din kyakkyawa ne da baki bazai iya fassara wa ba , yanxu ma ta elevator ya sakko kasa, ko kallan dining din da aka cika da kayan breakfast bayiba, zaki ne ya bude masa kofar falan shima fuskarsa a hade take sosai . Wasu irin tsadaddun motocine jere a wajan sai faman kyalli suke , wata farar Mercedes’ benz aka bude masa , basu tsaya ko ina ba sai wani babban part dake cikin gidan.
Cikin daya daga cikin kayataccen chairs din falon ya zauna , daddadan kamshin turarensa ya mamaye ko wana turare dake falon bakajin kamshin komai sai kamshin imperial majesty. Sanye take cikin wasu cotton din kaya masu laushi da sanshi, idanta sanye da farin glass sai faman mita take ita kadai, ganin wanda ke falon ne yasata tabe baki, “ nifa Adena zuwa ana takuramin, ina dalili Ance kayi aure kaki sai kazo ka tare min a daki da sassafe fisabilillah “, kara tsuke fuskarsa king yayi cikin daddadar muryarsa ya gaisheta “ Dada ina kwana , ya karfin jiki”, sallallami wacce aka kira da dada tayi , “yanxu fisabilillahi saraki zautacciya kamayar dani da har kakemun ya jiki!”to wallahi bari kaji, lapiyar da nake da ita ko ubanka baba tunanin yana da ita , bai kula taba Samm , dada kuwa sai faman mita take yace mata ya jiki,mikewa tayi tare da shiga wata kofa bata dade ba ta fito dauke da wani glass cup , ajje sa tayi a gabansa “maza maza ka shanye furar da kazo ka ka tattara ka Barmin daki”, ko kallan furar da ta ajje beyi ba sai da ya Mula dan Kansa sannan ya fara sipping din furar a hankali, furar tayi masa dadi sosai amma a zahiri sai ka dauka dole akai masa yasha,ko rabin cup din be shaba ya ajjeta “pray for me” , inma zagina Kayi kai da Allah “purey (pray ) din kawai naji,”Allah ya tsare ka dan Jikalle , Allah ya kawo auranka jibi jibi” tsuke fuskar sa yayi jin adduar ta ta karshe , diamond watches dinsa ya kalla tare da nufar hanyar fita daga falan Daidai lokacin da abeey da uncles dinsa ke kokarin shigowa,cikin tsokana uncle salim ya soma magana “wato kazo kacinyewa yar tsohuwarmu abinci kabarmu da kanzo ko”, duk murmushi suka saki yayinda fuskarsa take a haden ta har ynxu , wani murmushin abeey ya saki dan Sarai ya gane be san surutun da uncles din ke masa, uncle musaddiq ma sai faman dariyarsa yake ,sallama yayi musu tare da nufar part din mahaifiyarsa, bakowa a kantameman falon , direct dakin da yasan zai sameta ya nufa, knocking din kofar yayi, shiru ba’a amsa ba na kusan sakanni kafun ta bada izinin shigowa, cikin nutsuwarsa ya tura kofar dakin tana zaune cikin shigarta ta kullum, garage kyakkyawa irin asali da kyawun larabawa, doguwar jallabiya ce a jikinta red colour me shegen kyau da tsada , stone din jikin rigar sai faman kyalkyali yake, wata farar yarinyace a jikinta fara sol me kama da king kamar an tsaga kara, sallama yayi tare da karasa shigowa dakin, dagowa yarinyar tayi da sauri tare da nufarsa “AKHI!! ANA FI AINTIZARIK MUNDH ALBARIHA(yaya!! Tun jiya nake jiranka) ta karasa fada kamar zata saka kuka, lumshe mata idanunsa yayi tare da shafa fuskarsa da kyar ya furta “ana asf habibaty ( am sorry sweetheart), “hasanan akhi’usamihuk( okay brother , I forgive you).
Zoya !! Matar dake saune ta fada , cikin kinkina ta amsa mata “naam ummey”, ala yumkinuk an tahyiah lam ‘udadhirk min dhalik( bazaki gaishesaba , ban ja miki kunne ba) cewar ummey, kamar zatai kuka tace “ana asf ummey( kiyi hakuri ummey), sannan ta mayar da hankalin ta Kansa “ana asf akhi, sabah alkhaiyr( am sorry brother , ina kwana), girgiza Kai Kawai yayi dan har ta fara sa masa ciwon kai.

Cikin Yaren larabci ya gaishe da ummey, ba yabo ba fallasa ta amsa masa, bayan gaisuwa ba wanda ya kara magana sai zoya dake faman yi masa surutu, mikewa yayi tare da yi mata sallama , bin bayansa tayi da kallo har ya bar part din ka fun sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Tun daga entrance din falan ya fara jiyo hayaniya na tashi sama sama , yana shiga ya tarar dasu zazzaune a falon sai faman kwasan dariya suke, ammi na zaune tana kurban tea . Sallamar da yayine yasa falon yin shiru, kamar ba kowa aciki sai faman zare idanu suke , ganin sunyi shirune yasa ammi dago da idanuwanta, wanda ta ganine yasa ta sakin murmushi ,daman nasan za arina ta fada a zuciyarta, dukansu sak kowa sukai daga kan kujerar da suke , sai faman muzurai suke , cikin hada baki yan matan saka gaishesa” yaya king .. ina kwana”, kallan da yayi musune yasa hantar cikinsu kadawa, be amsa musu ba sai ma tanbayar da ya jefo musu, cikin husky voice dinsa “me ya hanaku zuwa makaranta”, ko waccensu tsure wa tayi suna kallan ammi ta gefan ido ko zata sa baki,ammi kuwa sharesu tayi, fingers din hannunsa ya daga musu “10 minutes only”, a guje ko waccensu ta bar part din dan sunsan ammi ce ta cecesu da bata wajan da Sunansu sorry. Suna barin part din ammi ta kalleshi, kaji da di daka tarwatsamun yaya , be amsa mata ba sai gaisuwar da yayi mata, itama bea dade ba yabar part din. Cikin wasu irin slow motocinnan suka fara fita, duk inda ya wuce sai kaga ana saramasa, suna hawa kan titi motocin suka fara gudu, sir ina zamu cewar zaki, ya dau mintu biyu kamar bazai tankaba sai kuma ya bude bakinsa” company “.

➰➰➰➰➰➰➰➰
Manage please abubuwane suka dan shamun kai..

Comment and share ✍️🫶

💖the talent troupe 🔥

Writers of ……

Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Sarki sameer
Jini daya
Ya fita zakka…

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖GIDAN AUNTY💖

By mss LEE

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

BOOK 1📕

FREE PAGE 6

Yau ma da asuba suka tashi, bayan sun idar da sallah aikin gidan suka fara , TAHEER da TAHEERA suka debo ruwa kafin suyi wanke wanke, yau ko buga kofarsu da aka saba yi ba ayi ba, gidan tsit kamar ba kowa a ciki, suna kammala aikin nasu daki suka koma, wata tsohuwar 200 oumma ta basu “nasan kunajin yunwa, kuje Wajan abu me kosai kuce ta baku kosai”, Godiya sukai mata tare da nufar kofar da zata sadasu da waje , a hanya suka hadu da Dije zata shiga ban daki , tana ganin su tai saurin shigewa bayi tana tsine musu, basu bi ta kansu ba dan yunwa suke ji . Basu dadeba suka dawo, ganin oumma na karatun azkhar dinta yasa basu kuma cewa komai ba har saida ta kammala . Kosan tahee ta Mika mata tare da dakko musu wani plate din robber , juye kosan sukai a ciki tare da faracin abinsu, bayan sun kammala ruwa suka sha tare da yin hamdala, sai lokacin suka fara yar hirarsu, musamman taheer da taheera , oumma na sa baki lokaci zuwa lokaci. “Oumma” cewar tahee, amsa mata oumma tayi da “uhm” ko muma kosannan zamu kwadayi ko za a siya,Jim kadan oumma tayi kamar ne tunani abinda zatace sai kuma ta kalli tahee” banki ta taki ba auta, amma kinsani ko mun fara ba barinmu zasuyi muyi ba, kinmanta abunda ya faru kwanaki”, turo baki tahee tayi jin oumma tace mata auta” wai TAHEER ne fa auta amma kullum ni kike cewa auta”, kallan up and done TAHEER yayi mata “shikenan zo mu kwada tsaho , duk Wanda ya fi tsaho a cikin mu shine babba”, dariya duk suka saki dan sun sa da biyu ya fada mata wato dan ya fita tsaho. Daga waje suna jin yadda yan gidan ke musu habaici da zagin su musamman Dije da yarta.
Chapter 5 · 0% Book details