Sashe 14
Gidan Aunty Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A daki Kuwa tahee wanka tayi bayan ta kammala cin abincin da ammi ta kawo mata, hijab dinta ta saka tare da kwashe kwanukan ta fito falo, Daidai lokacin da yan matan gidan ke shigowa, kallan tara saura kwata amrah ta bita dashi”ke kuma daga ina”,murmushin yake tahee ta saki”ina kwananku “wani hararan amrah ta bita dashi “bashi na tanbayeki ba”.ihsan ce ta katse mata zancen ta” easy amrah , ki bita a hankali mana”, kallanta ihsan tayi cikin sake fuska”yan mata ya sunan ki”, amsa mata tayi da “TAHEERA “tana sun kuyar dakai, lokaci d’aya zuciyar firdausi da amrah ya buga, “wow gaskiya kina da suna me dadi gaki kyakkyawa”,Shigowar ammi ne ya katse ihsan, “ah ah yan matana yana ganku a tsaye “, sumayyace tai saurin bata amsa “bakomai ammi mun shigone sai mukaga bakuwarki shine muke dan gaisawa”murmushi ammi tayi “kun kyauta kuwa , ku samu waje ku zazzauna , Kema tahee zo ki zauna”, kallan ammi tahee tayi “dama ina san wanke wadan nan kayan ne”girgiza mata kai ammi tayi “basai kin wahalar da kankiba”, wani dan button ta danna sai ga yan aiki guda biyu sun fito, kallan daya daga cikinsu ammi tayi “asabe ga kwanukwanan a hannun tahee su zaki kai kitchen”, toh hajiya cewar wadda aka kira da asabe,kwanukan hannun tahee asabe ta karba “nagode “murmushi asabe ta sakar mata ,”oya zo ki zauna “cewar ammi, waje ta samu daga kasa zata zauna ammi ta dakatar da ita, “ga waje zauna akan kujera”,batai musu ba ta hau daya daga cikin kujerun, “toh yan matana wannan sunan ta taheera ana ce mata tahee, Kema tahee wadaddan yayyunkine, wannan ta farkon ta nuna sumayya, sunanta sumayya,sai ihsan a kusa da ita , sai amrah da kuma firdausi”yawu firdausi ta hadiye”ammi ko itace wacce Kikace zaki kawo mana “, gyada mata kai ammi tayi, “tahee zata cigaba da zama tare damu, Inaso ku zauna kamar yadda nasan ku, hope zaku karbeta”, murmushin yake amrah ta saki “insha Allahu ammi”a haka suka dan taba hira kuwa da abunda yake sa’kawa a ransa, TAHEE ma duk a takure take ganin irin kallan da amrah take binta dashi,dama dama ihsan da ke janta da hira, sumayya da firdausi ko kallanta basa yi.
Zuciyarta tafarfasa take ba abunda take nanatawa sai “bazai yuba, it’s impossible “ tare da mikewa …..
Comment and share 💖
Alkalamin Mss Lee ✍️
💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖
LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA
👇👇👇👇👇
DUK KARFIN IZZATA (star lady )
GIDAN AUNTY ( mss Lee)
JINI DAYA ( mrs bbk)
YA FITA ZAKKA( maman sayyid )
SARKI SAMEER( xeenat love)
Alkalamin Mss LEE✍️✍️✍️✍️
Ina Godiya masu commenting , I heart you all💖💖.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(A heart touching love story)
Story & written
By
Mss Lee 💖
PAID BOOK
MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581
BOOK 1 📕
Free page 12 🦋
Zuciyarta tafarfasa take babu abunda take nana tawa sai “bazai yiwu ba , it’s impossible “ tare da mikewa , kallanta ammi tayi “ah ah amrah ina zaki”cikin dan rawar murya ta amsa mata “dama ina da lectures naga lokaci yana tafiya inaso na shirya”jinjina kai ammi tayi alamar gamsuwa “All the best daughter”, murmushin yake amrah ta sakar mata “thank you ammi”, tana gama fadar hakan ta bar part din, cikin sauri ta nufi part din auntyn ta, cikin sauri take tafiya ko kula da auntyn ta dake falon batai tai shigewa dakinta, ganin hakan yasa hajiya ameena bin bayanta , a tsaye ta tarar da ita sai faman safa da marwa take , “lapiyar ki kuwa amrah kika shigo duk a rude ko har kingansa “, jijjiga mata kai amrah tayi sai faman zagaye take , kallanta hajiya amena tayi ,” kiyi mun ba yani mana”,aunty akwai matsala “ cewar amrah “kinsan jiya ammi tayi tafiya , yanxu baki gani ba da wata yarinya ta dawo , itama wai anan zata zauna “ta be baki hajiya Amina tayi “to sai me dan ta kawo wata yar kauye”girgiza mata kai amrah tayi “ah ah aunty bazaki gane bane , kinsan sharadin da boka ya sa mana , baki ga yarinyar bane , kyakkyawace sosai , gata a cike ta ko ina kamar wata babba, koni da na ganta sai da naji sha’awata ta motsa, balantana king da yake namiji, dole yaji wani abu aka ta, banasan kwata kwata king ya ganta , Kema kinsan dalilin da yasa nake zuwa part din ammi sabida kawai acan zan iya ganinsa” bata bari hajiya Amina tayi magana ba ta dora “ aunty ya kamata kiyi wani abu,dan wallahi duk Wanda yayi kokarin rabani dashi sai nayi azalinsa, hakuri ya fara kare wa duk lokacin da na gansa sai sha’awata ta motsa”, jin maganganun amrah ba karamun jijjiga hajiya Amina yayi ba “dole na kaiwa boka ziyara dan bazan taba bari dukiya ahalin nahyan ta su bucemun ba, yanxu ki kwantar da hankalin ki karyi abunda zai sa a zargeki, dan Nima ko zanyi yawo tsirara sai dukiyar nan ta dawo waje na “tana gama fadar hakan ta har dakin, waya amrah ta dakko tare da kiran wata number, ringing 2 aka daga wayar , bata jira cewarsava ta soma magana “ Ina bukatar ka kashe mun kishirwar data tasomun, zan fada maka inda zamu hadu”, tana gama fadar haka ta kashe wayarta, sai faman lumshe ido take tana Cizan yatsa.
*****Apart din ammi duk yan matan sun koma part Dinsu, part din dada ammi ta nufa da tahee, sai faman bin ginin gidan take da kallo musamman wani dogon building din glass da ya burgeta , da wasu irin flowers me hade da pink colour , sosai flower din sukai mata kyau, falon dada suka shiga komai yana nan kamar yadda yake sai faman tashin kamshi yake kamar ba a amfani dashi,”Assalamu alaikum”cewar su ammi, itama dadan amsa wa tayi tana gyara farin glass din idanta, zama ammi tayi kan daya daga cikin kujerun falon, tahee kuwa samun waje tayi daga kasa kan carfet ta zauna, hakan da tayi ba karamun burge dada tayi ba amma bata ce komai ba. “Sannu da hutawa dada”, murmushi dada ta saki “Yauwa maman yara, a ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar”, murmushi ammi ta saki,”ina wuni “cewar tahee, amsawa dada tayi taba bin tahee da kallo, nutsuwar yarinyar ya birgeta,” dada wannan Itace yarinyar da nace miki inaso ta dawo waje na, na kawo miki itane ta gaisheki”,murmushin jin dadi dada ta saki “kin kyauta kuwa, yan mata ya sunanki” dada ta fada na mayar da hankali kan tahee, sun kuyar da Kai tahee tayi sunana Taheera , zaro ido dada tayi sai kuma ta tabe baki, yaran zamani kowa dai da irin nasa sunan , shi wancan bod’ararran ansa masa tahanuni (tahnoon), ke kuma ga naki salan sunan wai tahura (taheera), sun kuyar da Kai ammi tayi jin yadda ta kira sunan su, gashi ba halin dariya , dada kuwa bilhakki da gaske take ko dariya a fuskarta, kara kallan tahee tayi,”nikin ganni nan , wallahi iyayena sunan kwarai suka samun, ina dalili ai ku sunayan ku sai ku wallahi”,itama tahee dariya dada ta bata amma sai tai saurin gimshe kayarta amma murmushin yaki buya a fuskarta.”sannan ki saki jikinki nan ma gidan kune , ko me sikeso ki tanbaya za a miki kinji tahura “,sosai murmushin da take boyewa ya fito har dan gaf din hakorin ta fitowa “nagode sosai hajiya”dada bata bari ta karasa ba ta dakatar da ita”yau naji wani batu, dada zaki dunga cemun kamar sauran”,jinjina mata kai tahee tayi “nagode dada”sosai tayi wa dada adduar da har yar kwalla saida ta share “Allah yayi miki albarka “kasa kasa tahee ta amsa “ameen”ita de ammi sai binsu take da kallo tana sakin murmushi, kallanta dada tahee maman yara , gasky wannan ‘ya a kwai hankali, nasan a gajiye kuke , idan ta huta sai a gabatar mata da kowa na cikin a halin ta san yan uwanta, cikin girmamawa ammi ta amsa mata”mun gode sosai dada, Allah ya huta gajiya”, ameen aka wai dada tace mata kafin su kama hanyar fita da ga part din, bin bayansu da kallo dada tayi kafun ta saki wani murmushi akan fuskarta .