← Book details Duk Kyan Takalmi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 15

BABI NA GOMA SHA DAYA Aisha farida tayi

Duk Kyan Takalmi Part 1 Complete Hausa Novel · about 21 min read

kuka, har ta godewa Allah a wannan rana ta
asabar saboda jikin abida ya matsa, babban
yayanta yaya lurwanu yazo da mota har
kofar gida, yace a bashi ita ya tafi da ita
shagamu ayi maganin hausa. Yaya hussaini
ya zama bashi da zabi kasancewar shima
yana ganin ciown bai yi masa kama da na
asibiti ba, don sunyi ta yin na asibitin babu
alamar jin sauuki, kullum ciow kamar kara
shi ake yi. Aisha farida ta dage wajen yi
musu bayani, sunki su fahimce ta, suna
ganin don ita 'yar boko ce kuma malamar
asibiti shiyasa take son a dauwama da na
asibiti don likitoci ba sa kaunar a hada
maganinsu dana gida. Sunfi karfinta, tana ji
tana gani yaya hussaini da yaya lurwanu
suka ciccibi abida tamkar 'yar jaririya da
kayanta aka saka ta a mota. Yaya lurwanu
ke tukawa, yaya hussaini yana zaune a
gefensa, yayin da ita kuma aka kwantar da
ita a bayan mota. Aisha farida ta mika
hannu ta tagar motar ta rike kumburarrun
yatsun abida a hankali yayin da hawaye ya
surnano daga idanuwansu su duka. Aisha
farida tace Allah Ya baki lafiya. Abida ta
girgiza kai tace ba zan dawo ba farida, ki
kula da 'ya'ya na, kada ki manta abu uku
dana fada miki. Ki zama mai yawan addua,
mai tsananin hakuri mai yawan kama
mutuncinki. Biyun kuwa ba yanzu zan fada
miki ba sai nan gaba idan ban mutu ba.
Yaya hussaini ya juyo da sauri yana kallonsu
ba tare da ya fahimci abin da suke ba, shi
da lurwan suka cika da mamakin jin
kalaman da marar lafiya ta ke furtawa.
Hussaini ya tambayi aisha farida meye
hakan kuma yake nufi? Zance me kuke yi?
Aisha farida ta goge hawaye tace a'a sako
take bani. Yace sakon me kuma naji ana
maganar soyayya? Ki koma gida ki kula da
yara, gasu can suna ta kuka, nima gobe
zandawo na bar miki dari biyar a daki akan
katifa. Idan anyi wa yara hutun makaranta
sai mu dunguma mu tafi shagamu, ni ina jin
ma gara ku kaura can kacokan, ni zan dinga
zuwa ina dawowa, gara mu hakura da
zaman kanon ma. Kirjin aisha farida ya buga
bamm! Don fargabar tana tunanin yaDda
zata rabu da rabin ranta dr shuraim. Ta
zame hannunta a hankali daga hannun
abida, sai abida ta dago ido ta dube ta, tayi
mata murmushi. Tace Allah Ya baki nasara
akan abin da kike nema. Kuka yaci karfin
aisha farida, ta rushe da kuka. Tace Allah ya
tashi kafadunki anti abida.
Nan da nan yaya lurwanu yaja mota ya tafi,
saboda suma sun fara jin hawaye yana zubo
musu don tausayi. Idanuwan yaya hussaini
ya cika fal da kwallah. Aisha farida ta kame
a inda take tsaye tana kallon motar har sai
da suka kure sannan ta juyo gida. A hanya
jama'ar unguwa sai sannu suke yi mata, da
kuma fatan Allah Ya ba wa abida lafiya.
Kowa ya tausaya wa aisha farida ganin
kukan da take sharba, idanuwanta sunyi
jajawur. Ita kanta tana so kukan ya tsaya,
amma yaki saboda tsananin kunar da take ji
a ranta. Ta kama hannun 'ya'yan abida su
hudun dukka maza, faruk, sa'ad, muhd, da
ishak idan taja hannun wannan sai wannan
ya arce da kuka. Da kyar matan gida suka
taya ta da kamo su ana lallashi da alewa da
biskit. Da kyar suka zazzauna a daki suka
daina kukan. Aisha farida ma tazo ta zauna
a gabansu tana kallonsu, ba tare da ta iya
musu magana ba. Abin duniya ya ishe ta, ta
rasa abin da yake yi mata dadi. Ji take
tamkar zuciyarta zata fashe. Tana ambaton
Allah kar ka kashe abida, ina son abida a
rayuwata. Wayarta ce tayi kara, ta mika
hannu a sanyaye ta dauka, ta duba wata
lamba ce bakuwa babu suna, sai dai lambar
ta musamman ce, saboda kusan lambobin
duk iri daya ne. Tayi ta kallon lambar amma
batayi mamakin wanda ke kira ba, domin
'yan ajinsu da dama suna karbar lambarta
su kira ta maza da mata. Saboda bata cikin
hayyacinta , don haka bata son yin magana
har wayar ta katse ba ta amsa ba. Can ta
mike ta fito tsakar gida ta jawo risho ta dora
ruwan zafi a karamar tukunya, ba tare da ta
san abin da zata dafa ba.
Ta dubi babban dan abida faruk tayi
murmushin karfin hali tace yaya me zamu
dafa yau? Maganar ma shi ma dakyar yake
yi, sai ya langwabar da kai yace wake da
shinkafa. Ta dubi sa'ad mai binsa tace kai
fa dan lelena mai zan dafa muku? Shima
yace wake da shinkafa. Sai ishak yace
shinkafa da miya. Mohd yace a'a tuwon
shinkafa da miyar taushe. Aisha farida tayi
dariya tace a'a su yaya sun fiku gaskiya, ku
rage min aiki tunda muna da yaji mai dadi
da daddare sai inyi mana tuwo. Tana zaune
a dokin kofa tana tsice wake sai wayarta ta
dau ruri. Nan da nan yara suka hau tseren
dauko waya, ana dambe dai kamar za a yar
da wayarta samu ta karba. Taba dubawa
taga lambar dazu ce, sai ta tabbatar ko
waye wannan mai kiran wayar tana da
muhimmanci tunda ya sake kira, don haka
nan da nan ta danna. Cikin nutsuwa tayi
sallama, taci gaba da sauraron mai wayar,
mace ko namiji? Muryar namiji taji ya amsa
da wa alaikumul salam. Tayi kasake tana
sauraon abinda zai fada mata, har yanzu
bata gane muryar ba. Amma daga dukkan
alamu ta taba jin kamilalliyar muryar. Ya
tambaya don Allah ina magana da aisha
umar ne? Ta amsa da eh aisha ce. Yayi
gyaran murya kadan yayi murmushi yace
farida kina magana da dr shuraim imarn ne,
daga nan asibitin aminu kano. Tsarki ya
tabbata ga Ubangijin talikai. Kalmar da
aisha farida ta fada kenan a cikin zuciyarta,
yayin da ta sulale ta durkusa gwiwoyi guda
biyu a kasa don mamaki da kidimewa. Ta
rasa kalma daya da zata furta, sai gumi take
jikinta yana bari, ta rasa inda take. Shin
mafarki ne, ko kuma idonta biyu?
Ya ambaci sunata har sau biyu. Farida!
Farida!! Tayi doguwar ajiyar zuciya, ta
lumshe ido ta amsa cike da ladabi, cikin
sassanyar murya na'am. Yace kina mamaki
ne? Kada kiyi mamaki. Na sami lambarki ne
daga wajen dr lukman jiya aiki ya hana in
kira ki, sai yau da yake weekend ne, ina
gida. Ta mike ta shige dakin abida ta turo
kofa ta datse saboda hayaniyar yara, ta
sami lungu ta shige ta takure kai kace sanyi
take ji. Ta gaishe shi cikin nutsuwa. Ya
amsa cike da fara'a ya tambayeta ya mai
jiki? Cikin sanyi jika tace da sauki. Yace yaya
maganin da take sha, tana samun sauki?
Tayi jim kadan tace tana sha dai, amma
ciwon kamar gaba yake tayi. Yace
subhanallah, to yanzu abinda za a yi, ranar
litinin ki kawo ta wajen zan hada ta da
likitan da ya kamata ta gani, wato
rheumatologists. Ba damuwa idan nayi
masa magana zai duba ta ko babu
appointment. Hawaye ya surnano daga
idanuwan farida, ta marairaice murya tace
ai bata nan, anzo daga gida an dauke ta,
wai na hausa zaayi. Babu yadda banyi ba su
kyale ta muci gaba dana asibiti suka ki.......
Bata rufe bakinta ba sai ta rushe da kuka
cikin wata irin sautin murya mai ban
tausayi. Dr shuraim ya zabura yace
subhanallahi, wannan suna so su jawo mata
ciwon koda, daman ciwon yana da alaka da
ciwon koda. Kada su sake su bata sassake
sassake ta sha, don akwai mummunan
hatsari wajen shan jike jike. Kuka kawai
farida ta keyi, ba tare da ta iya magana ba.
Yayi ajiyar zuciya ya ambaci sunata cikin
wata lallausar murya. Yace farida kuka kike
yi? Daman ke haka kike sarkin kuka ce? Na
hadu dake fiye da sau hudu kullum kina
kuka, meya damuwarki? Ta girgiza kai ta
goge hawaye tace babu abinda ban fada
musu ba, babu irin maganar da banyi ba
akan su kyale ta, suka ki. Mijinta ma tun ba
ya yadda yanzu har ya yadda. Yanzu ko nay
waya shagamu nayi bayani kada su bata
maganin hausa ba zasu saurare ni ba. Shine
nake jin tsoro kada su jawo mata ciwon
koda.... Ta sake barke wa da wani kukan
DUK KYAN TAKALMI 2* 12
Ya sake jan doguwar ajiyar zuciya yace kada
ki damu, mu dukka muslmaii ne, mun yadda
da Allah Shi ne mai warkarwa, ba magani
ba. Muyi addua Allah Ya bata lafiya, Allah Ya
tsare duk wani tsautsayi. Ya ya kike da ita
marar lafiyar ne, mamarki ce? Aisha farida
ta marairaice murya tace anti abida yayata
ce, kakanninmu daya, kuma tana auren
yayana da muke uba daya, itace marikiyata
tun ina karama, itace tamkar uwata, ubana,
yayata, kuma aminiyata mai bani shawara
akan duk lamurana. Sai yayi murmushi ya
lumshe ido yace amma kin iya kwatance
yadda mutum zai gamsu. Ko kon taba bata
labarin wani dr lukman da abokinsa dr
shuraim da suke cinye miki dambu da
danwake? Aisha farida ta kwashe da dariya
tace a'a baka bani izinin na sanar mata ba.
Yayi dariya yace nasan kin fada mata. Ta
sake tuntsirewa da dariya tace sai dai yanzu
na fada mata. Yayi dariya yace to Allah Ya
sauwake Ya bata lafiya sai anjima. Aisha
farida tace nagde Allah ya saka maka da
alkhairin, sai anjima. Ya kashe wayar yana
lumshe ido saboda jin dadin muryarta. Har
yanzu aisha farida sankare take a lungu ta
kasa sauke wayar daga jikin kunnenta. Ji
take tamkar mafarki take yi, yayinda
farinciki marar misaltuwa suka cika
zuciyarta, ta cika da mamaki marar adadi,
sai ta tuna da bayanan ABida da tace babu
abin da ya gagari Ubangiji. Idan bawa ya
roke Shi, yana amsa ma sa duk sanda Ya so.
Ta ajiye hannunta a hankali daga jikin
kunnenta ta dafe kirji taji sassanyayiyar
bugun da zuciyarta take yi. Ta daga hannu
sama tayi wa Allah godiya sai ta malale ta
kwanta akan katofa tamkar ruwa.
Ta jawo wayar da sauri ta duba lambar, ta
kayatu ita kanta lambar abar kallo ce, sai ta
sumbaci wayar. Ta dannan lambar ta kira,
bugu daya ta shiga ta fara ruri, sai taga an
kashe. Hankalinta yayi mummunan tashi,
nan danan ta zabura ta tashi zaune ta dafe
kirji, yayin da farin ciki datake yi ya koma
ciki. Ta fada a bayyane innalillahi wainna
ilaihir rajiun! Me ya kaini sake kiransa, gashi
ya katse? Shikenan zai tsane ni. Ta na
zaune ta hada kai da gwiwa tana tunani sai
taji wayarta tayi ruri. Nan da nan ta zabura
ta dauka ta duba, sai taga lambar dr shiraim
ce, tay sauri ta dannan gami da yin sallama
cikin nutsuwa. Ya amsa mata gami da cewa
naga kin kira ko? Ta lumshe ido tace eh
daman zan tambaye ka ne, ranar litinnin
dambun zan kowa muku ko danwake? Ya
girgiza kai tamkar yana gabanta yayi
murmushi yace a'a babu, ba sai kin kawo
mana komai ba, mungode. Ta marairaice
tace haba doctor meyasa, ni ina so na kawo
muku. Yace a'a ki bari sai wani lokaci, idan
muna bukata zamu fada muki. Yanzu na
kira ne naji halin da marar lafiya ke ciki,
don na damu nasan ciwon nan yana da
tsananin zafi, sannan na damu da yadda
naga kinta ta koke koke na kora najji halin
da kuke ciki. Tayi murmushi tace nagoda ka
kyauta, nayi farin ciki da jin kiranka. Ko zan
iya saving din lambarka don mu dinga
gaiswa. Yace ba damuwa, zaki iya. Tayi
godiya, shima yayi mata godiya, suka kashe
waayar. Tayi tsalle akan katifa ta dire don
murna. Ta dubi gabas da yamma, kasa da
sama tana tunanin wanda zata ba wa
wannan kyakyawan labari. Ta tuno abida,
taji yau dama abida na nan ta fada mata
yadda sukayi da dr shuraim. Taji hawaye ya
cika mata ido, ta fada a bayyane. Allah sarki
anti abida, Allah ya baki lafiya. Tana rufe
bakinta faruk ya shigo dakin da gudu ya ce
anty aisha ruwan da kika dora a wuta yana
ta tafasa tun dazu, har ya kusa ya kone. Ta
zabura da gudu ta fito don ita har ta manta
da shi, tabbas yaro yayi gaskiya , ruwa dai
ya gaji da tafasa har ya kusa konewa. Sai da
ta kara wani yayi zafi sannan ta zuba wake
da shinkafa suka dahu. Ta ba wa yara suka
ci, yayin da farin ciki ya kosar da ita, ta kasa
ci, yunwar ma bata ji. Bayan tayi sallahr
azahar sai ta dinga jero nafilfili ba adadi,
duk ta godiya ce ga Allah da ya kawo mata
dr shuraim.
A cikin satin nan haka take yini cike da farin
ciki, saboda ta sami dr shuraim, sai dai
matsala daya ce take addabarta a rayuwa,
idan ta tuno rashin lafiyar abida sai taji
jikinta yayi sanyi lakwas. Koda yaushe sai ta
saka lambar dr shuraim a gaba tayi ta kallo,
sai taji kamar ta kira shi ko ta tura masa
sako, sai kuma ta fasa. Amma ranar juma'a
ta tura masa sakon adduoin juma'a amma
bai bata amsa ba. Ta fara shiga damuwa,
amma sai tayi masa uzuri , watakila bai cika
karanta sakonni ba kasancewar aiki yayi
masa yawa. Ranar litinin da misalin karfe
goma da rabi na safe aisha farida na
kwance akan tabarmarta tayi shiru tana
tunani, rashin lafiyra abida tana damunta
matuka, musamman yanzu da tayi waya
shagamu tayi tayi su ba wa abida waya suyi
magana, aka ce bacci take yi. Sai take ganin
kamar jikin ne yayi tsanani suke boye mata.
Tana so ta tashi ta dora abincin rana, domin
yara sun kusa dawowa daga makaranta,
amma ta kasa tashi saboda damuwar da
tayi mata yawa a zuciya. Wayarta tayi ruru
tayi sauri ta dauka ta duba, sunan yaya
hussaini ta gani, sai tayi matukar mmaamki
da ganin kiransa, don bai dade da fita aiki
ba ya bata kudin cefane. To me yasa ya
kira? Ko mantuwa yayi ne a gidan? Take
tambayar kanta da kanta. Tayi sauri ta
dannan gami dayi masa sallama cike da
tsananin fargaba, tayi shiru tana sauraron
abin da zai fada mata. Yayi gyaran murya
yace yaya kuke? Gidan duk lafiya? Yara basu
dawo daga makaranta ba ko? Sai tace eh
basu dawo ba. Ina gida kowa lafiya kalau.
Yace to madallah, daman na kira ne naji
halin da kuke ciki. Kada ki damu, ki cigaba
da hakuri, kici gaba da kula da yara. Muyi
wa abida addua, naga kin damu duk kin
rame, kina yawan koke koke. Nima na
damu har bana iya aiki yadda ya kamata,
har 'yan ofis dinmu sun gane ina cikin
damuwa. Yanzu na yanke shawara a raina
idan yara suka yi hutu sai nima na dauki
hutu mu tattara mu kaura shagamu. Idan
hutuna ya kare sai na dawo, idan kuma na
samu aikin yi a shagamu ko wata sana'a sai
muyi zamanmu ba sai mun dawo kano ba.
Rashin abida a kano ya zama tamkar tuwo
gaya babu miya. Ni, ke da yara duk bamu
jin dadin rayuwarmu. Ko abinci kika dafa
babu wanda yake iya ci yadda kika kawo
min haka kike zuwa ki dauke, haka na lura
yara ma ba sa iya ci, kema haka. Tulin
abinci ake juyewa almajirai kullum. Aisha
farida ta rushe da kuka, yayin da shima
kukan ya turnuke shi, sai yayi sauri ya katse
waya. Ta kifa kai akan filo tayi ta rusa kuka
tamkar idonta zai fashe. Tana ta addua
Allah Ya yayewa abida wannan ciwon.
Wayarta ce ta sake yin kara. Nan da nan ta
katse kukan ta dauka ta duba sunan barr
muazzam ne. Ta goge hawaye da sauri ta
tashi zaune, sannan ta matsa waya da yin
sallama. Barr muazzam yayi murmushi yace
kanwata kwana biyu, kina nan kuwa? Tayi
murmushi tace ina nan yayana, na sha
kiranka baka amsawa, ko aiki ne yayi maka
yawa? Yace kwarai kuwa, satittikan nan uku
duk bana zama, daga bakwai na safe zuwa
na dare. Alhmdlh abin da ake nema ya
samu. Daman case din dr janan ne an tafka
sharia na shawo kanta, ta bude baki tayi
bayani, ta tonawa su izzuddin asiri, ta kuma
fadi inda za a iya samunsa shi da abokansa.
Aka yiwa 'yan sandan can garin waya don su
kamo shi. Sun kawo mana shi kano, har ya
bayyana a kotu, kuma ya amsa laifinsa.
Yanzu haka kotu ta wanke janan, an
tabbatar ba ta da laifi, an sake ta tana
gidansu shi kuma yana daure. Farin ciki ya
lullube aisha farida, tayi dariya tace
alhmdlh, Allah Mai iko, amma yaya
muazzam na taya ka murna, Allah ya kiyaye
gaba. Yanzu a wanne hali kuke ciki kai da
ita? Yayi murmushi ya lumshe ido yace
komai ya daidaita amma dai ba dukka ba,
kinsan komai sai a hankali. Kanwata na riki
abubuwan nan guda uku, nayi addua, nayi
hakuri matukar hakuri kuma naci riba. Naja
mata aji, na nuna mata yanzu babu zancen
soyayya a tsakanin mu, ina da wacce zan
aura. Na nuna mata bani da wata alaka da
ita face ta aiki. Ta bani hadin kai kawai in
gudanar da aikina yadda ya kamata. Data
tabbatar da haka, sai ta saduda ta ajiye
wannan zaren da take ja na aji ta bude baki
ta amsa duk abubuwan da na tambaye ta,
sannan ta gudanar da duk abin da na
umurce ta tayi a kotu.
Na lura ashe daman tana sona, boyewa
kawai takeyi, ko kuma nace yanzu ta fara
sona da taga halaka. Ni daman bani da
matsala da iyayenta, tun da can suna sona
balle da suka ga irin taimakon da nayi
musu. Ji suke tamkar su dauko ta su kawo
min ita gidana. Ba soyayyar iyayenta nake
nema ba, ina so janan ta soni da kanta ba
sai wani ya tilasta mata ba, ko don wani
dalili ba. Ta soni don Allah, muyi zaman so
da yadda a tsakanin mu, ko babu ran
mahaifanta. Aisha farida tace gaskiya ne
wannan. Allah Ubangiji Ya tabbatar da
alkhairi. Yace amin malamata, menene
mataki na hudu da zan taka, kin san fa duk
abin da kika ce dashi nake amfani, don kin
fini wayo ke kuma anti abida ta fiki wayo.
Ku dora min karatun. Aisha farida ta
kyalkyale da dariya, tace uhmm yayana
kenan, har ka bani dariya wallahi. To mataki
na hudu da abida ta fada min shine tunda
yanzu ta san da kai, ta kuma san abinda ake
ciki, sai ka zama mai yawan kyautata mata,
da haka zata so ka fiye da kowa. Barr
muazzam yayi murmushi yace idan haka ne
to ai na riga na haye mataki na hudu don ni
mai yawan kyautata mata ne, har ita da
kanta ta rubuto min sakon godiya a waya,
ta yaba da hakan. Dazun nan ta rubuto min
wannan sakon. Mene mataki na biyar
kuma, ko baka taka shi ba? Aisha farida
tace eh to inaga nima a mataki na hudun
nake amma abida ta fada min mataki na
biyar din tace ka nuna kama sonta tamkar
kafi kowa sonta a duniya. Kamar kulawa da
duk halin da take ciki, da kuma tattalinta,
tamkar kwai, ka nuna ko kuda ba kaso ya
taba ta. Idan ka yi mata haka ita ma zata so
ka, zatayi kokarin ta mallake ka a
rayuwarta, kaga sai ka aure ta.
Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace kice
min gangaro na kusa samun janan kenan?
Zanje na dorawa baraka wannan karatun.
Aisha farida tace af! Na manta ban
tambaye ka baraka ba, ina take? Wanne hali
take ciki? Yayi dariya yace mutuminki
nurudden dai ya saduda daya ga ta share
shi, sai yake shishige mata, ita kuma tana
watsar dashi. Yanzu haka ya fara neman
shawarata wai yana ga zai rabu da nafisa.
Yace min baraka tace ta amince ta auro
nafisa ya hada su, su biyu. Ita kuma nafisa
tace sai ya saki baraka kafin ta aure shi.
Shine yake cemin da ya saki baraka gara ya
fasa auren, domin baraka ce mace ta gari
da take yi masa biyayya. Aisha farida tace
yawwa ka cewa baraka ta taka mataki na
hudu shine taci gaba da kyautata masa fiye
da na da. Sannan mataki na biyar ta nuna
masa tsantsar soyayya kamar tafi kowa
sonsa a duniya fiye da yadda nafisa ke
sonsa. Brr muazzam yace lallai ke malama
ce, ke kuma yaya naki gogan, me kuke ciki?
Tayi murmushi ta lumshe ido tace alhmdl.
Dr shuraim yasan dani yanzu, ya san
sunana, har ya damu da halin da nake ciki.
Ta kai ta kawo dr shuraim ya nemo lambar
wayata ya kira ni a waya ya gaishe ni ya
tambayi jikin antina abida. Ina ga yanzu zan
taka mataki na hudu, zan cigaba da
kyautata masa sosai har sai ya kaunace ni
yaji sona tamkar ransa zai fita, sai ya saki
jiki dani, don bana tantama ya fara sona.
Sai in taka mataki na biyar shine ina nuna
masa tsantsar kauna nima. Barr muazzam
yace amma abu yayi kyau, Allah ya tabbatar
da alkhairi, Ya zaba mana abin da yafi
alkhairi a rayuwarmu. Har yanzu jikin anti
abidar ne bataji sauki ba? Aisha farida ta
marairaice tace ba za'a ce babu sauki ba,
amma har yanzu ana nan ana fama. Babbar
matsalar ma da 'yan uwanta suka zo suka
dauke ta shine dr shuraim din yake fada
min kada su jifga mata sassake sassake ya
jawo mata ciown koda, domin ciwon yana
da alaka da ciwon koda. Barr ya girgiza kay
tace subhanallah! Allah Ya kiyaye, Allah Ya
bata lafiya. Kiyi kokari ki kira su a waya ki
fada musu abinda likita ya fada, kada su
bata sassake. Yanzu zan turo miki katin
waya don kiyi magana dasu yadda ya
kamata. Aisha faida ta matse hawaye tace
nagode da wannan hidima da kake yi min
ko wani dan uwan nawa na jini ba yayi min
abin da kake yi min.....sai ta rushe da
kuka. Ya girgiza kai yace dadina dake saurin
kuka kamar wata tsohuwa. Ki daina kuka
kinji ko? Duk abin da ya samu bawa
Ubangiji Yana sane, kuma Zai yaye masa.
Sai kinga sakona sai anjima. Aisha farida
tace sai anjima, Allah Ya saka da alkhairi.
Ya kashe waya ba dadewa taji kara a
wayarta, da alama sako ne ya shigo. Tayi
sauri ta duba sai taga brr ne ya turo mata
da kati. Data loda sai taga na 1500 ne. Ta
kira shi har ta katse bai dauka ba, sai ya
kirata daga baya. Tace dama godiya zanyi
maka, naga kati na gode. Yace ba damuwa
ba sai kin yi min godiya ba, don nabaki
wannan dan kati. Ya kashe wayar ta koma
ta kwanta ta dubo lambar dr shuraim tayi ta
kallo tana shawara a ranta ta kira shi ko
kada ta kira shi? Sai ta yanke shwarar ta
kyale don ta lura baya son damu, idan ya
kira da kansa zaifi kamar yadda rannan yaga
dama ya kira da kansa. Sai ta jiye wayar a
gefe zuwa jimawa sai ta sake jawo wayar ta
fara rubuta masa sakon gaisuwa da fatan
alkhairi. Har zata tura sai ta fasa ta goge da
ta tuna ta tura masa na juma'a bai bata
amsa ba, kuma bai kira ba. Ta duba agogo
karfe goma sha daya da rabi 'yan
makaranta karfe goma sha biyu zasu fara
dawowa daga makaranta, gashi bata dora
abinci ba, don haka sai ta mike tsaye zata
je ta dora abincin sai taji wayarta ta dauki
ruri. Ta dawo ta zauna da sauri ta jawo
wayar ta duba, sunan dr lukman ne ya
bayyana, sai farin ciki ya rufe ta, tayi
murmushi tayi sauri ta danna, cike da fara'a
tayi masa sallama gamu da cewa yayana ina
ka shige ne kwana biyu naji ka shiru? Yayi
dariya yace kaji marar kunya. Ni zan neme
ki ko ke zaki kira ki gaishe ni ki samu lada?
Ko baki kirani ba naga flashing ko pls call
me ai zan kira ki. Amma baki neme ni ba.
Ko da yake jan aji ne irin na 'yan mata ko?
Yanzu muke maganarki da abokina dr
shuraim. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe
ido ta tambaya cike da zumudi, me yace?
Dr lukman yace yanzun nan ya fice da yaga
zan kiraki. Daman nace sai na fada miki ko
baya so. Wai ya akayi kike burge abokina
ne, ni tunda nake dashi a asibitin nan
shekara da shekaru ban taba ganin macen
da ya taba maganarta ba balle ya yabe ta,
sai ke? Yace kina burge shi saboda kina da
hankali. Ga ki da kunya, kara, kawaici, ga
hakuri da shiga ta mutunci, uwa uba kin da
aji ba ki cika shishigi da rawar kai irin na
'yan matan yanzu ba. Sannan haka kawai
yake tausayinki musamman da ake ce ke
marainiya ce. Sannan yace kina da matukar
kirki da yaji ashe kace kike daho mana
dambu da danwake. Kinsan da hannunsa ya
dauki lambarki a wayata, yace zai kiraki ya ji
jikin yayarki. Aisha farida tayi ajiyar zuciya
tayi dariya. Tace Allah sarki, haka Allah Ya
ke shirya al'amuran Sa duk yadda yake so.
Dr lukman yace munafukai ne ke dashi,
kunsan abin da yake tsakaninku. Ai idan
tayi tsami zamuji. Shima sai kwana kwana
yake yi min, idan na tambaye shi. Amma
gaskiya na sha mamaki da naga yana yawan
USA Novels BOOK
DUK KYAN TAKALMI 2* 13
Damuwa dake, don ni nasan shi nasan
ra'yainsa, nga yadda yake kushe mata. Ban
taba jin ya yabi wata budurwa a duniya ba
ma balle a cikin asibitin nan, shine na kiraki
naji meye sirrrin? Aisha farida ta kyalkyale
da dariya tace ba wani sirrri wallahi, Allah
ne Ya hada jininmu, nima yana burge ni
sosai. Dr lukman ya gyada kai yace gaskiya
kanwata idan har wannan abu zai tabbata
tsakaninki da shuraim zanfi kowa taya ki
murna, don kinyi dace da mutum na gari,
mai tsananin kirki da tausayi, mai kulawa.
Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido tace
Allah yayana haka ne? Yace inayi miki fatan
alkhairi, sannan ina taya yayarki da addua ta
samin sauki. Zanje wajen marasa lafiya, sun
taru suna jirana. Ya katse hiran. Aisha
farida ta sulale ta kwanta, tayi shiru tana
sake maimaita kalaman dr lukmann,
mamaki ya rufe ta, tamkar a mafarki ba a
ido biyu abubuwan suke faruwa ba. Anya
kuwa itace, ko dai mafarki ne? Take
tambayar kanta da kanta. Ta sake
gasgatawa babu abin da yafi addua da
hakuri a duniya. Ta dinga yi wa Allah godiya
da Ya nuna mata wannan rana. T dinga
kwararo addua tana rokon Allah ya karawa
dr shuraim sonta, kuma Ya sa ya aure ta. Ta
tuno abida taji daman abida tana nan taji
irin wannan dadadan labari. Sai tayi wa
abida addua Allah Ya bata lafiya. Tana
zaune ta kasa tashi ta dora abinci bata
ankara ba, sai taji muryar 'yan makarnata
sun fara dawowa. Ta ji wani kara
kwarakwacam anyi wurgi da jaka da robar
abinci a bakin kofar dakinta, ta san gajiya ce
da yunwa take addabarsu. Tayi wuf! Ta fito.
Ta shiga llallabasu tana yi musu dubaru
tana koda musu dadin garin kwaki da mai
da yaji, ta aika su suka siyo ta kwada musu
suka ci suna murna. Tace musu haka 'yan
makarantar kwana suke yi, gara ku fara
koyon ci kafin ku tafi sakandire ta kwana.
AISHA SHURAIM HIMMA BA TA GA
RAGO!!!
Chapter 4 · 0% Book details