BABI NA BIYAR Washegari misalin karfe
Duk Kyan Takalmi Part 1 Complete Hausa Novel · about 99 min read
bakwai saura kwata na safe aisha farida ta
shirya tsaf tana sauraron 'yan gidan su
tashi. Ta hada kudaden nan ta kidaya naira
dubu goma sha biyu ne cif cif tasan dai
uwani zata daga mata kafa tunda sauran
naira dubu biyar ne kacal har zuwa wani
lokaci. Abida ce ta fito kofar daki tayi
hamma tayi mika yayin data murtsike luhu
luhun idanuwanta wadanda suka kumbura a
sanadiyyar kukan da ta sha yi a cikin dare,
ga rashin bacci. Ta tura kofar dakin aisha
farida don ta duba yaranta, tayi matukar
firgita a lokacin da ta ga fararen kayan jikin
aisha farida a tsaye a tsakiyar daki har sai
data daka tsalle tayi kara. Nan da nan aisha
farida tayi magana tace anty abida lafiya
kika firgita? Nice fa. Abida ta dafe kirji tayi
ajiyar zuciya tace aisha yaushe kika dawo?
Tayi murmushi tace ai anan na kwana.
Abida ta tambaya cike da mamaki yaya
akayi kika fito daga wajen 'yan sanda? Aisha
farida ta sake yin murmushi tayi ajiyar
zuciya sannan ta fito da himilin kudin nan
daga aljihun wandonta. Tace kinga na hado
naira dubu goma sha biyu saura naira dubu
biyar. Ai zasuyi min hakuri har in samu ko?
Abida tayi shiru kamar mai tunani yayin da
hankalinta yayi mummunan tashi ta dubi
aisha farida cike da fargaba. Ina kika sami
wadannan makudan kudin a dare daya?
Anya kuwa aisha kin kwana a gidan nan?
Kada ki boye min komai, ni mai baki
shawara ce a gaba daya matsalolinki.
Matsalarki matsalata ce, damuwarki
damuwata ce, haka duk abinda kika yi aka
zage ki a gari bake kadai aka zaga ba, ni sai
na fiki jin zafin zagin. Yadda hankalin abida
ya tashi na aisha fariida sai ya fi nata tashi,
nan da nan ta dago ta kafawa abida ido
tana kallonta yayin da kalma daya rak ta
gagare ta furtawa don tashin hankali. Kan
kace kwabo hawaye ya fara zazzagowa daga
idanuwan ta. Abida ta lura da tashin
hankalin da farida ta shiga sai itama ta fara
hawaye ta fara magana cikin sanyayyiyar
murya. Aisha farida ba wai ina zarginki
bane sai dai ina gudar miki fadawa
mummunan rayuwa a sandiyar dan karamin
bashin nan. Kije ki cuci rayuwarki a banza.
Dole in tuhume ki don nima nasan dole
yayanki zai tuhume ni haka kuma ya
kamata a shariance. Aisha farida ta matse
hawaye ta langabar da kai tace tabbas na
kwana da shirin zaki tambayeni haka amma
ban taba zaton zance a gida na kwana ba ki
karyata ni ba shine abinda ya bata min rai
amma inda zan yiwa Allah godiya shine na
hadu da yaya dazu da tsakar dare ina fitowa
daga bandaki shi kuma zai shiga har ya
ambaci sunana na amsa da alama shima
yayi mamakin gani na. Abida ta gyara
tsayuwar ta da alama taji dan sanyi a ranta
ta dubi aisha farida ta tambaya cike da
zumudi. Yaya akayi kika fito daga ofishin
'yan sanda? Kuma a ina kika samo
wadannan makudin kudi?
Aisha farida tayi murmushi ta jawo hannun
abida suka zauna akan tabarmarta tayi
ajiyar zucia sannan ta gyara zama ta
zayyanowa abida labarin duka abinda ya
faru da ita jiya tun daga sanda ta fita qofar
gida wajen 'yan sanda da yadda sukayi acan
ofishinsu da zamanta dakin da aka kulleta
zuwa lokacin da akayi belinta da kuma
zuwanta fish park harta hadu dasu barrister
mu'azzam da hirar da sukayi
Har zuwa yadda ya bata kudi da kuma
sanda ya kawota gida abida ta gamsu da
labarin Aisha humaira kuma taji dadi har
saida ta daga hannun sama tayi wa Allah
godia ya taimakesu ya basu yadda zasuyi su
biya bashin da basu dashi.kibani kudin nan
sannan ki tashi ki tafi makaranta salin. Alin
basai yan gidan sun tashi sun ganki ba
kuma babu ke babu bawa wasu labarin
abinda ya faru ko labarin inda kika samo
kudi gudun kada yayanki wata rana yaji
yazo ya titsiyeni da tambaya sannan
kibarshi akan kin yi mata tiyata kada ma ki
sake kiyi zancen malam kika kaiwa kudi
koda wasa kibarni dasu ni nasan
Ni nasan yadda zanyi inyi musu bayani kada
kice komai jikin A.farida na karkarwa da
dauki jakarta ta rataya tana gaggawa ta nufi
qofa zata fice abida ta kira sunanta a
sanyaye ta juyo ta kalli abida da cike da
tausayiabida tace kina da kudin acaba ne?
A.farida ta gyada kai tace inada naira 150
ragowar wanda canjin 200 dinda kika banina
hau acaba jiya zuwa ofishin yan sanda.abida
tayi ajiyar zucia tace kiyi haquriki gyara duk
abubuwanda aka wuce ki ki mayar da
hankalinkisosai harsai kin kamo 'yan ajinku
domin anbarki baya.A.farida ta gyada kai
tace insha'allah zan mayar da hankali akan
karatuna na tafi saina. Dawo ta juya a gigice
cikin sauri ta kuwa ci sa'a bata ci karo da
kowa ba a tsakar gida haka qofar gidansu
harta fito unguwarsu sannan ta samu acaba
ya fisgeta sai asibitin malam aminu kano
tana shiga cikin asibiti sai ta nufi bangaren
da pfishin gogan nata yake ba har sauri ta
qara gami da kawar da kai gefe don kada
ma ta kalli bangaren.bata marmarin taci
karo dashi ma balle ta tuna dinbin bacin ran
da ya kimtsa mata a baya ta qudiri niyya a
ranta ita dashi har abada koda kuwa shine
kadai da namiji da yayi saura a fadin doron
qasa.tana shiga aji sai yan aji suka mata
caaa!suna tambayarta ina ta shiga ne ta
bace kwata-kwata ba'a ganinta koba da
lafia ne? kasancewar ramar datayi kuma duk
tayi baqi don wahala.ai kuwa kun san
amsar da zata basu balle ma sun saka ta
akan hanya cewar ko bata da lafia ne? tuni
ta amsa musu da eh bani da lafia ta qara da
cewa harda kwancia a asibiti'',haka tayi ta
bin metron da nurses tayi musu irin
wadannan gunduma-gunduban karairayi su
kuwa suka bita da sannu Allah ya sauwaqe
dole su yarda mana saboda tsananin ramar
da tayi gata daman ba jiki ba.bata yi qarya
ba tabbas data sha jinyar zuci jinya a zucia
kuwa wani lokacin har tafi jinyar jiki ta rame
qurqet saboda tashin hankali.
Daga nan ta duqufa tambayar abubuwan da
kayi bata nan ta dinga kwafar jotin dinda
frnds sukayi akan cuttutuka da yawa ta
tabbatar an wuce ta sosai a cikin satitikan
da take qin zuwa.tambaya take tun qarfi
abun daba ta gane ba daga dalibai ,metrons
da doctrs abun da ya shafa sannan ta
bazama ta koma makarantarsu wajen
malamin da yake alhakin duba ta wato
(supervisor )dinta yazo har sau 2 baya
samunta don haka tana cikin matsananciyar
matsala idan batayi da gaske ba.saita
maimaita attachment din nan next year
hankalin A.farida yayi matuqar tashi a
lokacin da yan ajinsu suka zagayeta ta suna
neman mata mafita kowa yana bata
shawarar abun daya kamata tayi ta shiga
matsancin kokonto ana tantama anya kuwa
har akwai wani bayanin da zata yiwa malam
basiru ya saurare ta yadda ransa ya baci
yana ta fada akan yazo 2X duba ta bai same
ta.hawaye mai radadi ne ya surnano daga
idanunwanta yayin data tuno wanda yayi
mata silar abun daya same ta taji haushin
5r shuraim ya rafe ta .ta cije lebe ta girgiza
kai tace a ranta shuraim na biyewa sharrin
zucia a karo na farko na wahalar da kaina
insha'allah ba za'a sake ba a. Karo 2 zucia
nafi qarfinki yanzu duk inda kika kai ga
hango haduwar dr shuraim bazan saurare
kiba kece kika yi qayatamin shi a rai kika
dinga zuga ni gashi a kusa-kusa zan same
shi kikayi ta zurmuqani a rami har sai dana
yi zurfin da na kasa fita saida aka agaza min
na fito to ba za'a sake ba zanyi yaki dake
har inda qarfina ya qare babu ke babu
hasko min dr shuraim shi daban ni daban
kowa ya tsaya a matsayinsa.ta sharce
hawaye ta miqe ta suri jakarta ba tare da
tayi wa kowa sallama ba ta fice daga
asibitin kai tsaye ta nufi makarantarsu
ofishin malam basiru ta nufa sai dai kash ta
daki gurbi ya fitaa ita kuma tazo abokan
aikinsa suna ce mata yanzu zai dawo-yanzu
zai dawo taki qarewa abun qarfe 12 na rana
sai ga Aisha farida a zaune ofishinsa har
qarfe 5pm dole ta tafi gida tinda bai dawo
ba.
Ranta bace hankalinta a tashe ga qishin
ruwa da yunwa yini guda bataci abinci ba
dadinta ma dai tana zuwa tayi salla sannan
ta dawo tavi gaba da jira domin A.farida
bata wasa da sallarta.ta iso gidansu da
misalin 5:45saida ta hadu da jama'ar
unguwarsu da dama qofar gidansu zauren
gidansu da tsakar gidansu sai suke jin
kunyarta wasu ma basu iya hada da
ita.tana gaishe su suna qasqantar da ido a
qasa tamkar sunga surukarsu sai mamaki ya
rufe ta tana shiga dakin aunty abida ta tura
kai ta shiga kasancwar yay husaini bai dawo
ba kafin abida tace mata wani abu
Aisha.farida ta jero mata tambayoyi zokat
suka mata zucia tace anyi abida lafia yan
gidan nan kuwa?me yake faruwa ne?me
kika fada musu suke kasa hada ido da ni?ko
suna zargina da aikata wani abun kunya ne?
abida tayi murmushi ta girgiza kanta tace
ko daya kada kiyi zargin duk wannan jeki ki
cire kayan makarntarki ki dauki abincinki
kici yana gefen kayan ki kici naga alamar
kina jin yunwa ki saurareni ina zuwa dakin
naki yayanki ne yasani aiki yanzu zan gama
kada ya dawo ya iske ban gama ba ransa ya
baci.A.farida ta fice a sanyaye a zuciayarta
cike da fargabar abun da abida zata fada
mata ta cire kayan makarantarta ta saka
wata yar yaloluwar t-shirt fara da baqin
skirt kan ba kwali ta shinfida yar tabarnarta
ta jawo kwanon abincinta ta bude wake da
shinkafa ne da mai da yaji ga tashin hankali
ga abincin ya sanqare sannan ga
matsananciyar yunwa turawa take da kyar
take hadiyewa maqogwaronta ya tsuke
yayin da hanjin cikinta duk sun kanannade.
Ta miqe da sauri ta bude wani farin bokiti
mai murfi da moda akai shine ruwan da
suka tadana na musamman don shansu ta
debo a kofi ta dao ta zauna tana tura garau-
garau tana korawa da ruwa ta kusa gama ci
sai ga abida ta shigo fuskarta cike da
murmushi tazo gefen Aisha ta zauna yayin
da Aisha tayi qasaqe tana sauraronta abida
tace Aisha. Yay makaranta?yaya kuma
gogan naki likita?nan da nan Aisha ta hade
fuska murtuk daga gani zuciayrta ce ta
dugunzuma da jin kalmar sunan likita abida
bata sami wannan amsar ba don haka saita
sauya hira nan da nan.tace Aisha tayi ajiayr
zucia tace na shigo unguwar nan sai na ga
jama'a musamman mata suna ta kawar da
kai basa iya kallona idan na gaishe su sai
naga sun sunkuye-sunkuye haka dana shigo
gidan nan ma duk basa iya hada ido dani
me yake faruwa ne?abida ta tuntsire da
daria tace ai daman haka rayuwa take
maganinsu nayi''maganinsu kamar yaya?
Aisha farida ta tambaya yayin data ajiye
cokalin da yake hannunta gaba daya ta
tattara hankalinta gaba daya wajen abida
abida ta langwabar da kai gefe tayi shiru
zuwa wani dan lokaci tace bayan fitarki
dazu da safe nayi fiye da mintina 30 ina
zaune ina tunanin qaryar da zan shiryawa
su uwani da husaini yadda zan wanke ki
daga zargi na tshi na shiga daki na iske
husaini sai na fito da kudaden nan ina
qidayawa yayi min tsawa yace ina na samu
kudi da sassafe?
Nace masa ai kudin nan a hannuna ya
kwana tun bayan magrib aka kawo min sai
yace waye ya kawo min?na gyara zama
nace mace mai jegon da Aisha ta taimaka
mata itace ta taso da ita da mijinta suka
kawo kudin da yake Aisha tayi musu waya
ta fada musu halin data shiga a sanidiyyar
bashin data ci don ceto rayuwarta.dole
suma hankalinsu ya tashi a lokacin suka
bazamo suka hado kudin nan 12k suka
kawomin sannan suka je office din yan
sanda suka fito da Aisha ai a gidan nan ma
ta kwana a daki ta labe taqi fitowa sai da
safen nan ta shirya ta fice makaranta
husaini yayi shiru can yace dani ashe da
gaske ne kudin asibiti ta biyawa qawarta,ba
qarya take ba?nace da gaske ne mana me
Aisha zata yi da zunzurutun kudi kudin nan
yarinyar da abin dunia bai dame taba,bata
da buri ko kadan duk abun da ta samo
komai kanqantarsa sai ta godewa Allah.yace
yanzu saura nawa ne cikon kudin nace
saura saura cikon 5k shima sunce zasu je
su nemo su cika a cikin satin nan ma zasu
kawo sai ya miqe ya je ya bude aljihun
rigarsa ya zaro wasu kudade yan dubu_duba
sai ya qirgo 5k ya bani yace gashi idan
wadancan sun kawo sai a bani nima ba
kudina bane kudin qungiya muke hadawa a
office don tallafawa duk wanda ya shiga
damuwa a cikinmu rashin lafia ko aka
yimasa haihuwa ko kuma idan zaiyi aure a
bashi tallafi''na karba cike da murna gami
da durqusawa nayi masa godia bayan na
shirya shi na shirya yara sun tafi nima nayi
wanka na kammala dan aikin gida.hantsi
yayi kowacce ta fito da tabarmarta tsakar
gida ta zauna majalisar gulma ta hadu ta
cika tayi damqam da munafukan mata har
maqota kowacce ta zaro gyale ta shigo taji
inda aka kwana da maganar kudin wajen
Aisha.a wanne hali kike a can ofishin yan
sanda? shaci fadi iri-irihaka mugaye kalamai
ne ke fitowa daga bakunan masu dadin
zance sai sun ga nazo giftawa ma sannan
ake sake daga murya ana ambato
sunanki,harda mai cewa lallai Aisha ta
dauko ruwan dafa kanta a shekara 1 ma
bazasu iya wadannan kudade ba sai dai tayi
zaman gidan yari kawai.
Na dauko kujerata na nufo inuwar da
dandali yake fuskata cike ta da murmushi
na gaishe su wasu ne suka amsa a sheleqe
wasu kuwa sai suka kawar da kai gefe suka
yatsune fuska suka ci gaba da ambaton
Aisha tayi ganganci gobe ma ta qara na
dade a zaune na buga tagumi ina dubansu
ba kunya ba tsoron Allah a gabana basu
daina mugayen furucinsu ba akanki.talaka
ya shiga 3 a duniayar nan maganin abun
kada ka taba kayan wani saika zauna lafia
amma muddin ka shiga gonar wani tofa ka
hadu da wulaqanci Allah yabamu yadda
zamu yi don alfarmar Annabi Muhammad
(S.A.W)''Aisha farida ta karbi salatin suka
qarasa a tare suka shafa ta dafe qirji saboda
tsabagen fargaba ta qagu taji abun da ya far
tace me kika ce musu ke kuma? abida ta
gyara zama tace biyi kisha labari daman sai
irin haka ta same ka zaka su waye jama'ar
da kake zaune dasu su yan gidan nan ashe
haushin abin da kika yi ba ma suke ji ba
suna yi mana baqin cikin ashe daman can
akan irin rufin asirin Allah yayi mana ne
suke adawa.ummulkhairi ta tabe baki tace
ato qarshen alewa qasa qarshen tika-tiki
tik! qarshen qarya dai yazo da anayi mana
yatsuna ana wanka ana qalqale qafa ana
siyowa yara gwanjo suna tsukewa ana yi
mana gani-gani mu ba mu iya kula da miji
ba sai iya bini-bini ana kusa da miji ana
yimasa fari da ido.uwani tace kin manta a
dafa abinci haka kawai sai an zuba kori yayi
qamshi an yayyanka salat da tomatoes da
albasa''Mairo maqoriyarmu tace au irin
wannan iyayin ake yi muku ashe a gidan
lallai kuna shan kallo.
Ummulkhairi tace idan kince kallo ma ai
daya ke nan sai idan miji zai shiga bandaki
zoki ga yadda za'ayi ta kuza ruwa ana
sharewa ana yayyafa abin qamshi kamar fin
mazanmu yayi su da suke shiga da
zarnin''uwani tace kun manta yar gayun
gidan nan wai ita 'yar boko Aisha magana
daya sai an sako turanci goma kullun ana
qalqale kayan makaranta ana goge kaushi
anayi wa manu yan matan gani-gani saboda
suna soya awara a qofar gida su basu zuwa
boko''Aisha ta zubo da hawayen daya cika
mata ido ta girgiza kai anti abida me ya
kawo duk wannan? daman haushinmu suke
ji? abida ta zubo da hawaye tasa gefen
zaninta ta matse tace ke kya fada farida
daman sun dade suna so suci min mutunci
to basu ga fuska ba don bana shiga
harkarsu zunde da yafice kala-kala kullun
suna yimin basu isheni. Kallo ba sai in nuna
ban san suna yiba saboda iya zama da
jama'a.zan gaishe su ko baza su ansa ba.
Zan bawa ya'yansu duk abun dana dafa ko
su basu amsa ba zan bawa 'ya'yansu duk
abunda dana dafa ko su ban basu ba.bana
bari suga hudar da zasu shigo jikina balle
ayi gulmar wata dani haka ban damu da sai
naji gulmata da akeyi ba.bani da lokacinsa
sai lokacin mijina da ya'yana kema bakida
lokacin kanki ma balle na wasu mu ba yan
gari bane amma munfi sy yan garin sanin
jama'ar arziki da samun Alkhairi shine
haushinsu sai yanzu suka sami damar
amayarwa da abun da yake zuciyarsu.yadda
kika ga na zuciyarsu.yadda kika ga na zubo
da hawayen nan sau 1 na sharce da gefen
zanina haka nayi bance komai ba sai na
saka hannuna a gefen zanina na zaro
wadannan kudi na miqawa uwani ta zazzare
ido sai hannunta ya dauki karkarwa ta karba
a sanyaye.tana qirgawa a yayin da
idanuwan masu leqe suka fi nata firfitowa
masu kama baki sunayi haka masu susar
tsohuwar kwarkwata suka fara yi ba tare da
sun san ma abun da suke yi sunyi matuqar
mamakisun razana haka sun ji kunya uwani
da yan tayinta suka kidaya kudi naira 17k ta
cika cif-cif.
Uwani bata iya dago da ido ta dube ni ta
iya ce min komai ba sai nice tambaye ta
nace sun cika ko da saura kudin da farida ta
ranta?ta gyada kai tace sun cika haka suke
nace to ki kaiwa haj rabi kice tayi haquri ba
za'a sake ba yanzu ma qaddara ce Allah ya
aikowa Aisha tayi jihadi ne don ta ceto ran
qawarta data qoqarin mutuwa akan gadon
asibiti zata haihu saboda bata da jini kuma
ba zata iya haihuwa da kanta ba sai tiyata
shine tazo ranci kudin ta kai kafin mijin ya
aiko daga lagos anan aka sami matsala da
bai aiko da wuri har ta kai aka kai ta wajen
yan sanda aka daure.Allah yana bayan mai
gaskia. Allah yana taimakon wanda ya
nemi. Taimakonsa Allah yana duban zuciyar
na gari da mugu kuma yayi hukunci a kansu
tun daga nan dunia da qawar Aisha mai
jego taji labarin halin da Aisha ta shiga a
dalilinta tuni ta taso daga kan gadon asibiti
taje ta fito da farida ta kawo ta gida ta hado
kudin nan da aka ranta Allah ya dubi zuciyar
Aisha yaga kyakyawar niyyarta ya taimaketa
ya fitar da ita daga tozarci da abin kunya.
A gida aisha farida ta kwana, ta tashi da
safen nan ta tafi makaranta taci gaba da
karatunta. Yanzun abinda ya rage shine
idan ta dawo da yamma kuje wajen 'yan
sanda ku tabbatar musu da ta biya kun
janye kara, sai a soke shikenan a zauna
lafiya. Uwani mun gode da taimakon da
kikayi mana, akasi aka samu har ya zama
rigima. Kiyi hakuri, itama ba haka taso ba.
Su dukka suka yi shiru kamar wadanda ruwa
ya cinye su. Nayi murmushi na dube su
daya bayan daya nace ku gafarce ni, daman
ina da matsala daku bansani ba, kuma babu
wacce ta tare ni ta sanar dani? Ai da
tuntuni kun sanar dani halin da ake ciki don
ban san inayi muku laifi ba ma a tsawon
zamana daku, kusan shekaru goma. A
bangarena bani da matsala daku ko kadan,
ina taka tsantsan kada in batawa wani, ina
iyakacin kokari inga na fitar da hakkin
makotaka da Allah Ya wajabta a kaina shine
inyi muku sallama, in gaishe ku duk sanda
muka hadu a tsakar gida, in duba ki idan
baku da lafiya, inyi muku jaje ko gaisuwa
idan kun rasa wani dan uwa ko wani abu. In
taya ku murna idan aure ko haihuwa sun
same ku. Menene yayi saura kuma baya ga
duk wadannan? Ku gafarce, laifi daya ne da
nake muku, kuma ba zan daina ba shine ina
kula da mijina yadda ya kamata, ku kuma
ba kwa so. Nayi alkwari bazan daina tsafta
ba, haka ba zan daina ciwa 'ya'yana ado ba
da gwanjo, haka ba zan daina wankewa
mijina bandaki ba duk sanda zai shiga, haka
ba zan daina sanya curry ba ina dafa masa
dadadan abinci, koda kuwa ace mijinmu
daya ne daku, balle babu hadina daku.
DUK KYAN TAKALMI 2* 2

Menene laifin aisha farida kuma a cikin
gidan na, ko kuma ince a cikin unguwar
nan? Hana idanuwanta baccin da take yi ne
take zuwa karbar haihuwarku komai dare?
Ko kuwa allurar da takeyi muku idan likita
ya rubuto muka ta hutar daku zuwa
chemist? Kitson da take yi muku kyauta ko
kuwa ko yawa 'ya'yanki karatun da takeyi,
duk sati ba tare da ko sisinku ba? Taya ku
girki da takeyi, ko kuma rainon 'ya'yanku
da take yi muku koda yaushe shi ya zama
laifi? Gaishe ku da takeyi koda yaushe, ko
hirar da take zama kunayi da ita shine
laifinta? Allah sarki rayuwa, ai kuwa Aisha
farida mutum ce babu wacce bata morarta
a cikin gidan na, koma nace a layin nan
gaba daya. Ummulkhairi na dade da sanin
cewar ke kike wanke kafa kike zuwa ki sami
mahaifiyar musbahi ki caccaka mata karya
da gaskiya don ta tsani aisha farida a
matsayin surukarta, burinki ya cika har sai
da kika haddasa wannan gaba a zuciyar
uwar musbahu, ta tsinewa aurensa da aisha
farida, tace idan dai tana raye ba zai aure ta
ba. Na sani aisha farida ta sani, musbahu ne
ya fada mata shima ya sani. Sai
ummulkhairi ta mike tsaye ta hau
bambamin fada mai tafe da borin kunya
tsagwaronsa. Tana jan Allah Ya isa ba zata
yafe sharrin da nayi mata ba. Na mike
tsaye nima na nuna mata ruwa ba sa'an
kwando bane, haka shiru shiru ba tsoro
bane gudun magana ne. Kalmar da na fada
mata ta karshe daga ita na gaggauta barin
wajen itace kinji dadi, kin raba auren
musbahu da farida, amma baki isa ki hana
Allah Ya bata wani mijin ba, daga wani
bangaren, bangaren da baki sani ba. Kuma
wanda baki da matsayin da zaki taka kiyi
gulma. Ummulkhairi ke da sauran makiya,
ku bude idonku sosai zaku sha mamaki,
zaku sha kallo, zaku ga irin mijin da aisha
farida zata aura idan har muna raye.
Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da
babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya
unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan
nan Allah yana tare da mu kuma da shi
muka dogara yan gulma suka hau gasgata
maganata suka hau nadama suna fadar
alkhairin Aisha farida data taba yimusu a
rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale
su suna ta kame- kame kanka ce kwabo
dandali ya rore ya qare daya bayan daya
suna ta sulalewa suna guduwa saboda
kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki
gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi
mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace
anty abida dama ke iya fada?amma
bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah
meye abun burgewa a iya fada kuma?ni
zubar da mutunci ne fada dole ce tasani
sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina
da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk
zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu
muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa
kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki
dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne
ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu
daya ba balle suce nazo zan kwace musu
miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi
dani saina na zama abar zagi,abar kyama
daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka
suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba
kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen
su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki
basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara
bare wani miji?

Aisha farida kwarai kuwa hakane ai ana
zuba qazanta a gidan nan dukansu qazamai
ne duk dakin daka nufa warin datti ne abida
tace kece ma mai iya shiga dakunansu har
ki zauna ki cakumi gashinsu ki kitse ni ina
zan iya jure wari?ai shi yasa. Nakeso kici
gaba da dagewa har sai kin sami dr shuraim
shi kadai yafi dacewa da rayuwarki wani juyi
Aisha farida tayi tashin farko ta kifa ta
kwanta ta juya baya bata sake cewa komai
ba saboda bata da abun fada taki jinin a
ambaci sunan dr shuraim a halin yanzu
balle ayi hirarsa.Abida tayi dariya tace au
kiran sunan shuraim ma ba kya so shi ne
kika juya mun baya? masoyin naki ne ya
zama haka yanzu a wajenki?haba farida
kada kiyi fushi kada ki sare da wuri mutane
suna rasa ransu wajen neman abinda
zuciyarsu keso ke yanzu wacce wuya kika ji
har da zaki zame?keda shuraim kuna nan
daram ba gudu ba ja baya ina nan akan
bakana duk kyan takalmi qafa ce zata
tattaka shi''Aisha farida ta jawo filo ta dora
kanta ta toshe kunnenta sabida bata
buqatar ci gaba da sauraron abun da abida
ke cewa tamkar tana zuraro mata tsohon
gyambon data dade da warkewa bata fatan
gyambon nan ya dawo mata danye tafi son
idan ya warke ya warke kenan har abada
bata buqatar dayen ciwo ko maqiyinta bata
masa fatan ya shiga halin data shiga.
Abida ta fice tana daria ciki-ciki fitar abida
ke wuya sai ta tashi zaune ta jawo jakar
makaranta ta zubo littafanta da manyan
text books dinda ta aro daga wajen khadija
isma'I'll don ta karanta abubuwan da akayi
bata nan.tabbas an wuceta. Da yawa sai
tayi da gaske zata kamo su tana karatu
zuciyarta na zogi idan ta tuno dalilin daya ja
mata wannan matsalar sai taji haushin
kanta da kanta ta qudiri niyyar ba zata sake
bawa zuciyarta wannan dama ba balle takai
ta ta baro ta.bata fito ba sai data ji ana
kiran sallar magrib fitowarta keda wuya tayi
kicibis da yayanta ya dawo daga aiki ya
kuwa wurgo mata harara sai ta zube a qasa
ta kwashi gaisuwa ko amsa mata baiyi ba ya
shige dakinsa Aisha farida ta sake
gasgatawa har yanzu da sauran rina a kaba
maganar bata wuce ba kenan da saura?ta
miqe a sanyaye taje tayi alwala ta dawo
daki tayi sallah kafin ta idar taji motsin
shigowar abida daga dukkan alamu wajenta
tazo don har yanzu tana tsaye a kanta sai
da ta idar da wuri taji abinda ke tafe da ita
tana idarwa ta juyo ta dubi abida tace
aunty lafia? Abida tace ki zo inji yayanki
amma kada ma ki damu ba wani abu bane
kinsan dai duk abubuwan dana shirya to
duk abunda ya tambayeki ki haka zaki tsara
masa yanzu ya du da mijin uwani a qofar
gida suka tattauna suka wa juna haquri
shine zasu je wajen yan sandan su sunar
musu cewar an sulhunta an janye qara ba
sai kun je ba.Aisha farida ta miqe da sauri
dafe da qirji tace anti abida me zance masa
game da cikon 5k dinsa da kike ce zasu ciko
min?Abida tace a hakan zaki barshi zasu
ciko din,idan basu ciko ba ai laifinki bane
kuma ba zai kai ki qara ba dai shima sai ya
dauki asara daba ki samo 12k bama ai dole
ya nemo yayi belinki ba tunda ba zai bari a
daure ki ba wata da watanni.nasan dai zaki
sha fada ne da zagi kawai zagi kuwa baya
qari idan da sabo ai kin saba''
Abida ta wuce gaba Aisha na biye da ita a
baya ta sunne kai a cikin hijabi hannayenta
kuwa dukka 2 na dafe da qirjinta sai
karanto addu'io take iri-iri ba adadi tana
mai neman agaji daga wajen rabbil
samawati duk abun da zai zo yazo mata da
sauqi.Allah mai amsar addu'ar bawansa sai
ya sanyaya zucia yaya husaini maimakon
yayi mata fada data bayyana a gabansa sai
ya shiga yi mata nasiha yaji tamkar shima
ya fashe da kuka lokacin daya ga hawaye a
idon qanwarsa sai yaji tausayinta ya shiga
nasiha mai hade da rarrashi yace farida
haha farida kefa mai hankali ce mai sanin
ya kamata ga natsuwa nayi mamakin yadda
kike jefa rayuwarki cikinmatsla don kawai ki
fitar da wasu daga matsala ba'a hana
taimako ba amma kina so kina so kice min
bata da dangi ne ko dangin mijin sai ke kika
fiso sonta dasu?suna raye zasu bari ta mutu
ne basu samo kudin da za'ayi mata tiyata
ba sai ke?farida kinsan halin da muke
ciki,ta kanmu muke yi,bamu da wani
mataimaki sai Allah kullun hade-hade da
kame- kame mukeyi sannan muci abinci sai
naji tamkar na bar garin nan saina tuna
talauci dana baro a shagamu har gara nan
ma.ki riqe maraicinki ki riqe talaucinki ki
riqe matuncinki ki riqe karatunki ki lallaba
ki gama ki fara aiki ko zamu sami sa'ida
babu ke babu sake cin bashin wani babu ke
babu katsalandan akan matsalar wani ki
tashi ki tafi Allah ya kiyaye gaba Aisha
farida ta rushe da kuka tace nagode
insha'allah zan kiyaye ta fice ta nufi dakinta
ta shige ta takure tayi ta rusa kuka tana nai
tuno iyayenta da suka rigamu gidan gaskia
tabbas husaini ya fada mata gaskia dole ta
nutsu tasan me ye a gabanta kuma ita wace
ce a rayuwa?hawaye ya surnano daga
idanuwan husaini yasa hannu ya goge abida
ta matso kusa dashi ta fada cikin
sassanyiyar murya tace yaya kaima kukan
kake yi?kada ka damu fa kada ka saka
damuwa a ranka ciwo ya same ta tsautsayi
ne qaddara ce komai yazo qarshe ba za'a
sake ba insha'allah.
DUK KYAN TAKALMI 2* 3
Husaini ya girgiza kai yace ina son Aisha
saboda babanmu yana sonta tayi kama
dashi don haka idan na dube ta ina yawan
tunawa dashi hawayenta ne yake tayar min
da hankali.farida abar tausayi ce marainiya
babu uwa ba uba nida nake riqe ta talaka
ne ina matuqar tausayinta idan na ganta a
cikin qawayenta yan gata masu mota
baiwar Allah bata damuwa a haka take
daurewa tayi karatu sai naji tamkar dama
ina da yadda zanyi farida mata sami duk
abubuwan da yan mata suke buqata kamar
kayan kwalliya da dinkuna to babu
misbahun ma da yake sonta yake
taimakonta shima an raba su fatana Allah
ya fito mata da miji na gari inda zata huta
ko bayan raina ta taimaki kanta kota riqe
min 'ya'yana ba''Abida tayi shiru tana
tunani a ranta tace babu mijin daya dacewa
da ita irin dr shuraim insh'allah farida saita
sami shuraim ko don na hucewa mijina
takaici a ransa ko don in cika masa burinsa
na ganin farida ta sami gidan hutu nayi
alqawalin zan yaqi zuciyar shuraim da
addu'a da kuma kyautatawa har sai yaso
farida yaya husaini ya katse tunanin da
abida keyi yayi cimak ya miqe tsaye yace
zanje waje malam yusha'u na jirana mijin
uwani zamu je wajen yan sanda nan don a
janye casa dinsu Aisha.Abida tayi masa
fatan ya dawo dashi lafia ya fice da sauri.da
Aisha ta idar da sallar isha'I ko abinci bata
ci ba wajen datayi sallak kan tambarmarta a
wajen ta kudindine ta kwanta babu abin da
take yi sai sheshekar kuka da ajiyar zucia
har barci ya dauke ta.
Babu irin tashin da abida bata yimata don
taci abinci taqi tashi tace ta qoshi a haka ta
kwana saboda gajia da barcin data keji basu
bari taji yunwaa ba bata farka ba sai da
asuba kiran assalayu a kunneta ta miqe a
nutse tana mai addu'io taje tayi alwala tayi
sallah sannan ta shiga cuku-cukun yin
wanka da saka kayan makaranta so take
gari ya waye ta fice saboda gidan ya zama
mata tamkar kurkuku haka tunaninta da
hankalinta kakaf ya koma kan karatunta
bata da wani buri illa taga ta gyara inda ta
kuskuren kuma ta kamo yan ajinsu inda
suka wuceta ta zamana mai nadama akan
kuskuren data tafka a rayuwarta a kwanakin
baya a dalilin shuraim sai kuma ta qudiri
niyyar natsuwa da cire duk wani abu da zai
gundiri rayuwarta giftawar husaini ta gani ta
tagar dakinta ya dawo daga masallaci zai
shiga dakinsa sai tayi wuf ta fito ta durqusa
ta gaishe shi ya juyo ya dube ta duba mai
cike da tausayi kasancewar yaga ta rame
idanu wanta duk sun kode mata
musamman data kwana 2 baka kwalli ba ya
fada cikin yar siririyar murya farida lafiayar
qalau kuwa ko baki lafia?tayi sauri ta
sunkuyar da kai qasa gami da yin
murmushin qarfin hali ta girgiza kai tace
babu abinda yake damuna yay yace za a tafi
makaratar ne har kinci dumame?ta gyada
kai tace eh yasa hannu a aljihu ya dauko
wata tsohuwar 200 ya miqa mata kamar
kullun kamar yadda ya saba bata kudin
acaba zuwa da dawowa da kuma na shan
pure water.ta durqusa ta karba tayi godia
ta shiga daki shima ya shige daki tana shiga
ta mistsika yan powder a fuskarta ta gyara
dan guntun hajabin da yake jikinta sai ta
rataya jakarta a kafada gami da saqula 200
a zip din dake jikin jakar ta fito a bakin qofa
suka hadu da abida lokaci daya suka yiwa
juna murmushi Aisha ta gaishe ta abida ta
amsa gami da cewa har kin fito ki tsaya
kisha koko mana.Aisha tace sauri nake
kada na makara supervisor nake son gani
abida tace yunwa kuwa baza ta dame kiba
ba kici komai da daddare ba na jiya da
ranar ma da yawa kika ci ba Aisha ta
langwabar da kai tace ba damuwa idan na
dawo zanci abida ta kuncegefen zaninta ta
dauko 100 ta miqawa farida tace kici abinci
a can don nasan dole kiji yunwa farinciki
yaa lullube Aisha ta karba gami da
murmushi ta duqa tayi godia sannan ta juya
ta nufi hanyar fita harta kai zaure sai taji
muryar abida ni kiran sunanta sai ta juyo ta
tsaya cak!tana dubanta kanar marar gaskia
ta qarso inda take taja. Hannunta zuwa
bayan kyauren zauren.
Ta fada cikin rada daman inaso na tambaye
ki dazu, to nasan halin kunnen hussaini, sai
ya jiyo mu. Hankalin farida ya tashi ta dafe
kirji tace me ya faru? Abida tace dr shuraim
mana, zaku hadu yau kuwa? Kafin kace
kwabo farida ta bata fuska ta kara da kai
gefe, ta zumburo baki. Tace ba zamu hadu
ba. Ta juya a fusace zata fice. Abida ta sake
jawo hannunta tace fushi kike don naayi
mmiki zancen shuraim? Kin daina sonsa ne?
Aisha farida tayi caraf ta fada cike da gadara
da takaici tace eh. Sai abida ta kwashe da
dariya, yayin da aisha farida ta fice a fusace
ko waiwayowa ba ta sake yi ba. A hanya ta
hadu da musbahi ya fito daga gidan akan
babur dinsa zai tafi wajen nema, sai ya
tsaya a kusa da abar kaunarsa yana mata
murmushin kauna. Sai dai kash! Zuciyar
masoyiyar tasa a bace take, sai ta kawar da
kai taki yin dariya ta gasihe shi ranta a
bace.
Wai kwana biyu nan wa yake taba minke?
Musbahu ya fada yayin da yake duban
fuskarta, yake murmushi. Ta kawar da kai
gefe ta fara tafiya ba tare da ta bashi amsa
ba. Yayi sauri ya sake biyo ta, ya tari
gabanta har yanzu yana zaune akan babur
dinsa. Abun mamaki sai yaga hawaye yana
zubowa daga idanuwanta, nan da nan sai
hankalinsa ya tashi ya shiga lallashinta yana
bata hakuri, gami da rokonta ta hau bayan
babur dinsa ya kai ta asibitin. Da farko taki
sai da kyar ta hau suka fara tafiya. Ba tare
da wani ya sake magana ba a cikinsu,
sheshekar kuka kawai farida keyi a ciki ciki.
Cikin marainiyar murya ta ambaci sunansa
tace makarantarmu za ka kaini ba asibiti
ba. Nan da nan ya amsa mata da to...to
farida. Har bakin ofishin malam basiru ya
kaita, ta sauko tayi masa godiya ba tare da
ta dube shi ba. Ya kira sunanta cikin
lallausar murya, ta juyo a tsanake tana
sauraronsa, sai taga hawaye ya surnano
daga idanuwansa, ta sake dubansa sosai, sai
tayi mamaki tace lafiya? Yace farida kiyi
hakuri ki yafe min nima ba da son raina
haka ta faru ba. Ta tambaya cike da
damuwa meya faru? Yace kwanan na ga kin
shiga matsananciyar damuwa, har aka ce an
kai wajen 'yan sanda an kulle ki duk da ba
fada min takamaiman laifin da kikayi ba.
Farida da ace tun sanda kika gama
sakandire muka yi aure, da na killace ki duk
da haka ba ta faru ba. Amma nasan komai
mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa ya
tsarawa kansa rayuwar da yake so ba, sai
yadda Allah Ya so dashi.
Sanin kanki ne duk duniya ke nakeso, kuma
har abada ba zan daina sonki ba, matsalar
daga wajen goggo ne ba don ita ta haife ni
ba ina tsoron bakin uwa ba da tuni nayi faci
da maganarta munyi auren mu. Na kasa
son matar da ta aura min, na kasa cire raina
a kanki. Ba yadda zanyi nace kada kiyi aure
ki jirani, idan nayi haka na zalunce ki, tunda
bansan ranar da goggo zata hakura ba
amma kada kiyi gaggawar yin aure ki barni,
kullum ina ta fadawa Allah, nasan kema
kinayi. Toh muci gaba. Farida ta rushe da
kuka, tabbas musbahu yayi gaskiya, abin da
yake ranta kenan, cewar ba don yaki
aurenta ba da ya za'ayi ta afka cikin
wannan hatsarin? Sai ta juya da sauri ta nufi
ofishin da tazo, yayin da musbahu yake
kwalla mata kira taki ta waiwayo ma balle
ta amsa. Tana shiga ofishin taci s'a ta iske
malam basiru yana nan shi da abokinsa
malam sulaiman. Bayan ta gaishe su sai ta
barke da kuka marar kakkautawa, sai suka
shiga damuwa suka shiga yi mata
tambayoyi, lafiya take kuka? Suka bata
kujera ta zauna cikin sheshekar kuka ta fara
bayani. Sannan suka fahimci inda ta nufa da
kuma dalilin kukan nata.
ba 31 da 32 zan ci gaba da 33
Supervisor ya turo hula gaban goshi yace
rashin lafiyar da kikeyi ce ta hana ki aiko
'yan uwanki suzo su fada min ko kuma ki
aiko a rubuce a kawo min? Gashi yanzu sau
biyu ina zuwa duba ku ba kya nan, yaya
kike so nayi miki yanzu? Kije kawai wata
shekarar ki dawo ki maimata attachment
din. Ta sake fasa kuka taci gaba da ba da
hakuri. Mal sulaiman ya dubi abokinsa yace
a'a ba za'a yi haka ba, ka dai duba ka
taimaka mata. Itace fa monitor kasan aisha
umar bata da wasa, lalura ce ta jawo haka
da dai Khadija sani ce, kawarta ba zan ma
shiga zance ba, don nasan bata da kokari.
Malam basiru ya gyada kai yace shikenan
kije nan da kwana biyu zan shigo asibitin in
duba kiki zama cikin shiri dan a koda
yaushe zan iya fadowa. Ta durkusa tayi
godiya. Aisha umar ta fito tana matse
hawaya, amma zuciyarta cike da farin ciki,
hankalinta ya fara kwanciya. Tayi mamaki
da ta iske musbahu har yanzu yana nan
yana jira bai tafi ba. Jikinsa na rawa ya
kunna babur ya karaso inda ta ke yana
tambayarta ta gama su tafi, ko akwai inda
zai kaita kuma? Ta girgiza kai tace cikin
asibiti kawai zanje. Ta hau babur suka tafi
har yanzu ma dai babu wanda yake magana
a cikinsu, tana nuna masa hanya har ya
kaita inda take so, sannan ya tsaya.
Tana saukowa sai taga ya dauko kudi ya
mika mata, dubu daya 'yan dari biyar guda
biyu. Yace karbi wannan bashi da yawa, a
cikin kudin da na ranto miki ne ma zanje na
biya su, amma ba zai gagara ba. Daga nan
zuwa yamma zan cika in biya su. Aisha
farida ta girgiza kai tace ka barshi na gode.
Yace a'a ki karba farida babu komai, a shirye
nake nayi miki duk abin da kike so idan
baifi karfina ba, ko bani dashi zan nemo
bashi na baki. Ta mika hannu ta karba a
kunyace, ta duka tayi godiya. Ta dube shi
sai taji sanyi a ranta ganin annuri a fuskarsa
murmushi kawai yake yi mata naso da
kauna. Ta rike kan babur dinsa tana
murmurdawa ta dube shi tayi fari da ido.
Tace musbahu na gode da dawiniyar da ka
dade kana yi dani, nagode da kulawarka da
damuwar da kayi dani a tsawon zamana da
kai baka taba gajiya dani ba. Ko kadan ban
taba zarginka ba akan rashin aurenmu,
nasan daga inda matsalar take, ina adduar
Allah Ya zaba mana abin da yafi alkhairi
amma ba zan boye maka ba musbahu bana
jin a jikina zamu iya aure, don banson nayi
auren da zan kasance bani da kwanciyar
hankali. Saboda mahifiyarka ta fito baro
baro bata son abun. Koda naji sonka zai
mamaye min zuciyata nakan yi addua Allah
ya yaye min, sai nayi sauri na juya akalar
zuciyata wani bangaren.
Musbahu ya girgiza kai alamar takaici yace
yanzu aisha farida har addua kike Allah Ya
cire miki sona a ranki, koda yake bakiyi laifi
ba idan kinyi hakan, amma ni ban taba
fatan na daina sonki ba, ko da kuwa bama
tare. Wa kike so yanzu bayan ni? Nasan dai
ba zaki rasa ba, tunda a maganarki yanzu
kin furta wata kalma da take nuna
hakan....ke 'yar shagamu, lah lah lah zance
ma kikeyi da sassafen nan? Muryar da ta
jiyo daga bayanta kenan ita da musbahu
suka waiwaya da sauri, maza biyu ne suke
tafe akan doguwar barandar, su dukka suna
sanye da wando da riga na bakar suit
wuyansu sakale da abin gwaji. Ko ba a fada
maka ba manyan likitoci ne. Dr lukman ne
mai maganar, na kusa dashi kuwa dr
shureim ne, daga dukkan alamu daga duba
marasa lafiya suke, domin da daliba na biye
dasu a baya. Ta dubi dr lukman tayi
murmushi ta rufe ido da hannayenta biyu
ta fada a kunyace a'a ba zance nake yi ba,
yayana ne. Musbahu yace yayanmu ai
kanwata ce na kawo makaranta. Gogan
naka dr shureim baice komai ba, amma
yana tafe yana dubanta kasa kasa har suka
wuce. Kallo daya tayi masa ta watsar ba ta
sake waiwayarsa ba, taci gaba da duban
abin kaunarta musbahu, ta shiga yi masa
bayanin inda tasan dr lukman. Abin mamaki
abinda ya sake tsorata ta sai taji musbahu
yana yabon kyawun dr shureim.
Yace shi kuma daya likitan yay sunansa?
gaskia yana da kyau irin wannan ne fa yake
sawa wasu mazan suke hana matansu zuwa
aiki idan suna ganin mazaje kyawawa irin
wannan sai su tsani mazan su sai taji
zuciayarta ta harba bumm! don fargaba ta
tambayeshi me kace?ya maimaita abun da
fada tace a ranta haqiqa na daukowa kaina
ruwan dafa kaina amma Allah ya hayar dani
dana gane gaskia gaskia ce wato 'yar
uwansa maza ma kyawunsa suke gani balle
yan mata lallai shuraim ba sa'an soyayyarta
bane zuciata tayi garajen cusa kanta wajen
ajalinta.tayi zuciayarta ta yamutse fuska
tace bansan sunansa ba nima dai ina
ganinsa dai kawai misbahu yace kina
burgeni farida duk irin kyalkyalin dunia bai
cika damunki ba har dana fara kishi
musamman dana ga yana kallonki qasa-
qasa na dauka shima ya sanki Aisha tayi
murmushi tace ni banma kalleshi ba balle
insan yana kallona kai ka lura da hakan
misbahu yace aini tun daga nesa na hango
su suna tahowa kece baki gansu saboda kin
juya baya tunda ya tunkari mu yake kallo
har na tsorata na dauka shima yana ciki
Asiha tace aa ni ban ma sanshi bama zai
wuce babur dinka yake harara bana ji ance
ya tsani yaga mace ta hau babur.misbahu
ya kwashe da daria yace kai dalibai akwai
sharri waya fadawa haka?a zamanin kuwa ai
sai an hada da hawan babur abu zai tafi dai-
dai ba kowa yake da kudin daukar taxi drop
na musamman mu talakawan da muke
zaune a lunguna koda yake su manya ne
matansu ba zasu hau babur ba sai mota
ko? farida ta tabe baki tace shi ya sani
wannan matsalarsa ce ni har bana son
zancensa ma ya cika dagun kai.
Dadi ya kama misbahu kansa ya fara
huruwa wato saboda sonsa da farida keyi
har bata ganin fuskar wani da namiji sai shi
sai ya shiga washe baki tamkar sakaran
daya ga sabon dinki yace in dawo na dauke
ki idan kin tashi? ta riqe baki ce rufa min
aisir misbahu qasada ce ma yanzu dana hau
mashin dinka a unguwarmusaboda safiya ce
babu jama'a da bazan hau ba sai a yi mana
sharrin da ba zamu fita ba.anga mun fita
tare sannan da yamma aga mun dawo me
kake tunanin za'a ce mana?kaje kawai
nagode sai wani lokaci idan Allah ya sake
hada mu a hanya don goggo ta hana ka
zuwa qofar gidanmu kuma bana so ka saba
mata ta juya ta tafi tabarshi zaune akan
babur yana dubanta zuciyarsa cike da da
tsananin sonta gami da takaicin abun da
mahaifiyarsa tayi masa ina ma za'a hada
farida da matarsa?aiko kusa basu hadu ba
farida mutun ce kuma abar so ce yarinya
kyakyawa mai fara'a ga son mutane iya
magana tafiya a nuste da dadadan kalamai
mai dadin murya da iya kallo da sai kaji
kwakwal war kanka za zillo.ga kyakyawan
halaye bata da hassada ba kyashi ko
mugunta bai motsa ba har sai da ta bace
masa ya daina hango ta yayi ajiyar zuciya ya
girgiza kai ya kunna babur dinsa ya tafi a
sanyaye gabobinsa sunyi sanyi.
DUK KYAN TAKALMI 2* 4
Cikin satin nan kakaf babu abinda farida
keyi sai karatu agida da makaranta. Bata
shiga kawaye, har a gida ba ta fitowa tsakar
gida. Tana lungu ko da yaushe littafiinta ne
a hannunta. Burinta ta kamo 'yan ajinsu
inda suka wuce ta, ga uwa uba a cikin satin
supervisor dinta zai zo ya duba ta. Ta cire
damuwa a ranta, haka bata da sauran
tunani yanzu, sai karatunta. Abinci ma ba ta
fiye son ci ba, sallah ce kawai ta zame mata
dole ta tashi tayi, sai bacci barawo idan ya
sace ta, tayi kadan ta farka taci gaba. Kafin
kace kwabo farida ta rame, kowa ya kalle ta
sai yayi maganar ba ta damu ba, haka bata
tsahirta ba. Burinta taci nasara akan abin
da ta sa a gaba. Duk da wannan jajircewar
da tayi, da dagewa ta haddace kusan duk
inda take tunani za'a tambaye ta daga
kowane bangare na karatunsu zata amsa.
Amma sai ta hada da addua tana mai
neman taimakon Allah akan karatunta.
Alhamdulillah da supervisor yazo dubata a
karo na farko ta amsa tambayayin dukka
har sai da yayi mamakinta. Sati mai zuwa
karo ba biyu ya sake zuwa ya duba ta, a
wannan lokacin ta sake shiri sai yaji
rugurguza tambayoyin da ya jero mata har
ma tana kara masa bayanai akn abin da bai
tambaye ta. Ya jinjina mata, kuma ta burge
shi matuka. Taci maki da yawa don tafi
dukkanin 'yan ajinsu ci. Daga karshe ya
shawarce ta yadda take da kokari ta daina
wasa da karatunta, taci gaba da dagewa ta
fita da sakamako mai kyau, shi kuwa yayi
mata alkawari zai taimaka mata wajen
neman aiki, kuma ko cigaba da karatunta
take so zai taimake ta.
Farida dai sai farin cik take tana yi masa
godia ji take tamkar an sauke mata nauyin
da yake kanta sai yanzu hankalinta ya
kwanta walwalarta ta dawo ta shiga cikin
qawayenta kamar da suka ci gaba da
karatunsu da kuma koyon aikinsu.idan ta
dawo gida taci gaba da wasa da dariyarta ita
da abida da 'ya'yanta duk da Asiha bata
nunawa 'ya gidansu da maqotansu bacin
ranta akan abubuwanda da suka yimata
suna gaisawa sosai tayi musu fara'a amma
ta daina zama cikinsu tayi hira dasu kuma
sai suka dinga jin kunyarta ba kasafai bama
suke iya hada ido da ita ba saboda kunyar
abun da suka yimaya domin Aisha tana da
kirki kuma tana taimaka musu ta kowace
hanya.tun yaya husaini na tambayar kudin
da ka ranta 5k har ya gaji da dadin bakin
abida yayi shiru ya daina tambayarta.ranar
lahadi misalin qarfe goma sha biu na rana
bayan abida da aisha sun gama aikin tsaf
sunyi wanka sunyi wa yaransu wanka sun
tura su islamiyya yayin da yaya husaini ke
cikin daki yana shigar baccin gajia kamar
yadda ya saba ranar labadi ce kawai baya
zuwa aiki itace kadai ranar hutunsa a
sati.don haka abida da yaranta basa garajen
yin shige da fice a dakin abida kada a tashe
shi tunda sassafe take hado musu yan
komatsansu ta kawo dakin Aisha a karo
masa qofa daga ya karya kumallo yake
kwacia saida azahar kuma zai farka.Aisha ta
gama rangawa abida kitso ras a kanta kai ka
ce fula ce akasa dan kyau sannan itama
abida taya ta tsifar nata kan Aisha na
kwance akan tabarta yayin data dora kanta
akan cinyar abida wacce ke zaune ta
mimmiqe qafa hira kala-kala Aisha ke zaune
ke rerowa abida hirar da data yanzu ta
shagamu data kano hade da qawayenta na
makaranta.abida ta dubi Aisha sai tayi
murmushi misbahu kuwa yana nan? farida
ta gyada kai gami da yin
murmushi .misbahu yana nan kin manta
kwanaki na fada miki yabani 1k harna
saywa sa'id takalmi kito? abinda tace haka
ne na tuna Allah sarki misbahu yana sonki
har yanzu amma wannan uwar tasa bata
kyautawa danta ba taci amanar haihuwa
koda yake mijin wata baya auren matar
wani mijinki na nan tafe.Aisha ta dago ta
dubi abida saita mayar da kai ta kwanta
jikinta a sanyaye ta fada cikin marainiyar
murya insha'allahu.Abida tace ina dr
shuraim?
Takaici ya hana ta magana har zuwa wani
lokaci mai tsawo babu wanda ya sake
magana a cikinsu abida tayi ajiyar zucia tace
farida kin cika sarewa baki da juriya akan
abunda kike nema ki zama jaruma ki jajirce
har sai kin sami duk abunda kike so kada ki
tsorata domin qaramin aiki ne samun
shuraim amma kin biyea maganar qawaye
duk sun tsorata farida ta girgiza kai tace ba
zai yiwu ba nan da nan farida ta juyo ta
dube ta cike da mamaki marar misaltuwa ta
fada a bayyane ikon Allah yai naga abunda
yafi qarfina sai suka kwashe da dariya su
duka abida ta gyara zama taci gaba dayi
mata tsifa yayin da har yanzu farida na
kwance ta dora kanta akan cinyarta abida
tace idan dai har yanzu kina son shuraim
bana so ki fitar da ran sumunsa domin Allah
yana bawa bayinsa duk abin da suka roqe
shi;farida ta girgiza kai tace aunty na
haqura da dr shuraim ko maganarsa bana
so ayimun abida tace kin haqura akan dole
ko kin daina sonsa ne kwata-kwata?Aisha
tayi shiru yayin da hawaye ya cika mata ido
idan ta matse sai wani ya sake tsattsafowa
abida ta shafa kanta tace kiyi haquri kukan
naki zai koma dariya da izinin ubangiji idan
baki manta ba na umarce ki daki riqe abu 5
wannan abu 5 din zai kaiki da samun nasara
ki sami shuraim cikin ruwan sanyi uhmmm
farida ke ambato tana kwance ta kasa
magana sai bugun zuciyarta ke tsananin
yi.Abida tace bazaki tambayeni abu 5 din
bane? cikin sanssayar murya tace meye
abun 5 da zan riqe? abida tayi murmushi
gami da jiyar zucia tace Alhamdulillah a
cikin 5 din nan zan fara fada miki 3 daga
baya inga miki saura 2 a hankali.Aisha ta
daga kanta a hankali ta dubi Abida zuciyarta
cike da fargaba abun da abidar zata fada
tana tantama ko zata jure su don ta qudiri
aniyyar ba zata sake yin wahala ko zubar da
ajinta ba wurin shishigewa dr shuraim abida
tayi daria tace kada ki tsorata zaki iya ba
wani abun wahala bane.farida tayi ajiyar
zucia ta dafe qirji ta lumshe ido gami da
qirqiro wani basashen murmushin da bai
kai zuci ba ita dai a ranta tafi son abar
maganar dr shuraim kawai shi yafi
sauqi.abida tace abu na farko dana keso ki
riqe a rayuwarki itace addu'a idan kika
yawaita addu'a akan dukkan lamuranki zaki
ci nasara Aisha ta gyada kai tace ina addu'a
sosai ma kuwa abida tace wannan ta
musamman ce a tsakaninki da shuraim ki
roqi Allah ya zabar muku abinda da yafi
alkhairi amma ke alkhairin wajenki shine ki
sami soyayyarsa tunda kina sonsa,babu
hijabi tsakanin ubangiji da bawansa ki roqi
duk abunda kike nema a dunia da lahira
idan dai halak ne ki zayyano masa duk
yadda kike so babu kunya Allah mai karbar
addu'a ne idan kika riqe addu'a ki yarda
Allah zai amsa miki kin cika abu daya.Aisha
ta gyada kai naji menene na 2?
Abida tayi ajiyar zucia tace abu na 2 da zaki
riqe bayan addu'a shine kizama mai
tsananin haquri sai mai haquri ne yake cin
ribar rayuwa ki daure ki jure duk abunda
zaki gani haka duk nisan lokacin da za'a
dauka ki daure kada ki qagu ko ki girgiza ko
ki razana ba'a yiwa Allah dole kuma
gaggawa daga shaidan take ma'ana duk
tsawon lakacin da za'a dauka kafin shuraim
ya karkato gareki kada ki gaji kiyi fushi kice
kin haqura.sai na 3 shine ki riqe
mutumcinki. Kada ki fito da maitarki fili ya
gane halin da kike ciki na sonsa ma'ana kaja
ajinki.Aisha ya yamutse fuska alamar nuna
rashin fahimtarta a fili abida tayi murmushi
tace zaki fahimce sai a hankali.farida ta
tashi zaune ta dubi abida zuciyatra cike da
quna tace aunty abinda kina nufin inyi ta
bin shuraim ina zubar da ajina yana
wulaqantani shine haquri? idan ba haka ba
yaushe shuraim yasan dani balle yasan ina
haquri dashi wata rana yaso ni?kin kasa
gane waye shuraim idan ba office muka je
ba bama ganinsa abun da ya fiye min sauqi
shine na rabu dashi ni yanzu ko a hanya ma
bana so mu hadu bawai na tsane shi bane
ko yayimun wani laifi aa ko kadan bana
zarginsa don bai ma san abun da anke yi ba
sai dai don na samarwa zuciya ta
salama.abida ta girgiza kai ai wannan itace
juriyar da haqurin da nake kiyi ki taka inda
yake ki ganshi ya ganki sannan kija masa aji
Aisha taji tamkar abida ta dora mata dunia
akanta don nauyin da kanta yayi taji
hawayen takaici ya tsatsafo mata ta girgiza
kai tace aunty abida zancen jan aji kuma a
nan in har naje inda yake? ai na sayi
wulaqanci da kudina abida tayi murmushi
tasa gefen hannunta ta gogewa farida
hawaye tace ki biyo ni a sannu a hankali
zaki fahimce ni kuma zaki ga canji a wajen
dr shuraim insha'allah ke dai kija mu je ki
riqe matakan 3 addu'a.haquri da riqe
mutunci.farida ta koma ta kwanta akan
cinyar abida a sanyaye yayin da hawaye
yayi ta zuba ta tuna mata abinda taci gaba
dayi mata tsifa tana zayyano mata dadadan
kalamai game da yadda zata sami shuraim
idan har zata riqe addu'a zata riqi
haquri.Aisha farida tana yin duk abun da
abida ta shawarceta ta duqufa da yin addu'a
safe da rana harda tsakar dare dama can ita
gwanar yin addu'a ce tana da juriyar yin
addu'a sai dai lokacin taji a ranta kamar
abun ba zai yiwu ba bata lokacinta kawai
takeyi sai ta tuno abubuwan da abida ta
fada mata cewar ta roqi Allah duka abinda
take so kada ta boye babu hijabi tsakanin
bawa da ubangijinsa sai taci gaba dayi bata
gajiyawa.tafi ambaton Allah kasan ina son
shuraim idan da alkhairi shima ya soni.
A CIKIN ASIBITI Aisha farida ce ke zaune
akan wata doguwar kujera tana jiran
matron maryam ta fito daga duba mara
lafiya a babban dakin mata, zata bata sakon
data aike ta ta karbo. Duk da ita ma daliba
ce zata iya shiga, amma security ta hanata
wucewa tace sai dai ta jira anan kasancewar
shugaban asibitin aminu kano ne yake
zagaye. Don haka manyan likitoci sai
tururuwar wucewa ciki suke yi. Tana zaune
tana jira har ranta ya fara baci, don ba don
sakon nan ba da babu abinda zai rabota da
karatunta, ita yanzu bata so a wuce ta koda
dakika daya ne. Taji tamkar ta barwa
security sakon inta fito ta bata, sai ta tuna
zai iya bata kuma sakon yana da
muhimmanci, don ba dan faridar ba ma da
matron ta yadda da ita babu wacce zata
aika ta karbo mata. Kudi ne da wasika ta
karbo mata daga wajen matron aisha, a
dakin 'yan awo. Aisha farida taja dogon
tsaki sannan ta harari security din da ta
jawo mata wannan dogon bata lokacin,
sannan ta duba agogon dake daure a
tsintsiyar hannunta. Karfe goma da rabi na
safe daidai, ta daga ido zata kalli kofar dakin
da matron ke ciki. Kicibus idanuwanta
sukayi da abin da ya gigitata har sai ta
zuciyarta ta daki allon kirjinta don firgici.
Bata manta da ambaton innalillahi wainna
ilaihi rajiun ba, yayin da ta daure bata nuna
razanar da tayi a fili ba. Dr shuraim ne ya
tunkaro inda take a zaune, yana tafe
tamkar dawisu, cikin kyakkyawar shigarsa
wato bakar suit, hannunsa rungume da file.
Kallo daya tayi masa tayi saurin dauke
idanuwanta, haka nan da nan ta kawar da
fuskarta gefe daban, ko da ya karaso
saitinta sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta
kasa har ya wuce bata dago ba. Wucewarsa
ba dadewa sai taji wata sassanyar murya
wata mata tayi mata sallama, da ta daga kai
ta dubi matar sai taga wata zankadediyar ce
fara sol, doguwa 'yar gayun gaske, mai
kamshi na alfarma. Gefenta kuwa wata 'yar
budrwa ce ke goye da yaro a baya, da
alama dai mai aikinta ce ke goye da danta.
Aisha farida tayi murmushi gami da amsa
mata sallamar. Ta zauna kusa da aisha
farida, sannan ta umarci mai aikinta ma
tazo ta zauna, yayin da ta dubi aisha farida
ta gaishe ta hade da tambayarta. Sai dai
fargabar da farida ke ciki ta sake karuwa,
don wannan zankadediyar matar dr
shureiim take tambayarta. Aisha farida tayi
sauri ta girgiza kai tace a'a bansan shi ba,
sai dai ki tambayi security, nasan dai duk
manyan likitoci suna ciki.
Sai matar tace ai naga kamar security din
nan bata da mutunci, bari kawai in kira shi
a waya, da zan fito daga gida munyi waya
yace min yana nan female medical ward,
naga kuma ba a bari a shiga. Ta jawo
wayarta sabuwa dal kirar blackberry ta
matso sunan dr shureim idanuwan aisha
farida na kai yayin da taci gaba da zazzare
ido tana tunane tunane kala kala daban a
ranta. Shin wannan wacece take neman
abin kaunata? Toko matarsa ce? Cikin
harshen turanci tayi masa magana tace
faridarka ce ina nan female medical ward,
an hana ni shiga. Aisha farida ta maimaita a
zuciyarta. Faridah! Faridah!! Daman yana
da wata farida bayan ni? Lallai abida tana
so ta kaini ta baro ni, domin wahala kawai
zansha babu alamar nasara a nan. Sai ta
tuna da abubuwan da abida tace cewar tayi
addua kuma tayi hakuri. Farida ce ta katse
tunanin da aisha farida keyi, ta dube ta tace
gashi nan zuwa ashe, baya ciki ya dan fita.
Aisha farida ta gyada kai tace okay! Matar
ta sake duban aisha farida tace yaya na
ganki a nan zaune, ke ba ma'aikaciya bace,
ko wani kike jira? Aisha farida tayi
murmushi tace wata matron nake jira, ta
shiga ciki aini daliba ce. Security ta hana ni
shiga. Kuma dai yau ne ake hana mu shiga
shima saboda shugaban asibitin yana
zagaye.
Haj farida tace toh shiyasa naga duk an
koro 'yan zaman jinya a waje? Alla dai Ya ba
wa kowa lafiya. Nima wallahi yarona na
kawo bashi da lafiya, kwana yayi zazzabi
kuma ga amai. Aisha farida tace
subhanallah, ko hakori ne? Haj farida tace
anya kuwa hakori ne? Bana jin hakori ne,
don ya gama hakoransa, shekarunsa fa biyu
da rabi, don kin ganshi a baya ne kamar
jariri. Ina ga canjin yanayi ne, kinsan sauron
kasar nan. Aisha farida ta gyara zama tace
daga wacce kasa kukazo? Haj farida tace
daga london, ai can nake aure. Nan da nan
jijiyoyin jikin aisha farida suka rike, ta kasa
cewa komai, babu makawa itace matar dr.
To amma sai dai in 'ya'yan nasa guda biyu
ne babbar mace ce, kuma tayi wayo don
tana amsa waya radau. Cikin sanyin murya
aisha farida ta tambaya shi kadai ne danki,
ko akwai wasu? Haj farida tayi murmushi
tace akwai yayarsu na baro ta a gida.
Tabbas matar dr ce wannan, amma Allah
yayi kyau da gayu a nan. Ai ruwa ma ba
sa'an kwando bane, ina ni ina jera kishi da
wadannan mata masu shigen kama da
matan hurul ain? Aisha farida ta fada a
ranta.
Taji gaba daya bata da sauran wani tunani,
kuma tasan shuraim yayi mata nisa. Rashin
sanin shuraim na hakika ne abida take
wannan daddagwar tana cewa sai anyi. Haj
farida ta dubi aisha tayi murmushi tace
yaya sunanki? Aisha farida tayi jim kadan,
can tace sunana farida. Wow! What a
coincidence is that? Sunanmu daya ai nima
farida sunanan. Matar ta fada yayin da
takeyin dariya, fararan hakoranta suka dau
walkiya. Aisha farida ma tayi dariya tace oh
haka ne kuma naji sanda kina waya kin fadi
sunanki. Yaya sunan yaronki? Tace rislan.
Aisha farida ta gyada kai tace rislan suna
mai dadi, yaya sunan yayarsa ta gida? Tace
sunan mamanmu ne aka saka. Aisha amma
muna kiranta da momi. Aisha farida tace
Allah Ya raya su. Haj farida tace amin.
Yawwa ga dr shuraim nan zuwa. Aisha
farida tahi wuyanta ya sage, har ba zata iya
juyawa ta dubi bangaren da ya taho ba, don
haka can gefe ta juyar da kanta har ya
karaso gabansu ya tsaya. Kamshin turaren
jikinsa mai sanyi shine ya daki hancin aisha
farida, yayin da tattausar muryrasa da
hadadden turancinsa yake ta dukan dodon
kunnuwanta a inda aka hau dambe tsakanin
zuciyarta da idanuwanta, idanu suka su juya
su kalle shi, yayin da zuciyar ke son kallon
abin da take kauna. Idanu suka rinjayi
zuciyar aisha farida taki dagowa ta kalle shi
Me yake damun dana ne? Oh my God rislan
ciwo ne ya taba min kai? Inji dr shuraim a
lokacin da yake shafa kan rislan. Haj farida
tace jiyya bamuyi bacci ba wallahi, sai naji
kamar yau in yanki ticket in juya london. Dr
shuraim yayi murmushi yace no kar ki
damu, mu nan asibitin muna da kwararrun
likitocin yara, bari in kira kawata dr
rukayya. Ya dauko hadaddiyar wayarsa kirar
blackberry ya matso sunan dr rukayya ya
fara da sallama, sannan ya gabatar da
kansa. Yace dr shuraim imran ne yake
magana, nasan baki san wannan layin nawa
ba ko don sabo ne? Dr rukayya tayi
murmushi tace ai kowa ya sanka da canje
canjen layi kullum. Ya aiki? Dr shuraim yace
alhmdlh, dama ina so in turo miki patient
dinku, sister tace farida imran yaronta bashi
da lafiya nake so ki duba shi, duk wani
taimako da ya kama kiyi musu. Dafatan dai
kina cikin asibitin? Dr rukayya tace haba
meya abin yi min magiya, kanwar ka ai
kanwata ce, to ka turo ta razo ina nan
speciality yanzu. Dr shuraim yace nagode,
gata nan zuwa. Sannan ya kashe wayar ya
mayar aljihunsa
DUK KYAN TAKALMI 2* 5
Aisha farida taji wani irin sanyi a ranta da
Allah Ya sa kanwarsa ce ba matarsa ba, sai
a lokacin kamanninsu suka bayyana. Tabbas
kamarsu daya tamkar an tsaga kara. Har
yanzu bata kallonsa ta juyar da kanta can
gefe, amma fa kunnuwanta radau a bude
tana sauraronsu. Dr shuraim ya dubi 'yar
uwarsa yayi murmushi yace kinga ni yanzu
ina tsakiyar aiki, bari in samo wacce zata
raka ku speciality don nasan baki san kan
asibitin nan ba, da sai in kwatanta miki,
kuma ma da nisa. Ya dade yana kallon aisha
farida, sai taji a jikinta kamar ana kallonta,
tana dago ido sai suka hada ido dashi, nan
da nan ta bata fuska, har da murguda baki,
ta kawar da kanta gefe, don kada ma yaga
fuskar aikenta. Shima yayi saurin dauke
idanuwansa daga kanta ya bata fuska, ya
juya ya nufi wani office ba jimawa ya fito
tare da wata daliba likita na biye dashi a
baya. Suka iso inda aisha farida ke zaune.
Haj farida kuwa sai takalo aisha farida
takeyi da hira, yayin da ita kuwa bata cikin
hayyacinta. Dr shuraim ya kade mata
hankali gaba daya ta rasa me yake
damunta, sai da ta sake ganinsa ta tabbatar
har yanzu sonsa na nan dankare a zuciyarta
sai taji haushin zuciyarta da take jawo mata
masifa iri iri.
Dr shuraim yace ga dr zainab dalibata ce
zata raka ku, kuma zata tsaya ki gama
komai, sannan ta dawo. Dr zainab farin ciki
fal a zuciyarta fara'a cike a fuskarta saboda
yau dr shuraim ya kula ta har ya zabe ta ta
raka kanwarsa, don haka ji take tafi kowa
samun shiga. Tayi sauri ta duka ta gaishe da
haj farida yayin da ta hau shafa kan rislan
tana ta faman iyayi. Tanayi tana satar kallon
dr shuraim, shi kuwa gogan abin da yafi
tsana kenan, irin wannan shishigin sai ya
fara bata fuska. Aisha farida tayi murmushi
a zuci tace a ranta wayyo zainab ina
tausaya miki indai dr shuraim ne zaki hadu
da tsagewar zuciya bama bugun zuciya ba.
Muma nan munyi mun warke. Haj farida da
mai aikinta suka mike suka dunguma suka
fara tafiya har haj farida ta wuce sai ta tuna
ba tayiwa aisha farida sallama ba, sai ta
waiwayo da sauri. Tace af kawata,
takawarata na tafi ko, sai Allah Ya kara sada
mu da alkhairi. Aisha farida ta dube ta, tayi
dan murmushi ta gyada kai. Tace yawwa sai
anjima Allah ya sadamu da alkhairi, Allah Ya
bashi lafiya. Yayin da dr shuraim ya dubi
kanwarsa ya juya ya dubi aisha farida da
alama yana mamaki kuma daga dukkan
alamu akwai alamomin tambaya a tattatre
da bakinsa. Abin da kunnen aisha farida ya
jiyo mata bayan sun juya suna tafiya shine
ya dubi kanwarsa yace a ina kika san
wannan yarinyar har ta zama kawarki, kuma
takwararki? Haj farida tayi murmushi tace a
nan na santa, yanzu ma na taba ganinta a
duniya. Dr shuraim yayi dariya ya girgiza kai
yace hmm mata, akwai kwashe kwashe,
daga dan zaman da kukayi tare shikenan
har kunsan juna, har da dogayen lanarai da
sanin sunan juna. Suna ta maganar har
sukayi nisa ta daina jiyo abin da suke cewa
Aisha farida tayi ajiyar zuciya yayin da farin
ciki ya rufeta, tasan dr shuraim yanzu ya
santa duk inda suka hadu zai shaida
fuskarta sannan zai tuna da sunanta tunda
dai ba zai mance sunan kanwarsa ba uwa
daya uba daya ba. Ko ba komai aisha farida
taci riba tunda har ya damu yake yi wa
kanwarsa tammbayoyi akanta. Ta fara Allah
Allah a tashi daga asibiti taje gida ta bawa
abida labrin cigaban da aka fara
samu......bata gama tunanin da takeyi ba
taji karan takalmi ana tahowa a baranda, ko
da ta daga ido dr shuraim imran ta hango
yana tahowa. Kallo daya tayi masa sai tayi
sauri ta kawar da kai gefe, sai da ya wuce
ta sai ta sake juyar da kai wani bangaren ta
rantse shi dinne dai ba zata kalla ba. Abin
mamaki sai taga ya wuce yana kallonta har
da waiwaye. Don son ya gasgata abun da
yake gani, sai ya dawo ya sake wucewa ta
gabanta, wannan karon ma can gefe ta
muskuta bayan kan ma har da jikinta ta juya
ta nuno masa keya. Ya fice ya sake
dawowa, sai yaga ta juya daya bangaren
gaba dayanta. Tabbas ya shaida dashi take
ba zata kalle shi ba. Baifi minti uku da
shiga ba dakin marasa lafiya ba, sai gashi ya
fito a karo na uku yana ta waya, amma fa
yanayi yana duban aisha farida donya ga
abun da zata yi. Sai tayi saurin dangwafar
da kanta kasa ba ta dago ba har ya wuce
waje, iyakacinsa kan baranda yaje ya dawo
har yanzu wayar yake yi, da alama da
kanwarsa farida suke magana tana wajen
likita. Bata dago ba, sai da ta tabbatar ya
shige babban dakin kwanciya na mata. Sai
mamaki ya rufe aisha farida matukar
mamaki kuwa. Wato ashe rububin nan da
mata sukeyi a kansa da kallonsa, da
shishige masa dadi yake ji kenan? Da
gangan yake basarwa yasan ana sonsa
kenan, ai ga shi yanzu bai ji dadi da ta share
shi ba, tabbas ya bata satar amsa ya hadu
da shariya sai ta rama duk abubuwan da
yayi mata, inyaso ta rabu dashi daman ta
fitar da ran samunsa. Bata gama tunanin da
takeyi bi sai ta tsinkayo shi ya fito shi da
matron maryam suna tafe suna magana har
da kyakyata dariya. Dariyarsa tana tayarwa
da aisha farida hankali, saboda sai yayi
dariya kyawunsa yake kara bayyana.
Aisha farida ta mike tsaye a nutse tana
duban Matron maryam ita kadai, yayin da
suka tunkaro inda take tsaye. Bai kalle ta
ba, haka itama. Matron maryam ta dafa
kafadarta tace Allah sarki 'ya ta yi hakuri na
zaunar dake ko? Ina so in fito aka tsayar
dani ai munyi waya da ita tace ba ta baki
sakon ma yana nan waje shima yazo tun
dazu, gezawa zai kai. Wannan shiriirta tawa
dai Allah Ya shirya na barku ku biyu kuna
jira, ke baki sanshi ba shi bai sanki ba balle
ince ki bashi. Gashi baki da waya da na baki
lambarsa, dole dai sai nazo.
aisha farida tayi murmushi tace babu komai
matron. Ta duka cikin ladabi ta mika mata
'yar karamar ambulan din. Matron maryam
ta karba tayi godiya fuskarta cike da fara'a.
Dr shuraim na tsaue a gefe hannayensa
dukka biyi na cikin aljihun wandonsa kansa
a sunkye a kasa bai cika kallonsu ba, yayin
da aisha farida take gaggawar barin wajen,
matron kuwa sai tsayar da ita take tana
damunta da surutai barkatai. Dr shuraim ya
dubi agogon dake hannunsa ya huya ya
dubi matron yace sister maryam zan koma
ciki, zamu hadu anjima, kinsan ina duba
patient. Tsaya tsaya kanina, gara mu gama
magana don idan ka zille min bansan sanda
zan sake nemo ka ba, da gaske nake ni da
mijina muna neman visa london ya za'ayi
kenan? Aisha faroda ta samu ta sulale ta
barsu nan a tsaye suna magana. Tana tafe
tana mamakin wannan kyauta da Allah yayi
mata a yau, Ya jeho mata sahibinta ta
ganshi har ta gaji sabanin da, da sai ta yini
tana zagaye bata ganshi ba.
Tabbas abida tayi gaskiya, babu abinda yafi
irin ka daga hannu ka roki Allah abinda kake
so, zai biya maka bukatunka cikin gaggawa.
Ta kudiri niyyar zagewa ta lullunka yin
addua fiye da yadda take yi a baya. Ta isa
wajen 'yan ajinsu sunyi aiki yadda ya
kamata, har zuwa lokacin tashinsu, kowa ya
lura yau aisha farida tana cikin walwala har
ma wasu na tambayarta meyasa take
murna yau. Da ta isa gida tun daga tsakar
gida abida ta lura da yawan fara'arta don
haka sai tabi ta cikin daki tana tambayarta.
Lafiya meya faru yau naga kina ta fara'a? Ko
aisha farida bata fada ba, abida ta canki
daidai cewa tayi nasan dr shuraim ne ya
saka ki walwala yau. Aisha farida ta kwashe
da dariya ta gyara zama ta zayyane mata
duk abubuwan da suka faru a yau.
Tambayar da farida ta furta itace anty
meye abunyi a nan gaba? Abida har kamar
tafi farida farin ciki, sai tayi dariya tace ki
zuba min ido gobe ni nasan abin da zanyi
masa. Mamaki mara iyaka zaka iya gani
daga idanuwan farida, zatayi tambaya abida
ta katse ta, tace kada ki tambayeni, ki saka
min ido kawai. Allah Ya kaimu gobe. Asuba
ta gari AISHA SHURAIM!!!
Washe gari da asuba kiran farko aisha farida
ta bude ido, abin mamaki sai ta dinga jin
motsi a kofar dakinta. Ta kame a kwance
sannnan dai ta tabbatar ba aljanu bane,
haka ba bakin dare bane wato barayi.
Motsin abida ne don ta jiyo tarinta. Aisha
farida ta cika da mamaki me ya fito da
abida ne daidai wannan lokaci? Shine me
takeyi a waje ta dade haka? Aisha farida ta
mike a hankali tana sanda taje ta tura
window ta leka duhu kirin tsakar gida,
amma da hasken fitilar kwai a gaba abida,
tana gaban murhu tana dahuwa. Sai
mamaki ya sake lullube zuciyar aisha farida.
Ta ambaci sunan abida atsorace a hankali
cikin rada. Nan da nan abida ta dago ido ta
dubi window tayi murmushi tace farida
tsoro kika ji? Kada ki firgita nice dahuwa
nakeyi. Aisha farida ta maimata dahuwa?
Me kike dafawa da tsakar daren nan? Abida
tayi dariya tace asuba ce ai yanzu, idan ya
dahu zaki gani. Tayi wuf ta bude kofa ta fito
tana kokarin bude tukunyar don taga abin
da ake dafawa. Abida ta rike mata hannun.
Tace idan ya dahu da safe zaki gani, abincin
mijina ne. Aisha farida tace bulaguro zaiyi?
Abida tace eh. Aisha farida tace ina zaije?
Abida tace lagos. Aisha farida tace zai bi ta
shagamu? Abida tace ba lallai bane don
daga ofis zasu tafi. Aisha farida tace zai
dade ne? Abida tace zai kwana biyu, kina da
sako ne a fada masa? Aisha farida tace a'a
zan so muyi sallamai dai kafin ya tafi
saboda halin tafiya. Abida tace kada ki
damu zan masa magana kafin ya fita sai
kuyi sallama. Aisha farida tayi murmushi
tace anti bari nayi alwala inyi nafilfili kafin a
kira assalatu, sai inzo inci dadi, ina jin dai
kaje ne ake rababbaka mana. Abida tayi
dariya ba tare da ta bata amsa ba. Doguwar
sujjada aisha darida keyi tana ta addua tana
kai kukanta wajen Ubangijinta Ya bata abin
da take so wato dr shureim idan har shine
mafi alkhairi a gare ta. Idan kuwa babu
alkhairi tana rokon Allah Ya yaye maata
sonsa Ya bata wanda ya fishi alkhairi. Sai
taji hawaye yana surnanowa daga
idanuwanta, don tana tausayawa kanta da
kanta, halin da ta tsunduma na soyayya.
Ba ta bar kan tabarmar sallarta ba sai bayan
datayi raka'atanil fijr da kuma sallar asuba,
ta tofa adduoi a tafin hannunta ta shafa a
fuska sannan ta mike zuciyarta cike da farin
ciki tana da tabbacin Allah Ya amshi
adduointa. Don shi kadai ne mai bayarwa
wahidul kahharu. Daga nan sai ta shiga cuku
cukun yin wanka da shiryawa saboda tafiya
asibiti. Kafin ta kammala gari ya waye
wasai, sai ga abida dauke da dan faranta da
cokali a ciki ta mikawa farida. Aisha farida
ta karba da sauri cike da mamaki, sai ta
duba taga ai dambun shinkafa ne ya sha
zogale da gyada, ya tiraru kuwa sai kamshi
yake yana hayaki, da zafinsa kau. Ta koma
ta zauna ta dandana, sai taji zakwai ya sha
maggi da gishiri, ga dan yaji yaji sabida
attaruhu da albasar da aka yayyanka yiri yiri
a ciki, aka turara dasu sai kamshi yake
tashi, hade da kamshin man gyada ziryan.
Aisha farida ta girgiza kai ta sosa kunne
tace tunda Allah Ya halicce ni ban taba cin
dambu mai dadi irim wannan dambun ba.
Lallai yaya yana cabawa irin wannan
haduwa haka? Abida dai na tsaye a kanta
murmushi kawai take yi bata ce komai ba
har yanzu yayin da aisha farida ke faman
turawa a cikinta tana ta santi.
Aisha farida ta dagi ido ta dubi abida tace
abin mamaki kuma dambu da aka sanshi da
shakewa mutum makogoro sai gashi
wannan dambun baya shake mutum silif
silif yake wucewa. Wai, yaushe rabon in
karya kumallo a gida, lallai yau zanfi jin
dadin aiki don cikina yayi nauyi. Allah dai ya
saka da alkhairi, Yaya hussani yayi sa'ar
mata. Da dambun zai tafi a cikin food flask
su dinga ci a hanya? Abida ta fita bakin
kofa, sai ga tata shigo riki riki dauke da dan
kwandon roba mai marika, irin wanda ake
saka flask din abinci. Aisha farida tace lallai
haduwa irin wannan sabon food flask haka?
Yau aka bude shi daga leda duk saboda
yayana tabbas babu mu babu kara aure.
Abida tayi dariya tace bude ma kiga yadda
aka shirya ciki. Aisha farida ta jawo
kwandon ta daga wani babban hankici sakin
ulu, wanda dashi aka lullube saman. Ta zaro
wani dallelan flask mai madaidaicin girma,
tsaka tsaki karkashinsa kuwa farantai biyu
ne na tangaran da babban cokalin diba
wato serving spoon da cokula biyu
dukkansu sababbi ne filfil a wanke tas tas.
Aisha farida ta gyada kai tace lallai wannan
kwandon abin sha'awa ne tun kafin na
bude ma abinda yake ciki. Abida tace bude
mana ki gani. Aisha farida tayi bismillah ta
bude, tana budewa sai wani kamshi ya daki
hancinansu. Aisha farida tace humm lallai
abin ma son kaine ko anty, ashe har da
hanta da koda aka yayyanka a ciki shine ba
a sako min bako daya sai maigida aka
tulawa gasu nan burjik a ciki.
DUK KYAN TAKALMI 2* 7
Abida tace me kika yi masa haka a rayuwa
da zai tsane ki? Ba zai tsane ki ba, saboda
kin riga kin kai kararsa wajen mahaliccinsa,
zan sake baki wasu adduoi masu zafi
wadanda suke kara soyayya da tausasa
zuciyar wanda kake so. Idan kina karanta su
hakika dole yaji yana sonki sosai. Adduar
itace "Allahumma ya mukallibul kulubi
wamusarrafuha kaifa ya sha'u usaibarul
muhabbati fi kalbi (ambaton suna) bi hakki
ismikal wadudu Ya wadudu. Ya wadudu sai
dubu daya da dari daya da goma sha daya.
Kiyi tayi kullum har zuwa lokacin da zai
sanke kece mai dambu sai ya hadu da
kaunar dambun da aikin wanna adduar su
fara aiki. Ni kuma a lokacin zan fada miki
abu na hudu da zaki rike nan gaba, kinsan
yanzu uku na fada miki shine ADDUA,
HAKURI da RIKE MUTUNCI. Bazan fadi na
hudun ba, sai a lokacin da kika tabbatar min
ya gama saninki. Idan ya ganki a ko ina zai
shaidaki, zai kira sunanki, zaiyi miki
murmushi, zaki gaishe shi ya amsa cikin
farin ciki, to sai na jeho miki makami na
hudu wato taryo soyayyarsa. Aisha farida ta
lumshe ido don dadi tace kamar a mafarki
nake jina. Sai nake jin bayaninki kamar na
samu shuraim na gama. Abida tace shi yasa
ake so mutum ya rike Allah, Shi zai biya
masa bukatunsa banda bin boka ba ko 'yan
bori. Shiyasa mata muka fi yawa a wuta,
saboda karamin tunaninsu da gaggawa.
Gaggawa kuma daga shaidan take, yanzu da
kika riki Allah zaki ga yadda Allah zai
taimake ki, ko baki samu shuraim ba zai
musanya miki da wanda ya fishi, kuma zai
tanadar miki babban rabo a lahira. Aisha
farida ta gyada kai tace haka ne. Allah Ya sa
mu dace, wadanda suka bata irin su Ummi
Allah Ya ganar dasu gaskiya. Abida tace
amin. Ci abinci ki fita kije ki cefano min
kayan dambu. Asuba ta gari AISHA
SHURAIM!!
Washe gari aisha farida tayi sammakon
zuwa ofishin dr lukman tayi sa'a kuwa tana
isowa kamar tare suka zo, shima yazo yana
bude ofis dinsa, don haka sai suka dunguma
suka shiga tare. Ta gaishe shi ta ajiye katon
kwandon mai dauke da katon food flask din
abinci, babban na jiya ne da farantai hudu
da cokula hudu. Dr lukman yayi murna da
ganin dambu kuma yayi godiya. Yau ma yayi
kokarin bata kudin taki karba, tayi gaggawar
fita daga ofishin ta rufo masa kofa. Misalin
karfe uku da rabi ta koma ofishin ta iske
ofishin a kulle baya nan, amma ta jiyo
muryarsa a ofishin dr shuraim, don haka sai
ta sadada ta bar wajen. Ta dade a labe tana
hango kofar ofishin ko zai fito bai fito ba,
sai ta hakura ta tafi gida. Yau dai bata
walwala sosai, don bata jiyo sakamakon
jarabwar dahuwar dambu ba. Shin gogan
nata yaci koma bai ci ba? Ya yaba ko ma bai
yaba ba? Data fadawa abida sai tayi dariya
tace ai ya ci ma kawai tunda kika jiyo
muryar dr lukman a ofishinsa suna tare,
babu yadda za'ayi yaga dambun yaki ci.
Aisha farida tace ya za'ayi kuma gobe?
Abida tace dan wake zanyi musu ki kai
musu tunda shuraim yana son dan wake.
Aisha farida tace a'a kada ayi, ki bari dai a
kwana biyu kada lukman din ya zargi wani
abu, ko yaji tsoro. Abida tayi darriya tace
tsoron me? Idan kika kai musu dan waken
kika dauko duka food flask dinn sai muyi
shiru muji abinda zasu ce, kuma muji
wanne suka fiso, suka fi jin dadinsa. Sai mu
dinga yi musu shi. Aisha farida tace ni sai
nake ganin kamar duk ba zai damu da sai
yasan waye yake dahowa ba, balle ya
sanni. Abida tayi murmushi tace kin manta
abinda nake fada miki, ki zama mai hakuri
duk mahakurci shi yake cin riba.
Aisha farida ta jinjina kai tace haka ne,
shikenan zanci gaba da hakuri. Abida tace
yawwa tashi muje mu daka yaji mai dadin
gaske yadda zasuji dadin danwaken sosai.
Sai ki siyo tumatur, albasa, kokunba duk a
yayyanka musu a ciki. Aisha farida tayi
dariya tace har naji yawuna ya tsinke,
gaskiya danwaken nan zaiyi dadi, zaiso shi.
Rana ta uku ranar alhamis kenan kamar
kullum da sassafe aisha farida ke fitowa
daga gida tana fin kowa sammako. Tayi jira
fiye da awa biyu sannan dr lukman ya iso.
Sai da ya jima da shiga sannan tabi
bayansa. Yayi farin ciki da ganinta, sai dai
yayi matukar mamaki da jin dadi da ya ga
ta sake dire masa wani kwandon abinci a
gabansa. Yace lafiya, meye wannan kuma?
Dama kin dauki kwandon jiya? Ta girgiza kai
tace nazo baka nan sai na wuce gida kawai.
Wannan wani ne na kawo muku, wannan
karon ba dambu bane, wani launin abincin
gargajiyar ne. Dr lukman yace a'a 'yar
shagamu kinaso muyi fada ko? Yaya zaki
tayi mana wahala, kartai muna taruwa
muna cinyewa babu ko sinsinmu? To
gaskiya bazan karbi wannan ba, ki koma
dashi gida, ko ajiyar ma bazan yi ba. Aisha
farida tayi dariya tace yi hakuri yayana,
daga yau shikenan. Yace kwanukan jiya
suna ofishin dr shuraim, kuma bana jin yazo
yanzu, don bai cika zuwa da wuri ba. Ina da
mukullin ofishinsa bari in bude in dauko
miki kwandon da farantai da cokulan,
amma ainahin food flask din ta tafi dashi
gida, dambun jiya yayi dadi sosai, har yafi
na shekaran jiya. Sai yace dole ya kai wa
babansa yaci yaji irinsa, donshi ya koya
masa cin dambu. To wallahi kinji yadda
akayi, sai anjima zai zo zan ma sake yi masa
waya kada ya mance dashi a gida, lallai lallai
ya taho dashi. Tuni farin ciki ya cika zuciyar
aisha farida, taji tamkar ta daka tsalle don
murna. Tayi dariya tace ba koma dr ai ko
food flask dinnan ba yanzu zan dauka ba,
sai da yamma. Yanzu aji zan tafi. Sukayi
sallama aisha farida ta tafi, kowannensu na
farin ciki.
La'asar sakaliya Aisha ta tunkaro ofishin dr
lukman saita hango gogan nata yana shige
da fice tsakanin wannan ofishin zuwa
wancan dauke da wasu fayil don haka saita
diro daga kan barandar ta shige lungu ta
samu waje ta zauna har saida ta ga fitarsa
ya shiga motarsa ya tafi gida bata bari ya
ganta ba.ta tashi cimak ta nufi ofishin dr
lukman hankalinta a kwance baby wata
fargaba dr lukman ta iske shi kadai da
alama shima ya miqe yana shirin tafia gida
yana ganinta yayi dariya yace yar shagamu
gaskia kin iya girki kice daman tun farko a
shagamu na nemi mace ba'a yobe ba
kinsan yadda mukayi santin dan waken nan
dr shuraim har cewa yayi week end zaizo in
kaishi ya gaida kakata mai dambu da dan
wake da yake nace musu itace take daho
min Aisha ta tuntsire da daria tace lallai
kuwa daka zo shagamu an baka mata daka
sha girki mai dadi ya miqo mata
kwandunanta guda 2 yana godia tana godia
suka yi sallama ta tafi tana fitowa bakin get
ta dane acaba sai gida tana mai farin cikin
zuwa sanrwa da abida labari.Abida na
ganinta sai tabi ta daki suka rungume juna
suna murna tun ma kafin abidar taji labarin
abunda ya faru. Aisha tace zauna in baki ki
sha suka zauna Aisha ta zayyana mata suk
abubuwan da suka faru yau tsakaninta da
dr lukman da abunda dr shuraim ya
fada.Abida tayi murna sai ta shiga bubbude
food flask din ta bude na farko saiga kudi
yan 500 sabbi har guda 4 tayi sauri ta bude
daya food falsk saiga yan 1k har guda 3
suma sabbi sai su duka suka bude baki suna
mamakin wannan kudi da suka gani Aisha
tasa hannu a hankali ta debo yan dari biyar
din ta shinshina saita a jiye a gefe ta sake
yan 1k ta shinshina saita lumshe ido tayi
murmushi ta dubi abida tace wadannan
kudin daga dr shuraim suka fito shinshina
kiji qamshin turarensa Abida ta karba da
sauri ta shinshina tace ehmm qamshi farida
har a jikin kudi kike gane qamshin turaren
masoyinki?lallai kin laqanci qamshin
turarensa to shine ya zuba wadannan kudi
kenan dr lukman ya zuba yar dari 500
dinnan daya ga kinki karba?Aisha tayi fari
da ido tace Allah sarki mai karbar addu'a
kalli daki-daki yana koro mana hanyar
haduwa da shuraim a cikin ruwan sanyi
yanzu ga kudinsa ya shigo hannu cikin
hikimar ubangiji sai ta fara kuka Abida tace
kada kiyi kuka kici gaba da dagewa da
addu'a to yanzu kin ga kudin dr
shuraimkinyi kuka ina ga ranar da kika
ganshi kacokan a qofar gidanku yazo zaance
balle ranar da zaki ganshi a dakinki a
matsayin mijinki?sumewa zakiyi kenan don
dadi?Aisha tayi daria tace gobe jumu'a yaya
za'ayi a sake musu ko a bari?abida tace aa
tsahirta gobe jumu'a sai kije ofishin dr
lukman kice doctor ranar litinin me kuke so
a dafo mukudambu ko dan wake kiji
abunda zai zaba saiki zo tun ranar asabar
mu fara aikin hada musu mai dadi da kunun
gyada ko kunun tsamiya zakiyi musu mu
zuba kofuna qanana zasu so shi kinga suma
duk abincin gargajiya ne Aisha tace gaskia
koba a fada ba dr shuraim zai so kunu sosai
shike nan haka za'a yi.Anan dai suka bar
hirar Aisha ta hadawa abida dukka kudin 5k
ta ce ta riqe a wajenta ba sai ta dau ko sisi
ba tunda ita ce take cefanen nan a aljihunta
asuba ta gari farida shuraim.
Khadija sani isma'I'll ce ta duni Aisha tace
wai me yasa kullun idan nace kizo ki rakani
babban daki na maza saiki turje ki tsaya
daga nan kice inje in dawo ba kya son
shiga?Aisha tace babu komai wlh ni dai
kibar ni nan kije ki dawo zan jiraki ko hour
nawa zakiyi khadija tace idan dai bazaki
raka ni ba nima ba zan je ba daman ba
wani abu zanyi ba illa in leqa ta wajen ofis
din kyakyawan likitana dr shuraim musu
mukeyi da mrym kinsan yanzu ta saki ranta
ta daina kishin dani data ga ta rasa nima na
rasa kuma bazamu samu ba mu duka sai
dai in mun hadu muyita labarinsa cewa tayi
yafi kama da larabawa ni kuma nace kyan
indiyawa gare shi shine nake so mubi ta
ofishinsa mu tantan ce nida ke kinjin Aisha
ya ne ya buga bummm!don fargaba nan da
nan taji hankalinta ya tashi tace a ranta
daman har yanzu khadija da maryam basu
daina son abuda nake matuqar so ba? Lallai
ashe akwai hargitsi a nan gaba gara ma dai
kawai in haqura da son mutunmin nan in
hutawa raina abida ce taqi haqura dana cije
na daure na watsar da son koda kuwa
zuciata zata lahanta koda ciwon zucia zai
zama shine ajalina in mutu in huta.sai taji
kwalla ta cika mata ido sai khadija ta
mungure ta sannan ta fara fahimtar
maganar khadija keyi khadija ta kalli farida
tayi murmushi tace kiyi min wannan
taimako yau dai ki raka ni har ofishinsa ba
komai zanyi ba illa in kare masa kallo in
tantance nidai nasan akwai wanda yayi min
kama dashi a film din india Aisha ta fusata
tace shirme kenan haba khadija kamar
wasu yan primary?ki tuna fa jami'a muke
shirin gamawa kuma manyan ma'aikata
muke shirin zama ma'aikatan ma na jinya
masu kula da lafia jama'a wadan ake
girmamawa a al'umma ya kike abu kamar
marar ilimi?kinsan mutumin nan kinsan
halinsa ke za ki fadawa wani irin salo da
launin wulaqancinsa.ke kika cemin min kin
haqura dashi baki yadda kika burge ni ba
har kika umarci muhammad saurayinki ya
kawo kudin aure ya kawo aka saka muku
rana tamkar matar aure kike saboda anyi
miki baiko ma'ana anyi wa wani alqawalin
bambancinki da matar aure kadan ne
mijinki kyakyawa dan gayu mai ilimi babban
ma'aikacin banki da kadan shuraim yafi shi
kyau habah khadija kada kibani kunya mana
ashe har yanzu akwai namijin da zai burge
ki bayan mijinki?kada fa ki zama irin matan
nan da zasu yi aute kuma suna son wasu
mazan a waje babban bala'I ne yin haka
dunia da lahira halaka ce.idan kin san
zuciayarki bata kwanta da auren
muhammad ba gara kada ayi kice kin fasa
kizo mu tayaki yaqin neman soyayyar
wannan dan wulaqancin!kahadija ta tuntsire
daria tace dadina dake Aisha umar akwai
fadar gaskia komai dacinta wlh ko dan
bazan zama daga cikin irin matan nan da
kika zano ba insha'allahu ba zan sake zuwa
ganinsa ba daman sai na manta dashi sai
maryam ta tsokano min zancen itace har
yau bata gama haqura ba Aisha umar ta
kalli barandar can ki gani.
Aisha ta wurga ido da sauri dr shuraim
imran ta hango yana tahowa tafia yake a
tsanake fuskarsa cike da fara'a jama'a suna
ta gaishe shi yana amsawa idonsa ne ya
wurga ya wurgo kansu Aisha farida
wadanda ke tsaye a jikin bishiyar dake kusa
da barandar da yake tafe kai kace ita da
khadija saurayi da budurwa ne suke
zantawa sun fuskanci juna suna tsaye cirko-
cirko babu wanda ya sake magana a cikinsu
yayin da khadija ke kallonsa tana yi masa
murmushi. Aisha kuwa sauri tayi ta juyar da
kanta gefe bata duban bangaren da yake
ma Aisha taji tamkar ta kurma ihu don
takaici tada ji khadija ta maqe murya ta
gaishe shi saii ya amsa cikin farin ciki ya
wuce abinsa sai da yayi nisa khadija ta
zungure ta tace amma bakida kirki kina
ganin malaminki amma kika qi gaishes shi ?
naga alama fa baiji dadin ba da baki gaishe
shi ba Aisha ta tabe baki tace yaya akayi
kika san baiji dadi ba? Khadija tace saboda
naga irin kallon da yake yi miki ne leqen
fuskarki yane tafe yana waiwaye so yake ki
juyo ya ganki Aisha tace ai ba dole ne in
gaishe shi ba tunda in an gaishe shi sai
yaga dama yake amsawa ke rabi ni da
wahala kinji ta kaina nake bani da lokacin
kowa.khadija tace kin huta ai shiyasa kike
burgeni ina son halinki ko bayan idonki ina
fada daman tun farko ma dai naga alamar
kin tsani dr shuraim ko zancensa ba kya ayi
miki Aisha tayi wani lalausan murmushi ta
gyada kai tace me yasa zan tsani musulmi
dan uwana ?aa wlh ban tsane shiba ko
kadan ina sonsa so tamkar raina zai fice
kamar yadda nake son dan uwana na jini
saboda shi ma musilmi ne musulmin ma
mumini mai riqe addini irinsa khadija tayi
doguwar ajiyar zucia ta dauka Aisha ma zata
ce itama ta mato a sonsa yadda itama take
sonsa sai taji farida tayi kwana.suna tafe
suna firarsa har zuwa bangaren da suke
wato wajen masu ciwon hawan jini da
ciwon suga Akan barandar da suke tafe a
nan shuraim ya taho suna daga ido sai suka
hango shi daf dasu shi yana tahowa su suna
tafia sai suka yi gum da bakinsu don birarsa
suke a lokacin dan halak yaqi ambato inji
khadija Aisha ta duqar da kanta qasa bata
sakw dagowa bahar sai daya gifta ya wuce
kamshin jikins ya daki hancinta sai ta
lumshe ido ta fada a zuciayar ya Allah ina
son wannan bawa naka sannu likita sanna
da qoqari kalaman da suka rikito kunnen
Aisha ke nan daga bakin khadija take
fadawa dr shuraim dai-dai sanda yazo
giftawa ya fada cikin qasaita thank u ya
wuce abinsa Aisha farida tafia take kawai
amma tamkar ta hadiyi zucia don jin
haushin barar da ajin da khadija keyia
wajen bawan Allah nan.
Khadija ta zunguri Aisha tace saki dago da
kanki dodon naki ya wuce don naga ko
kallonsa ba kya son yi ikon Allah shi kuwa
sai ya tsura miki iso yayi ta kallonki don
Allah ki dinga gaishe shi bin na gaba fa bin
Allah ne Aisha tayi ajiyar zucia tace Allah
yabamu ikon bin shugabanninmu amma
wadanda suke bin Allah khadija tayi daria
tace shegiya Aisha umar akwai iya magana
nasan baki yarda da abun dana fada miki ba
zaki dinga gaishe shi ba kenan?kin jini ne
dai kawai Aisha tace uhmm kawai take
fadin sai kuma gyada kai take tayi tamkar
kadangaruwar ta kasa cewa komai saboda
ganin dr shuraim dinnan da tayi yau yayi
mummunan fama mata son data keyi masa
Aisha shuraim haquri shine maganin zaman
duniya! Aisha ta cika mamaki a lokacin da
yaro ya leqo dakinta yace tazo wani yana
sallama da ita a qofar gida a motarsa a
zaune ta duba agogo karfe 7:30 na dare ko
isha'I ba'a kira ba yadda take zaune akan
abun sallarta sanye da hijabi da carbi a
hannuta haka tayi zunbur ta miqe tace da
yaron tsaya ni mu tafi tare ka kai ni wajen
mai yin sallamar dani faruk ta gani dan
abida a tsakar gida tace idan mamarka ta
idara salla a kace mata anyi kirana a qofar
gida ina zuwa ya amsa da to aunty Aisha
zaki siyo mun alewa da biscuit?aisha ta
girgiza kai banyi maka wannan alqawalin ba
nima nan daka ganni na dade ban sha
alawaba ta wuce da sauri ita da dan aike ta
kama hannunsa tace yaro a ina mai motar
yake?wayace ka kira?yaron yace a wajen ya
tsaya kafon a hayo sai ya kirani yace inzo
nan gidan nan mai bishiyar dirimi in kira
masa Aisha umar qanwar husaida mijin
abida shine nake ta leqawa ina tambaya har
aka nuna min dakinki mamaki ya sake
lullube farida ta dafe qirji tace inalillahi wa
inna ilaihi raji'un Allah yasa baqon nan
baqon Alkhairi ne toni waye wannan?ba dai
dr lukman bane balle in saka ran dr
shuraim sune kadai nasani a dunia masu
mota su kuwa basu san gidanmu ba haka
yaro yaya suffar mutumin take?yaro yace
dogo ne haka fari mai dan gemu a habarsa
kyakyawa mai kudi motar hadaddiya Aisha
ta juya kawai tana kallon yaron tana
mamakin yadda yake suffanta
mutumin.tabba s suffofin dr shuraim ya
zano mata amma tana tabbacin ba dr
shuraim bane a wanne dalilin ma zata saka
ran dr shuraim zaizo gidansu mutumin da
har yanzu bai game gane taba a hanya balle
wata hulda ta hada su harma ya tako a
qafarsa ya zo inda take don haka ta cire dr
shuraim a tunanin ko shine sai ta koma
sake saqen wasu daban suna tafe fakam-
fakam sai sauri suke zubawa ta sake juyowa
ta dubi yaron tace yaro shi kadai ne koda
macea motar?yace shi kadai ne! Aisha ta
fada a bayyane toni Aisha waye wannan da
akwai mace a motar sai ince khadija ce ta
kawo min mijinta mu gaisa yaro kawo bakin
wata dalleliyar motar qirar BMW baqa
wuliq sabuwa dal!har sheqi take ya ce ga
motar mutumin yana ciki,
Gabanta ya yanke ya fadi daf-daf taja ta cije
ta tsya a gefe tace kwankwasa masa gilashi
kace masa gata ka kira ta don inga ko waye
yaro ya qarasa da sauri ya daddage ya daki
glass kai kace qofar qarfe yake bugawa
lallausan hannu hade da kyakyawar fuskar
dan adamu ne ta fito fili sai gashi ya
bayyana a lokacin da ya sauke gilashin
wundonsa qasa Aisha ta kaikace tana
leqensa daga nesa har yanzu bata gane shi
ba kasancewar akwai duhu wajen duk da
akwai hasken redio motarsa na haska shi
kadan yaron ya dawo wajen farida yace ki
qarasa kinga har yabani N100 Aisha tace
lallai ka caba kaje na gode tafia take a
nutse amma a tsorace kamar ace kulle tace
cas!nauyi kunya fargaba da tsanaanin tsoro
sun gallabe ta ta isa jikin window da yake
zaune ya zuba mata ido yana kallonta
fuskarsa cike da annuri yana nuna farin cikin
da ganinta ta kasa kallonsa saita duqa ta
gaishe shi ya amsa cike da fara'a hadi da
cewa hajia Aisha farida yar shagamu nasan
zakiyi mamakin ganina ko?wannan karon da
sauri ta dago kai ta dubi kyakyawar fuskarsa
domin tana jin muryarsa ta gane ko
wanene tabbasa muryarsa ta tabbatar mata
dashi dinne wanda take zato a lokacin data
dubi fuskarsa.dadi marar misaltuwa suka
tabbata a zucia yar Aisha ta dafe qirji ta
fada cike da mamaki marar adadi barista
mu'azzam yau kaine a gidanmu nayi
matuqar mamaki hade da dinbin farin ciki
dana ganka a gidanmu ka kyauta gaskia
Allah ya bar zumunci yayi daria yace miki
wannan shine zuwana na farko aina sha
zuwa nansai in aika yaro ya dawo yace min.
Ance ba kya nan kai rannan ma ce min kayi
gidan naga wasu maza 3 a zazzaune akan
tabarma suke cemin kina ciki amma
shwararda zasu bani kada in sake dawowa
ba kula zaki yiba haka yayanki ma idan ya
ganni korar kare zaiyi min.na fahimci dai
hassada ce kawai na tafi na barsu yau dai
Allah yasa na sami yaro mai wayo nace ya
shiga ciki ya nemo har. Dakinki ya kirawo ki
amma wanne irin zama kuke da
mutanengidanku haka shin bakwa shiri ne?
sai hawaye ya fara surnanowa a idontaAisha
tana sharbewa da hijabinta barista
mu'azzam ya warwaro toilet paper ya miqa
mata yace aa qanwata kin fara koke -koken
naki ko?bana son kukan nan yanzu zaki
kore ni fa Aisha farida ta goge idanuwanta
tace na daina kuka yayana abun ne yabani
mamaki muna zaune dasu zucia daya muna
qoqarin kyautata musu su basa qaunarmu
ba'a son ci gabanmu ko zaka rufe motar
kazo muje kan dakalin qofar gidan mu
zauna kada in shiga motarka ayi ta
yamudidi dani a unguwa da sharri kala-kala
Alhamdulillah daka san yadda mutanenmu
suke. Barista mu'azzam yace kwarai kuwa
yi gaba zan biyo bayanki kada a ganmu mun
jera muna tafia Aisha tayi sauri ta shiga
gida don dauko sallaya da pure water.
Abida tabi ta daki a gigice tana tambayarta
wai waye yazo a dalleliyar mota ne, naji
matan gidan nan suna ta yamadidi, har
suna aika 'ya'yansu suje su gano musu ke.
Aisha farida ta rike baki tace mun shiga uku
da zaman haya, au faruk ba fada miki sakon
dana bashi ba, nace ana kirana a waje na
tafi. Abida tace bai fada min ba a tsakar
gida nake jiyo gulmar. Kada fa kice min dr
shuraim ne? Aisha farida tace in dr shuraim
ne ba sai mu gudu ba? Bashi bane, barister
muazzam ne. Ta kwashe labarin daya bata
ta fadawa abida, na 'yan hassada. Mamaki
ya rufe abida ita ma sai da tayi kuka. Aisha
farida ta hanzarta daukar sallaya da pure
water guda biyu ta fice da sauri ta iske har
barrister muazzam ya karaso kofar gidan,
kasancewar bayan magriba ne don haka
yawancin mazan gidan duk suna masallatai,
sai anyi sallar ishai zasu dawo. Ta shimfida
akan dogon dakalin mai fadi, sannan ta
umurce shi da ya zauna. Yana zama sai ta
duka ta mika masa pure water ko sanyi
babu, ya karba yayi murmushi yace nagode
ki zauna mana ya zaki tsaya a tsaye, ai ina
ganin akwai tazara a tsakanin mu idan kin
zauna a karshen dakalin, ni ma ina karshe
ba za a ce kinyi rashin kunya ba dai ko? Don
naga alamar unguwar nan taku abar tsoro
ce, suna da saka ido da gulma, koda yake
duk cikin gari haka suke, 'yan gargajiya ne
kawai. Babu maganar wayewa a tattare
dasu.
Aisha farida tayi murmushi ta zauna a
tsorace ta sake gaishe shi, sannan tace yaya
muazzam sai hakuri, bamu da fridge kuma
inda ake sayar da ruwan sanyi babu saboda
munfi sata ba a kawo mana wuta ba, zaka ji
ruwan babu sanyi. Muazzam yayi dariya
yace kada ki damu, yanzun nan na sha ruwa
har roba biyu a mota, na karba ne dai don
kar kiji babu dadi, nagode. Aisha farida tayi
dariya tace a'a nice da godiya, naji dadi da
na ganka, Allah Ya bar zumunci. Ina
abokinka barr nurruddin? Ina baraka
matarsa? Ina kuma matarka dr janan? Barr
muazzam ya kwashe da dariya yace har kin
daura mana aure ne ta zama matata? Duk
suna nan lafiya kamar yadda kika barsu,
babu wanda ya sauya a cikinsu. Nuraddin
yana nan yana taurin kansa, da gallazawa
baraka. Haka itama baraka tana nan tana
hakuri. Ko da yake kwanan nan ta fara ce
min hakurinta ya fara karewa, zata fadawa
magabata a raba auren. Ita kuwa janan
tana nan a daure ana ta tafka sharia babu
wani canji a tsakanina da ita. Iyayenta ne
dai kawai suke ganin kokarina da nake a
kanta, ita har yanzu bana gabanta. Ni har
haushin kaina nake ji wata rana ince to wai
me yasa na nace sai janan bayan a gari ga
'yan mata nan reras wadanda ma suka fi ta
kyau da kwalliya, saboda a yanzu idan kika
ga yadda janan ta koma idan kinsan ta a da
ba zaki ce ita bace, kamar wacce aka sauya
ta gaba daya duk tayi muni, tayi baki, an
aske wannan gashin nata mai tsawo sai
kwas kwas. A ficika wani ba zai dauke ta ba,
amma har yanzu zuciyata bata daina sonta
ba, kuma ita kadai nake so bana son wata.
Wannan al'amaro yana bani tsoro da
mamaki. Aisha farida ta girgiza kai tace
Allah sarki rayuwa, har naji tausayinka.
Wannan shine ake kira soyayyar gaskiya, so
saboda Allah kenan ba don wani abu ba.
K KYAN TAKALMI 2* 9
Dr lukman yace kin tabbata baki gane abin
da yake nufi ba? Kada ki boye min komai.
Aisha farida ta girgiza kai ta zubo da
hawaye da ya cika mata ido tace bansani ba
wallahi. Yace to jeki zanyi miki waya anjima
kada kiyi kuka. Aisha farida ta tashi da sauri
ta fice yayin da dr shuraim ya bi ta da
harara. Tana fita sai ta rufe kofar kuma ta
labe ta dora kunne a jikin kofa tana
sauraronsu. Dr lukman ya juya ya dubi
shuraim yace wai me yake faruwa ne?
Yarinya ce fa kimtsatsiya. Tana bin maza ne
ma'aikata? Dr shuraim yace kaji matsalar ku
kenan, baku da kyakkyawan zato, nan da na
sai ku ballo bala'I. Meya kawo wannan
zargin kuma? Dr lukman ya juya ya dubi dr
mohd yace don Allah dr a kasar hausa idan
aka dubi mace akace ki kama mutunci da
darajarki ta 'ya mace meke nan? Ba 'yar
iska ba kenan? Dr mohd yace kwarai kusa,
kasan bature ne su a london ustazan mata
ake fadawa haka. Suka kwashe da dariya su
dukka, dr shuraim yace uhumm kai kake
ganin hankalin yarinyar na, ai ni tuni nasan
maciji sari ka noke ce. Nafi ku karantar
halayanta. Wato tunda Allah Ya halicce ni a
duniya tsakanin jinsin mace ko namiji ban
taba ganin wacce ta iya hawa acaba irin
wannan yarinyar ba. Sai su dr lukman suka
kwashe da dariya, yayin da dariya ta
kubcewa aisha farida sai tayi sauri ta toshe
bakinta. Dr shuraim ya bata fuska yace ai
ku abin ma dariya ya baku? Wallahi ba abin
dariya bane, ya kamata kayi mata fada.
Hawan jini ne kawai rannan banyi ba,
shekaran jiya ne ma ba adade ba. Caraf
zaka ga ta haye acaba da yake ba nauyi ne
da ita ba, kuma ta kware. Dan acabar nan
ya wulwula da ita suna kallon kudu sai sai
gasu sun juyo arewa ba tare da ya duba ko
ya saka sigina ba, suka rufta kan wasu 'yan
acabar suka tafi tangal tangal kamar zasu
fada kwalbati. Allah Ya kiyaye basu fada ba,
ya tashi hayaki da kara mai tsanani, sannan
ya zuga da gudu kamar zai tashi sama.
Kunsan yarinyar nan ko a jikinta, mutane
babu wanda bai dora hannu a ka ba ya dau
salati don ni sankarewa nayi a zaune wallahi
na dade a daren banyi bacci ba. Dr lukman
yace to don wannan ne ma shine kaki fada
a gabata, kaga ka tayar mata da hankali har
tana kuka.
Dr lukman yace to don wannan ne ma
shine kaki fada a gabanta,kaga ka tayar
mata da hankali har tana kuka. Dr shuraim
yace kukan munafunci ne, tasan abinda
nake nufi ai tana shigowa ta kalli idona ta
dauke kai, tasan na ganta kuma da zata lura
dani tasan na tsani hawan acaba to yadda
kasan tsokanata take yi, ina yawan hango ta
ta dane. Da ace tasan ni ta san ra'ayina
akan tsanar mace ta hau babur da sai ince
da gangan take yi, don inji haushi. To bata
sanni ba, amma tana bani haushi wallahi.
Dr lukman yace ni kuwa yarinyar burge ni
take yi, tana da natsuwa. Dr shuraim yace
tana da hankali amma da ace zata rabu da
hawan acaba da tafi hankali. Aisha farida ta
shafa kirji tayi ajiyar zuciyar jin dadi, ta daga
idonta sama tayi wa Allah godiya, sannan
taci gaba da kasa kunne tana sauraronsu.
Bata damu da mutanen da suke wucewa
suna ta kallonta ba, ko tantama babu sun
san gulma take saurare.
Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin
hankalinta ma idan yau na sanar maka
cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun
nan da danwake wanda kake ci kana santi
kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan
zan fada mata ta daho mana gobe. Shine
daga shigowarta kuka hau yi mata
shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan
duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr
shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana
ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi,
data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr
shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi
dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa
wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata
nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita
baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba,
duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata
karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su
da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau
acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita
sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus
bane. *nxt page din is damaged, bana
ganin rubutun sosai*

Dr shuraim ya ja doguwar ajiyar zuciya yace
Lukman don Allah da gaske kake ita ce ke
dafa ma dambun nan da kanta?dan iska
kace kakarka ce ko kakarku daya ne? Dr L
yayi dariya yace ka taba ganin dangina a
kano balle in yi kaka? wallahi itace ta ke
kawo min da farko ma ajiya ta kawo ta
dahowa kawarta an kwantar da ita anan
asibitin to bata san an sallameta ba nace
mata za mu dandana tace mu cinye dukka"
dr Sh yace to me yasa ka boye mana kace
kakarka ce take dahowa? Lukma yace kawai
don inji dadin bakina ni ma kun koya min
shakiyanci ne ai? Dr sh yayi shiru can yace
kuma yarinyar ta tabbatar maka da
hannunta take dafawa ko dai mamanta?
Lukman yace eai kai me ye abun mamaki ta
tabbatar min ita take dafawa zata min
karya ne?Shuraim yace ashe alkawarinmu
ya tashi ke nan da muka saka ran zuwa
gaishe da tsohuwa mai dambu,ashe
karyarka ce? Lukman yace ga yarinya mai
dambu ta gaishe ka ka ki ka amsa ka yiwa
kanka"shuraim yayi murmushi yace Daman
ai don kai take yi ba don ni ba idan ka yi
mana bakin ciki don kada mu ci to ai shi ke
nan don ta ni mai sauki ne don kada mu ci
to ai shi ke nan don ta ni mai sauki
ne .kada yake Abbana fa ya kamu da son
dambun nan jiya ma ya tambaye ni yaushe
zan kawo masa dambun nan mai dadi inda
ya sake son dambbun ma da nace ba na
gidan sayarwa bane a gida ake yinsa na
musamman ga tsafta"
Lukman yace ka ci albarkacin abba bari in
kirata ta zo in ce ta yi mana"dr shuraim
yace kada ka bari ta san mune muke ci
kasan abun da zaka fada mata"Dr L yace
ban iya karya ba ko karyar kuma zaka koya
mani? Ya dauko wayarsa ya lalubo sunan
Aisha farida ba ta ankara ba ta ji wayarta
tana kokarin daukar kara alhali ga ta a
jingine a jikin kofarsu sai ta falla da gudu ta
fita daga farfajiyar ofisoshin sannan ta
matsa dr Lukmn ya ce kanwata kina kusa
ne ki zo mana ina da magana dake"Aisha ta
amsa masa na da yi nisa yayana sai nan da
minti 30 zan karaso"yace babu komai sai
kin zo tana ganin Dr Shuraim da Dr Mohd
suka fita daga ofishin Dr Lukmn don kada ta
zo ta same su ita ma saboda su din ne ta ki
zuwa da farko da suka fice sai ta yi wuf ta
fada ofishin.Dr L yayi murmushi da ganinta
yace a'a ai ko minti 5 baki yi ba kika zo?ta
ce Ashe zamu gama da wuri na dauka zamu
dade kasan tafiya shi ne muka dan harhada
kayayyakinmu"yayi dariya yace mata dai
duk inda kuka je sai an barbaza shirgi wato
dan zaman da kukayi asibitinmu har kun
baza mana shirgi kenan? Aisha Farida ta yi
dariya tace Wallahi kuwa don wasu jaka
guda cika a nan suke cire kayan
makarantasu wata ma jakar kayan
siyarwarta a nan take bari duk a ofishin
metron Maryam.
Doctor ina so inyi muk dambu da danwake
gobe, ina fatan kana gari ko? Yayi dariyar
farinciki yace kai haba! Kina wahala da
kanki, ki bari kawai. Aisha farida tace a'a ai
nayi niyya ba a mayar da hannun kyauta
baya. Dr lukman yayi dariya yace koda yake
na bankwana ne ko? Gashi zaki tafi ba
ganinki zamu dinga yi ba. Aisha farida tace
haba yayana ko kasar ka bari inda hali ai
zan ziyarce ka balle nan da nan. Ai duk
sanda kake da bukatar dambu ko ba kai
bane, ko abokanka ne kada kaji komai, kayi
min waya kawai. Dr lukman yayi godiya
yace to amma abin da yasa zaki sage min
gwiwa idan na baki kudi ba kya karba, ni
kuwa banga dalilin da tika tika damu mun
daukar albashi mai tskoka zamu zauna
muna tsotse dan alawus din dalibarmu. In
kina so mu shirya to duk abin da na baki ki
karba, idan da ciko na yadda ki cika mana
idan babu yawa, idan kudin sunyi yawa ki
rike canjin. Haka ake rayuwa, sai muma mu
sami kwarin gwiwar cewa a kawo mana
gobe. Aisha farida tace to yayana amma
banji dadin kudin da zan dinga karba ba,
adduarku manyanmu muke nema. Dr
lukman yace kaji uwar iya magana, kin cika
wayo kanwata. Baki tambaye ni laifin da
abokina yake zarginki dashi ba. Kin fita kina
kuka, na dauka kina shigowa abin da zaki
fara tambaya ta kenan.
Aisha farida tayi murmushi ta langabar da
kai kasa tace bana son in cika tambayar
manya, amma tambayar tana raina. Dr
lukman yace uhmm aisha tsiri kenan, ko ba
haka bane sunanki, don naji haka yahaya
yake kiranki. Kina da hankali sabanin 'yan
matan zamanin nan. Dr shuraim yace kina
da hankali amma da zaki daina dane bayan
acaba da sai kinfi hankali. Suka tuntsire da
dariya su dukka. Dr lukman yace ai baya
son yaga mutum akan acaba, musamman
ma mace. Aisha farida tace a zuciyatya ni
da acaba kuwa har abada, tunda yin haka
zai jawo min samun kaunar wanda nake
kauna. Kudin da dr lukman ya miko mata
ne jimus dashi ya firgita ta, ta dafe kirji tace
na meye wannan kudin? Karbi mana. Ya
fada cikin tsawa a lokacin da yake zunguro
mata kudin gabanta. Ta girgiza kai tace dr
kudin yayi yawa fa. Yace nawa ne kike
tunani? Naira dubu uke ne fa kawai, ba
yawa don dai 'yan dari bibbiyu ne shiyasa
kika gansu da yawa. Nifa bana son mu
dinga irin wannan abun, ke fa ni yayanki
ne. Bana son ina baki abu kina kin karba.
Aisha farida tasa hannu biyu ta durkusa ta
karba sannan tayi masa godiya tayi masa
sallamaa ta tafi. Yau farin cikin da yake
lullube a cikin zuciyarta Allah ne kadai Ya
sani, saboda ta sami canji da yawa daga
wajen masoyinta.
Ba ta da wani buri wanda ya wuce ta ganta
a wajen abida ta bata labarin abubuwan da
suka faru tsakaninta da dr shuraim a yau. Ai
kuwa tana isa gida ta iske abida a zaune ita
da matan gida dankar suna hira, suna ta
soya awarar siyarwa. Aisha farida ta kasa
daurewa ta bari har sanda abida zata gama
ta shiga daki sannan suyi hira don haka sai
ta damko hannunta. Tace maman farouk zo
muje ciki in baki sakonki daga shagamu.
Abida na biye da aisha farida har cikin daki.
Suna shiga aisha farida ta jefar da jaka. Tace
Allah Shine Allah, Allah Shi ne mamallakin
duniya da lahira, Shine mai yawan kyuta ba
Ya gajiyawa. Tsarki da yabo sun tabbata ga
Ubangijina, sarkin sarakuna. Bai haifa ba, ba
a haife shi ba. Abida ta runguma aisha
farida yayin da ita ma farin ciki ya lullube
zuciyarta tun kafin taji abin alherin da ya
sami aisha farida, ko ba a fada ba tasan
akan dr shuraim ne. Tace alhmdl farida me
ya faru? Dr shuraim ko? Aisha farida ta jawo
hannun abida suka zauna ta jawo jakarta ta
zaro kudin da dr lukman ya bata ta mika
mata. Tace inji dr lukman suna son dambu
da danwake gobe. Abida ta karba cike da
murna, ta kirga ta daga ido ta dubi aisha
farida ta harare ta. Tace na dauka dr
shuraim ne ya baki kudin da kansa yace a yi
masa?
See Translation
DUK KYAN TAKALMI 2* 10
Aisha farida tace antina kin cika gaggawa,
karkade kunnenki kiji labari. Aisha farida ta
zazzagewa abida labarin abin da ya faru yau
a asibiti tsakaninta da dr shuraim babu dadi
babu kari. Daga karshe ta zurawa abida ido.
Tace kinji abin da ya faru, meye shawararki
kuma meye abinyi nan gaba? Abida tayi
dariya tace Ikon Allah kenan, farida kinga
faidar addua ko? Kinga banbancin
madanfaran bokaye ko? To duk abin da kike
so ki nema a wajen Allah Shi kadai, kuma ki
yarda Zai baki. Aisha farida ta gyada kai
tace na yadda da haka na dade da yin imani
da wannan. Abida tace a yanzu da Allah Ya
sa shuraim ya sanki, yasan kina raye, yasan
sunanki, yasan kina da amfani a wajensa, ya
fara damuwa da rayuwarki, ya fara gane
halayyarki, ya yabe ki da bakinsa. To anzo
gangara, lokaci yayi da zan fada miki mataki
na hudu da zaki taka. Aisha farida ta gyara
zama ta dafe kirji da hannayenta biyu taja
doguwar ajiyar zuciya tace Allah Ya sa zan
iya. Abida tayi dariya ta dafa kafadar aisha
farida tace kada ki damu, ba abu ne mai
wuya ba, guda ukun na farko sun fishi
wahala. Ai abin bi da bi ne, na daya yafi na
biyu wahala, na biyu zai fi na uku wahala,
na uku zai fi na hudu wahala, na biyar duk
yafi su sauki.
Har yanzu dai ajiyar zuciya aisha farida take
yi, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi don
fargabar abin da abida zata fada, so take
taji mai yiwuwa ne ko ba mai yiwuwa bane?
Abida tayi shiru kamar mai tunani, can
dagao ta kalli aisha farida tace idan na fada
miki wannan mataki na hudu, ba wai ina
nufin ki zubar da matakai uku na baya ba,
a'a duk zaki hada kici gaba. Kici gaba da
addua sosai ki ma kara wata akan ta da.
Haka hakuri sai kin sake ci gaba sannan ki
hada da na ukun ki rike mutuncinki sai na
hudun da zan fada....saboda kaguwa aisha
farida ta katse ta tace fadi na hudun
wannene? Abida tayi murmushi ta gyada
kai tace ki zamo mai yawan biyayya da
ladabi a gare shi. Jikin aisha farida sai ya
dauki rawa ta rike abida cike da rudani tace
antina ban fahimce ki ba, ta yaya zanyi
masa biyayya ni da ba ganina zai dinga yi
ba, musamman ma mu da zamu bar asibiti?
Abida ta mike ta dube aisha farida tayi
murmushi tace haba farida bafa na son
rikicewa, kina tsoron shuraim kamar wani
malaikan da zai dauki ranki alhali
TAKALMIN da zaki sura ne ki saka a kafarki.
Ki dauki wannan ruguntsumin da ake ciki
tamkar wasan 'yar tsana ne da yara suke yi,
ki dauka tamkar wasan kwaikwayo ne don
nishadi, ki dauka tamkar cartoon din tom
and jerry ne da yara suke kallo a talabijin,
sai ki daina fargaba. Ko kin manta DUK
KYAN TAKALMI KAFA CE MAI TAKA SHI?
Nace ki saka a ranki daurin dan kwalin da
kike yi a kanki yafi wahala akan samun dr
shuraim. Abu ne sassauka dalilina kuwa
shine kince yana da ilimi, yana da wayewa,
yana da tausayi uwa uba yana da riko
addini, ma'ana tsoron Allah ne. To sai kibi
duk hanyoyin nan da kika san yana so kiyi
kane kane. Abin nufi ki zama mai amfani da
iliminki duk abinda zakiyia agabansa, ki
zama mai wayyayyen kai, idan yana wajen.
Ki zama abar tausayi don ya tausaya miki,
sannan ki nuna masa kinfi shi rikon addini,
sai kiga hankalinsa ya karkato gare ki. Aisha
farida ta dora hannu biyu aka tace anti kin
sake rudani, don Allah yi min misalin yadda
zanyi. Abida ta girgiza kai tace bazan fada
miki yadda zakiyi ba, saboda ke mace ce,
kuma nayi imani kowacce mace an haife ta
da irin tata kissar a jikinta. Musamman ke
aisha tun kina yarinya kin kware da iya
zama da mutane da lafazai dadada. Haba
kin manta zamanki a cikin tsofaffi ne? Kin
manta halinki na kissa wanda ko zaginki
akayi sai kiyi dariya ki ba wa mai zaginki
hakuri? To shine wannan. Kije Allah Ya baki
sa'a, sai mun hadu a mataki na biyar in kinci
nasarar cinye wannan jarabawar. Abida ta
juya zata fita, aisha farida ta lngwabe kai
tace anti mataki na hudu yafi na daya dana
biyu dana uku wahala. Abida tace hakuri
yafi komai wahala, tunda kikayi hakuri zaki
iya wannan. Idan baki gane biyayya ba, to
bansan yadda kike so nace miki ba. To bari
dai in baki misalain abin da nake nufi, ki
durkusa har kasa ki gaishe dashi a duk inda
kika ganshi, zaki fita daban daga cikin 'yan
mata a idanuwansa, don 'yan matan yanzu
basu da wannan tarbiyar. Ki rabu da hawan
acaba tunda baya so, sauran kuma kinfini
sani. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tace sai
yanzu na fahimce ki, godiya nake. Abida ta
fice yayin da aisha farida ta daka tsalle ta
rungume pillow gami da cewa waYyo
shuraim dina. Da tazo kwanciya ta jima
tana juyi, don tunanin shuraim yayi mata
katutu a rai, ta rasa dalilin da yasa ta tsinci
kanta tana cikin farin ciki yau. Ta kagu gari
ya waye ta dauki dambu ta kai masa da
alama hadin da sukayi wa dambun nan zaiyi
dadi. Daga barci ya soma wartarta sai tayi
firgigit ta bude ido ta jawo wayarta ta duba
agogo tana gudun kada asuba ta shude su
makara ba ta tashi ta dora dambu ba. Karfe
uku saura ta mike taje tayi alwala tazo ta
fara sallah. Rakaoi ba adadi, doguwar
sujjada take yi tana zayyanowa Allah yadda
take so ta kasance a cikin zuciyar shuraim.
Karfe hudu da rabi ta fita ta fara kokarin
dora dambu don ya turara sosai, bayan ta
dora da jimawa sannan taji motsin fitowar
abida daga daki. Abida ta shigo dakin ta
dube ta tayi dariya. Tace kaji mai himma,
wato kin daura dambun tun kafin assalatu
tayi, koda yake aikin shuraim ne babu bata
lokaci. Aisha farida tayi murmushi ba tare
da ta bata amsa ba, saboda tana wuridi.
Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita
sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan
abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen
food flask guda 2 manya,daya a shake da
hadadden dambu daya a shake da danwake
sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai
wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya
yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya
man gyada zaryan aka soya da albasa sai
kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka
shi kanana da tumatir da albasa da
kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu
shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan
nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa
da wuri ba.

Ta kwankwasa kofa sai ta murda ta tura kai
dauke da kwandunan abinci riki-riki a
hannunta ta yi sallama ta shiga sai ta ga
wayam babu kowa a ofishin.babu tantama
ko ya shiga bandaki ne don haka sai ta daiki
gwandunan ta tura lungun da take ganin
yana ajiyewa dan ta kawo masa.tana tsaye
a gaban teburin tana jiran ya fiti amman
shiru kuma abun da ya bata tsoro ba ta jin
motsin komai a bandakin. Motsi ta ji an
turo kofa da karfi yayin da ta waiwaya da
sauri fuskarta cike da fara'a tana murna da
ganin yayanta.tace a ranta ashe ba'a
bandaki yake ba yana waje"sai dai kash da
ta hada ido da mai shigowar ba fuskar Dr
Lkman ta gani ba tayi matukar firgita gami
da razana a bayyane wanda shi kansa
wanda aka yi razanar dominsa ya gane.
Kallonta yake yi a nutse har sai da ya shigo
cikin ofishin ya mayar da kofar ya rufe ya
fara tafiya a hankali zuwa gaban teburin
kusa da inda take a tsaye. Numfashinta ne
yake kokarin daukewa, idanuwanta kuwa
sai suka kasa tsayawa a waje guda suka
dauki farfari yayin da ta nemi yawun
bakinta ta rasa, balle ta samu damar fitar
da lafaxi guda daya. Ya dauke kansa daga
kanta ya zagaya ya jawo kujera ya zauna
yaci gaba da bincike wani file. Da taimakon
addoui aisha farida taji numfashinta ya
daidaita, ta sami nutsuwa a cikin zuciyarta.
Ta dube shi cikin kunya hade da ladabi ta
sunkuyar da kai kasa, sannan ta kaskantar
da muryarta kasa ta zakaka makoshinta, ta
duka har kasa ta gaishe shi. Dr shuraim ya
daga ido ya dube kasa kasa da alama yaji
dadin yadda ta gaishe shi, sai ya amsa cikin
sakin fuska. Ya kara da cewa kina neman
lukman ne ko? Ta gyada kai ba tare da ta
iya hada ido dashi ba, tace eh. Ya dube ta
da gefen ido yace ai bai karaso ba, sai
anjima nine na bude ofishin. Aisha farida ta
duka tace nagode. Sannan ta juya zata fita.
Kamar a mafarki taji yayi mata magana.
Babu abinda za'a ce masa? Ta juyo a nutse
ta dube shi sannan tayi masa wani
dandasheshen murmushi, wanda ta
tabbatar an sha tabbatar mata idan tayi shi
yana kara mata kyau. Siririyar wushiryarta
ta bayyana yayin da kumatunta gefen dama
ya lotsa, fararen hakoranta sai su sake
haske. Tace dama sakonsa ne na kawo
masa, gashi can na ajiye masa. Sai ta nuna
lungun data ajiye kwandunan. Ya wurga
dara dara idanuwansa ya kalli wajen sannan
yaci gaba da dube duben file dinsa. Har
yanzu aisha farida tana tsaye a jikin kofa ta
rike kofa ita bata fita ba, ita bata dawo ciki
ba. Ya dago da kai a hankali ya dube ta,
yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta
kasa a hankali. Yace okay zan fada masa.
Tace kace masa kanwarsa ce aisha farida
umar. Ya dago da kai ya dube ta da alama
yaso yayi mata wata tambaya ya fasa, sai ya
gyda kai yace idan nace masa kanwarsa mai
hawan acaba ai ya sani. Sai ta ya danyi
murmushi lokacin da yake karshen
maganar. Ta langwabe kai ta marairaice ido
kamar mai shirin fasa kuka. Tace yaya
lukman ya fada min laifina jiya, nayi
kuskure bazan sake ba, nima nayi tunanin
naga ban kyauta ba. Sai ya kalle ta kawai ya
ci gaba da rubutu, can yayi magana ba tare
da ya sake dubanta ba. Yace hakan dai zaifi,
ki yiwa kanki fada, don ke mace ce, a
addinance ma bai dace ba. Dan wasu 'yan
acaba ba su da hankali. Ta duka tayi masa
godiya ta murda kofa ta fita. Ta jawo kofar a
hankali ta tafi. Taji kamar ta fasa ihu, ko ta
daka tsalle ta dire don murna. Ta shaki iska
ta lumshe ido ta daga ido sama tayi wa
Allah godiya gami da yiwa alkawarin zata yi
ma Sa azumi gobe don godiya, da Ya fara
karkato da hankalin dr shuraim kanta.
ALLAH ABIN GODIYA!!