← Book details Duk Kyan Takalmi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 15

kashi in tafi dashi, wasu a kano zamuyi

Duk Kyan Takalmi Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

gwajin wasu kuma a abj zamu aika lab suna
harhada jinin mutane da yawa, su tashi
mutum a kai south africa a gwada. Yaya
hussaini ya langabar da kai yace nawa ne
kudin maganin? Kuma nawa ne zamu bada
na wannan gwaje gwajen naji har da wanda
za aika kasar waje. Dr dayyabu yayi
murmushi ya girgiza kai yace kada ka damu
da wannan, abokina shuraim ya gama
shirya komai. Dan yanzu ma lagos zanje in
hau jirgi cikin dare in isa abj in bada
wannan jinin, kwana goma zaiyi sannan ya
fito, to sauran gwaje gwajen ma sai inyi a
national hospital abuja don yawo da jini
babu dadi, duk dr shuraim zai biya. Gwajin
jinin wanda za'a aika south africa ma dubu
sittin za a biya, yace shi zai biya.
Sai aisha farida ta fara hawaye haka itama
abida hawaye ya fara kwaranyo daga
idanuwanta dan tana jin duk abin da ake
cewa. Yaya hussaini ya hau godiya yana shi
albarka. Dr dayyabu ya zaro sirinji da
kwalabe ya zuzzuki jinin abida ya ciccika. Ya
dauko wata 'yar akwati ya jera su ya mayar
ya rufe. Suka mike suna yiwa abida sannu
da fatan Allah Ya bata lafiya. Aisha farida da
yaya hussaini ne suka kinkimi abida suka
shiga da ita cikin gida. A take yaya hussaini
yace aisha farida ta dibo ruwa ya bata
magani, bayan ya bata ta sha sai yace aisha
farida ta boye maganin a wurinta. Sanda
zata sha tazo ta bata kada ta barsu a fili
goggo ta zubar dan bata yadda da maganin
asibiti ba. Yaya hussaini ne kadai ya dawo
wurin su dr shuraim suka dunguma zuwa
kofar gidan su aisha farida wajen tsofaFfi.
Babu abinda yaya hussaini da yahaya umar
sukeyi sai godiya da shi albarka. Yaya
hussaini ya yiwa tsofaffin bayanin duk
abubuwann da ya faru da irin zunzurutun
kudin da dr shuraim ya kashe da wanda zai
kashe nan gaba. Sai suka kacame da yi
masa godiya da shi albarka, shi da
abokansa sauran likitoci.
Hussaini ya gyara zama ya dubi tsofaffin
nan ya nuna shuraim yace shine mai son
farida, da farko naki amincewa saboda ko
ba a fada ba shi ba sa'an aurenta bane, mu
talakawa ne kuma baki. Toh a haka muka
rabu. Yahaya umar yace kayi kuskure
hussaini tunda kayi wannan tunanin, ai
al'amarin soyayya ba a ayin ta don kudi, shi
ya ganta yana so, itama tana sonsa kayi
garaje da ka tarki raba su. Ba 'asan inda
rana zata fadi ba, haka baka san wanda zai
yi maka amfani a rayuwa ba. Ga shi dai
yanzu ya taimake mu a lokacin da bamu
zata ba, kuma bamu da matsayin samun
wannan. Dr lukman ya fada min komai
daga haduwarsu har zuwa tahowar aisha
farida. Naji ra'ayin shuraim akanta alkhairi
ne kuma aurenta yake so yayi. Yanzu
wannan tahowar da sukayi sunzo dan su
duba abida su bata magani kuma su nemi
auren farida ayi magana daya. Hussaini
ance ka kauro gida kacokan zaka bar aiki, to
zamanka a shagamu ba zai yiwu ba, ko ba
dan aisha da shuraim ba, kuma ba dan
karatun 'ya'yanka ba , don lafiyar matarka
da rufin asirinka aikinka sai ka koma kano
don abida yanzu dole ta kasance kusa da
likitanta dr dayyabu yawan yawan bincikar
lafiyarta. Yaya hussaini yayi shiru yana
gyada kai don ya gasgata maganar yayansa.
Can ya dago ya dubi yahaya yace tabbas ka
fadi gaskiya, dama ni ban gama tsayar da
shawarrar barin aikin ba, na dauko hutu ne
na shekara. A cikin hutun ne dama nake so
naga yadda halin zaman namu a shagamu
zai kasance idan na samu abinyi sai in
zauna. Idan ban samu ba in koma kano
iyalina in barsu a nan. Yahaya yace to
iyalinka ne ma zaman a kano ya kamasu
saboda lafiyar matarka, wannan likitan da
kake gani babu inda zakaje a kasar nan ka
samu iirinshi , su biyu ne kadai
rheumatologists , daya na kudu shi yana
arewa. Saboda masu irin ciwon basuyi yawa
ba. Saboda haka hutunka na karewa ko bai
kare ba ka hada su ku koma dan naji yace
sati biyu zai gama hada sakamakon gwaje
gwajen sannan ya gano kan ciwon. Yaya
hussaini fadi yake gaskiya in sha Allahu
zamu koma nagode.
Tsofaffi ma suna bayan yahaya, shawara
suka ci gaba da bawa hussaini su hada su
koma kano. Dr lukman ya gyara zama yace
toh mu dai yanzu munzo a shirye tafi da
gidanka mukayi, ma'ana muna neman
auren aisha farida. Yahaya ya dubi tsofaffi
yace toh me za a jira tunda gaku kacokan
kun hallara? Mutumin nan sananne ne
tunda ga lukman nasan gidansu yasan
gidanmu. Farida na son shuraim shima yana
so, ayi magana kawai. Dr shuraim ya
sunkuyar da kai kasa yace saboda rashin
lafiyar nan ne ta abida bamu san yadda
zamu tarar da jikin bane yasa bamu taho da
iyayena ba. Amma tunda komai yazo da
sauki idan an amince mana sai mu bada
kudin aure, sai kuyi magana da mahaifina a
waya ya lamunce in nemi auren. Su dukka
suka ce babu damuwa ai. Dr shuraim ya
dakko wayarsa ya kira tsohonsa , bayan sun
gaisa ya shaida masa gashi a gaban iyaye da
kakannin aisha farida kakaf sun hallara ,
kuma sun amince zasu karbi kudin aurensa.
Abban shuraim yace masa ya basu wayar,
daya bayan daya abban shuraim ya dinga
gaisawa dasu suna yi masa fatan alkhairi,
shima yana yi musu har suka kashe wayan.
Dr lukman ya tashi yaje mota sai gashi ya
dawo da bakar jakar leda yazo ya zauna, sai
ya mikawa yahaya umar. Yahaya ya bude
yaga damin kudi dauri biyu 'yan naira dubu
daya-daya. Kowanne dami dubu dari ne,
dami biyu dubu dari biyu kenan.
Dakata yahaya. Inji baban abida. Kowa yayi
carko carko yaji abin da zai fada. Yace ba
himilin kudi ba, haka ba wayar da mukayi
da tsohonsa bane aure. Shin an tambayi
yarinya tana sonsa? Don idan yayana umar
yana da rai zai iya yiwa kowacce 'yarsa
auren dole banda aisha farida. Don yana
matukar sonta, baya son abinda zai bata
mata rai. Hankalin dr shuraim ya tashi, sai
yayi ta zungurar dr lukman wai yayi
magana. Hussaini yayi murmushi yace
wallahi tana son shi, matukar so kuwa. Don
nine shaida saboda ni ta tara tace min ina
kokarin raba ta da shuraim, to in sani
kamar ina kokarin raba tane da rayuwarta,
don tanayi masa tsananin son da zata iya
rasa rayuwarta. Babu wanda bai kyalkyace
da dariya ba a cikinsu, yayin da dr shuraim
yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Salati goma ga
annabi (SAW) suka fara kawowa, sannan dr
lukman ya fara warware kudade yana
bayani. Naira dubu 100 shine kudin na gani
inaso, naira dubu 50 gaisuwar uwa da uba,
sai naira dubu 50 kudi ne kyauta a
rarrabawa dangi , wani a siya alawa da goro
shaidar an bada ita. Sai tsofaffi suka rike
haba don mamaki da jin wadannan
makudan kudi tunda suke aurar da
'ya'yansu da jikokinsu babu wacce ta taba
yin tsadar da farida tayi. Sai wasu suka
barke da kukan dadi don ko naira ashirin
babu a aljihunsu. Wasu kukan tunawa da
mahaifin farida sukayi. A lokacin malam
sule ya shiga yiwa farida kirari irin wanda
baban yake yi mata tun tana karama.
"Aisha sarauniyar mata, fara mai farar
aniya, kinfi mata dubu". Kowa yana ta
adduar fatan alheri da fatan ayi auren cikin
sa'a da zaman lafiya. Dr dayyabu ne zai tafi
a yau, dr shuraim da lukman zasu kwana sai
washe gari zasu koma, da mota suka taho
don haka yahaya zai raka su masauki. Wani
tsadadden hotel zai kaisu, sai suka yi musu
sallama suka shiga mota suka tafi.
HAUSA Novels BOOK
DUK KYAN TAKALMI 3* 9
Aisha farida tana zaune a gefen katifar
abida tayi shiru tana sauraron bambamin
fadan da goggo keyi, saboda an kawo
likitoci sunzo sun korar mata mai magani da
suka kashe kudi sannan ta yadda tazo. Tana
shiga tana fita, ta na fada ita kadai, babu
wanda ya tanka mata a cikin gidan saboda
ranta yayi matukar baci. Ko hakuri aka bata
sai taji tamkar an zage ta. Abida ta dubi
aisha farida tayi dan murmushi yayin da
itama ta dube ta tayi murmushin. Abida ta
yi magana a hankali sai da aisha farida ta
dora kunnenta a kusa da bakin abida
sannan taji abinda take cewa. Cewa tayi
allurar nan da akayi min naji dadinta, yadda
kika san yawo takeyi kusurwa kusurwa duk
inda ciwon yake tana wanko shi. Gashi ina
iya daga hannaye sama. Dadi ya rufe aisha
farida tayi dariya tace mungode Allah, Allah
Ya karo sauki. Abida tace amin, naga
shuraim, Allah Ya sa ayi auren nan. Aisha
farida tayi dariya tace samun lafiyar ki shine
fatan mu , kafin ayi wata magana
antina......bata rufe bakinta ba saiga
maimuna ta fado cikin dakin budik! Ko
sallama babu kai kace jeho ta akayi. Sai haki
take daga gani tasha gudu. Cikin sheshekar
gudu ta rirrike aisha farida tace albishirinki?
An bada ke, yanzu aka kawo kudin aurenki
dubu dari biyu. Kallon rashin fahimta aisha
farida da abida sukeyi wa maimuna.
Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta
dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah
abin godiya. Wai nice yau ake maganar
aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta
barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau
karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin
ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta
danna da sauri sai taji muryarsa cike da
farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira
wayarki taki shiga sai da na aika yara suka
fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura
shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko?
Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi
murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar
ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti
abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta
mutu ne shine muka dungumo, muna nan
dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin
muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu
an samu rabin warakar ciown, tunda an
samu likita da ya gano matsalar. Barr
muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji
sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da
naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti
abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir
nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji
dadi ba.
Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta
dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah
abin godiya. Wai nice yau ake maganar
aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta
barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau
karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin
ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta
danna da sauri sai taji muryarsa cike da
farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira
wayarki taki shiga sai da na aika yara suka
fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura
shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko?
Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi
murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar
ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti
abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta
mutu ne shine muka dungumo, muna nan
dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin
muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu
an samu rabin warakar ciown, tunda an
samu likita da ya gano matsalar. Barr
muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji
sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da
naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti
abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir
nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji
dadi ba.
Aisha farida ta dafe haba tayi dariya tace
albishir din meye? Yace alewar saka aurena
da janan na kawo miki. An bani ita har an
kai kudi da kayan sa rana , nan da wata uku
za a sha biki. Alewarki ta musamman ce,
bounty na kawo miki har jaka biyu saboda
matsayin ki a auren nan, sai gashi ba kya
nan. Ko 'ya'yan yayanki suna ciki a kirawo
mun su na basu? Aisha farida tayi dariya
tace Allahi abin godiya, amma na taya ka
murna yayana. Kuma na gode da
karramawar da kayi min. Babu kowa a 'yan
gidanmu, dukka muka taho. Nima kuma
yanzu zan zankado maka nawa albishir din.
Dr shuraim yana shagamu yazo da likita an
duba anti abida, ya siya mata magunguna ,
ya biya makudan kudi za a kai jininta kasar
waje a gwado. Sannan daga karshe ya
kunso kudin aurensa ya kawo yanzu yanzun
nan nima labari yazo min, suna can a kofar
gida shi da yayyena da tsofaffin maza. Barr
muazzam ya cika da farin ciki da mamaki,
ya kyalkyale dariya yace ikon Allah, Allah
mai yadda yaso. Wato auren namu ma tare
za'ayi kamar yadda muka fara nema tare.
Na taya ki murna kanwata. Baraka ma
komai ya daidaita, ita da mijinta suna cikin
farin ciki, ya rabu da nafisa , hankalinsa
kacokan akan baraka. Ciki ne ma da ita, sai
ririta cikin yake yi. Tace in gaishe ki da
kyau, kuma tana matukar yi miki godiya,
tana so ta ganki a rayuwarta. Tace in
gayyato ki suna idan ta haihu. Aisha farida
tayi dariya tace Allah Ya kaimu , idan dai ina
kano zanje. Sukayi sallama ya kashe waya.
3 missed calls din dr shuraim ta gani a
wayarta a lokacin da take waya yake kira,
sai ta fara kokarin kiransa, shima ya kirata.
Ta amsa sallamarsa cikin nutsuwa kafin ta
gaishe shi ya jero mata tambayoyi guda
uku, ta rasa wacce zata fara amsawa a
cikinsu. Farida da wa kike waya nayi ta kira
har sau 3 naji call waiting? Meyasa da kika
shiga gida dazu baki fito ba mun gaisa har
na tafi? Meyasa kwana biyun nan naga
alamar kin daina damuwa dani? Sai ta
lumshe ido tayi ajiyar zuciya sannan tayi
murmushi. Tace bari na fara amsa maka
tambayarka ta uku, sannan a gangaro ta
biyu, sai in gangaro ta daya. Zancen na
daina damuwa da kai wallahi ba haka bane,
tunda ina tuna ka a rana sama da dubu.
Sannan tambayarka ta biyu ina shiga gida
na bawa anti abida magani sai na zauna ina
saurarom fadan da goggo keyi mana ni da
yaya hussaini, wai mun kawo likitoci sun
duba ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini
ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda
nagama zan fita aka ce min kunja mota kun
tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake
waya dashi wani ne sunansa barr muazzam ,
bansan kai kira ba da na bashi hakuri na
katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi
hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar
da yakeyi yace waye barr muazzam? Na
fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki,
kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba?
A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa
ya kamata sannan tambayar ta daga mata
hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki
my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da
ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode
ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka
tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim
kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a
bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min
laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka
baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani.
Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah
Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a
lokacin da na shiga ukuba, sai muke
gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr
janan bai same ni ba, shine yake shaida
min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya
tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace
kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin
rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta
shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr
shuraim yace tabbas ta dade ana shariar
nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki
nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai
Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi
aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban
taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura.
Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki
bani labari mai dadi mana wanda zai sani
inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun
bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji
anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha
farida tayi dariya tace zanso nima ka
kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na
biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare
ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin
jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da
alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi,
yau farida ta zama ta shuraim, shima ya
zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace
bani labarin me ya faru? Haka dai suka
cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da
kauna har tsawon awa guda. Abida na
kwance ta kafawa farida ido sai murmushi
takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta
mike tayi rawa don babu hali ne. Tana
adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi
auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI
AISHA FARIDA!!!
Chapter 11 · 0% Book details