← Book details Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Deejamah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabadaya bude mouth baba Ayuba ya bude Yana kallo na,Yana mamakin wani irin hatsabibanci ne dani haka?
Shiru yayi batare da yayi magana ba ya fita daga gidan,karyayyen langa-langar mu yabuga yafita, Abba ne yadawo da dubanshi kaina yace"zonan mamana,tsakanin ki da Allah meyafaru?Jin ta tambayi tsakani na da Allah yasa nafadi gasky,Nan ko Abba ya Shiga yimun fada inda yake Shiga banan yake fita ba,Ammi ma haka Bayan sun gama suka dasa nasiha akan narage tsiwa da rashin kunya.
Amsa kawai na Basu da toh sannan na nemi yafiyarsu,Sam banson bacin ran iyayena a gefe guda kuwa ta shiga tanan ne tafita ta can tabi iskaaaaa.
Washe gari kuwa muka sake daukar tallan bread din duk idan muka fita sai mun siye tasss,dalilin haka kuwa Allah ya albarkaci Dan ribar dubu dayan da muke samu,ganin haka yasa Abba yasamu a islamiya,ajinmu Daya da Aunty Saudah tunda inada kokari sosai,kwana na biyu a islamiyar sunana ya zagaya makarantar,a dalilin na fasa ma wani yaro kai yakawomun wargi,kullum sai iyayen yara sunkawo karana wajen headmaster,ganin haka yasa headmaster ya sanar ma da Abba,wanna Karan fushi Abba ya dauka sosai a kaina domin har zaneni yayi yace Kuma zai cire ni a makarantar.
Hakuri Nashiga bashi,sannan nayi mai alkawarin bazan Kara ba,tsaki yaja yace"keda Kika Saba da dama tuban mazuru.
Ita dai Ammi ko me akayi sai dai Ido.

~After 3 month~

Mun cigaba da zuwa islamiya Alhamdulillah Allah nata rufa Mana asiri,sannan a gefe guda bamu dena zuwa tallah ba.
Ranar sati na shirya ni kadai na tafi islamiya da yake Aunty Saudah bataman tabi kanwar Ammi Agadez domin Ammi 'yar agadez ne can wani kauye,namanta sunan shi,ita Kuma tana aure a cikin garin nijar.
Latti nayi,da yake malam shafi'u azzalumi ne yasan bansan duka,Aiko nan yamun dukan tsiya,kuka nayi sosai tare da duban hannu na yanda ya fashe.Don haka na dauki alwashi da ramuwa da *daukan fansa* a dalilin dukan wallahi sai na Rama.
Washe gari kuwa Bayan antashi islamiya na dai-dai ci dai-dai lungun da malam shafi'u ke wucewa na zuzzuba kososhi tunda ga farkon lungun har tsakiya,sannan nasu wani waje na boye,hannu na da katon icce.
Aiko bayan antashi malam shafi'u ya shigo lungun,kunnensa sanye da earpeace bai ankare ba yaji mashin tafara selow slow slow alamun Babu iska,sauka yayi tare da Jan tsaki,Yana duban tayar mashin dinsa Bai ankare ba yaji saukan sanda a bayansa say kwala masa,wani irin ihu yasake tare da gantsarewa,cikin bacin Rai ya juyo Cike da mamaki da takai ci yake duba na,nikuwa hade rai nayi kamar wata babba ku Kuma wani sa'a na nace"ai dama ramuwar gayya tafi ta gayya zafi Ina magana Ina jujjuya sandar da take hannu na.
Cikin bacin rai yanufo inda nake,Aiko na hau tsalle tsalle kamar 'yar Cali-cali Allah kuwa yabani nasara nashige ta osin shi,abin fitsarin shi na Kama na murdeeee,duk da a lokacin bansan menene ita ba,kawai hannu na ne yakai kanta.
Kyalkyalewa da dariya su Fauzi sukayi,khadee tace"lallai Shakeerah kin bar history a unguwar ku.
Murmushi Shakeerah tayi tace"hmmmm ku dai Bari,in takaicemu ku tunda na Kama abin fitsarin shi na murde sai da yayi ihun wahala nasake shi,sannan na dauki icce na kwala ma goshin sa Aiko atake anan yafashe goshin yafara fitar da jini.
Nesa dashi nayi sannan na nuna masa hannuna da ya fasa da dorina nace"kaga wannan somun tabu ne,Ina Gama fadar haka na arta a 360 na bar wajen nayi gida.

Washegari na dauki tallar pure water da bread dina natafi wajen Sha daya na dawo Bayan nayi ciniki ansaye tasss.
Tunda nashigo gidan daga Ammi har Abba babu wanda ya kalleni daka gansuu kasan ransu a bace yake,Cike da farin ciki na nufi jikin Ammi na fada kamar yarda na Saba nace Ammi kin.........ko karisawa banyi ba naji saukar Mari,Wanda yasani gigicewa duk da bansan Wanda ya mareni tsakanin Ammi da Abba ba to nafi kyautata zaton Ammi saboda shi Abba mutum ne Mai sanyi kamar yanda Ammi take,babban cinsu Ammi na duka Abba Kuma ba yayi.
Ihu nake Ina fadin na Shiga uku,sanda Ammi ta dauko tace"au don ma bandake kiba shine kike kokarin tara mun jama'a?iccen miyar tsanya ta dauko zata zabga mun tana cewa"Bari inmiki Mai dalilin inyaso kyayi kukan da hujja.
Zumbur na mike nanufi Bayan Abba ina cewa"A'ah Ammi kuyahakuri wallahi bazan sake ba nayi alkawari.
A halin Ammi na kunya ko me muka Mata bata iya dukan mu a gaban Abba domin tana ganin kamar cin fuska ne.
Jawo ni Abba yayi gabansa ya dorani a Kan tabarman da yake ya dubi Ammi yace"kikawo Mata abbin Karin kumallo,da toh Ammi ta'amsa ma Abba,sannan tashiga dakin Wanda yake ciki dai-dai guda biyu,daya nata da Abba Daya Kuma nida Aunty Saudah,sai bayin mu da kitchen waje guda.

Dauko mun Karin kumallon tayi ta aje tare da dallamin harara.
Cike da yunwa najawo kofin Koko na da roban kosai na mike naje na wanke hannu nadawo,bismillah nayi na fara cin abinci.
Bayan na gama Abba yadubeni yace"mama na meya hadaki da malamin islamiyar ku har Kika masa rauni?shiru nayi kaman munafuka Ina tunanin wani karyan zan gindayo ma Abba......katse tunanin nawa nayi a dalilin Jin yace anjima zai daukeni muje har islamiyar,idan nice da lefi zaisa amun assembly a zaneni.

Kirji na ne yabuga na fara kokarin samo mafita.

Xahratty ce✍🏽
Lallai Alqalami 🖋️Yafi takobi 🗡️
💕💕
❤️
[7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨
( Daukar Fansa )

Story& writing
By
PATEEMA ZAHRA LAWAL
______✍🏽______

*TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah))

*_T.W.A_*
_________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/
_________________________

Marubuciyar⬇️

_ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_

*DA*

_ _MIJIN ZAHRA_

*Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.*

Bismillahir-rahmanir-raheem.

*Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai....*

Page:1️⃣5️⃣🖊️

__________Abba kuwa cikin hukuncin Allah Allah yabuda masa,yakuwa samu a makaranta Aunty saudah tana zuwa Zaria children school tana S S 2 tunda lamarin na jumping ne,nikuma Akasa J S S 3 maida hankali mukayi sosai wajen karatun mu tunda muna da experience a gefe Daya Kuma Abba ya dauko Mana Mai lesson a gida sikuma muna Yana kula da karatun addinimmu
Abba yataso Mai temako sosai Sam baiso yaga ana zalinci a waje sau dayawa idan ka kawo Masa kukan ka zai magance maka damuwar a dalilin haka yasa ake kiransa da muhammadu Adali.

A Zaria children school kuwa daga student har teacher's sun Sani ba'amun na kyale,da haka yaza kowa yaci maganin Zama Dani,a kullum nasihar mu da Abba shine muji tsoron Allah sannan mukula da rayuwa.

Wata Rana da baAzan taba mantawa nida Abba da Aunty saudah mun rakasa kasuwar sabon garin Zaria akasiyo atamfofo kusan hamsin da yadikan maza ba Dan kadan ba,domin shagon da mujaje siyayyar motar shagon ta Daukar Mana kayak,gidan nakasassu da marayu daje kofan kibo nan mukaje Aiko Abba yadinga rarrabawa Wanda ma'aikatan wajen sukayi farin cikin matuka,a gajiye muka dawo gida.
Muna zaune naga Abba yafita cikin Sauri a dalilin kiranshi da akayi a waya mikewa nayi nima don inaso muyi mgnr su baba Ayuba sai dai banaso Ammi taji balle ta kobeni.

Koda na karisa ji nayi Yana waya Yana cewa"Haba Alhj mukhtar yaza'ayi nabaka dukinyan marayu,Kuma hakkin marayu?wallahi bazai yuwuba sai dai duk abinda zakuyi mun kuyimun nacema takaddun komai baya kasan nan nasan akwai ire-iren ka,Kuma nasan za'a bibiyeni shiyasa ma nabar kasar Nan dashi,babsan me akace a Daya bangaren ba,na daiji Abba ya daga murya Yana cewa"wallahi sai dai kuyi abinda zakuyi da dai na taba dukiyan marayu,still sakeji naji nayi yace"Eah Alhj mukhtar na yarda ka kasheni abinda nasani shine nayi imani cewa Babu Mai rayawa kuma Babu Mai kashewa sai Allah, Yana Gama fadar haka yakashe wayan tare da jingina da gate din.

Wani hawayeni masu dumi suka tsiyayomin da yake a lokacin hankali yazomini sannan inada wayau da kaifin baseera,juyowa Abba yayi turus yatsaya ganina da yayi bavtare da yayi magana ba yakama hannuna mukabi ta kofan baya muka Shiga bedroom dinshi.
Zaunar Dani yayi a bakin gadon tare da Kama kafadu na yace"Mama na! idanuwa na dago ina kallonshi bakina na rawa nace"Abba wanene wannan?sannan meyasa zasu kasheka?
Girgiza Kai yayi tare da murmushin gefen baking yace"Mama na wannan ba huruminki bane.
Girgiza Kai nayi cikin muryan kuka tace"Abba sanarmun nada amfani bakasan amfanin da zanyi ba.
Kai yadaga yace haka NE wato akwai wani business partner dina Wanda muka hadu a kano mutum ne Mai hakuri da kawaici ajiyan wani dukiya abokinsa ya bashi na wanni abokinsa ne da yarasu dukiyan yaransa da documents na abubuwa masu mahimmanci Wanda ba'a bama yaran ba har yanzu,tunda suka fahimci dukiyan na hannun sa sai suka dinga bibiyarsa ganin haka NE sannan yaga ba garin mu Daya ba yasa Nima yabani amanar su,shi wancan Abokin NASA kasheshi sukayi yayyinsa.
To Yana bani Bayan nadawo nan da kwana biyu suka kasheshi,Nima bazan Basu ba sai dai sukasheni,kama hannuna yayi yace"mama na Ina alfahari dake don Haka zanbaki dukiyan nan ki rike.
Diddilo idanuwa nayi Cike da tsoro nace nikuma Abba ? Dagamun Kai yayi alamun Eah.
Nace"Abba na Ni yarinya CE kuma idan haka NE basai mugudu ba?
Kada Kai yayi yace"mama na Kenan mutanen hatsabibanci ne duk inda kike tunani sun wuce,kedin jarumar macece zan baki dukiyan a hannunki duk runtsi duk wuya ki tabbatar da duk abinda zan baki kin cikamun kinji mama na?
Daga Masa Kai nayi nace to Abba na insha Allah wani tausayi yabani rungumesa nayi na fashe da kuka.

Kwana biyu da faruwar hakan suka Kira Abba sukace yau zasu Zo don Haka yabasu files ko su kaishi barzahu,Abba yace Yana jiransu,ta Bayan gidanmu Abba yafita damu wajen Sha dayan dare ya Shiga damu wani lungu Wanda duk kwa-kwan ka bazaka San da mutum ba nida Ammi da Aunty saudah,duk cikanmu kuka muke Ni kuwa ina rungume say files a hannuna.
Chapter 8 · 0% Book details