Sashe 4
Dan Iskan Miji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sani na cinkai harda za a kawowa yarana Kaya ki jefa musu kayansu ki nadawa Yara duka badai kishi kike ba to ko haukacewa Zaki saina auro Laila wallahi kinsan bana magana biyu ke Baki Isa ba Koda uwata da ubana zasu dawo duniya basu isa Susa nafasa auren Laila ba bare wata ke banza Kuma wallahi kigama haukan ba saki tsakaninmu aurena dake mutu ka raba danke kadaice Zaki iya jure halin Zama dani ko kinki kokinso baki Isa ki wani Abu akan wannan auren ba ya hankadata ciki tanata kuka ga duka ga tsinka jaka dama ya Saba agaban yayanta ma dukanta yake Yaushe kika Zama Yar iska me kika sani a iskanci kiduba kitabul fantsara suna nane a shafin farko Dan haka dawasa Kika kara korar duk Wanda yazo wajena kema sai jikinki yagaya Miki aurenmu ba saki bare yaji Kuma yanzu zanje na karbo kayan sai dai ki mutu Dan sai sunsa wannan kayan sallah ta kusa Dan bakin ciki Zaki mayar musu da kayansu cikin kuka tasa dariya ai wallahi bazawu taba moruwaba Dan gutsi gutsi na yankasu na mayar Mata dakayanta leda har takalman na farka kutumar uba yau zakisan Dan iskane Ni nizakiwa iskanci a gida Nizaki zubarwa da mutunci mutunci Ina kaga mutuncin waye besan Kai Dan iska bane a unguwar Nan Banda ana tsoron tijararka ai da ko kofar gida yayanka basu isa sun lekaba Dan dai kowa yasan Kai Dan iskane bakajin kunyar kasha giya kazo Kai tanbele a layi kazubar min da mutunci masu ganina da mutunci duk sundena ai baka da sauran mitunci tunda yaran unguwa ma baka barsu ba indai yarinya zata baka hadin Kai zaka nemeta nikike gayawa haka Zaki ci ubanki yau ya dakko bulalar yafara dukanta ta ko Ina sai ga yaran sun shigo suna ganin haka suka sa kuka sukai kan uwar suka rungumeta ya hada duka ya zanesu Maryam ce ta fito dauke da jaka ahannunta nafeesat na falo taga mace Ina zuwa haka Rana fatsar fatsar wallahi anty gida zan koma Dan bazan iya Zama Ina kallonki mijinki na jibgarki ba zan iya Rama Miki wata Rana nafeesa Tai murmushi Allah sarki sis ba halinsa bane kinsan mutumin kirkine arfan din kawai tsautsayi ne suna meeting a office jiya aka kawo giya besantaba ya Sha shiyasa Amma haka baze Kara faruwaba Cike da mamaki take kallonta wato harya tsarata ta tsaru dama ita Sam Bata da wayo duk abunda kace mata yarda take kamar yarinya take zuciyarta akwai saurin yadda Bata da zafafa fawa ta kalleta haka dai ya gaya Miki Amma Ni banyardaba anty kawai ki zamanki ke da mijinki Amma Ni bazan zaunaba aiko Zama Dole Bari kiga ta Kira babansu tagaya masa Bata da lafiya Kuma Maryam ta dage sai ta taho handsfree tasa ita maryamun eh baba Bata wayar ta karba tana turo Baki baba haba auta ta kwantar da hankalin ki Aina barwa nafeesa ke har aurenki nafeesa ta sheke da dariya itakuma tafasa ihu tana kuka nafeesa ta fusge wayar ta kashe Ba kukan komai takeba sai na Zama gidan Dan iska tanaji aka sanar Mata da halinsa yaushe zata iya wannan zaman Sam bazata iyaba Zama gidan mashayi mazinaci ita kanta yayar tata tana tausaya Mata anmata lumbu lumbu an aureta bisa rashin sani tafado gidan Cikakken takadiri Dan iska Wanda duk wani abun iskanci Yana aikatawa tunda ance har caca yakeyi to meye bayayi na iskanci da haramci Haka taita lallabata har yamma da kyar taci abinci wajen magariba sai ga shi ya shigo a nutse yai sallama suka amsa yaga taci kunu tayi dam sai Tai Masa kyau Dan yafi yarta kyau Dan dai ita batada hasken fatane a a lafiya nafeesa Naga kanwarmu nata fushi tana zumbura Baki wallahi gata Nan tun bayan fitarka taketa fushi Wai lallai saita tafi gida baba yace yabar Mana har aurenta wow gaskiya ya kyauta Mana mun gode Kuma tunda gidan takeso ku shirya na kaiku ku gaishesu nima na Kwan biyu banjeba bara nai wanka naci abinci mutafi ko Cike da murna ta sakar masa kiss Tama manta da wata Maryam ganin haka Tai sum sum ta koma daki mutum a fuska a zuciya shedan mtsww Taja tsaki ku kainin wallahi bazan dawoba guduwa zanyi Nan shima ya rungumeta suka Fara shiga wata duniyar chak ya dauketa yai sama da ita saida suka gamsu sannan sukai wanka sukai sallar magriba sukaci abinci har Maryam sannan suka tafi gidansu A hanya yake sanar dasu su Gama da wuri dan karfe goma da rabi ze tafi office ita dai Maryam abun yana bata mamaki wane irin aikine sai dare Shiba police ba ba soldier ba ba shi dawani kaki to aikin me take ta tambayi kanta ba amsa Nima tasani a tunani kujira mu tunano *Naga alama book din Nan be muku ba Dan Haka na ajiye alkalamina daga yau indai Banga comment masu yawaba sannan banasan thanks ko sticker yadda nake typing nake rubutawa rubutu nakeso* Nice Taku akoda yaushe *Feedyn bash* [10/3, 4:46 PM] Ummu Subai'a DAN ISKAN NAMIJI *NA* *FAREEDA ABDULLAHI* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN HALITTA* *Wannan page din sadaukarwane ga kainuwa fans 1-12 nakune wannan kuyi yadda kukeso dashi nagode da comment dinku agareni Allah ya bar kauna ameen* 9-10 Haka suka karasa gidan sunata kowa nata sake sakensa a zuciya suka shiga sukai masa iso ya gaisa da umma da mama aka bude masa sitroom suka zauna da babansu sunata hira ya suna dakin umma sunata hira chan maryam ta mike tafito shiga dakin mamanta ta fada cinyarta mama gaskiya kisa baki ni bazan koma gidan nan ba nagaji badadi ke bana san iskanci kinsan halin mahaifinku jibi yadda kikai kyau kwana biyun nan dan kikai sannan kice ba dadi dan haka sawunki a likkafa tashi ku tafi Inda kuka fito bazaki jazan bala'I ba gun ubanku Wallahi umma ba inda zani nan ne gidan ubana dan haka anan zan zauna rai bace ta koma wajen umman nafeesat tasa kuka ita batasan komawa gidan nafeesat gaskiya ita tagaji umma tace bazaki komaba yi zamanki yata bawanda ze takura miki Dama sangartace daga mura tawani kwasheki kwanta ki huta ki zamanki haba umma cewar nafeesat babane fa yace ya bar mana ita umma ta hade rai kebansan hauka yammata biyu muka aura masane Koko muma mahaukatanne irinku wuce ku tafi gida dare yafara nafeesat tana ta sharar kwalla ta fito taje dakin mama dan siyi sallama kafin taje dakin umma chan taje suka gaisa suka sha hira Lafiya yata naga kina kuka cikin kuka tagaya mata umma ta hana maryam ta tashi su tafi ranta idan yai dubu ya baci jira ina zuwa taje takaraci fadanta basu tanka mata ba tunda kun maidani dutse bara naje na turo me iko da yar taki dan yata tana bukatar zamanta za'ai mata haka Ana wani wulakantata harda sata kuka me yar taki ta iya banda shagwaba da sangartata dakike A fusace tajuya taje sitroom takira babansu tagaya masa rai bace ya ce muje gidan dan sirikin nasa yaji meke faruwa bayan shiya rokeshi alfarma tun jiya ya kirashi yace yabarta a gidan saboda aikin dare yakeyi shiko wani nauyin aka rage masa shiyasa da suka Kira yace yabar musu ita tazauna danshi anrage masa wahala rai bace ya shiga gida A fusace ke fito koni sa ankine bangaya miki kin koma gidan kenan ba fito nace jiki a sanyayeY umma tace haba Alhaji dakata bansa dakeba balle na kwashe dake bakuji takarar danai muku akan wannan maganarba ko jiki a sanyaye tace allah ya baka hakuri ke kuma maryam tashi ku tafi ta fashe da kuka ta rike umma dan ita harga allah tunda mutanen nan najiya suka gaya mata komai take tsoron arfan da gidansa dakyar umma ta bambareta ta fito tanata kuka nafeesat tace menai miki maryam kike guduna kike gudun zama dani ko ina cutar dbbake bansaniba ke yar uwatace karkimun wannan horon dan allah nasaba zama dake ke kike deban kewa kinsan shi bama zauni bane da daddare da yardarsa zaki zauna a gidan ai ki kwatar da hankalinki kanwata itama kwalla take tasan tsoron abunda ya faru jiyane a ranta Itama maryam tarungume yar uwarta tana kuka bagudunki nake ba inada dalilina wanda ku bazaku ganeba tundaga jiya naji gidanki ya siremun rufe mata baki tayi dan karta Tona mata asiri kuwuce muje kwayi koke koken naku a hanya haka suka fice jiki a salube ko sallamar kirki basiyi da iyayensuba kowacce ranta cike da tausayin yayansu dakewa kawai sukai sunsan Alhaji akan kudi kuma yai musu takara indai maryam tadawo to kowacce ta tafi gidansu shiyasa umma tai haka badan ranta yaso ba Ita kanta tana kewar autar tata Ya koma sitroom din jikinsa har rawa yake ai sun fita Kai suke jira allah ya tsare tashi kuje dare ya fara dubu Dari biyu ya bashi baba gashi ayi hidamar gida baba jiki na rawa ya karba sai zabga Addu'a yake godiya yake tamkar wani zautacce ko maroki sai haka ya isa haka dan allah baba nace banasan godiya kagamaimun komai tunda kaban auren nafeesat bara nashiga ciki miyi sallama dasu umma ya shiga ciki ya basu dubu Dari Dari dakyar suka karba dan su basu da kwadayi ga tsantseni kansu a hade yake tamkar tagwaye bazaka taba cewa kishiyoyi bane idan kagansu kansu a hade yake komai tare sukeyi allah Besa musu mugun kishin nan ba na hauka Ko magani zasu sha tare suke sha kome zasi tare sukeyi baruwansu da hassada a tsakaninsu samun kishiyoyi kamarsu gaskiya ba karamin dace bane mama ce uwar gida umma amarya ya fice yaja motar suka tafi gida maryam nata kuka nafeesat na aikin rarrashi shiko gogan uffan yakasa cewa yarasa a wane hali yake bayasan kuka ko kadan ko cutarsa zaki a kwalta sa masa kuka kingama dashi gashi wani irin kuka take me kamar shagwaba har buga kafa take kamar ya janyota jikinsa ya rungume haka yakeji har suka isa gida tana kuka Suna jan motar Alhaji