← Book details Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 32

Sashe 8

Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻‍♀
Glow🧖‍♀️

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
*BUDURWAR MIJINA*

*NA SADNAF*

*E.W.F.*

*PAID BOOK*

*PAGE 5*

HADIZA

Kukanta taci ta koshi,duk zagin da Lubna ta mata ya hau tafasa mata zuciya,ashe dai hasashen da takeyi akan Mahfuz tsoron matarsa yake ji da gaske ne,Karo na uku kenan da Lubna ke zaginta, ta rasa ya ake yi wayar ke zuwa hannunta,duk uban wahalar nan da take sha duk dan ta samu Mahfuz ya aureta,bata San tana San shi ba sai da yayi Aure, duk da sai da Wanda ta kwalafa rai da auren wani saurayinta mustapha ya yaudareta,hakane yasa ta komawa Mahfuz,dak'yar dak'yar ta samu ya fara kulata, shine matarsa take neman hanata rawan gaban hansti, taga alamar idan har batayi da gaske ba,bazata bari Mahfuz ya aureta ba,aikuwa idan ta san wata bata san wata ba ba boka ba Mallam sai ta auri mahfuz ta wulakanta Yar iskar matarsa da sam bata ma san sunanta ba balle tasan kamaninta ta matukar tsanar matar mahfuz Kamar ta kasheta haka takeji,shi Kuma mahfuz bari taga karyar da zai Kara shara mata tun jiya yake raina Mata hankali har ace ya kasa tsawatar wa shegiyar matarsa da take zaginta idan ta kirashi.

Bakin ciki ne yasa ta kashe wayar gabad'aya dan tasan ta kafu a zuciyar mahfuz gwara ta Masa barazana akan zata hakura dashi idan yaga da gaske ne dole ya tura manya gidansu ta gaji so take kawai ta samu ta Shiga daga ciki ta fitar da lubna ma daga gidan ta bar mata mahfuz dinta.

Mahfuz

Gigicewar da yayi yasa Sam bai bi takan wayarsa ba har suka isa asibiti da lubna dake ta zunduma ihun wayo cikinta sai kuka take.

Koda suka isa ihun da lubna ke zubawa taki bari ma likita ya dubata dak'yar dak'yar aka samu tayi shiru.

Likitan ya dudubata,yanda take ihun cikinta yasa likitan yi mata allura.

Ba abinda yafi komai faranta min rai sama da zagin da nayiwa Yar iskar yarinya nan, yanda na zuba drama ba mai yarda ba Ciwon marar nake ba,dan har da kukana awar mu daya a asibiti aka sallame mu ya kashe wajen Dubu biyar a siyan magani sai yaje ya biya kudin kunshi da kitso nagani.

Koda muka isa gida yanda nake langab'ewa Ina matsar kwalla yasa bai motsa daga kusa dani ba sai aikin yimin sannu da yake.

Abincin ma sai shi ya shiga kitchen ya dora da wanan na samu na goge Kiran da tayi dazu so nake nayi ta hadasu fada.

Sai da ya bani abinci naci na koshi Ina yamutsa fuska ya bani magunguna na Sha.

Sanan naga ya dauki wayarsa yayi hanyar palo

Na riga nasan Kiranta zaiyi a waya.

Fitarsa da minti biyar sai gashi ya shigo bansani ba wayar yayi ko baiyi waya ba,Ya zauna a gefen gadon Yana matsamin kafa da hannu daya Yana latsa wayarsa da hannu daya,Sam fuskarsa ba walwala ba Kuma abinda ya shafeni addua ma nake Allah yasa ta sosoka masa Ashar wlh da wayar zai shigo hannuna text zan Mata na zazzageta.

A ranar ma ban bari ya fita waje waya ba dan kwanciya nayi a kirjinsa,ko da bacci ya fara daukana idan na tuna sai nayi sauri na kankame shi.

A ranar dai baiyi waya da ita ba duk da naga alamar idonsa biyu ba bacci yayi ba

MAHFUZ

Tunda suka dawo gida yake gwada lambar Hadeeza yake jinta a kashe,ya dubata ta WhatsApp nan ma Bata hau ba ya rasa duk Mai ke mai dadi,yasan fushi tayi sam bai so yau baije wajenta ba,dan shima ji yayi Kamar ya dade bai ganta ba,burinsa bacci ya dauki lubna ya fita waje ya kirata a waya idan yaji a kashe ya kira Ameera kanwarta,muryrta da zaiji kawai zai saka ya samu nutsuwa sai dai lubna kankame shi tayi taki barin jikinsa abu kadan sai yaga ta bud'e idonta a haka ya kwanta kamar yayi kuka baccin Kuma yak'i daukarsa.

Allah Allah yake gari ya waye idan ya fita massallaci ya kirata a waya.

Wajen tara yaje gidan nasu.

Kiran sallahr asuba a kunnensa hakane yasa ya mik'e da sauri ya fada bandaki ya daura alwala a daidai lokacin da Lubna ta mik'e zaune itama tana yamutsa fuska

"sannu ya jikin naki"?

"Wlh har yanzu ciwo yake min ga kaina Kamar ya rabe gida biyu dan Allah ka zauna kaja mu sallah ba sai kaje massallaci ba"

"Haba Lubna jiya ma fa banje massallaci ba ai ana iddar wa zan dawo bari naje"

Yace da sauri tare da yin waje ya jefa wayarsa a aljihunsa.

Na tabe baki dan nasan Kiranta zaiyi a waya,yau ma bazan bari yaje ko'ina ba

Sai dai mayyar taci kanta,na tsaya ma Ina neman dorawa kaina hawan jini bayan ga hanyoyi nan da Zan bi wajen rabasu,yanzu wayarsa ta kara zuwa hannuna lambarta zan d'auka

Bai dawo gidan ba sai wajen shidda da rabi.

Daga yanda naga fuskarsa ba walwala nasan ko bai samu yin waya da ita ba ko Kuma ta zazzage shi Kamar yanda nake fata da Addu'a.

Ban koma bacci ba na dafe marata na fara wash wash,ya dafe kansa Yana "Lubna wanan wane irin ciwon Mara ne"

Ban bashi amsa ba na hau matsar kwalla.

Mahfuz kamar ya sa kuka dan bakin ciki,dan Yana ta Kiran Hadeeza a waya bata d'auka ba,karshe sai text tayi Masa da Allah ya hada kowa da rabonsa bazata iya ba tunda matarsa ke controlling dinsa.

Ya Kira dan ya bata hakuri Sam taki dagawa,bashida burin daya wuce tara yayi yaje gidan nasu.

Sam bazai iya hakura da Hadeeza ba Yana jinta a ransa ba abinda yake Balain so da ita sama da shagwabarta ko ba'a fada ba yasan idan ya mallaketa zai Sha soyayya sai gashi yau ma Lubna na neman hana shi fita.

magungunan ta ya d'auko mata ya siyo kayan shayi ya hada mata.

Sai dai Koda ta Sha bata fasa ihun ciwo mara ba,Yana ji Yana gani Lubna ta dabaibaye shi bai samu ya fita ba a ranar.

Hadeeza kuwa ta Kara cika tayi fam tana ganin wulakanci mahfuz din ke san yi Mata ta dauka da ta Masa text din zai zo gidansu da sassafe sai dai ko keyarsa bata gani ba.

Sam ba walwala a fuskar mahfuz har wani tsawa tsawa yake min idan zaiyi magana hannunsa manne da wayarsa nima bakin cikin duk wanan abun akan wata can a waje ya keyi dan kawai bai samu fita wajenta ba,har mamaki yake bani wlh bantab'a zaton haka daga wajen sa ba,
banga ta Zama ba ko Ina so ko bana so dole gobe zai fita Kuma yaje gidan nasu sai dai Allah ya kawomin mafita.

Daddaren ma ban bashi space ba haka.na manne Masa banga Kuma alamar zai fita waje waya ba sai tsaki da nakeji yanayi akai akai.

Washegari kuwa da sassafe ya fice daga gidan kamar akan Kaya yake mahfuz da ni nake tilasta.masa fita sabida kar ya makara sai gashi yau wata ta d'auke masa hankali koma wacce yarinya nan ban yafe mata ba na share hawayen daya zubomin na dauki wayata dan na Kira Mahaifiyata ita kawai zan Kira na samu kwanciyar hankali dan nasan zata bani shawarwari masu kyau.

Mahfuz

Dak'yar ya samu Hadeeza ta fito dan sai da yayi ta turawa gidansu Tama k'i d'aukar wayarsa.

Koda ta fito shi kadai ya hau maganar sa Yana bata hakurin dalilin dayasa bata ganshi ba Lubna ce bata da lafiya kwanan su biyu a asibiti bada gangan yak'i zuwa ba

Sai a lokacin Hadeeza ta kalleshi idonta cike da kwalla tana "Mahfuz Ina kaunarka amma ya zama dole na hakura da Kai dan na riga da nasan b'atamin lokaci kake,wlh bazaka iya Aurena ba,bazaka iya rik'e Mata biyu ba,dan kana balain tsoron matarka mahfuz zagi da cin mutunci haka ta zuba min sau uku kenan tana zagina da iyayena har karuwa tace min idan har bata da lafiya zata zageni ne"?

"Wlh da gaske Lubna bata da lafiya ko dai wata ce ta kiraki ta zageki matar da bata da lafiya taya har zata kiraki ta zageki"?

"Hmm Mahfuz kenan karya Zan Mata kenan wlh Azeem bamu dade da waya da kai ba na sake kiranka ta d'auka ta hau zazzagina har da cemin Kai ba sona kake ba,na like ma Ina ta dafa maka abinci Kamar wata matarka"
Chapter 8 · 0% Book details