← Book details Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 32

Sashe 24

Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata san Mai yasa mahfuz yake neman wulakanta ta ba,bayan uban dukan da ta sha awajen lubna a yanzu ya Kamata yafi kula da ita ya turo kudin aurenta gidansu,sai gashi a madadin kulawar nema yake ya juya Mata baya,haka ta rike wayar tana tunanin zai Kira,bayan minti goma sai ga sallamar almajiri da akwatin ta tayi sauri ta mik'e ta leka waje ko zata ganshi dan tasan dole shine ya kawo Mata kayanta.

Sai dai babu shi babu dalilinsa jiki a sanyaye ta ja akwatin ta bayan ta bawa mmn khairat wayarta ta bude gidansu ta shige dole ta zauna a gidan ita kadai har sai sun dawo daga aikin Hajjin.

Mahfuz

Ji yayi Kamar ya rabu da K'aya a lokacin da Hadeeza ta ta tafi,a lokacin da ta kirashi dama Yana gida sabida ya kwashe kayanta ya Kai Mata sai gashi ta kirashi duk abinan da ya faru gani yake ita ta jawo Masa,balain haushinta Yake ji,duk kayanta ya tattara mata nesa da gidan ya tsaya ya samu almajiri ya bashi akan ya Kai gidan dake jikin gidansu dan yasan Dole tana can, bashida burin daya wuce ya samu ya shawo Kan lubna,indai Lubnar daya sani ne yasan wuyanta su keb'e ya marairaice Mata,da kwarin gwiwarsa ya Kara wanka ya saka sabon kayan daya dinka na sallah,ya nufi gidan ya Usman ya riga da yasan Mai ya kawo shi hakane yasa basu wani b'ata lokaci ba suka nufi gidansu Lubna,a k'ofar gida Suka tarar da zainab na zance kanwar lubna,bata ko kalli mahfuz ba iya ya Usman din ta gaisar yace mata ta musu iso wajen mahaifiyar su Suka zo dan mahaifinsu ya dade da rasuwa,kuma bata sake aure ba.

Mahfuz kuwa ganinsa a k'ofar gidansu lubna Kuma sai duk yaji hankalinsa ya tashi dan baisan Mai zai tarar ba.

Gabansa ne ya hau faduwa a lokacin da suka shiga gidan har palon mahaifiyar lubna da aka fi Kira da Aunty nurse ita kadai suka samu a palon da alama da baki a gidan sabida ranar take sallah suna Kuma jiyo hirar mutane a dakunan palon.

Mahfuz sai wurga Ido yake yaga ko zai ga lubna daga yanda Aunty nurse ta amsa gaisuwar shi sai yaji jikinsa ya Kara sanyi ya sunkuyar da kansa Yana Jan ya Usman na mata bayanin basu dadin abinda ya faru ba,ya hau bada hakuri yana a dubi zuriar dake tsakani.

Aunty nurse bata katse shi ba har ya gama kafin itama tayi gyaran murya tana "Abinda Mahfuz yayi ya munana,ba uwar da zaa yiwa yarta haka bata ji zafin abinda aka mata ba,kafin ya Kai budurwarsa gidan ta sha dan min korafin wayar da yake yi da budurwa a cikin gidanta,har barota yake yi a daki ya fita dan kawai yaji muryar budurwarsa wlh idan ta fadamin hakuri nake bata, tana ta Kai zuciyarta nesa,a iya sanina basu wani Dade da Aure ba da har ta cancanci haka daga wajensa iya nan bai ishe shi ba sai gashi ya dauko budurwar ya kawota har cikin gidansa ya zuba karyar Yar uwar abokinsa ce tsakani da Allah yayiwa yarinya nan adalci duk macen da mijinta zai iya Mata haka wlh ba kaunarta yake ba,dan haka a ganina kuyi hakuri yaje ya auri wancan din dan yafi kaunarta,ita Kuma Lubna Allah ya mata zabin daya fi alheri"

Mahfuz nasan baiyi daidai ba,abinda yayi ba abinda zaa yi saurin mantawa bane ko a yafe,amma idan kuka tuna Allah ma muna mishi laifi ya yafe Mana Ina ga mu Yan Adam,dan Allah dan annabi kuyi hakuri"

Mahfuz baki ya sa ya hau bada hakuri shima

Aunty nurse ajiyar zuciya ta sauke tana "ba fa nice lubna ba idan lubna taga zata koma bazan hanata ba dan haka bari na turo muku ita"

Ta mik'e ta bar palon ta shige daya daga dakunan dake cikin palon.

Lubna

Nayi kukan fili nayi na zuciya har na gaji,nasan daga jiya zuwa yau sai da jinina ya hau, duk abinda ya faru dawo min yake kawai a kaina daga lokacin da Hadeeza ta taka kafarta zuwa gidana har jiya da ya kasance min bak'ar Rana, mahfuz yaci mutuncina ya wulakanta ni da yanzu asirinsu bai tonu ba har ta samu ta tafi,da ahaka Zan saki baki ya aurota bayan ta gama sanin komai nawa sai a yanzu na tsani halina na saurin sabo da mutum Koda a ranar na fara haduwa da mutum,Banda mmn Iman ta kwabeni da komai nawa Zan kwasa na fadawa Hadeeza,Ina Jin Haushin mamn Iman har a cikin zuciyata da ace ta fadamin tun wuri da Hadeeza bata Dade a gidanan haka ba,tsabar munafirci mahfuz ko kallonta baya yi Ina murna ba ruwansa ashe yaudarata suke har abin ya Kai ya sakamin magani a lemo,a yanda nakejin zuciyata bana Jin akwai Wanda na tsana kamar mahfuz domin ya ci amanata,Ina matarsa ya hadani da dubu biyar ya bawa budurwarsa Dubu ashirin,wlh ko zaa na rantse min mahfuz zai iya kusanta kansa ga zina karyatawa zanyi,sai gashi a cikin gidana yaje ya kwanta da Hadeeza Ina can dakina ya bugar dani Ina bacci.

Mummy gajiya tayi da rarrashina ta hau ni da fada akan Kar naja wa kaina wani matsalar akan abinda ya riga da ya faru ya Kuma wuce dan kuka da saka damuwa a zuciya bashi zai canza komai ba.

Hakane yasa na koma kukan zuci,da ciwo Wanda ka aminta dashi ka bashi Amana ya maka irin Wanan cin amanar.

Shigowar Mummy data zauna a gefena da Sam bansan da shigowar ta ba sai da ta zauna a gefena na dawo daga tunanin dana tafi.

Ido ta zubamin har sai da na sunkuyar da kaina
"Haba Lubna wai bazaki sasautawa kanki bane Kinga yanda Kika rame daga jiya zuwa yau haba dan Allah dan annabi so kike ki mutu da bakin ciki ko abinda ya faru ya Riga da ya faru ba abinda zai iya canza hakan nasan da ciwo amma haka zakiyi hakuri ki fuskanci kuma gaba Aure gabad'ayansa dan hakuri ne,duk wata macen da Zaki gani a gidan mijinta da nata kalar jarrabawa da take fuskanta ke naki jarrabawar kenan,dan haka kiyi addua Allah ya baki ikon cinye wanan jarrabawa"

Jinta kawai nake dan gani nake ba Wanda ya Kai nawa zafi

"Kije Palo yayan mahfuz na kiranki"

"Mummy wlh bazan koma wa mahfuz ba na gama Zama dashi idan ma hakuri yazo bani gwara kar ya wahalar da kansa dan na Gama auren mahfuz yaje can ya karata da Hadeeza data fiye Masa ni ya Aiko min da takadar da ta cikin ruwan sanyi idan ba haka ba wlh hisba Zan Kai shi Kuma na Kai shi Kara kowa sai yasan mai ya aikata"

"Ki tashi ki saka hijabinki duk sai ki fada masa nidai bazan miki dole ba amma inaso kisan indan Zama bai Kare a tsakanin ku ba haka Zaki hakura ki koma ana abinda yafi wanan ma a koma a cigaba da Zama"

Zuciyata tafasa take har nasa ka hijabina bana san ganin Wanda ya danganci mahfuz amma gwara naje idan Yana tunanin dan ya turo yayansa zan hakura toh yayi a banza ba abinda zai taba mayar dani gidansa.

Sai dai ga mamakina Ina fita naga ashe har da mahfuz yazo,hada idon da mukayi dashi yasa na watsa mishi wani mugun kallo Ina Munafiki kawai ni nasan yajini haka ma yayansa da isana wajensu na samu waje na zauna banso ma gaida yayansa ba amma sam sai naji bazan iya k'in gaishe shi ba,

Ciki ciki na gaida shi ya amsa da murmushi a fuskar sa Mahfuz kuwa yayi rau rau da fuska Kamar zaiyi kuka

"Lubna kiyi hakuri Mahfuz bai kyauta ba duk Wanda aka bashi hakuri ansan an cutar dashi,ki dubi girman Allah kiyi hakuri ki yafe Masa wlh yayi nadama ya Kuma gane kuransa ko dan yarinyar dake tsakanin ku kiyi hakuri ba Wanda baya kuskure tunda baki tab'a kamashi da irin wanan laifin ba insha Allahu wanan shine Karo na farko Kuma shine na karshe da Zaki Kama shi da laifi irin wanan"

A dake na dago na fara magana ba tare da naji wani nauyinsa ba

"Ya Usman wlh ko mahfuz shine autan maza na gama aurensa bazan tab'a komawa gidansa ba inaga karyar da ya Saba yi mutane ya ma shiyasa baka san ainihin abinda ya faru ba bari na baka labarin abinda ya aikata kasa kanka a matsayin yayana idan kanwarka ce ni wane mataki zaka ce na d'auka.

Tiryan tiryan na kwashe komai na fada masa game da duk abinda Hadeeza ta fada min har yanda ta shawo kansa kafin ya kawota gidan da duk abinda sukayi na zayyane masa

"Idan har Mahfuz zai min haka ya zuba min magani a lemo na Sha dan yaje d'akin budurwarsa karshen cin mutunci yamin wlh Mai kaunarka bazai tab'a maka haka ba tsananin Santa da yake yasa ya kawota gidansa dan ya ringa ganinta bama zai iya Hakuri har sai an daura musu aure ba taya zan komawa Mahfuz da idona nagansa kwance a jikin ta da wane idon zai kalleni na kalleshi har ya samu matsayi a zuciyata da Sunan mijina wane irin Zama zanyi dashi, mutuncinsa ya Riga da ya zube a idona,bazan tab'a girmama shi har na iya Masa biyayyan Aure ba har yaji dadin Zama dani dan haka yaje ya auri hadeezar sa ya kawomin takarda sakina idan na yaye mimi yazo ya d'auketa"

Daga yanda Ya Usman ya kasa motsi nasan ya rasa Mai zai cemin ne hakane yasa na fara k'ok'arin mik'ewa mahfuz yayi sauri ya Sha gabana ya zube akan gwiwar sa idonsa ya Kada yayi jajjur kiriss yake jira ya saka kuka"Lubna dan Allah badan halina ba kiyi hakuri,wlh tallahi sharrin shaidan ne kema kinsan Ina balain kaunarki wlh na hadu da shaidaniyar mace ne,banyi niyyar kaita gida ba wlh Allah haka ta dagemin har ta shawo kaina"
Chapter 24 · 0% Book details