← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 13

Sashe 9

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shagon siyar da wayoyi ta nufa, kawai jefa ƙafarta take kamar wanda ake hankaɗata, tana zuwa kuwa ta yi sa'a a buɗe, ta sanar da mai shagon wayar take son siyarwa ganin wayar kamar ma yanzu aka buɗeta a kwalinta ya shiga son jin dalilin siyar da wayar dan dai ya fara tunanin ko dai wayar ce take da matsala dan a zahiri dai babu wasu alamu da suka nuna haka. Faɗa masa ta yi amfani take son yi da kuɗin, nan ya sayi wayar dubu 25 wayar da dubu 35 aka siya haja ta siyar masa dan ita bata da lokaci ko nutsuwar da za fa yi ciniki ko jayayya da shi. Kuɗinta ya bata ta kamo hanyar gida, tana shigowa ta ɗauki ƙaramar pos ɗinta ta sanya kuɗin wani hoton kati na Beelal ta ɗakko ta tsaya kallon hoton cike da alhinin nisa da ya yi da ita, hoton lokacin Beelal yana tsayuwa aka ɗaukeshi, ƙafar nan marar lafiya ta karkace ya ɗaga hannunsa mai lafiyar sama yana dariya, tunowa da shekaran jiya tana gyaran ɗaki ta ɗakko hoton Beelal da ke game a wayarta ya dakata ya karɓi hoton yana dariya ya ce cikin in'innarsa.

"Mama kamar ba ni ba a nan kin ga na girma" Ya faɗa yana dariya.

"Eh mana ai kowa ma da haka ya girma, wata rana ma magidanci za ka zama" Ta faɗa tana dariya.

"Mama ki bani hoton in ajiye shi a wurina"

"Ai wannan hoton babu wanda zan baiwa nawa ne sai dia idan ka girma zan sa a wanka maka shi, sai kaima ka ajiye, amma dai wannan nawa ne, duk inda ka gan shi to ni ce na kaishi wurin dan babu wanda zan iya bawa sai dai in mutuwa na yi" Maganar da suka yi da Beelal shekaran jiya a kan hoton ta faɗo mata, kafin ta ankare sai ganin ɗigon hawayenta ta yi a jikin hoton cikin sauri ta goge hawayen daga jikin hoton ta sanya a cikin jakar.

Tsayawa ta yi tana ƙarewa ɗakin kallo yana rayawa a ranta cewar sai kuma in rai ya kai, dan ita dai ta san a ƙudurin da ta yi babu gudu ba ja da baya.Ƙwaɗo ta ɗakko da mukullan ta kulle ɗakin, tana fitowa waje ma ta rufe ƙofar gidan. Shagon mai caji ta nufa wanda suke waya wani lokacin da Hajiya Laɗifa a wayarsa idan Hajiyar ta kira wayar Fatima ta ji a kashe, saƙo ta bashi a kan cewa idan Hajiyar ta kira ya ce mata ta tafi Lagos. Mai machine ta samu ta ce ya kaita Kazaure, a tasha ya sauketa ta biyashi haƙƙinsa motar Kano ta hau suka ɗau hanya. Wajen sha ɗaya da rabi suka ido cikin Kano.

"Allah sarki Yayata ki yi haƙuri da abin da zan aikata na san ba za ki ji daɗi ba, sai dai hakan shi ne mafita kuma shi ne kwanciyad hankalina dan matsawar na zauna a nan ban tafi neman Beelal ba to tabbas rayuwata za ta ƙare ne a ƙunci! Ki yafe mini yau gani a cikin garin Kano amma ba wai dan in je gidanki in kai miki ziyara ba sai dan kawai hanya ce ta kawo ni, ki min afuwa Yaya!" Cewar Fatima a zuciyarta tana share hawaye, dan shigowar motarsu garin Kano ya ƙara tada mata mikin abin da ke damunta a cikin ranta. A ƴan kaba aka saukesu, ɗan sahu ta samu ta ce dan Allah ya kai ta inda za ta samu motar da za ta kaita Lagos, har wurin ya kaita ta bashi haƙƙinsa ta samu wuri ta zauna dan ba ma lokacin motar za ta tashi ba.

Sai wajen ƙarfe uku motarsu ta tashi, amma duk zaman Fatima a wurin ko ruwa bata sanya a bakinta ba sallah kawai ta gabatar, ko yanzu ma da suke tafiya kanta kawai ta jingina idanunta a rufe tana jin yadda mutane ke ta hira a motar amma ita ko abin da suke cewa bata sani ba damuwar da ke tattare ita ta wargaza mata komai, dan rashin Beelal a kusa da ita ba ƙaramin abu bane.

MMN AFARAH 09030283375

❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BEELAL*

💦💦💦💦💦💦

NA

MAMAN AFARAH

*FCW*💛

Book 2

Page 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣

*HAMEEDA*

Tana ƙoƙarin buɗe baki ta yi magana Musty ya aika mata da wata uwar hararar da ta sanya ta kama bakinta ta yi shiru. Hajiya Zulaiha kallon Mustyn ta yi ganin sai wani kumbura baki yake yana ƙunƙune sai ta ce

"Hameeda maza jeki uzurinki"

"To" Haeeda ta faɗa cike da ladabi ta tashi ta bar falon.

"Haba Mom wai ya kike min haka ne, a gaban wannan ƙaramar yarinyar kina son ta rainani ne?"

"Oh wato ka san ma ƙarama ce yarinyar da bata fi 7yrs ba kai kana kusan 19yrs amma kamsr wata sa'arka kawai daga shigowarta sai kake neman dukanta kuma na san halinka babu wani laifi da ta maka"

"Ko ma ta mini laifi ko bata mini ba ai dai bakya fifita ƴar aiki a kan ɗan gida ba ko"

"Sannu masu gida" Cewar Hajiya tana kallonsa.

Alhaji Tahir ne ya shigo da sallama. Amsa masa Hajiyar ta yi shi kuma Musty ya ce

"Oyoyo Dad"

"Wato baka san ma na dawo gidan ba, daga masallaci fa nake yanzu kana can yawonka na dawo ba yanzu na dawo ba"

"Haba Dad yawo kuma ai ina can wajen friends ɗina"

"Ohk hakan ma ya yi kyau"

Kallonsu kawai Hajiya ta yi ta ɗauke kai abinta ta yi wajen dinning ɗin, su ma bin bayanta suka yi Dad ne ya jawa Musty kujera ya zauna sai shi ma ya zauna Mom ta shiga zuzzuba musu abinci. Sai da suka kammala cin abincin nasu sannan suka dawo falon suka cigaba da hira abinsu.

*BAYAN SATI BIYU*

Da la'asar sakaliya ne Musty ya shigo gidan da moyarsa bayan mai gadi ya wangale masa get, yana yin parking ya buɗe mptar ya fito hannunsa riƙe da leda, hango Hameeda ya yi tana shanya wasu dosters da ta yi goge -goge shi ne ta wanke su take shanyawa.

Tun daga nesa yake kallonta da yake ta bashi baya ne, bata ma san yana yi ba. Wajen ya ƙarewa kallo sai da ya tabbatar ba kowa ya a kusa ya ƙarasa wajenta.

"Ke!" Ya faɗa ƙasa-ƙasa. Da sauri Hameeda ta waiwayo dan kwata-kwata bata san da zuwansa wajen ba dan haka maganar da ya mata sai ta ɗan razana.

"Ungo nan wuce ki kai min part ɗina ki ajiye mini a falo a kan kujera" Ya faɗa yana miƙa mata baƙar ledar da ke hannunsa. Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ɗan ja da baya ganin ya zo dab da ita ita dama kuma tsoronsa take.

"Wuce ki tafi kuma ki yi sauri kin wani miƙo hannu kina ja baya kamar wanda kika ga dodo" Ya faɗa yana miƙa mata ledar. Karɓa ta yi tare da cewa

"To" Ta faɗa muryarta har rawa take, haka ta wuce ta nufi ɓangaren nasa duk da bata taɓa ko da bin hanyar ba ma, dan ita bata son duk wani abu da zai haɗa ta da Musty dan ta lura da take-takensa ba ya ƙaunar ko da ganinta ne.

Tun da ta karɓi ledar ta kama hanyar part ɗin nasa sai sauri take zubawa da yake da ɗan tazara tsakanin part ɗin da sauran ɓangarorin. Tun da ta juya ta tafi ya shiga waige-waige irin na marar gaskiya wanda ko cikin ruwa gumi yake. Sai da ya tabbatar babu kowa a wajen kuma babu wanda ya ganshi ya kama hanya bi bayanta.

Sauri take yi dan so take kawai ta je ta ajiye ta fito masa daga ɓangarensa dan ma kar ya je ya ga wani abu ba dai dai ba ya ce ita ce ta ɓata masa. Da yake wani corridor ne a farko idan ka shiga dan haka kafin ta kai falon sai da ta wuce shi, tana shiga falon ta ajiye ledar a kan kujera kamar yadda ya buƙata, cikin sauri ta juyo za ta fita sai kawai ta ji ta yi karo da mutum, da sauri ta ɗago kanta aikuwa ta sauke su a kan fuskar Musty yana wani washe haƙora tare da shafa haɓarsa da hannun damarsa na hagun ɗin kuma ya kama ƙugu da shi.

"Ka yi haƙuri dan ALLAH ban lura da kai ba" Cewar Hameeda cikin sanyin murya. Jin bai ce mata komai ba sai wani kallonta yake hakan ya sanya ta ɗan raɓa shi za ta wuce, aikuwa ya miƙa hannu ya kamo hijabin da ke jikinta, Hameeda da ke tafiya sai ji ta yi an janyo da ita baya ƙiii an dawo da ita ta hanyar janyo hijabinta.

Sai da ya dawo da ita gabansa sannan ya kafe ta da ido kamar yau ya fara ganinta, Hameeda kuwa duk da bata san manufarsa ba sai ta ji tsoro ya mamaye ta, a take sai jikinta ya ɗauki karkarwa dan ita duk tunaninta ma dukanta zai yi ko wani laifi ta yi a shigowarta falon yanzu.

"Dan, dan Allah ka yi haƙuri Ya Musty" Ta faɗa cike da tsoro.

"Haba baby mai kyau laifin me kika yi da kike bani haƙuri in ma laifin ne ni ne nan zan miki shi yanzu, dan na san laifin da zan miki yanzu wataƙila ba za ki taɓa yafe mini ba domin laifi ne da zai ruguza rayuwarki gabaɗaya, laifi ne da zai shafi kowane fanni da kowane ɓangare na rayuwarki wataƙila ma ki kasa yin farinciki har abada!" Ya faɗa yana wani lashe baki kamar tsohon maye. Hameeda kuwa bata san ina kalamansa suka dosa ba sai dai kawai ta tsorata sosai burinta kawai ya sakar mata hijabinta ta fice daga ɓangarensa.

"Duk abin da zan miki idan kika sake kika mini kuka ko ihu sai na yanka ki, kuma ij saka ki a buhu in fita da ke in jifa a kwata ba tare da kowa ya sani ba amma idan kika yi shiru baki yi kuka ko ihu ba ana ɗan jimawa zan ce ki tafiyarki har da alawa zan baki" Ya faɗa yana kallon Hameeda da gabaɗaya kan kallonta ka san a mugun tsorace take kamar ka ce kulle ta ce cass.
Chapter 9 · 0% Book details