Sashe 5
Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Wallahi da a ce mutane za su san waye Beelal wace irin baiwa Allah ya yiwa yaron ta fili da ta ɓoye, baiwar ƙwalƙwalwar da ba kowa yake da ita ba, Beelal Allah ya halicceshi da nakasa amma kuma ya bashi ɗinbin baiwar da mararsa nakasa basu da ita ga kyan zuciya. Ni na kasa gane kan mutane na kasa gane kansu bare ƙafarsu ɗan adam da bashi da ikon canja mutum amma yana adawa da yadda aka halicceshi, shin sai yaushe ne mutane za su farga, sai yaushe ne za su farka daga baccin da suka yi mai nauyi su gane cewa Allah dai ɗaya ne kuma bashi da abokin tarayya a komai shi ke halitta kowa kuma babu wani wanda ya isa ya canja dan haka kowa ya godewa Allah a yadda ya halicce shi ba wai a tsaya kai da fata sai an samu wanda za a tsangwama dan kawai Allah ya masa halittar da ya so, shin jiki da fata da ƙasusuwan da za a maida su cikin ƙasa menene na damuwa da su? Komai daren daɗewa mutuwa ce za ta ɗauki kowa kuma cikin ƙasa za a sanya kowa duk kyau da tsarin halittar mutum, fari ne ko baƙi ne, ƙasa ce makomarsa, duk mulki da sarautar mutum bashi da makomar da ta wuce cikin ƙasa dan haka babu abin da ya dace da kowa face yin biyayya da bin dokokin ubangiji da yin ibadah da ƙasƙan da kai domin samun rabauta da kuma samun sakamako mai kyau domin bautar Allah ita ce gaba da komai ƙauracewa shirka da manyan zunubai su ne abin gudu. Saɓawa Allah ba shi ne abin yi ba ga wanda bashi da tabbacin ƙara second ɗaya a koyaushe a duniyarsa,mutane su bar kiwon mutane ƴan uwansu su maida hankali da abin da ke gabansu, shi ne ya fi dacewa da kowa ba wai lura da rayuwar wasu ko ƙyamatarsu dan wata halittarsu ba" Fatima ta kai ƙarshen maganar tana kuka sosai, lokacin har mutane maza da mata sun taru yara da manya duk suna sauraron abin da take faɗa kowa sai jijjiga kai yake alamar tausayawa da kuma da na sani a kan abubuwan da ake musu a gari ita da ɗanta, basu da damar su raɓi mutane, basu da damar su sake, su yi rayuwa irin yadda kowa ke yi, ɗanta bashi da halin ya shiga cikin yara ya yi wasa, bashi da damar ya je makarantar boko ko ta arabiya sai an rakoshi har gida ana tsokanarsa, kuma ba dan ya yi komai ba sai dai suna yi ne a kan abu ɗaya kawai wato NAKASAR da ke tare da shi nakasar da bashi ya yi kansa ba, Allah ne ya yi shi, nakasar da ita kanta wacce ta haifeshi a haka ta ga ta haifeshi amma aka ɗauki gabaɗaya laifin aka ɗora a kansu, ita da ta haifa da shi wanda aka haifa, hatta wanda suka haɗu suka haifi ɗan bai barta ba wato uban ɗan shi ma ƙyamatarsa yake, to shin ina suke so Fatima da Beelal su sanya ransu?.
"Dan Allah Aunty Fati ki yi haƙuri ki bar kukan nan wallahi waɗannan kalaman naki sun sanya na ji gabaɗaya duniyar ta ishe ni, sun sanya na ji nadama a kan duk wata ƙyamatar wata halittar ubangiji koda kuwa masu nakasar da ta fi ta kowa abin ƙyama kama daga kuturu makaho da dai wasu masu nakasa kowacce iri ce, tabbas yau kin zama madubi da kika haska mini abubuwa da dama da suka shige mini duhu" Cewar wannan matashin mashayin yana share hawayen fuskarsa.
"Ba komai kar ka damu ni zan bi sawun nan domin zuwa in ga inda Idrisu yake ko Allah zai sa in ga Beelal a tare da shi in samu sassauci duk da na ga ban ga sawun takalmi ko ƙafar Beelal ba amma na tabbata Beelal ba zai fita daga gida ba tare da sani na ba. Dole zan bi sawun Idrisu dan na san tabbas akwai lauje cikin naɗi"
"Zan faɗa miki inda Idrisu yake kuma ina tabbatar miki suna tare da Beelal sabodanna gansu da idanuna a daren jiya su...
"Dan Allah yana ina ka faɗa mini dan girman Allah" Cewar Fatima cikin tashin hankali dan jin ya ce suna tare kuma tun daren jiya sai ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi.
" A daren jiya bayan dare ya tsala, duk da bansan ko ƙarfe nawa ba amma na san tsakiyar dare ne, na dawo daga yawo wurin wani abokina da ke ƙauyen sama da mu, to tare muke da abokin nawa ya ɗakko ni a machine amma dama tun daga can yace ba zai kai ni har cikin garin nan ba, tun da dare ya yi zai ajiye ni a bakin bari in ƙaraso shi ma ya koma dan yana tsoron Babansa ya san baya gida, dan ba a san ya fito ba ta katanga ya ƙetara ya fito muka je mu da sauran abokananmu muka haɗu muka yi shaye-shaye, amma in sha Allahu ni da shaye-shaye har abada dan kalamanki na yanzu sun shigeni har na ji cewar ina so in zama mutumin kirkin da za a yi alfahri da ni. Ina cikin tafiya sai na hango wani machine ya taho daga bayana ya samu wuri ya faka ua sauka ya tsaya kamar dai yana jiran wani abu, to bai ganni ba da yake akwai duhu, sai na ɓuya inaso in ga mai zai aikata, duk tunanina cikin ƙauyen zai je yin sata, zuwa can sai na hango wani mutum ya taho da yaro a saɓe a kafaɗarsa, cikin mamaki sai nake tunanin masu satar yara ne, gabana na faɗuwa ina so na fito amma ina tsoro dan ni a buge nake duk da dai ba sosai ba amma dai babu wani ƙarfi a tare da ni, mutumin na ƙarasowa sai na ga ashe Idrisu ne ya ɗakko Beelal a kafaɗarsa dan yana zuwa wajen mai machine ɗin suka fara magana ya ɗora Beelal ɗin da ke bacci da alama ma bai san ya ɗakkoshi ba, sai da ya ɗora shi a machine ɗin ya falka.
amma haka Idrisu ya tsawatarwa yaron dan dole ya yiwa bakinsa linzami ba dan ya so ba, cikin mugun gudu abokin nasa ya ja machine ɗin suka bar wajen, ni kuma dama da na ga ƴan garin nan ba ƙaunar yaron kowa yake ba sai kawai na ga an samawa kowa lafiya duk da ban san ina zai kai yaron ba bare kuma da na ga Babansa ne ma duk da kowa ya san ba ya ƙaunar yaron, sai kawai na taɓe baki na fito daga moɓoyata na tafi, amma ki gafarceni "
Kallonsa kawai Fatima take da idanunta da ke zubar da hawaye tamkar an kunna famfo ita kan ta ba za ta ce ga irin tsananin damuwar da ta kaiwa zuciyarta farmaki ba lokaci guda, ban da wacce take ciki. Ji take tamkar a jijjigata a ce ta tashi bacci ne take komai da ya faru ba a gaske bane mafarki ne.