← Book details Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Na ce maka ina Idrisu yake, saboda an faɗa mini kai ne ka ɗakko shi a machine jiya da dare tare da Beelal ka faɗa min ina ka kai su?" Ta jefa masa tambayar a karo na biyu.

"Eh, eh, am eh haka ne" Ya faɗa yana wani inda -inda.

"Yana ina???" Shi ne tambayar da Fatima ta masa cikin gushewar hankali dan gabaɗaya a firgice take ji take kamar kawai ta shaƙe shi ta yi da jibgarsa ko hakan zai sa ya yi gaggawar bata amsar da take nema, sai dai a gefe ɗaya kuma tana cike da fargabar amsar da zai bata.

"Idrisu fa ya tafi Lagos da yaron nan" Wannan ita ce wata mummunar kalma da ta ziyarci kunnuwan Fatima wacce har sai da maganar ta yi amsa kuwwa a cikin kunnuwanta. Sai da jinta ya ɗauke na wasu sakanni kafin ya dawo mata.

"Ya, ya, ya" Ta rinƙa maimaita ya, ta ma kasa haɗa kalmomin da za ta yi masa maganar da su, hakan ya yi dai dai da ƙarasowar Babangida wurin yana tura machine ɗin da suka zo a ka.

"Ki yi haƙuri dan yanzu na san sun bar Kano sun hau hanyar Lagos dan tun sassafe suka bar garin nan, a can bakin titi suka hau mota" Ya faɗa yana mata nuni da bakin titin. Da ido Fatima ta bi hannun nasa da ke mata nuni da bakin titin, tun da ta ƙura ido a titin ta kasa ɗauke idanunta daga wurin sai hawaye kawai da ke malala daga idanun nata.Kallon wurin take ko ƙiftawa babu, kamar dai wanda aka ce ta yi ta kallon wurin za ta ga Beelal ɗin ya fito.

"Lagos kuma amma me yasa zai tafi da yaron Lagos? Ba tare da sanin mahaifiyarsa ba?" Babangida ya jefa masa tambayar.

"Ni ma dai ban sani ba, kawai dai ya mini waya jiya ya ce in zo in ɗakkoshi a machine, sai da na je ma na ga ashe harda yaro to ni dai bansan dalilinsa ba kuma ma da na ga ɗansa ne waye zai masa shamaki da ɗansa shi yasa ban kawo komai a kai ba" Ya faɗa yana wani sussunƙui da kai ƙasa.

Fatima a hankali ta shiga juyo da fuskarta daga kallon bakin titi zuwa fuskar abokin Idrisu, ta ma rasa mai za ta ce wani haushi take ji wanda da a ce yanzu za ta ga Idrisu tabbas idan ta ci kwalarsa sai dai a ƙwaceshi a hannunta in yaso hakan ya zama sanadin mutuwar wannan ƙaddararren auren nata da shi.

"Kai yanzu ko da ɗansa ne zai ɗakko yaro mai larura ya tafi da shi Lagos ba tare da sanin mahaifiyarsa ba? Kuma ma dai in har tafiyar tsakani da Allah ce, zai ce ka je ka ɗaukeshi tsakiyar dare?" Babangida ya faɗa yana kallonsa.

"Dakata malam ba fa za ku zo kuna min wasu tambayoyi ba kamar wasu ƴan sanda, kamar wani ɓarawon da ya yi ƙatuwar sata, kuma wannan tambayoyin ai ba ni ya dace ku yiwa su ba, Idrisu ya kamata ku yiwa" Ya faɗa yana wani haɗe rai kamar zai hau su da zagi, dan yana ganin kamar abin nasu ya zo da rainin hankali tun da dai shi ai ba shi ne ya kar zomon ba rataya aka bashi.

"Au haka ma za ka ce ko, to shikenan amma ka saka kan ka a matsayin da nake, shin ya za ka ji? Ko ka saka matarka ko ƙanwarka idan su ne wani irin abu za ka ji a cikin zuciyarka? Shin ka san ciwo da raɗaɗin da suke yiwa uwa suka a duk lokacin da ta rasa ɗanta kuwa, ka san yadda nake ji kuwa a cikin zuciyata, amma tambayoyin da muke maka domin samun mafita su ne har ka ƙosa da su, bayan kuma kai kan ka, ka san babu inda za mu samu amsar tambayarmu sai a wajenka, babu wanda ya san amsar tambayarmu sai kai, to babu damuwa Allah mana maganin matsalarmu" Cewar Fatima cikin kuka duk wanda ya ganta a halin da take ciki yanzu sai ya tausaya mata.

Mutane har sun fara taruwa, juyawa Fatima ta yi ta kalli Babangida idanunta cike da hawaye ta ce.

"Tada machine ɗin mu tafi Babangida" Ta faɗa tana sanya bayan hannunta ta goge hawayenta, shi ma Babangidan bashi da ta cewa dan gabaɗaya tausayin Fatima da ma Beelal ɗin baki ɗaya ya cika masa zuciya, haka ya tada mashine ɗin ta hau ya ja suka tafi, shi kuma abokin Idrisu ya bisu da ido jikinsa sanyi ƙalaw dan kalamin Fatima sun gama kashe masa jiki.

Tun da suka ɗau hanya babu wanda ya yi magana daga Fatimar har Babangidan, sai dai Fatima tun da suka fara tafiya hawaye ya kasa ƙauracewa idanunta, saboda kawai ganin abin take tamkar almara, wai yau Beelal ɗinta ne bai kwana a gida ba abin takaici ma wai Idrisu ne ya ɗauke mata shi ya tafi da shi Lagos, wannan abin idan ta tuna shi yake sa ranta yake ƙuna. Ji take da a ce tana da dama da tuni ta zama tsuntsuwa ta bi bayansu, tana ta saƙar jakin nan ta saƙa ta warware a hakan har suka shigo garinsu, har ƙofar gida Babangida ya kai ta, yana ta faman bata haƙuri ita dai kai kawai take iya ɗaga masa dan hawaye sun ƙi yankewa idanunta, ji take har ƙwara a ce da mutuwa Beelal ɗin ya yi ake bata haƙuri da sauƙi tun da dama kowa ya san mutuwa dole ce, amma yanzu kuma yana raye bata san halin da yake ciki ba wannan abu yana matuƙar sanya zuciyarta damuwa.

Fakyar ta iya yiwa Babangida godiya ta juya ta shige gida, dan mutane har sun fara taruwa masu son jin ƙwaƙwaf suna tambayar Babangida ba a samo Beelal ɗin ba, bayan da lokacin yana nan babu wanda ya damu da su.Fatima kuwa ta san tana buɗe baki kuka zai ƙwace mata dan yanzu ma burinta kawai ta gan ta a cikin gida.

Tun da ta shigo cikin gidan idanunta suka sauka a kan kayan Beelal na wanki wanda ta wanke masa jiya da yamma, tana kallonsu wata shuɗiyar riga da shi da kansa ya shanya rigar yana ta cewa take bashi shi ma yana wankin, ta ce sai dai suke shanya tare saboda hannunsa marar lafiyar har yana cewa idan ya ƙara girma zai ke yin wankin take ce masa.

"Haba Beelal ai duk girmanka ni zan ke maka wanki saboda larurar da ke tare da kai, idan kuma Allah ya hore mini sai in ke biya ana wanke maka idan ka yi aure dan kar a ɗorawa matarka wahala dan ba kowace mace ce za ta ɗau ɗawainiyar wanki ba bare matan yanzu da basa son wahala su ma so suke a hidimta musu"

"Ni ba wani aure da zan yi Mama a gida zan zauna muke zaman mu tare da ke, ni fa a duniya kwata-kwata ba na son rabuwa da ke sai sai in mutuwa ce kaɗai za ta raba mu ita ma dan dole ce" Wannan kalaman nasa na jiya suna faɗo mata sai kuwa wani kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata ganin gashi ma ashe kwana ɗaya ya rage musu jiyan raba tsakaninsu duk da kasancewarsu masoya na haƙiƙa amma rashin imani da tsoron Allah ya sanya Idrisu ya raba su, idanunta ta sauke a kan katifar da Idrisu ya kwanta a kanta jiya wacce ke a waje ɗaure da net ɗin da ta sanya masa wani haushi da takaici ta ji a lokaci da ta kalli katifar kuka ne ya ƙwace mata. Hannu ta sanya ta toshe bakinta da kukan ke fitowa ɗaki ta nufa da ɗan gudu-gudu, tana shiga ɗakin ta faɗa kan katifar ta a ribda cike ta kwanta tare da kifa fuskarta a kan tafukan hannayenta ta saki wani kuka mai ƙarfi wanda yake fitowa da ɓacin rai haɗe da zunzurutun kewar ɗanta tilo Beelal, tana jin zafin da zuciyarta take mata, tausayin yaronta yana daɗa ninkuwa a ranta tana tunanin irin rayuwar da zai yi a wani waje da babu ita babu wani wanda ya sani sai Idrisu mutumin da ba ya ƙaunarsa kuma yanzun ma ta tabbata ba ƙaunar ce ta sanya ya ɗauke yaron ba, illa wani ƙudiri nasa marar kyau da Allah ne kaɗai ya sani, tausayin Beelal na ƙara shigewa zuciyarta tana tunani ya zai ke aiwatar da abubuwan da ba ya iya wa sai dai ita ta masa saboda NAKASAR da ke tare da shi.

Sai da ta yi kuka mai isarta, aikuwa idanun suka sake suntumewa, amma bata damu da hakan ba, cikin sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi ta ɗauki abu ta goge fuskarta tas, da hanzari ta tashi domin duba wayarta wacce Hajiya Laɗifa ta turowa wani mai pos da ya tura mata acc no sa ta turo kuɗi aka sake mata wayar ko sati biyu bata yi ba, fatan ta dai Allah sa Idrisu bai ɗauke wayar ba, wurin da ta ajiye wayar ta je ta duba cikin ikon ALLAH sai ta ga wayar tana nan, dan dama ta siyar da tsohuwar, hannunta har karkarwa yake da ta ɗakko wayar dan ta tabbata idan har da ya ɗauke wayar shikenan ya datse mata abin da ta saƙa a ranta yanzun nan. Wayar ta kunna ta kamo sunan Yayarta har ya kira kafin kiran ya shiga sai ta katse saboda tana ganin Hajiya Laɗifa idan ta ji abin da take shirin yi za ta iya dakatar da ita dan haka sai ta fsa kiranta, buɗe wayar ta yi ta fitar da sim ɗin ta karya shi, cikin hanzari ta tashi kamar an tsikareta ta fito da sauri, takalmanta ta saka ta nufi hanyar ƙofar gida.
Chapter 8 · 0% Book details