Sashe 7
Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hameedatuwa kuma suna ne?" Cewar Hajiya Zulaiha tana kallon Ramma.
"Eh mana" Cewar Ramma.
"Ke yarinya ya sunanki" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda.
"Hameeda" Cewar Hameeda tana wasa da yatsunta na hannu.
"Ma sha Allah suna mai daɗi" Cewar Hajiyar tana kallonsu.
"To Hajiya ya kika ganta ta yi kuwa?" Cewar Ramma tana washe baki.
"Haba Ramma wannan ai ta yi ƙanƙanta, ba za ta iya yin aikin da nake buƙata ba sai dai kawai a barta take yin goge -goge da ɗan abubuwan da ba a rasa ba"
"Hajiya ƙanƙantar ta kike gani, amma wannan babu abin da ba za ta iya ba saboda mariƙiyarta sai da ta tabbatar ta hore ta sannan ta bayar da ita aiki"
"Ikon Allah, wato ma ba mahaifiyarta bace ta bayar da ita?"
"Eh ba ita bace mahaifiyarta ta rasu ita da mahaifin suka ci maganin ɓera a abu shi ne silar barinsu duniya, ita wannan matar Yayan Babanta ce"
"Ayya marainiya ce ashe?"
"Eh wallahi"
Hameeda tun da suka fara maganar iyayenta, hawaye ya gama wanke mata fuska, sosai rayuwarta da mahaifanta ta dawo mata da Yayanta Beelal amma mutuwa ta mata yankan ƙauna, gashi Beelal ɗin ma an rabata da shi, Allah sarki maraici.
Jaraba Ramma ta fara mata wai daga zuwan su ta fara kuka saboda ita kuka ba ya mata wahala, sai da Hajiya Zulaiha ta ce ta ƙyaleta ai kuka dole ne kuma wajibi ga duk wanda ya rasa iyaye tabbas ya yi kuka.
Abinci Hajiyar ta sanya aka gabatar musu Hameeda dai bata ci ba amma Ramma ta zage ta ci ta ƙoshi duk da sun ci abinci a wasu gidajen da ta je kai sauran yaran amma a nan ɗin ma dai bata tsallake tayi ba. Sai da ta ci ta yi nata sannan Hajiya ta kawo kuɗi dubu goma ta bata kuɗin aikin Hameeda na watan da za ta fara sannan ta bata dubu biyar nata da atamfofi guda biyu, haka ta yiwa Hajiyargodiya tare da sallama ta tafi tana murna, da yake tana da ƴar uwa a cikin Katsinar to a can take zaune sai dai ƴar Mai mazari ce tana zuwa lokaci- lokaci.
Tun da ta tafi Hajiya ta sanya wata dattijuwa mai mata aiki mai suna Baba Ramatu ta tafi da ita sashensu na ƴan aiki. Baba Ramatu a ɗakinta ma ta ce Hameeda ta zauna saboda ganin ƙanƙantar ta bata ce ta je ɗakin sauran ma'aikatan ba kuma tana ganim ta yi ƙanƙanta a ce ta zauna a ɗakinta da ban Sosai Hameeda ta ji daɗin zama a wajen dattijuwar saboda yadda take bata kulawa da nuna tausayi a gareta.
Bayan sallar magariba Hameeda Hajiya ta bata plates daga kicin ta kai kan dinning, da sallama ta shigo falon da ƙaran TV a cika shi, tana shigowa ba tare da ta tsaya komai ba ta nufi kan dinning ɗin za ta ajiye plates ɗin.
"Ke! Bakya ganin mutane ne ko baki iya gaishe da mutane ba" Cewar wani matashi da ke zaune a kan kujera ya jingina bayansa a jikin kujerar ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana danna waya ba tare da ya ɗago ya koda kalleta ba.
Da sauri ta baro dinning area ɗin ta taho har gabansa ta zubar da gwiwoyinta a ƙasa ta ce.
"Barka da dare" A fusace ya ɗaga hannu zai wanke ta da mari Hajiya da fitowarta daga kicin kenan idanunta suka sauka a kan su cikin hanzari ta ce.
"Kar ka kuskura ka dake ta musty shin me ma wannan ƙaramar yarinyar ta maka da zaka ɗaga hannu ka dage ƙarfinka za ka duketa?" Ta faɗa tana ƙarasowa wajensu.
Jimƙe hannun nasa ya yi wanda zai yi marin da shi ya naushi iska yana wani kumbura baki, tare da aikawa Hameeda wata uwar harara.
"Hameeda me kika masa?" Cewar Hajiya tana kallon Hameeda da ke dafe da kuncinta dan tun da ya ɗago hannu zai mareta ta sanya hanu ta dafe kumatunta, duk da cewa mari duka da duk wasu uƙubobi babu wanda bata fuskancesu ba a hannun matar wan mahaifinta.
*BEELAL*
Tun da ya fara tuƙa keken nan sai ya ji gabaɗaya tausayin kansa ya kama shi, tabbas ana shiga damuwa idan aka rasa iyaye kamar yadda ya ga Hameeda ta shiga ƙuncin rayuwa tun daga lokacin da iyayenta suka rasu. Sai dai shi gashi iyayensa a raye amma ya zama tamkar maraya marar uwa da uba.
Duk da cewa babu sanin mahaifiyarsa, kuma babu hannunta a tahowarsa amma dai ga mahaifinsa nan da saninsa kuma da sanya hannunsa kai shi ne ma ummul aba isin shigarsa wannan halin. Haka ya cigaba da tuƙa tsohon keken nan gashi babu katifa ko wani tsumma a wajen zaman, ga duk tsatsar jiki sai zuba take jajawur da ita, hawaye gabaɗaya ya gama wanke masa fuska a lokacin da ya tuno irin halin da Mamarsa za ta shiga ta kuma kasance a duk lokaci da ta gane ba ya nan, sannan ya san da ace ta san yana nan yana bara to da kuwa ya san ko ta halin ƙaƙa ba za ta bari haka ta kasance ba. Hannu ya sanya ya goge hawayensa saboda ganin ya zo cikin mutane. Haka ya ƙarasa wani waje inda mutane ke ta siye da siyarwa ya tsaya daga gefe kusa da wani maina, yana tunanin ta ina zai fara bara.
Bayansa ya waiwaya inda su Idrisu suke, aikuwa dama kamar jira suke suka fara wani ɗaɗɗaga masa hannu suna masa alama da ya fara bara, kansa ya ɗauke daga kallonsu, zuciyarsa na masa ƙuna wai yau shi ne zai yi bara ba wai kuma dan ya fi ƙarfin hakan ba sai dan wadatar zuci da suke da ita shi da mahaifiyarsa duk rintsi basa yin bara duk halin da za su shiga kuwa. Yana cikin tunanin abin da zai ke cewa in zai fara barar ya jiyo waji sautin wani almajiri yana cewa.
"A bani ta annabi, a taimaka min da sadaka da abin da Allah ya hore" Cikin sauri Beelal ya waiga ya kalli mai barar aikuwa idanunsa suka sauka a kan wani matashin gurgu da ke rarrafe a ƙasa, gwiwar ƙafarsa ya sanya tsumma ya ɗaure saboda rarrafen, sannan takalmansa sai ya saƙala kowane ɗaya a hannu ɗaya yana rarrafawa gabaɗaya ƙafafunsa a lanƙwashe suke, da sauri Beelal ya kalli keken da yake zaune a kai sai ya ga da wannan gurgun ya dace ba shi ba, sai ya ga gurgun ya fi buƙatar keken ba shi ba da yake da ƙafafunsa amma dole uwan naƙi ta sanya shi ya hau ba tare da ya shirya hakan ba. Ƙwallar da ta cika idanunsa ya yi ƙoƙarin maidata, cikin sanyin jiki ya fara tuƙa keken a hankali wajen mutane ya nufa amma laɓɓansa sun ƙi bashi haɗin kai ya furta abin da yake son furtawa. Yana nan ya ga wannan gurgun ya zo ta kusa da shi ya wuce. ganij a wurin babu wanda ya baiwa gurgun sadaka sai ya cigaba da ɗan tafiya kaɗan ya ƙara tsayawa ba tare da ya ce komai ba.
"Ungo nan almajiri" Cewar wani mutum da ke suɗe hannu yana miƙawa Beelal sauran abinci a cikin kwano. Hannu biyu Beelal ya sanya ya karɓi kwanan yana mai cewa.
"Allah saka da gidan aljanna"
"Amin yaro" Cewar mutumin yana wanke hannunsa da pure water.
"Idan ka cinye ka baiwa waccen mai siyar da abincin kwanon" Mutumin ya faɗa yana nunawa Beelal wata budurwa dake siyar da abinci.
"To" Beelal ya ce, ganin mutumin ya juya ya yi tafiyarsa, sai ya ɗakko ledar da Imran ya bashi ya shiga juye abincin a ciki dan ya tabbata su Imran suna hangoshi yunwa yake ji amma babu damar ya ci saboda kar ya yi laifi haka yana ji yana gani ya kuye abincin ya ƙulle ledar tare da rataye ta a jikin hannun keken, kwanon ya suɗe tare da hannunsa ya ƙarasa ya baiwa mai abincin kwanonta, ya ɗauki wata buta mai ruwa da ya gani a wajen ya wanke hannunsa, ya cigaba da zagaya wurin amma har lokacin bai yi bara ba.
MMN AFRA 09030283375
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦
NA
MAMAN AFARAH
*FCW*💛
Book 2
Page1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣
*FATIMA*
Tun da Babangida ya ɗauke ta a machine ɗin gabanta yake mugun bugawa tana jin kamar dai akwai wani abu da ke shirin faruwa dan haka sai ta kasance a cikin muguwar damuwa. Tafiya suke amma gani take kamar ma basa sauri gani take garin ya mata nisa sosai. Sunayen Allah ta fara karantowa tare da yiwa annabin rahma S.A.W salati cikin hikimar ubangiji sai ta ji hankalinta ya ɗan kwanta ta samu nutsuwa.
Suna shiga garin suka yi tambaya gidan su abokin Idrisun sai wani daga cikin mutanen da suka tambaya na majalissar ya kwatanta musu inda za su samu mutumin.
Haka suka tafi wajensa, tun daga nesa suka hangoshi a wajen mai gyaran machine yana tsaye ana duba masa iska a machin ɗinsa. Sun kusa ƙarasawa sai machine ɗin nasu ya tsaya, da sauri Fatima ta sauka daga kan machine ɗin dan ita dama ji take kamar ta tashi sama ta isa gareshi.
Cinkin hanzari ta isa wurinsa har tana tuntuɓe zuciyarta tamkar ta tsaga ƙirjinta ta fito haka take ji musamman da ta hango shi babu Idrisu bare Beelal, amma dai tana rayawa a ranta cewa ba zai rasa sanin inda suke ba tun da an sanar mata shi ne ya ɗaukesu da daddare.
Gabaɗaya bata cikin nutsuwarta dan haka komai ya kwance mata, sallama ma baya zo mata a ranta ba, shi ma abokin Idrisun da bai kula da zuwanta ba kawai sai ganinta ya yi a gabansa tamkar an jefo ta. Kafin ya gama tantance daga ina take, mai kuma ya kawo ta sai ji ya yi ta jefo masa tambaya.
"Ina Idrisu yake???" Ita ce tambayar da ta fara jefo masa, da farko bai gane ta ba sai da ta yi masa tambayar ya gane matar Idrisun ce. A maimakon ya bata amsa sai ya fara zare ido kamar ya yiwa sarki ƙarya, abinka da marar gaskiya ko cikin ruwa sai ya yi gumi a take a wurin sai ya fara inda-inda a maimakon ya bata amsa kai tsaye.