Sashe 6
Beelal Buk Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah jama'a ku jijjijgani in falka daga wannan mummunan mafarkin da nake, mafarkin nan da yake kokarin rabani da wanda na fi ƙauna duk cikin duniyar nan, shin ya mutum zai ji a lokacin da aka rabashi da wanda ya fi ƙauna? Ya uwa take ji a lokacin da mutuwa ta rabata da ɗanta, duk da ta san mutuwa dole ce kuma wanda ya karɓi kayansa dama shi ne ya bata kuma ya fi ƙaunar ɗan nata fiye da yadda take ƙaunarsa, amma a haka take jin damuwa ta mutuwar ɗan nata shin ni kuma da wane kwatance za a kwatanta halin da nake ciki, har gwara mutuwa mutum ya ce mutuwa ce amma fa a raba uwa da ɗanta bayan yana raye shi kuma wane irin ƙunci zuciyar uwa za ta shiga? Shin matan aure da mazanjensu suke sakinsu su rabasu da yaransu ya suke ji a duk lokacin da suka koma gidan iyayensu , ji suke tamkar an rabasu da wani sashe na farincikin rayuwarsu, a koyaushe uwa tafi so ta kasance a tare da ƴaƴanta, idan har wacce ta baro yaranta a gidan mijinta za ta shiga damuwa duk da ta san inda yaran suke, to ina kuma ga wacce bata ma san inda yaronta yake ba, sannan ta san yaron yana hannun wanda baya ƙaunarsa, dan Allah jama'a ku kwantanta yadda nake ji yanzu a cikin raina, kowa ya san Idrisu ba ya son Beelal saboda nakasar dake tare da shi, kamar yadda mutanen gari ma basa son sa basa ƙaunar ya raɓi inda suke ma, yau kuma ya ɗauke min shi cikin talatainin dare ya gudu dashi dan Allah ku taimaka min" Fatima dake bin mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya tana kuka tare da neman agaji a garesu dan ta kasa dakatar da zuciya da kuma hawayenta, babban tashin hankalinta ma shi ne ina Idrisun ya kai yaron. Kowa na wurin babu wanda za ka kalli fuskarsa ba tare da ka yi arba da hawaye sun gama wanke masa fuska ba, gabaɗaya wurin sun matuƙar tausaya mata irin tausayin da kaf garin babu wanda ya taɓa musu, haka suke rayuwa a cikin garin tamkar wasu haure da basu da kowa da komai a cikin garin, amma sai gashi yau sanadin kalaman Fatima kowa ya ji tausayinsu ya kamashi, kalaman Fatima kalamai ne wanda akwai hikima, ilimi da kuma iya furta kalma kowacce a mazauninta an bata haƙƙinta. Haƙuri aka shiga bata wata dattijuwa ce ta kama Fatimar ta rungume ta dan ta samu sassauci, dan tabbas a duk lokacin da ɗan adam ya tsinci kansa cikin damuwa to idan har aka rungumeshi aka lallashe shi to ko da a ce damuwar nan bata bar shi duka ba zai samu sassauci ko da kaɗan ne a cikin ransa. Musamman a ce wanda zai rungumi mutum ya kasance uwa ce wato mahaifiya dan ita uwa ɗumin jikinta da ban yake haka nan soyayyarta ta zarta ta kowa ta kuma wuce a misalta ta. Fatimar kwa kamar jira take sai kawai ta kwantar da kanta a jikin matar da ta mata ƙawanya da hannayenta a bayanta, Fatima idanu ta rufe hawaye na kai koma a fuskarta, ji take tamkar a jikin mahaifiyarta, ko Kakarta, ko Yayarta take domin su ne duk duniya suke bata mafaka a baya kafin barinsu duniya, yanzu kuma sai Yayarta Hajiya Laɗifa kawai wacce kuma yanzu ta yi nisa da ba za ta samu taimakon gaggawa na runguma da lallashi a gareta ba.
Da a baya ko Yayarta bata nan idan tana cikin damuwa mijinta wanda ya kasance abin so da ƙauna a gareta wato Idrisu shi yake sanyata farinciki a duk lokacin da ta shiga damuwa in Yayarta bata kusa, kafin ya juya mata baya, kafin ya sauya mata daga Idris zuwa Idrisu, kafin ya manta da so da duk wata ƙauna da yake mata ya maye gurbin ƙauna da ƙiyayya, haka kuma ya yi watsi a duk wata kulawa da nauyinta da ke kansa, kafin ya canja daga fari zuwa baƙiƙƙirin wanda har yau bata san dalilin yin hakan ba, duk da an ce mata da dama su kan auri namiji aure irin na so da ƙauna amma idan an je gidan daga baya komai ya kan canja, sukan rasa duk wanann abubuwan zaman ya dawo sai na haƙuri da zaman ƴaƴansu, amma ita nata salon da ban yake da na saura dan ita abin ya wuce misali sai dai fatan Allah kawo ƙarshen abin.
Dattijuwar nan bata cire Fatima daga jikinta ba har sai da ta ji ta ɗan tsagaita kukanta tana sauke ajiyar zuciya, sannan kuma Fatimar ce da kanta ta ɗago kanta daga jikin tsohuwar tana share hawayenta, dan kuka ya zame mata jiki dan ita kullum idan har za ta tuna da damuwarta to kuwa za ta kasance ne ciki kuka, kuka kamar matar marigayi, dama kuma Beelal shi ne yake ɗauke mata kewa da duk wata damuwa, zama da ita ne da kuma halin da suka tsinci kansu shi da ita ya sanya yaron ya zama tamkar wani babba, ya iya lafazi da kalamin da yake kwantar mata da hankali waɗanda a wajenta yake koya saboda da su take amfani wajen lallashin sa da kuma koya masa zama da mutane da haƙuri da rayuwa a duk halin da mutum zai tsinci kansa daɗi ko akasin haka.
"Bari na je na bi sawu na karɓo Beelal ɗin na gane garin kusa da Kazaure ne wajen abokinsa ne zan je in gani" Ta faɗa tana runtse idanunta ta buɗe su ko ta ke gani sosai saboda kukan da ta yi sun kumbura suntum, har bata iya gani sosai.
"Babangida ɗakko machin ka kaita" Cewar wani mutum da ke tsaye ya faɗa wa ɗansa, da to matashin ya amsa ya je ya ɗakko machine ɗin Fatima ta hau ya ja suka tafi kowa yana tsaye ana jimantawa har sai da suka daina gango machine ɗin su Fatima sannan kowa da ya taru ya watse dan lokacin sosai rana ma ta fito wajen ƙarfe tara saura ne.
MMN AFRAH 09030283375
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BEELAL*
💦💦💦💦💦💦
NA
MAMAN AFARAH
*FCW*💛
Book 2
Page 9️⃣➡️1️⃣0️⃣
*KATSINA STATE*
*UNGUWAR* *KAFIN SOLI*
~HAMEEDA~
Tun lokacin da Ramma wacce za ta kaita wurin aiki ta je ta taho da ita, Ramma tana kai yara ƴan mata da yara mata gidan masu kuɗi su yi aikace -aikace kama daga shara wanke-wanke goge-goge raino da dai sauransu. Ta tafi da Hameeda da sauran wasu yaran a inda ta yiwa iyayen kowacce yarinya alƙawarin idan an biya kuɗin aiki za ta kawo musu sannan duk ƙarshen wata idan aka bada kuɗin aikin yaran za ta kawo musu ita ma su bata kason ta. Garin Katsina ta nufa da su Hameeda su bakwai ne amma Hameeda ce ƙarama a cikinsu.
Sai da ta kai duka yaran saura Hameeda kaɗai ta rage dama kuma akwai wata Hajiya da ta ce tana son yarinya ƙarama dan haka can gidan Hajiyar suka nufa.
A ƙofar tangamemen get ɗin ɗan sahun ya ajiyesu Ramma ta biya shi kuɗinsa. Tun da aka sauke su a ƙofar gidan Hameeda ta maida hankalinta kwacakom a kan tsararren gidan kallo kawai take tana tunanin gida ne za a kaita aiki.
"Wuce mu je kin tsaya saboda ƙauyanci kina kalle-kalle" Muryar Ramma ta katse mata tunaninta, cikin sauri ta yi gaba riƙe da ledar kayanta. Sai da suka je jikin get ɗin Ramma ta sanya hannu ta shiga ƙwanƙwasa get ɗin gidan, mai gadi ne ya buɗe ƙofar ganin Ramma sai ya washe baki ganin Ramma dan ya gae ta Hajiya Zulaiha matar gidan ta sanar da shi zuwanta kuma sai da ta tabbatar ta masa kwatancenta dan dama tana ɗan zuwa gaishe da Hajiyar lokaci zuwa lokaci.
Gaishe da shi Hameeda ta yi cikin ladabi ya amsa yana gaishe da Ramma suka gaisa tare da tambayar bayan saduwa. Cikin gidan suka nufa domin Hajiyar ta san da zuwansu, kuma gidna ba baƙon Ramma bane, Hameeda gabaɗaya ta shagala da kallon cikin gidan dan sai da ta ga cikin gidan ne ma ta ga ashe dai bata ga komai a waje ba gidan ya haɗu ya kuma tsaru. Ramma ce ta wani fisgi hannunta suka fara sauri sai wani hararar Hameeda take, a ƙofar part ɗin Hajiya Zulaiha suka tsaya Ramma ta fito da waya ta kira Hajiyar ta sanar mata gasu a ɓangarenta, umarni ta musu a kan su shiga, haka suka kutsa kai cikin ɓangaren nata, tangamemen falon da ya gaji da haɗuwa da kayan alatu suka shiga bakinsu ɗauke da sallama sai dai ba kowa a falo dan haka shiga suka yi kawai tun da ta ce su shiga.
A ƙasa Hameeda ta zauna rungume da jakar ledarta, sai ƙarewa falon kallo take tana rayawa a ranta wannan ce aljannar duniya. Ramma kuwa kan kujera ta haye ɗare -ɗare. Jim kaɗan sai ga Hajiya Zulaiha tana sakkowa daga upstairs sanye take da rigar leshi an mata ɗinkin buba, sai sarƙa da ɗankunne na gwal sanye a jikinta, ƙafarta cikin takalmi wanda ya yiwa ƙafarta kyau. A hankali take sakkowa kai da ganinta ka san kuɗi sun samu wurin zama, Ramma ganin Hajiyar na sakkowa sai ta sauka daga kujera ra zauna a ƙasa tana washe haƙora.
Ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata falon ta samu ta zauna, da ɗan murmushi a fuskarta take kallon kyakkyawar fuskar Hameeda a gefe ɗaya tana ganin kamar ta yi ƙanƙanta a kan aikin da za ta mata, sannan kuma tana ganin wautar wasu iyayen dake aika yaransu aikatau ba tare da tabbas ɗin a hannun waye za su yi aikin ba ko kuma wane irin zama za su yi a gidan su dai kawai burinsu a samo kuɗi a basu.
"Hajiya barka da yamma" Cewar Ramma tana ɗan rusunawa daga zaune da take.
"Barka Ramma ya hanya"
"Lafiya lau wallahi "
"Saukar yaushe?"
"Wallahi da azahar muka sauka to na tafi raba sauran yaran gidajen aikinsu, to wannan ita ta rage kuma ita na ga ta yi dai dai da wacce kika ce kina so" Cewar Ramma tana nuna mata Hameeda.
"Ina yini" Cewar Hameeda cikin sanyin murya.
"Lafiya lau, yarinya ya sunanki?"
"Hameedatuwa" Ramma ta karɓe.