← Book details Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BASAM ne yakaraso wajan dasauri yafito amotarshi yayinda jama'ar wajan suketa kallonsu ana nunashi shine wannan dan kwallon dokin,'

Yakaraso yanata gaggaisawa da mutane kana yashiga Gidan yaimusu ta'aziyya nanyaga Ummu tasaka Khadija ajikinta tana rarrashinta,'

____"BASAM kaga ikon Allah ko mutuwa kenan medauke wanda wa'adinshi yacika kowa dan hakane,'. Momy da kausar suna asibity wajan meenal tayanke jiki tafadine,'

___"to ummu Allah yajikan mama khadija sai hakuri kiyi hakuri nizankoma waje wajan maza,'

Yafita yasamu gefen wasu matasa yatsaya yayi shiru shikanshi baisan meyake tunaniba wadannan matasa kuwa saisuka soma magana,'

___"ohhh mutuwa kenan yanzu gashi mamansu meenal tarasu zataje ta taradda diyarta wanda suka jagoranceta tamutu wajan subarda cikin shege ,'

BASAM yayi tsai tareda mamakin abunda samarinnan suke fada amadu yace,'

____"duniya ba gaskia saikuga yarannan acikin hijabi da kamala a fuska amma abun ba hakaba shege ayarsu sukeyi awajan layi inace ahakanne Fatima kanwar tasu takwaso cikin shege Yan uwanta kuma sukakaita azubar garin zubarwan kuma tarasu ohh jama'a

Bello yace,'

____"kuhangacan zakuga Anas inace shine da zai auri meenal din har anmusu baiko iyayan sukaji labarin yaisu meenal Yan iskane rikakkun Yan iska kanwarsuma garin zubarda ciki tarasu akafasa to kamun Anas dinma kunga wancan farin saurayin?,' dukkansu sukajuya sukaga Yusuf ciki harda BASAM dayakeji kanshi yana saramai ,'. ___"toda shiza yakawo sadaki akafasa Saikuma kwatsab naji labarin ta auri wani hamshakin me kudi,'. Ai inaji nace nasan baisan suwaye meenal ba shiyasa ya aureta amma dukranda allura zata tono garma zaijine,'

Sunata gulmarsu BASAM kuwa harwani jiri yakeji yayinda ranshi yayi mummunan baci yanata maimaita kalamansu akanshi aranshi yace,'. ____"lallai yarinyarnan asirinsu yatonu dan ko momy datakesanta intaji wannan labarin bazata sake kaunartaba Allah nagodema daka baiyanamun gaskia acikin sauki,'

Anfitoda gawar mama Khadija tanata kuka aka ajjiyeta agaban Gidan akasomayi mata sallah gashi tayi mutane sosai daganan aka dauki mama zuwa gidanta Na gaskia,'

ALLAHU AKBAR

Meenal kuwa anshiga da'ita wani daki anata kokarin ceto rayuwarta cikin gaggawa dakyar suka samu nunfashinta yadawo tasamu bacci dan anmata allurar bacci Dr yafito yanadan share zufarshi,'

Momy tataso dasauri itada kausar

___"Dr yaya tafarfado kuwa ko haryanzu?,'

___"relax hajia tafarfado amma munyimata allurar bacci sabida tasamu ishashshen bacci dan tana bukatar hutu kuma a kallah sai gobe da rana zata samu farkawa babu wata damuwa a tattare,' da'ita tasamu dimuwane da razana,'. Allah yabata lafiya zaku iya shiga,'

Momy da kausar suka shiga dakinnan meenal tana kwance ga Karin ruwa a hannunta fuskarta hartayi wata Yar rama kadan momy tace,'

___"Allah sarki mutuwa yanzu sunzama marayu basuda Uwa basuda uba kenanfa abun tausayine gaskia mudama bamuda uba mukeda Uwa ake tausaya mana balle megabadaya,'

Kausar tace,'. ___"nima banida uba sai Uwa yarasu banma sanshiba nikam,'

Momy tariketa gabaki dayansu sunacikin wani mawuyacin Hali,'
Meenal dai batasanma ina kanta yakeba,'

BASAM yanadai zaune acikin Yan zaman makoki yanajin labarurruka dadama akan rasuwar kanwarsu meenal wacce tamutu wajan zubarda cikin shege acewarsu fa kenan labarin aketayi BASAM yakurama Yusuf da Anas idanu yanata kallonsu,'

Aranshi yace,'. ___"suma kenan iyayansu sukaki yadda su auri meenal saini momy ta jajirce saina aureta nidanake sananne sunana bawuya zai baci ina bazan cigaba da zamada Yar iskaba sunana saiyabaci dole murabu kosunaso kobasaso domun lokacin rabuwar yazo,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*_Badiat Ibrahim_*

*______________116to120✍🏻*

"Anata zaman makoki yayinda khadija taketa amsar gaisuwa duk wanda yazo saiya tambayi meenal sai'asanar dasu tana asibity batada lfy,'

Dangin mama sunata Dora abincin daza'a fitarma da maza yayinda aketa kawo abinci daga waje waje nan fiffitarma da maza abinci sunataci yayinda BASAM yayi shiru yanata tunane tunane kala kala aranshi,' ansoma kiran sallah Na magrib awajan kowa yayi alwala akatada sallah awajan bayan an idarne akaitama mama adda'a kana aka shafa,'

Ahankali BASAM yamike tareda Shiga cikin Gidan yasake gaida matan Gidan anata ambayar yajikin meenal sai cewa yakeyi dasauki yadauki Ummu suka wuce,'

____"megida asibityn zamuje muga yaya jikin matar taka,'

Baicemata komaiba yajuya kan motar zuwa kwanar asibityn badan ranshi yasoba danyatsani yaga fuskar meenal Sam haka sukakarasa tareda kiran wayar kausar tafito taimusu jagora zuwa dakin,'

Tana kuwa fitowa tagansu suna biye da'ita harzuwa dakinda meenal take da sallama suka shigo dukkansu momy ta amsa sallamar tasu suka shigo,'

Ummu tace,'. ___"Salma yayadai jikin nata naga tasamu baccima ko?,'

___"eh Ummu allurar bacci Dr yaimata domun yace tanada bukatar Hutu dan tana cikin dimuwa saizuwa gobe da rana zata farka insha Allah,'

BASAM yakura mata idanu cikin tsana take kallonta aranshi yace,'. ___"munafuka zakiyi bayanine zamana dake yakare zan yarda kwallon mangwaro inhuta da kuda,'

Ummu tace,'. ___"ayya am Yar uwar tanacan abun tausayi tanata tunanin Yar uwarta domun yanzu meenal itace Uwa itace uba agareta mutuwa kenan Allah yasa mutafi asa'a tata tayi Kyau dantasamu mutane sosai,'

Sunata jimamin abunda yake gabansu yayinda BASAM yaji dukyatsagu yabar asibityn danji yakeyi tamkar yakashe meenal kowa yahuta tsabar tsanarta dayayi Ummu ce takatsemai maganarda yakeyi azuchi,'

___"to yanzu kausar tazauna da'ita sukwana kenan kokuma za'aje adauko daya daga cikin Yan uwanta sukwana da'ita?,'

___"aa Ummu kukutafi gida nizankwana da meenal anan basaima antaso wasuba Ai tamuce meenal wlh rasuwarnan da'akaimusu yasa nasake Kaunar yarinyar tareda tausayinta,'

__"to Allah yabaki lada Salma muzamu wuce asaukemu agida abakar zaikawo miki abinci da kayan tea saiki ajjiye saimumzo da safen,'

BASAM yace', ___"saidasafe momy saimunzo,'

Sukaimata sallama suka wuce dukkansu idanun BASAM yakada yayi jajir yayinda yakeji zuchiyarshi tanawani tafasa yarasa yadda zaitsoma rayuwarshi yaji Dadi Sam,'
Ahaka suka karaso gida

Ummu tana shiga tabama abakar komai da komai tace yakai asibity BASAM baikula kowaba yawuce kaitsaye dakinshi

Yana tsaye yarasa mekemai Dadi aduniya maganganun su amadu da bello sune suketa yawo akanshi yayinda kwakwalwarshi taketa haskomai hotunansu Anas da Yusuf yanata sintiri adakinshi yayinda idanunshi suka Tara ruwan hawaye

___"an cuceni da'aka hadani aure da Yar iska fasika mazinaciya me kisan kai domun su meenal rai biyu suka kashe sunkashe kanwarsu yayinda suka kashe abunda yake cikinta Allah ya'isa tsakanina da meenal tacutar dani data amsa sunan matata,'

Yafada kan gadanshi yana kallon sillin hawayene me dankaran zafi yazubomai a ido daya yayinda wutar tsanar meenal taketa ruruwa acikin zuchiyarshi ahaka daran yakasancema BASAM cikin tunane tunane har akakira sallar asuba yamike

Yaje yadauro alwala kana yasaka jallabiyya yawuce masallaci

Da asubannan Ummu tasaka akayi girki meraida motsi cikeda katuwar kula hardasu kaji tasaka abakar yadauka yatafi yakai sukuma suka karya suna zaune suna jiran fitowar BASAM

Fitowa yayi jikinshi duk asanyaye yagaida Ummu ta amsa tareda sakemai ta'aziyya kausar ta gaisheshi kana suka wuce kaitsaye Ummu tace awuce dasu asibity suga ko meenal ta farfado dan shadaya tawuce,'

Kafafunta suka soma motsawa ahankali yayinda taketa kokarin bude idanunta momy tamike tana tofa mata adda'a ahankali tabude idanunta tana salati hawayene yaketa kwararowa a idanun meenal,'

___"mama tatafi tabarmu ko momy tatafi kamar yadda Fatima da abbanmu suka tafi innalillahi wa'innah'ilaiyin rajiun mutuwa zanyi nima momy,' ga amanar Yar uwata khadija nabaki kikakaita Kano wajan hajia kaltume yayar mamanmu zanmutune Nima bazan yaruba,'

Sallama su Ummu sukayi tareda shigowa sukazo suka samesu ahalinda suke ciki,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*_______________121to125✍🏻*

Momy tana rikeda meenal tanaimata adda'a tana hawaye tace,'. ____"bazaki mutuba meenal bayanzuba saikinga 'ya'yanki da jikokinki insha Allah,'. Kausar kirawo Dr yazo yadubata,'

Dasauri kausar tatafi tanatajin tausayin antynta domun ahalinda take Dole a tausaya mata,'

Meenal tabude idanunta wanda suketa zubarda ruwa tace,'. ___"momy mama tatafi tabarmu wazamu dinga kallo muji Dadi yanzu?,'

___"meenal mutuwa tanakan kowa Allah baya barin wani danwani kisani iya wa'adinda Allah yadibar mata kenan kisani kuma bazata wuce hakanba kidaure kiyi tawakkali ki karfafama Yar uwarki guiwa dan Allah babu abunda mahaifiyarki tafi bukata ayanzu daya wuce adda'a domun itace iyakar soyayyar dazaki nuna mata,'

"Ummu tace ____"sannan kidaure ansani da daci amma hakuri zakuyi ki rungumi kanwarki kidinga rarrashinta dan yanzu kece Uwa kece uba agareta ayi hakuri adanne xuchiya,'

"BASAM jiyakeyi tamkar yaje yashaketa tamutu domun yatsaneta fiyeda komai arayuwarshi yatsaneta over idanunshi suka kada sukayi jajir yatsagu yabar asibityn kozaidena ganinta yaji sanyi,'

Meenal tashare hawayanta tadan samu sassauci kausarce suka shigo da Dr,'

Ya gaishesu kana yasoma Yan gwaje gwahansa yace,'. ___"amm. Jikin dasauki gaskia yanzudai abata abinci taci saitasha magani tukunna,'. Kaikuma BASAM biyoni muje office zanrubuta muku sallama kaje kabiya shikenan saikutafi gida Allah yakara sauki ko?,'

Ummu tace ___"Ameen Dr mungode BASAM jeka mana katsaya abunka kabishi kuje,'

Wani kululun bakin cikine ya turnikeshi ahaka yabi bayan Dr suka wuce,'

Meenal momy tanata bata abinci abaki kadan taci tace takoshi akabata magani tasha sukuma suka fiffita dakomai sukasa amota BASAM kawai suke jira yazo suwuce.'

Bawanda zaiyi haka yabiya kudin yadawo suka wuce meenal tana zaune tanata tunane tunanen rayuwa haka harsuka karaso kofar gidansu datasake ganin mutane zuchiyarta tasake tsinkewa tashiga hawaye,'

Ahaka aka rirrike meenal akashiga da'ita dasauri Khadija tamike tareda karasowa ta rungume meenal sukasaka kuka dasauri BASAM yajuya yafice,'

___"ayi hakuri ayi hakuri dan Allah,"

Anshigada meenal daki anata zuwa gaisheta tareda mata ta'aziyya itadai tanata daga kai dan kuka takeyi sosai dangin abbansu sunata zage zage suna surutai,'

Haka akaita zaman makoki har akayi bakwai ranar Gidan kowa yawatse yarage daga Khadija sai meenal sunadan tattaunawa,'

___"Ashe mama tayi gaskia datace cikin danginta nanan da dangin abbanmu babu me rikeki kiduba yadda suketa zaginmu suna aibanta mamanmu baiwar Allah mehalin kirki mudai babu abunda zamucema mama saidai Allah yajikanta yaimata rahma,' zuwa jibi zankaiki Kano Khadija domun hankalina yau bazai taba kwanciyaba innatafi gida nabarki kekadai anan,'

Cikin muryar kuka Khadija tace,'. ___"banaso inrabu dake Anty meenal nafiso inkasance da'Yar uwata akoyaushe amma babu yadda zamuyi dole mubi umarnin mama muyi abunda takeso.'

___"Khadija namiki alkawarin zandinga zuwa akai akai ina dubaki insha Allah karki damu kinji?.'

__"to Anty meenal inasanki sabida kimdamu dani sosai I so much love u.'

Murmushi sukaima junansu kawai meenal tatashi tasaka hijabinta har kasa tareda rataya Jakarta takamo hannun Khadija suka fito tazauna amota taciro dubu goma tace,'

___"kidinga siyan abinci kamun jibin da sassafe zanzo mutafi Khadija yanzu danatafi kisaka sakata agidan kiyi zamanki abunki banda fitowa.'

___"nagode Anty meenal Allah yabarmunke,'
Chapter 9 · 0% Book details