← Book details Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 12

Sashe 11

Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motarsu meenal ce tashawo kwanar layinnasu motocine guda uku susuna tatsakiya yayinda sauran Yan uwansu suke sauran dansundawo gidane za'ayi bikin khadija ta kammala karatunta hartasamu aikinta awani company ananne me company din yaganta yace yanaso dayake Allah yayi rabomshice shine gashi yanzu za'ayi bikin,'

Gidansu meenal din abude yake ragowar Yan uwan mamanta da dangin abbansu suna ciki anata girke girken biki danyaune za'asa Salle,'

Daga gefe BASAM ne zaune amota shida abokinshi Khalid sunata kallon kofar gidansu meenal din wanda sukaga anata Shiga ana fita da dukkan alamu biki akeyi,'

___"waini BASAM yaushe kakamu da soyayyar meenal ne metsanani haka dakullum saikazo kofar gidannan yanzufa rabonka da meenal shekara guda kenan kaduba yadda karame kayi duhu sabida soyayya dakasa agaba yakamata kaima kanka fada kilama tayi auranta kananan kanata haukarka yarinyarda ada katsani koda a ambaci sunanta amma wai yanzu itace takebaka wuya harkina wulakanta basmah akanta,'

___"✋🏻😠 dan Allah dakata Malam kabarni naji da radadin da zuchiyata takemun akan tsantsar kaunar meenal sannan tayaya meenal zatayi aure da'akwai aurena akanta aibazai yuyuba zancan basmah kuma dakake magana kaikaje ka aureta aikaima namijine meenal dinna tafimun komai arayuwata inasanta inasanta da dukkan rayuwata,'

Motarsu takaraso kofar Gidan ahankali akabude murfin motar tasako kafafunta wanda sukasha Jan lalli fulawarnam tafito tazauna afatarta sosai takalmine baki metsinin gaske akafarta ahankali tazaro jikinta sanye take dawani danyan lace baki me fulawowi pink tayi hadadden daurinta me hawa hawa yazauna akanta sosai idanunta. Manne da bakin glass metsadar gaske saidan mayafinta madaidaici pink tayi mugun Kyau takalminta dajakarta bakake sukuma sannu ahankali tasoma takawa zuwa kofar Gidan nasu ranawani shan kamshi tana daga kanta,'

BASAM yazare idanunshi tareda shagala wajan kallon meenal cikin rawar murya yace,'. ___"Khalid wannan ba meenal dinabace kuwa itace tazama haka?,'

Khalid da mamakin ganin haduwar meenal yasashi dimaucewa yace,'. ___"itace abokina amma tahadu sosai wlh,'

Khadijace itama tafito cikin ado yayinda sauran Yan uwansu tareda kawayan Khadija da kawayan meenal suma suka fito,'

Batareda bata lokaciba suka shige Gidan,'

"BASAM yaballe murfin motarshi dasauri zaifita Khalid yarike hannunshi,'

___"mekake kokarinyi BASAM karkacemun zakabi matarkane cikin danginta?,' kasani duk irin wulakancin dasukaima kaikajawo kamanta wulakantata dakayi kakoreta alokacinda take tsananin bukatar taimakonka,'

"Idanimshi suka cicciko da ruwan hawaye yace,'. ___"menene mafita yanzu khalid banaso tasake kubcemunne yanzu kaje kakira mun momy da Ummu saisuzo susushiga adawomunda matata plz bazan iya barin kofar gidannanba,'

___"to naji relax zanje inkirasu yanzu kaikatsaya ammafa karka sake kashiga ina fadama kenan,:

___"bazan shigaba kayi Sauri khalid,'

Haka khalid yaje yasanardasu momy abunda ake ciki aikuwa bashiri sukataho,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*_Badiat Ibrahim_*

*_______________156to160✍🏻*

"Suna karasowa suka samu BASAM acikin Mota inbanda kallon kofar gidansu meenal babu abunda yakeyi,'

___"BASAM gamu munzo zamuje mubada hakuri akan abunda yafaru abaya insha Allah kwantar da hankalinka,'

Yasauke kanshi yana zubarda hawaye baice komaiba Ummu da momy suka shiga Gidan da sallama,'

Kawai da meenal sukaci karo momy taganta tayi Kyau tayi kiba ga kirjinta yacika dam komanta yazauna,'. ___"meenal dina kece?,'

Gabaki daya kallo yadawo garesu meenal tataho aguje ta rungume momy saisuka kuka dukkansu suna kankame da juna hajia kaltume takada kanta kawai tanajin tausayinsu domum talura meenal takamu da matsanancin san mijinta sosai.'

____"nice momy inata missing dinki momy ina kausar?,'

Murmushi tayi ___"kausar tayi aure tana Abuja da mijinta meenal ina kikaje kikabarmu mijinki yashiga wani Hali akanki,?'

Hajia kaltume takaraso ___"sannunku meenal suwaye kuma wadannam?,'

Kanta yana kasa tace,'. ___"mahaifiyar BASAM ce da kakarshi,'

___"ayya bismillah kushigo. Mana kwatsaya anan meenal kaisu falo suzauna tunda bakowa,'

Taimusu jagora zuwa falo suka zauna anata gaggaisawa sukayi ammaba meke faruwa akasanar dasu bikin khadija akeyi sukayi murna taredasa alkhairi,'

Hajia kaltume tazo tace,'. ___"to dama kobakuzoba dama zanzoni dakaina akan maganar takaddar meenal tasaki domun yakamata danku yasaketa domun tasamu tayi auranta manema sunmata cakowa soyake ya aureta.'

"Ummu tace,'. ___"aa hajia abunda yafaru abaya aiyawuce domum mubamuda laifi yaro shine yayi kuskure kuma wlh yanzu yagane kuranshi aimasa afuwa awanke matarshi takoma suyi zamansu kuyi hakuri kuduba,'

____"babu zancan afuwa domun shima lokacin aibaimata afuwaba danhaka takaddarta kawai nakeso abamu itama tasamu freedom tayi auranta nadadi,'

___"momy tace kuyi hakuri dan albarkacin annabi da alqur'ani karku kashema meenal auranta inasan meenal asalima Nina zabamai meenal amatsayin mata azamanda nayi da:ita kitbayeta soyayya nakenuna mata dan banyarda wani Abu yatabataba sannan aranarda abun yafaru nabartane tatafi badan komaiba sabida ranta yabaci shima nashi yabaci akan in dukkansu suka sakko sai aimusu sulhu washe gari danazo natarar gida akulle mama Ladi tanada ranta ainashiga nasameta munyi magana tacemun sunce Kano zasuje amma suma basusan takamaimai akanon ina zasuba sannan acikin mutanena nasaka aimun bincike koza'agansu amma shiru dan Allah dan girman Allah dan soyayyar dake tsakaninku da annabi (S A W) kubar meenal da BASAM,'

Hajia kaltume tace kunhadamu da babban bango to badamuwa kuturomun BASAM din inji daga bakinshi tukunna,'

___"aiyana waje ina meenal taje takirashi to,'

____"meenal meenal,'

___"naam momy ina zuwa dasauri takaraso "gani momy,'

___"kifita waje kikarawo BASAM kutaho tare harda abokin nashima suzo,'

Asanyaye meenal tafita tatsaya azaure tasake kyarawa gabanta yanata faduwa tafito tanufi motarsu cikin tsoro,'

Kalid yace,'. ___"yimaza kashare hawayanka ga meenal nan tanufomun maza,'..

Yasaka tissue yagoge hawayansa daidai karasowarta

Sallamar datayi tasauya tunaninshi sautin muryarta daya sauka akunnanshi sautinda ya firgita tsigar jikinshi dasauri yadago suka zubama junansu idanu kofiyoyin soyayyace ta harbi zuchiyoyinsu dukkansu biyun tausayin BASAM yakamata taga yarame yayi duhu dashi,'

Tasauke kanta kasa,'. ____"sannunku dama cewa akayi kushigo ciki anasan ganinku,' tajuya dantaji tanasan tayi kuka dasauri suka fito sukabiyo bayanta sun tsugunna sungaida matan tsakar gida kana sukashiga falon Yan uwantane kab acikin falon saisu momy waje sukasamu suka tsugunna suka kwashi gaisuwa kana suna zauna kannan nasu akasa harda meenal ma tanaso tadago takalli farin cikinta amma abun ya faskara takasa kyaran muryar hajia kaltume ne yakatseta

__"amm BASAM gashi tamikamai bairo da takadda yadawo ya amsa hannunshi yana rawa.'

____"takaddace danakeso karubutama meenal saki uku taje tayi auranta tahuta itama,'

Jiyayi kamar ankwadamai guduma akanshi bashiri yasaki takaddar da bairon yana hawaye

Meenal itama wata faduwar gaba tayi dataji abunda momy tace tasauke kanta tana kuka dan tanasan mijinta sosai,'

Yace ___"kugafarceni wlh koda amafarki bazan iya sakin meenal ba domun meenal matatace kuma inasanta yanzu fiyeda kaina karku tursasamun insaketa domun zan iya rasa raina baki daya dan Allah kugafarramun laifinda Na aikatama meenal domun nasan natabka babban kuskure,'

__"meenal kiyafemun dan Allah nasan nacutar dake nazalunceki to ina Neman gafararki kiyafemun badanniba plzz inasanki,'

Kuka yakeyi sosai meenal tadago itama kukan takeyi tace ,'. __"nayafema dukdadai dama niban rikekaba Allah yayafemu nima kayafemun abunda naima,'

Hajia kaltume tace ____"algamdullah komai yadaidaita tunda sun daidaita Kansu aishikenan saikuma mukiyaye gaba zuwa gobe zamusamu wakilin ita meenal din shima yaturo wakilinshi sai akyara auran takoma Gidan mijinta shikenan saidai akiyeye gaba in angama biki jibi zatadawo dakinta,'

Godia BASAM yashigayi shida khalid sunata farin ciki su momy ma sunata godia sunzauna za'_ayi biki dasu yayinda Meenal tafita rakasu BASAM,'

Suna hada idanu azaure sukaima junansu murmushi jawota yayi jikinshi yakankameta suna daria rada yaimata '

___"I love u my heart I so much missed u ,'

Tawaniji Dadi yana shigarta waiyau itace ajikin BASAM kuma yakefada mata kalaman soyayya,'. ___"I love u too,'

Sukasaki juna hannunsu yana rikedana juna haryashiga Mota sannan yajuyo yana kallonta yace ,'. ____"sai gobe inmunhadu kenan ko amma zamuyi waya Ai sakamun nber ki,'

Yamika mata wayar tasakamai tanamai murmushi,'. ____"to sai kazo goben,'

____"wlh kamar karna barki haka nakeji tsoro nakehi karki gudu kabani akarona biyu,'

Daria sukasa dukkansu yashiga Mota yanatafe yanadaga mata hannu harta bace musu

Ihu yasaka tareda tafawa da khalid yanawani murna Mara musaltuwa,'

*love u oll

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN*
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*BADIAT IBRAHIM*_

*____________161to165✍🏻*

*THE END*

"Misalin karfe takwas nadaran ranar BASAM yana Gidan TV ana tattaunawa dashi kamar yadda akasaba,'

___"assalamu alaikum masu sauraranmu barka da warhaka barkanmu dasake saduwa acikin wannan shiri namu shirine Wanda yakebamu dama tattaunawa da manyan mutane wadanda sukayi suna duniya tasanmu to yauma Muna tareda bakonmu wato BASAM B SALEES ,' bakonmu bismillah,'

___"assalamu alaikum masoyana dawanda suke gaban akwatin tvnsu da wadandaba basanan inamuku fatan alkairi,'

Sanye yake cikin wasu kananan kaya hadaddu wandone fari Sol ajikinshi tareda wani takalmi green hadadde yasanya rigarshi medogon hannu shima green yatoshe idanunshi da bakin glass yayi mugun Kyau yanata murmushi

Meenal datake gaban TV tana kallon hadadden mijinta tayi murmushi wani Sanshi da kaunarshi yana shigarta

___"amm Malam BASAM kwanakin baya akwai kwallo da'akayi takasa baki daya Wanda ake gabatarwa duk shekara sannan awannan karonma ance kaikasakecin nasarar lashe gasar menene cikakken gaskiar?,'

____"ammm hakane Nina nashe wannan gasa awannan karonma sannan hakanne yasa nasake samun matsayi Na musamman gaskia ne dannayi hira da Yan jaridu dadama akan gasar danaci uhm,'

____"to Malam BASAM jita jita yayi yawa Agari wasu sunacewa kayi aure wasukuma sunacewa bakayiba shin kayi auran kobakayiba inkayi wacece wannan mesa'ar data sameka?,'

Murmushi yayi hadadde yace,'. ____"tabbas nayi aure shekara daya da Rabi dasuka wuce nayi auranne aboye cikin sirri kamar yadda naima kaina alkawari dakuma matarda zan aura cewar zamuyi auranmu aboye batareda duniya tasaniba hakane inada aure,'

___"ammm malam BASAM kozamu iya ganin matarka koda awayane domun masoyanka suma suganta susamata albarka sannan zamu iyasanin sunan Matar tamu?,'

___"dukda nakasance metsananin kishin matata amma lokaci yayi da duniya zatasan wacece Na aura sunanta MEENAL wannan shine hotonta,'

Wani katon hotontane yacika gaban TV tana sanye da doguwar Riga pink tayane kanta da bakin gyale tayi mugun Kyau tana murmushinta Na burgewa,'

Kankace Me akashiga surutai kowa da albarkacin bakinshi momy da Ummu farin ciki Mara musaltuwa a fuskokinsu meenal da Yan uwanta kuwa ba'a magana,'

___"gaskia matarka tayi sanar samunka kamar yadda kaima kayi sa'ar samunta domun tahadu da dukkan alamu kanasanta matuka,'

___"hhhhh sosai kuwa dan koda ina cikin damuwa innatuno cewar itace matata sainaji da sanyi zuchiyata tadenayin kuna nasan tana jina tana ganina u love u meenal my beautiful wife,'

Anan suka dakatar da tattaunawarsu yadawo gida angama bikin Khadija ankaita Gidan mijinta yayinda aka rako meenal gidanta tanata musu nasihohi masu ratsa xuchiya dagabaya sukayimata sallama suka wuce,'
Chapter 11 · 0% Book details