← Book details Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 12

Sashe 2

Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

___"come on Bby girl relax just smile bawani dadewa zamuyiba just 2 week's zamu dawo kinji banaso kina damun kanki I'm always with u kinji ko?,'

__"to naji heart beat dina,'

___"olrigt hot milk love u bye take care,' uhm muah kisses 😘

Kiss ya manna mata awaya kana yadawo tareda zama nanfa akabukaci dasu taso sunsoma shiga jirgi kasancewar sukadaine acikin jirgin yam club dinsu baki daya minty goma da shigarsu jirginnan yayi sama ✈ yasoma keta hazo,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓
🏓

*BASAN*🏓
*RAINA BACE*

*by______________*
*_badiat Ibrahim_*

*_______________11to15✍🏻*

Su Meenal ne suka fito daga aji antafi break Na Rabin awa azaune take itakadai tana tunanin Anas dinta kawartace takaraso gareta tazauna akusa da'ita

___"Kawata kiyi hakuri wannan wani kaddarace sannan wannan abunda yafaru rubutaccen al, amarine daga allah koda tsautsayi bai fadama Fatima ba hakan zaifaru dake Kawata akwai daci tareda ciwo wanda kakeso yake sanka yarabu dakai alokacinda kafi kowa bukatarshi lokacinda kafi tsananin bukatar taimakonshi amma yazamuyi haka allah yaso kuma kinsan ance Matar mutum kabarinshi allah baiyi zakuyi aure da samarinki biyu dasuka fasa auranki haka Allah yaso.'

Wasu siraran hawayene masu dumin gaske suka gangaro akumatunta tadago tanadan murmushi,'. ____"nagode hajjo da dukkan kulawarki agareni wlh komai yawuce inadai kokarin rarrashin zuchiyatane kawai domun kinsan taciremun soyayyar Anas araina kozan samu kwanciyar hankali Hajjo tasaka hannunta tana sharema Meenal hawayanta

Khadija wacce take bakin ajinsu tayi murmushi dan ganin yayarta tayi murmushi kanta tasauke kasa kawai,'

Misalin karfe shiddan yamma su Meenal suka tashi makaranta kaitsaye suka wuce gida suna shiga ana kiran magrib kaitsaye suka zari butoci suka daura alwala suka gabatarda Allah,'

Mama tashigo da sallama tace,'. ___"khadija jeki Dibo muku abincinku kuci kamun akira sallar isha,'

___"to mama khadija taje kichin tadebo musu jalob din shinkafa da taliya ta mankyada sunaci yayinda kowa yashiga tunane tunanen rayuwa kowa da abunda yake sakawa Meenal dai tadan cakkakala abinci tamike tareda kuskure bakinta tashinfida sallaya tasoma gabatarda sallar esha,"

Mama tace___"yayadai karatun naku ankara muku akai kuwa Meenal,?'

Kamun Meenal tayi magana yaro yayi sallama akofar dakinsu,'

___"dama Anas ne ya aikoni inkawoma Meenal wannan takaddar,'

Meenal takauda kanta gefe khadija ce tasaka hannu ta amsa tamikama Meenal bata dubaba takawai jefa acikin jakar makarantarta,' mama tadingajansu da hira tareda basu labaran abun daria har saida lokacin baccinsu yayi suka nufi dakin kwanansu,'

Meenal tana zaune atsakiyar gadanta bacci yaki zuwa mata Sam tanata tunani kanwarsu Fatima marigayiya idanu tadaga ta kalli bango hotonsune su ukune acikin hoton yayinda Fatima tadafa kafadar Meenal Suna daria,'. Meenal tatuno randa abun yafaru da Fatima,'

Da yamma ne lis mama ta aiki Fatima kai kudin adashi kasancewar layinda mama ta aiketa sabuwar anguwace akwai gine gine dadama daba'a kammalasuba anan tahaduda Yan iskan suka jata sukaimata fyade kusansu uku ahaka su Meenal sukaga Yar uwarsu jina jina dakyarma suka ganta asume kuma,'

Kukane yaci karfin Meenal tace,'. ___"Allah yasaka miki kanwata allah yasa kinhuta Allah yajikanki da Rahama,' Meenal tajuya takoma tareda kwanciya akan gadanta tareda runtse idanunta dakyar bacci yayi awon gaba da'ita taso karanta sakon Anas amma ina takasa koda bude takaddar sannan tayima kanta alkawarim bazata budeba domun ahalin yanzu tanata kokarin tursasama zuchiyartane domun tamanta da Anas,'

Dasafe Meenal tanata shirin zuwa islamiyya domun tanada jarabawa yau karfe bakwai nasafe a gaggauce tayi Karin kumallo sannan taima mama sallama tawuce dasaurinta dan batasan tayi latti,'

Tana tsaye abakin titi tarasa abun hawa duk kekenda tatawo acike take dam da Yan makaranta Meenal duktabi tadamu kanta gashi lokaci yanata tafiya,'

Suna tafe abota tana bayan motar direba yana tukata aikuwa tahango Meenal atsaye abakin titi tanata tare Keke,'

__"abakar kadawo baya daidai gaban waccan Yar makarantar,'
.___"angama ranki yadade yadda kikeso haka zamuyi,'

Meenal dataga motarnan tanufota saita sake dan matsawa gefe daidai karasowar motar gabanta Momy tazuge glass din motar cikin fara'a tace

___"'yata ina zakijene dahalama makaranta zakitafi ko?

Cikin murmushi tareda girmamawa Meenal tace,'. ___"wlh mama nadade anan wajan inata tare Keke amma shiru kowacce acike gashi inada jarabawa a islamiyya,'

Murmushi taima Meenal tace,'. ___"'yata inkin yadda da Allah kin yadda dani kishigo Mota mukaiki makaranta karkiji tsoro domun nibame cutarwa bace inkuma bakyaso shikenam ammadai bazanji dadiba,'

Meenal tadanyi murmushi ta kalli wannan hajia tace,'. ___"to mama zanshigane sabida kince innaki bazakiji dadiba nikuma banaso inzama silar rashinjin dadin wani dan haka Na yadda dake nakuma gode,'

Momy taji Meenal taburgeta azahiridai yanayinta akwai kyan nutsuwa gatada kwarjini daganinta kasan tafito Gidan tarbiya,'

Mota tabude tashiga yayinda tadan takure agefe guda,'

Momy tajuyo ta kalleta tana murmushi tadafa hannun Meenal tace,'. ___"menene sunanki,'?

Da fara'a tace ___"sunana Meenal Al amin,'

___"sunanki me Dadi Meenal gakida nutsuwa dasanin girman manya a gaskia kin burgeni kuma kin bambamta da'irin matasan Yan matan zamaninnan namu gakida shigar kamala arayuwa inasan ganin macce tana kishin jikinta tareda suturta jikinta,'

Murmushi Meenal tayi tasauke kanta kasa tace,'. ____"nagode mama,'

Murmushi tayima Meenal tace,'. ___"Meenal kikirani Momy kinji domunni tamkar mahaifiya nake agareki ,'

Kan Meenal adaure dukta takura inbanda murmushi babu abunda takeyi sunkaraso makarantar

Meenal tace,'. ____"nagode Momy Allah yasaka da alkairi naji Dadi Allah yakaiku gida lafiya,'

___"Ameen Meenal nagode nima ga wannan kyasai wani abun,' kudi tamikama Meenal a dunkule,'

__"aa wlh Momy kibarshi bazan karbaba,' tafita amotar tanadan sunne kanta kasa,'

Momy taji Meenal tarafida da imaninta domun tamatukar yaba halin Meenal sosai murmushi tayi dataga Meenal tasamu shiga class ahankali motarsu tabar bakin get din makarantar

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*_______________16 to20✍🏻*

Basam sunsauka a airport yayinda suna sakkowa motocin dazasu daukesu suka karaso kowa yashiga Mota Kai tsaye sai hotel aka diresu tareda rarrabama kowa dakinshi Na alfarma dakine da babu abunda babu aciki yahadu over kamarba hotel ba,' *BASAM* kaitsaye yafada toilet yayo wanka tareda dauro alwala daure yake da towel a kugunshi Saikuma karami wanda yakedan goge ruwan jikinshi Dana kanshi mai yadauko hadadde irinna hadaddun maza yasoma shafawa mannan ga kamshi ga laushi haka yashafe jikinshi da mannan tsab kana yadauko singlet dinshi fara yasaka tareda farin boxer wandonshi yadauko baki tsadadden gaske yasaka tareda bakar Riga hadadddiya classic nanyashiga taje sumarshi tareda shafeta damai takwanta lub lub abun shaaawa nankuma yafeshe jikinshi da tattausan turare dzaina hadadde yadan kalli mirrow *BASAM* kyakykyawane nakarshe dogone ingarman namiji me daukeda faffadan kirji domun yawan direning dayakeyi hannunshi. Amurde Amurde suke yayinda pags dinsa suke baro baro ajere abun shaawa inyasa Riga tana zamamai taimasa Kyau sosai farine Sol kamar balarabe yanada zarkadeden hanci mekamada bensir idanunshi farare kuma manya gawani Zara zaran gashi a idan nashi wandasuka Karama fuskarshi Kyau bakinshi karami kuma tsukakke lips dinshi pick abun shaawa gawani hadadden saje daya zagaye fuskarsa hakan yasake fitoda ainihin kalarshi saidan karamin gemunshi nagayu dan bantaba ganin wanda gemu ya amsa kamar *BASAM* ba inkuma yayi murmushi kumatunshi yana lotsawa dukka biyun yanada *DIMPLE'S* hakoranshi farare kamar kankara gasu shiryayyu gawani gargasar gashi wacce takwanta afatarshi tasake kyara masa skin dinshi hannunshi mekyau kasancewar yatsunshi Zara Zara dogaye abun shaawa hakama kafarshi medan karan Kyau atakaice komai nashi abun shaawane domun *BASAM YACIKA 100%* danshidin mekyaune shima yasan hakan domun kocikin turawa yashiga yafisu Kyau tareda kyan launin fata saidai inyashiga cikin larabawa saisusaje domunshi yafi kamada balarabe,'

Dadduma ya shinfida tareda hawa yasoma rama sallah da'ake binshi ya'idar kenan ma'aikatan hotel din sukashigo tareda jeramai lafiyayyan abinci a daining tasowa yayi tareda hawa daining din dan yunwa yakeji yasomacin lafiyayyan abincinnan meshegen dadin gaske harsaidayaji yakoshi sosai sannan yamike tareda zaro katan takalminshi camvars baki yadaura igiyoyin takalmin yasake kyara rigarshi sannan yadauki wayoyinshi yafita,'. Yana zuwa reasapshion ya amshi key din Mota yafice dagudu ahabar hotel din zuwa cikin gari,' sim yashiyo nacan kasar tareda dan zagawa yatsaya awani pack yana zaune yasoma kiran hot milk dinshi aikuwa ringing daya zuwa biyu tayi wub tadauka,'

___"heart beat barkanka da sauka kasauka lafiya ko?,'

Idanunshi ya lumshe yace,'. ___"hot milk kenan inata kewarki kinsani duknakasa sukuni damuwata indawo kawai inganki sai inajina wani single sabida baki a bangarena,'

___"heart beat hakika nafika san hakan yafaru domun kasan ninafi sanka fiyeda yadda kake sona kasani nasani inasanka fiyeda kaina ina tattalin ruhinka fiyeda yadda nake tattalin Nawa,'

___"I knew kina sona fiyeda yadda nake sanki but kinasani nima inashan wuya inbama tare dake Bby girl bagashi daga shigowata naje nasake sim domun inkirakiba kofa mom bankiraba kena soma kira amma yanzu zankirasu inji yadda suke saimuyi waya dake inna koma gida ko Bby girl?,'

___"olright heart beat kakira su mom dan hankalinsu yakwanta ba bye love u plz take care of ur self for me,'

Sukayi sallama yasoma kiran wayarda zata sadashi da gida,'

Ummu itakadaice agidan kausar tatafi makaranta Momy tafita motsa jiki,' taji waya tana kuka dasaurinta tatashi hardadan gudunta tana dagawa takara akunne,"

___"hellow Wake magana?,'

____" 😃😃 ahhh matas naji dadin jin muryarki harkinsani daria domun inata missing dinki me gidanki ke magana Ai,'

___"ahhhh *BASAM* kunsauka lafiya ko ya hanya toh?,'

___"alhamdullah Ummu ina kausar da mom?,'

___"kausar tatafi school mom kuma tafita motsa jiki itada direba,'

___"duk filin motsa jiki nagida be ishetaba duk kayan motsa jiki dake filin bai ishetaba saitaje wani waje kuma haba ummuna why?,'

___"tanasan tadan fita wajanne kasan zaman hakan badadi bakayin aikin komai,'

___"it's okey Ummu well dama aikenakira muyi soyayyarmu abunmu bandafa fita dankinga me gidanki baya kasar kita tawo?'

Daria sukasa dukkansu tace,'

___"kajimun ja'irin yaro aigaradai kayi aure kozanhuta nima,'

Yace,'. ___"nidama nakeda zukekiyar budurwa sankowa kin wanda yarasa innadawo zankawo miki ita kiganta ammafa nafi sanki kamar,'

Sukaita hirarsu abun shaawa haryadawo hotel din yana kwance,' sunyi sallama kowa ya ajjiye wayarshi *BASAM* bacci yayi abunshi

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN*🏓
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*_Badiat Ibrahim_*

*_________________21to25✍🏻*

Motarsu Momy ce tashigo harabar Gidan harzuwa parking place abakar yafito yabude mata kofar tafito hartasoma takawa tajuyo tace,'. ____"abakar kayi maza kayi breakfast saikakoma makarantarsu Meenal kajira atashi kakaita gida kaga Gidan nasu,'

____"angama hajia zantafi yanzu amma waye zai dauko kausar daga makaranta?,'

____"kaje kawai har zaka kai Meenal gida kadawo dan Auta sai shidda zasu fito lecture,'

___"to to hajia aishikenan nagode zantafi yanzunnan,'
Chapter 2 · 0% Book details