← Book details Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 12

Sashe 3

Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi taimasa sannan tashiga palon tasamu goggo tana karanta mijallah karasowa tayi gabanta taga tabudo shafin hirarda akayi da *BASAM*tanata karantawa ' murmushi tayi.

___"sannu da karatu Ummu kina zaune kekadai badadi ko?,:

Murmushi Ummu tadago tanayi tace,'. ___"eh shirun badadi danma megida yakirani munyi hira sosai dashi danaji shiru shiru baki dawoba shine nadauko mujalla ina karanta hira a akayi da megida Na wancan satin daya dawo daga tokky,'

___"Ummu ta *BASAM* gaskia kinasanshi dayawa kinfifa damuwa dashi feyeda autata mukam gaskia ana nuna mana banbanci bazamu yaddaba,'

Daria Ummu tayi___"Ai *BASAM* nawane saidai kuyi hakuri kawai ni damuwatama wlh auran *BASAM* Inaso inga yasamu macce ya aura nitsatstsiya wlh domun kinga kuma duk wacce zata aureshi ba lallai ta aureshi dan Allah ba kila ta aureshi dan dukiyarki kokuma dan daukakar da Allah yaimishi,' dazu yacemun inyadawo zaikawomun matarda zai aura ingani,' amma Salma hankalina dai bai kwantaba kinsanfa Yan matan zamaninnan da abun duniya yarufe musu idanu,"

Ajjiyar xuchiya Momy tayi tace,'. ___"Ummu Nima kaina wlh abunda yake cimun tuwo agwarya kenan akan matarda *BASAM* zai aura mata yanzu sun lalace dasan abun duniya indai kanada kudi Kaine nasu inkuma kudin yakare sai iskanci da wulakanci yabiyo baya wata kuma tana San namijene me dukiya danta rabashi da dukiyarshi kota halin kaka matsaloli kala kala dai to balle *BASAM* daya hada abubbuwa uku matashine mekudine star ne kinga kuwa dawuya asamu macce ta aureshi dan Allah to wlh wannan abun nasani tunani,'

___"hakane Salma zancanki gaskia ne yanzu zamani ya lalace Mata sunzama abunda suka zama saikiga yan kananan Yan mata waisuna suntirin zuwa Gidan malamai da bokaye akan maza suna jefa kawunansu acikin masifa,' Salma Nima kaina inata tunanin wacce maccece zata auri *BASAM* badan tarin dukiyarshiba badan daukakarshiba?,' azamaninnan zaiyi wuya kuma daukaka tana karewa kamar yadda kudi kekarewa kinga inhaka tafaru ananne matsaloli zamu soma tashi ta bangare dadama,"

Momy tasauke ajjiyar xuchiya tace,'. ___"Ummu akwai wata Yarinya Dana gani sau biyu Ummu nayaba da hankalinta da nutsuwarta sosai gatada shigar mutunci ga kunya ga girmama manya Ummu mundauketa amota munkaita islamiyya wlh Ummu Dana dauko kudi nabata yarinyarnan Sam taki amsa tanatamun godia tawuce tashiga makarantarsu wlh Ummu hankalina yakwanta da Meenal sosai tashiga raina,'

___"ikon Allah amma Salma da mamaki yanda yanzu zamani yacanja harkika bata kudi taki amsa Allah sarki Yar albarka tabbas duk inda tafito tafito Gidan manyan mutane dan hakan tarbiyyace mezaman kanta,' amma Salma meyasa baki kaita gida kinga gidanba?,'

Murmushi Momy tayi tace,'. ___"yanzu abakar zaikoma makarantar zaikaita gida kinga saiya gano mana Gidan,'

__"to aishikenan Allah ya tabbatar da abunda zaifi zama alkhairi agaremu baki daya,'. Mairo mairo?,'

Yar aikin ta amsa ___"naam Ummu ina zuwa,' dasauri mairo tafito tareda zubewa agabanta Mairo tajuyoda kallonta gun Momy tace,"

__"ina kwana hajia ainafito akace kinfita bamu gaisaba,'

__"lafiya lau mairo kawomun breakfast tea n bread nakeso,' sannan abakar anbashi breakfast dinshi?,'

__"eh ambashi nagama kamar fita zaiyi bara inkawo miki,'

Tamike tatafi cikin minty biyar tadawo daukeda kakkauran tea da biredi yasha bota Momy taimata godia mairo takoma bakin aikinta yayinda itakuma tashiga karyawa,'

Abakar yatafi dauko Meenal daga islamiyya yana zaune amota yana jiranta,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY__________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*___________________26to30✍🏻*

Sunfito daga class itada kawarta hajjo Suna tafe sunadan hirarsu Meenal tace,'

___"yaukam munfito da wuri gaskia kiduba kigafa saiyanzu Sha biyu tayi,'

Hajjo tace,'. ___"eh wlh ga fitowar safen wuya wlh dakyar nasamu abun hawa,'

Meenal tace,'. _____"aina manta Kawata banfada mikiba wlh dazu dasafe Ina titi narasa abun hawa kawai wata hajia tatsaya tacemun inbazan damuba sunaso sukaini makaranta dansunga inata tare Keke Kawata dabazan hauba kinsan duniya babu gaskia saitacemun bazataji dadiba inban hauba shinefa nahau muna motarnan bakiji sanyi da dadiba gashi tanata Jana da hira harmuka kawo makaranta,'

Hajjo tace,' ikon allah amma da mamaki Meenal kinsan wasu masu kudin suna kyamar suga talaka akusa dasu amma ita hartamiki tayi kishiga motarsu gaskia tanada kirki sosai gaskia,'

___"wlh hajjo hartana tabani kuma babbar mata mekyau da'ita.'

Suna fitowa meenal tahango motar Momy tazare idanunta tace,'. ___"Meenal kinga ga motar danake baki labari takawoni dasafe mesukeyi anan kuma?,'

___"wannan wai motar Meenal tohfa koma menene zamuji Ai Meenal,'

Abakar yahangosu dasauri yafito tareda tsallako titin yakaraso gabansu,'

___"sannunku kuntashi?,' toh dama hajia ce tacemun indawo inmaidaki gida nadanma jima anan ina jiranki.'

Cikin mamaki Meenal ta kalli hajjo suka hada idanu,'. ___"aa wlh nagode kabarshi zantafi gida aiyanzu akwai abubbuwan hawa nagode matuka Allah yabiyaku,'

___"kiyi hakuri wlh hajia bazataji dadiba indai tasan bankaiki gidaba malama kisa baki dan Allah,'

Hajjo tace,'. ___"badamuwa Meenal inaga kishiga motar yakaiki gida kingashi umarni akabashi saimun hadu gobe kigaida mama da khadija,' hajjo tawuce abunta

Adarare Meenal tashiga motarnan tanata nunamai hanya harsukazo bakin daidai inda suka dauketa dasafe

___"nanma zaka saukeni ya'isa nagode zan karasa gida kacema Momy nagode sosai,'

___"ahh kiyi hakuri incika ladana inkaiki Gidan mana indai babu damuwa hajia,'

Badan tasoba tace__'to muje layinnan zaka shiga kamike,'

Yasha kwanar layin tareda mikewa Meenal tanunamai kofar gidansu yana tsayawa tabude motar tashifo,'

___"nagode Malam kaimata godia inkaje naji Dadi sosai,'

___"bakomai malama Meenal kigaidasu mama inkin shiga

__"zataji insha Allah Meenal tawuce kaitsaye cikin gidansu yayinda abakar shima yaja motarshi dankomawa gida,'

*love u ollw*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*__________________31to35✍🏻*

Meenal tashiga gida da sallama khadija tana zaune tana wanke tumatur zatakai Nika mama tanakan tabarma tana tsintar wake atare suka amsa Mata sallamarta,'

___"sannu dagida mama nadawo,' takarasa kan tabarnan tazauna,'

___"harkungama kindawo gida dawuri yau Meenal,'

____"wlh kuwa dawuri aka gama ne mama kinsan menene yafaru akan hanyata tazuwa makaranta?,'

Waken da mama take tsincewa ta ajjiye tareda dafa diyarta,' ____"menene Meenal fadamun inji,'

Meenal takwashe komai tasanarda mama har kawota gida da'akayi yanzu,'

Mama ta kada kanta tace,'. ___"to mungode Allah yasaka amma kidena shiga motar mutane koda kinsansu kice kingode kinga ahalinda muke ciki yanzu saikiga wani sharrin yasake biyo baya cewar anga ansauke amota kinji ko meenal?,'

___"to mama wlh banyi niyar hawaba ita momyn ce tanace saina shiga kuma tace bazataji dadiba shiyasa nashiga sabida in girmamata kuma daya dawo daukata yadinga mun magiya akan lallai tace adawo dani gida shiyasa nashiga mama,'

Murmushi mama tayi tace,'. ___"Allah yasa mudace Allah yaimuku albarka dukkanku kitashi kije kisake kayanki ga abinci a kichin kizo kici.'

Tamike tareda tafiya daki murmushi mama tayi tabi diyarta da kallo khadija takaraso wajan mama,'

___"mama nawanke bani kudin nikan,'

__"to khadija gashi inkika ajjiye nikan saikije karamar kasuwa tabakin titi kisiyo mana nama Na Dari biyu muma mudan taba gashi ,'. Dari biyu da hamsin Tamika mata,'

Hannu tasaka ta amsa tawuce tana sanye cikin hijabi katoto har kasa,'

Meenal ce tafito daga daki tasake kaya kichin tawuce tadauko abincinta tanaci sunadan taba hira data gama sunadai zaune akan tabarma subadan aikace aikacan gida,'

Abakar yadawo kaitsaye yawuce falon Momy da sallama suna zaune momy tanacin apple Ummu kuwa tana saki tayi bacci,'

__"barka da hutawa hajia,'

__"yauwa abakar kadawo inadai fatan kakaita gida ko?,'

___"eh hajia nakaita gida dukda dakyar tayadda ma naga Gidan nasu anguwar shahararren fais ne suke,'

___"meenal kenan akwai hankali to yayi gobe zamuje darana zaka kaini saika shirya da wuri zaka iya tafiya,'

Yawuce waje yayinda ma'aikatan Gidan suketa aiyukansu masu girki nayi masu shara nayi masu wanke wanke masu shara damasu bama fulawa ruwa kowa dai yakama aikinshi haka wannan hadadden Gidan yake kasancewa kullum acikin kyara zakaganshi a tsabtace yanata kamshi abun shaawa,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
07039625239
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN*🏓
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*_Badiat Ibrahim_*
*________________36to40✍🏻*

Washe gari tundasafe Momy tagama shiryawa tsab tana zaune tana jiran lokaci domun zuwa gidansu meenal kausarce tafito tana karasowa tazube akan cinyar Momy

Sanye take cikin bakin gajeran wando tareda karamar farar Riga kanta ba dankwali

___"Momy wai ina zakijene kiketa kallon agogo?,'

Murmushi taimata tareda shafa sumar kausar tace,'. ___"zanje Gidan antynkine kausar shiyasa kikaga inata kallon agogo banaso lokaci yakure mun,'

Tashi tayi tana kallon Momy cikin tukuma tace,'. ___"antyna kuma Momy wacece ita a'ina take tayaya tazama antyna ma bansantaba ni?,'

Tadafata ,'. ____"Auta antynkice amma baki santaba itama bata sankiba but I'm sure inkika ganta zata kwanta miki aranki sosai karki damu zakisanta insha allah.' Agogo Momy takallah tareda mikewa,'

___"I have too go know idan Ummu tatashi kisanar da'ita natafi plz Auta karkifa tasheta abacci kinji magani tasha,'

Kausar tamike tareda mannama mom dinta kiss a kumatu,'. ____"saikindawo Momy bazan tashetaba nima sama zankoma indan kwanta.'

Sukayi sallama Momy tawuce kausar ma takoma sama abunta,'

Meenal tana tsugunne tana wankema mama kayanta yayinda khadija kuma take wanke wanken kwanuka mama tana zaune takurama meenal idanu tana nazari akanta,'

Meenal kuwa tashagala wajan tunanin Anas tareda abubbuwan dasuka faru take zuchiyarta ta jagule har idanunta suka cika tab daruwan hawaye,"

Sallama suka tsinkayo Na macce mama ce ta amsa tareda cewa,'. ___"bismillah shigo mana,'

Momy tashigo dasauri meenal tadago suka hada idanu da Momy dasauri tamike tsaye,'

___"Momy sannu dazuwa shigo momy gawaje kizauna,"

Mama cikin fara'a tace,'. ___"sannu dazuwa gawajan zama zauna bismillah,'

Momy taji dadin tarbar da akaimata zama tayi tana murmushi,'

Khadija tamike tareda debo ruwa akofin silver me murfi tatsugunna ta gaida Momy cikin fara'a ta amsa tareda tambayar sunanta,'.

Meenal ta tsugunna,'. ___"Momy ina wuni kinkoma gida rannan lafiya? Nagode sosai Momy,' tajuyoda kallonta ga mama tace,'. "Mama wannan itace wacce nake baki labari sunkaini makaranta rannan,'

Cikin fara'a mama tace,'. ___"ayya mungode sosai hajia da taimakonki Allah yasaka da alkhairi,'

Meenal tatashi tabasu waje,'

___"a haba haba wlh bakomai meenal Ai diyatace nayabada hankalinta Dari bisa Dari musamman danazo naga irin tarbar dakukaimun kun amsheni hannu bibbiyu batareda kunsanniba naji Dadi a gaskia,'. Hakanne yasake bani karfin guiwa kan musabbabin abunda yakawoni gareku,'

Mama tace,'. __"to Allah yasa muji alkhairi hajia,'
Chapter 3 · 0% Book details