← Book details Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

Basan Raina Bace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khadija tace,'. _____"to mama balalle bane BASAM yaci wani Abu ba domun kinga yafito Gidan arziki yasaba da cima masu Kyau to mukuma talakawane kila bazai iyacin abincinmuba,'

"Mama tayi shiru tana nazari tace,'. ____"amma khadija koda bazaiciba muyidin yagani aizaiji Dadi itama mahaifiyarshi zataji Dadi kuma hakan tamkar an mutunta meenal ne,'

___"to mama shikenan inaga to muyi jalob din shinkafa saimuyi cake saikuma drinks dazamu siya sai nama yayi Ai,'

____"to khadija kije Gidan Maman Safiya kicemata dan Allah acikin kudin adashannan tarantamun dubu uku zandawo mata dashi indai tabaki kiwuce kisiyo duk abunda zakiyi amfani dashi sabida yakwana a hannunmu dasafe ssimusoma aikin ko?,'

___"to mama bari najedin saina dawo,'

Khadija tafita abunta tareda nufar gidansu Maman Safiya me adashi takuwaci sa'a akabata kudin tashiga kasuwa tasiyo kayan cake tareda kayan lambu dazatayi amfani dashi a jalob din su kori ne dasu taim magi iri iri sannan tayiso nama da shinkafa Rabin loka sauran kudin daya saura tasiyo coke tareda ruwan gora swan,'
Haka khadija tadawo ta nunnunama mama kayan sannan suka ajjiye,'

Sukaci gaba da tattaunawa itakuma meenak tana zaune yayinda fargaba dukya cika Mata ciki,'

*BASAM* yayi wanka tareda saka rigar bacci nanyakashe wayoyinshi danso yakeyi yahuta nanfa yabi lafiyar gado yayi baccinshi,'

Daga bangaran Basma budurwar BASAM kuma tanata kokarin kiran wayar BASAM taji koya sauka lafiya amma duk layikanshi akashe suke,' duktabi tadamu kanta tanadai kwance abun duniya yabi ya isheta ,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY_________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*________________56to60✍🏻*

*SAI MISALIN KARFE SHIDDA DA RABI*
*BASAM* yafarka daga baccin dayayi ahankali yake bude idanunshi yayinda yakai dubanshi kan tabkeken agogon dakinshi me daukeda dankareren hotonshi yanakan katoton farin dokinshi yasanya fararen kaya dokinnan yana gudu shikuma yana daria sosai ahaka akadauki hoton sai akayi katoton agogon bango dashi,:

Dasauri BASAM yamike tareda fadawa hadadden toilet dinshi yasaki shawar akanshi yayi wankanshi tareda dauro alwala yana fitowa ya goggoge jikinshi da towel tareda shafe jikinshi damai yafeshi jikinshi da turare jarrabiya yazaro fara me wando yasaka yataje sumar kanshi tanata sheki kayan sunyi mugunyi mashi Kyau tamkar balarabe kiraye kirayan sallah yasomaji amasallacin kofar gidansu Wanda yake hade da gidansu fitowa yayi dasauri yanata kamshi yafice zuwa masallaci,'

Anyi sallar magrib basam yana masallaci yanata laximi har aka kira sallar isha sannan yafito yadan gaggaisa da mutane sukuma sunata tuttudowa dan sugaisa dashi juyawa yayi yakoma gida da sallama yashigo falon,'

Bakowa afalon kaitsaye yawuce shashen Momy tareda sallama,' tanakan sallaya tanajan carbi yashigo tareda zama atattausan kafet din dakin nata,'

Saidata gamajan carbinta tayi adda'a suka shafa tare tajuyo tace,'. ____"katashi Ashe natura kausar tatasheka taga bakanan sainace to katafi masallaci,"

____"eh Momy ainatafi masallaci yanzu shigowata shine nazo akan maganar dakikace zamuyi ina sauraranki,' BASAM yayi tsai yana kallon mom dinshi yaji mezatace,'

____"gaskia ne BASAM to dama bawani Abu bane akwai wata Yarinya wato damuka hadu kwanakin baya da'ita akofar makarantarsu sannan danasake fita nasake ganinta yarinyar ta kwantamun araina sosai nayaba da kamalarta da shigar mutuncinta hakanne yasa harna dauketa amota zuwa islamiyya wlh bakaji kalaman bakintaba cikin biyayya gasu masu Dadi,' sainatura abakar yaganomun gidansu kuma mukayi nasara yagano naje Gidan iyayanta Yan mutunci masu San mutane an karramani agidan sosai BASAM sunan yarinyar *MEENAL*",

Yayima Momy murmushi yace ___"Allah sarki mekikeso to aimusu suna bukatar taimakone?,'

___"eh to kusan hakan domun natura kawunanka wajan iyayanta antsaida magana yanzuma haka da baikonka akanta kaimuke jira dama kadawo sai agama komai,'

Dasauri yadago yayinda yaji wani razanannen faduwar gaba kanshi yawani saramai bakinshi yana rawa yace,'. _____"mom banganeba mekikeso kicemunne bangane hausarkiba,'

______"uhm BASAM ina nufin meenal itace matarda Na zabama kuma kawunanka sukaje nemamaka auranta kuma anbaka dan har'ankai akwatin Nagani inaso anyi baiko,'

Rassss rasss yagabanshi yasake yankewa yazube yayinda yaji kanshi yanata wani Sarawa yadafe kanshi tareda sauke idanunshi kasa zuface tashiga ketomai takota ina dukda sanyin a c din dakin wani dacine yasoma keto mashi daga kirjinshi zuwa bakinshi gawani jiri dayake kwasarshi idanunshi sukayi jajir suka cicciko da kwalla yamarasa mezaice,'

___"inkaganta zaka yaba sosai sannan kasandai bazan zabarma abunda zai cutar dakaiba amatsayina na mahaifiyarka banida burin daya wuce inga kasamu macce tagari wacce zata tsarema mutuncinka da darajar iyayanka Na tabbata meenal duk zatayi abubbuwan Dana lissafo dinnan,'

Idanunshi sunzama tamkar garwashin wuta yayinda fuskarshi tazama jajir yace,'. ____"to Momy bakomai nagode dskulawarki agareni tunda tayimiki shikenan Ai,' amma meyasa ba'ayi shawara daniba kuka yanke hukuncin........

____"aa BASAM meenal itace wacce tadace tazama matarka
Domun annabi (s a w) yace ana auran mace sabida Abu hudu,
Nafarko zaka iya auran macce sabida dukiyarta
Nabiyu zaka iya auran macce dan kyawunta
Na uku ka auri macce domun danginta wato nasabarta
Sannan Na hudu ka auri macce dan addininta
Sannan daga karshe Annabi (s a w) yabamu shawara ka auri macce ma'abociyar addini hannunka ta yalwata ma'ana iyalanka zasu tarbiyya irinta addinin musulunci
Dan haka na kwadaitama auran meenal BASAM inkanaso raina yayi fari to ka auri meenal,'

Kanshi yadafe dayake kokarin tarwatsemai wai kamarshi za'a zabama macce baza'a barshi yazabi San ranshiba yace,'. ____"shikenan Momy Na amince da auran tundahar takwanta miki aranki,"

Murmushi tayi mai,'. ___"alhamdullah naji dadin wannan zancan Allah ya tabbatar da alkairinshi sannan gobe kashirya da yamma zanmuje gidansu meenal din ,'

Aranshi yace,' ___"ninema zanje gidansu bayan ko Bby girl dina bantaba zuwa gidansuba saidai muhadu a park wainine zanje wajan wata dasunan zance tarainanima kenan hartadauka ta'isane ina bazai yuyuba gaskia,' afili yace,'. ____"gobe inada mitting dazan attending da misalin karfe uku kuma bansan yaushe zamu fitoba kibari musaka wata rana,' mikewa yayi tsaye cikin kunan xuchiya da bacin rai yace,'. ___"nizantafi mukwana lfy,'

Tace ___"to tunda kanada mitting da yamma maje da rana sabida nariga nasanar dasu goben zamuzo so yakamata muje,'

Baice komaiba yafice adakin bayako iya kallon gabanshi haka yakarasa dakinshi tareda fadawa Gado yana dafeda kanshi wanda yakeji kamar zai dagargaje yace,'. _____"why Momy meyasa zakisa baki acikin rayuwata meyasazaki zabamun Matar aure bayan inada wacce nakeso why why???,'

Yanaushi pillow dake kusa dashi tareda mikewa yazabura tace,'. ____"ina bazai yuyuba baxan auretaba domun *BASAN RAINA BACE,'* inada wacce nabama zuchiyata I'm so sorry Momy bazan iyaba,' bude kofar yayi tareda fita yanufi dakin Ummu yasameta tana zaune tanashan maganinta Na hawan jini yasamu waje yazauna babu annuri Sam a idanunshi,'

Ummu tace,'. ____"megida takobin yaki yanaga ranka abace kazomun ayanayinda bansaba ganinkaba lafiya incedai bawani Abun bane yafaruba ko?,'

Yadago idanunshi dasukayi jajir dasu yace,'. ____"magana nazo muyi domunni nasan kezaki taimakamun dan bazakiso abunda zai zamemun matsalaba arayuwata ba .'
Tasowa yayi tareda tsugunnawa agabanta aguiwowinshi biyu yakamo hannunta yace,'. ___"kitaimaka kisa baki kifadama Momy inada wacce nakeso wacce zuchiyata tazama mallakinta dan nariga nabata amanar zuchiyata Momy tazomun dawani batu wanda kwakwalwata takasa dauka balle zuchiyata plz kisaka baki tajanye furucinta,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN🏓*
*RAINA BACE*

*BY__________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*________________61to65✍🏻*

__"wlh banasanta,'

Ummu tazame hannunta acikin Na BASAM tareda matsawa gefe .'. ____"kasani duk wacce kakeso bazatakai nagartar meenal ba nima nakwadaitama auran meenal domun meenal salahace BASAM matan yanzu basuda tabbas ta'iya yuyuwa wacce kake ikirarin kabata amanar zuchiyarka ita awajanta bahaka bane ta'iya yuyuwa tanasankane dan wani Abu daka mallaka amma meenal ta amince da auranka batareda tasankaba balle tasan kokai waye tanayima mahaifiyayyar ka biyayya tareda kyautata mata danima kaina,' zama tayi akusa dashi takamo hannunshi tace. __"inasan kayima mahaifiyarka biyayya kaso abunda takeso karkaki bin umarninta akaronta nafarko data bukaci wani abu daga gareka kuma kanada halin yimata abun sannan Kai mijin macce hudune kana iya auran waccan bayan ka auri meenal,'

Hawayanshi dayaketa kokarin tarewane suka biyo kumatunshi zurrrr zurr yamike tsaye tareda juyama Ummu baya,'. ____"naji zan aureka tundakema kin amince in aureta din amma kisani *BASAN RAINA BACE* ummu I'm so much love Basma she's the love of my life yazanyi in tunkareta da zancannan ta'ina zanfara ni atsarina babu auran mata biyu kuma bazanyiba dan bazan iyaba yazanyi da Bby girl dina?,: yasauke kanshi yayinda zuchiyarshi tashiga tafasa

___"saika bata hakuri aitasan iyaye tasan mahimmancin iyaye indai da gaske tanasanka zata tayaka kayima Salma biyayya tayi hakuri tasamu wani mijin ta aura aidama ance Matar mutum kabarinshi in kaddara ta lissafota acikin matanka dole ka aureta inkuma dama ba matarka bace bazaku tabayin aureba,'. Babana kayi hakuri ka yadda zaka faranta ran Salma dani kakarka?,'

Yadago kanshi ya kalli Ummu yaga duktabi tadamu kanta gashi yana bala'in San kakarshi yadaure tareda karasowa gareta yace,'. ___"Na amince shikenan bawani Abu Ummu kiyi murmushi plz karkiyi fishi da mijinki kuma karki fadama Momy munyi wannan maganar.'

Murmushi taimasa tareda kamo hannayansa tace,'. ____"Allah yaima albarka kuma bazan sanar da'itaba aini takace kokaifa.'

Sukayi daria dukkansu yaimata sallama yafita,'

Daki yakoma yakasama yin komai yana kwance rigingine yanata tunane tunanen yadda zaiyi zuchiyarsa tanawani tafasa tunkamun yaga wacece meenal yaji duk duniya babu wanda yatsana kamarta idanunshi sunkada sunyi jajir dukyashiga firgici,'.

Yashiga tunanin Basma dinshi wanda yaimata alkawari zasu hadu yau yanada tabbacin takira wayarshi yafi sau Dari zataji akashe,' yalumshe idanunshi yayinda yabude yakurama wani zabgegen hotonshi dake jikin bango idanu shi ba hoton yake kalloba amma kai inkashigo zakaga hoton yakurama idanu tunaninshi yayi zurfi,' yabude bakinshi yace,'

___"I'm so so sorry my Basma duk duniya bawacce nakeso sama dake kuma nayimiki alkawari bazanso wataba never,'

Haka yaki bude wayarshi danyasan yana budewa zata kirashi shikuma baisan mezaice mataba dankuma yasan yana daga wayarta zatasamai kuka yarasa mekiyimai Dadi a duniyarshi gashi yakasa koda runtsawa ga yunwa yanaji but bazai iyasa komai abakinshi,'

Meenal tana kwance itama sai tunane tunane taketayi yayinda zuchiyarta tacika dam da fargaban gobe badan komaiba saidai tana tsoron ganin waye BASAM tareda fargabar karyaganta yace tafasa auranta inkuwa hakan yafaru batasan yazayi da rarraunar zuchiyarta mecikeda miki meyawan gaske

Basma tana tsaye tareda wayarta ahannu tanata Kiran layukan BASAM amma abun mamaki harzuwa lokacin akashe idanunta dasuke jike da ruwan hawaye tadago ta zubama agogo idanu karfe 2:30am nadare tafada gadanta sharab tareda sakin kuka,'. ____"why heart beat why do u do this to me baka taba sabamun alkawariba saiyau why kasan ina mutuwar sanka gashi wayoyinka duk akashe narasa yadda zanyi,'
Chapter 5 · 0% Book details