← Book details Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 8

Sashe 7

Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Jiki a sanyaye Abba da momy suka karasa gefan gadon tare da ruke mata hannu, Abba kuwa junata Ido yayi Yana kallonta cikin mamaki,momy kuwa cewa tayi" tabbas son yayi gaskiya dayace saiyazo ya dakko "yar,uwarsa sai dai Kuma wannan ba mufida bace ""me ba mufida bace to idan ba ita bace wannan wace? Cewar ADEENA "Mufida tafi wannan girma sannan mufida akwai dugon tawada a gefan idonta Kuma fatar wannan yarinyar data mufida da banbanci sannan yanayin idonsu kwayar idon nufi da bakace itakuma wannan blue ce kuma kunsan mufida ta rasu meyasa bazamu yarda da kaddara ba duk mutumin da yamutu baya dawowa kuma muma Dole saï mun je inda tatafi ,wannan dakuke gani kamace kawai da ubangiji yayi halittarsa daman ance duk mutum irinsa su bakwaine a duniya tayuwu Allah ya bamu wannan yarinyar domin ta mayemana gurbin mufida Allah sarki son yanacan Babu bacci Babu cin abinci duk Sabi da damuwa saikuma gashi Allah ya dawo Mana da madadinta tabbas Babu abin da zamuyi was Allah sai godiya" tun da momy ta soma magana sai yanzu KHADEEJA ta kula da gaskiyar lamarin tabbas itama yanzu ta tabbatar wannan ba nafisa bace domin ko a tsarin halittarsu fuskar wannan yarinyar tafi ta nafisa kyau . Shiko Abba bece komai ba sai juyawa dayiyi ya kalli ADEENA yace" yarinya yaushe akace za a sallemeku daga asbitin Nan Kuma kanwarkice wannan din" uhm a,a Abba ba kanwata bace Nima bigetanayi cikin wani hali Mara kyangani shine na kawota asbiti ananne nake ganin kamatsu da mufida shine nace afada muku" Kuma yanzu ma an sallame mu ku muke jira kawai" ayya Allah sarki munko gode sosai ina fatan zaku barmana ita murike ahannunmu ko" eh Abba mu yanzuma hucewa gida zamuyi daganan saiku huce da ita" oh Babu damuwa mungode kkwarai daga Haka abba yayi musu kyauta meyawan gaske sannan suka fito momy ta kama hannun NABEHA, Tun da suka Shiga mota NABEHA babu abin da take sai kallonsu cike da tsoro da fargaba kaddai ace dagaske tamutu wannan aljanna ne tasamu gata Haka?,bata karasa tunaninba taga an yankwa kwana sunshiga wani katafaren get Wanda shikadaine gida alayin inda kasan duk mutanen duniyane zasu zauna aciki Haka girman gidan yake ga sojoji ta ko Ina ka huce saï kaga suna dagawa su abba hannu, saï da sukayi tafiya me nisa sannan suka nufi get na beyu ananne suka karasa parking space sukayi parking sannan suka fito ,Kai tsaye gidan suka shiga a falo suka samu genaral saï sintiri yakeyi a falo Yana muzurai , tun da yaji sallamar su momy ya karaso dasauri Nan take idanunsa sukayi arba da NABEHA wadda fuskarta tayi jagajaga da majina da kwalla, Allah sarki jikinsa har rawa yake yakaraso gabanta ya Kama kafadarta yasaki wani kuka kamar karamin yaro can Kuma ya mannata a kirjinsa da saki kuka,ita kanta NABEHA batasan meyasa ba kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,dasauri ya dagota ya Kama fuskarta ya dauki lallausan hannayensa ya dorasu a kan fuskarta yashiga gogemata wahaye da majina Yana rarrashinta murya asanyaye ya ce" jery na meyasa za ahada Baki dake Amin irin wanan wasan eh meyasa eh kinsan halin da nashiga wallahi badaban irin son danake mikiba saina dakeki" Baki da hanci NABEHA tasaka murya adashe Tace" waye Kai nifa bansanka ba " Dan Allah kufuddani a haski duk kunsa nashiga rudani" zame hannunsa yayi daga kan fuskarta yayi baya kadan a razane sabi da abin da yagani" tabbas keba jery n'a bace saiyanzu nakula da kwayar idonki sanan da maganarki muryarku ba iri daya bace Wai shin dagaske jary na ta rasu hmm bakomai momy koma dai menene inason wannan domin nadinga ganinta a madadin jery inason ki barta a part Dina kamaryadda muke zama atare da jery "gabaki daya Abba da momy dago ido sukayi cikin kaduwa suna cewa"baka da hankali bazai yuwuba idan mufida maharramar kace wannan ba maharramar kabace "Abba koma dai menene Ni inason ta zauna a tare Dani" bazai yuwu ba Abba ya shiga daki fuu momy kuwa hannun NABEHA takama sukayi bangarenta suka bar genaral a tsaye idonsa cike tab da hawaye.

*Tun da suka shiga dakin momy ta zaunar da NABEHA a gefan gadon tare da fuce wa batace mata komai ba Kai tsaye bathroom ta shiga ta hada ruwan zafi wan da zai kwarara jikinta domin likita yayi mata bayanin abin da yasameta bayan ta hada ruwan ne ta dawo Bédroom d'in ta kamo hannun NABEHA suka Shiga bathroom ,zaunar da ita tayi sannan ta Kama gashin kanta tawanke shi sosai da sabulu masu kamshi sannan ta daure da tawul Tace"Zan fita Ina jiranki adaki kiyi wankan maza ki fito kada ki manta ki gasa kanki sosai" tama Gama fadar Haka tayi waje,itako NABEHA kallon tabita dashi tare da dawo da idonta cikin bandakin ganin yadda komai ya tsaru kamar ba bandaki ba ruwan wankan takalla yadda kamshi ke tashi a cikin kwamin wankan kamar ba ruwaba gashi ya canza kala daga fari ya koma blue , mikewa tayi tsaye duk da batasan yadda ake amfani da kayan bandakin ba Haka ta daure tayi wankan ,sosai taji dadin jikinta bayan tagama ne ta dauki tawul ta daura a jikinta sannan ta fito ,azaune tasamu momy hannunta dauke da wasu Kaya ruga da wando farar riga bakin wando na jins sai hula a hannun ta itama fara me tatsin Baki , tasowa tayi ta karaso ta Kama hannunta sannan ta jata zuwa gaban mudubi ta zaunar da ita,kanta ta bude Nan take yalwataccen gashinta ya bayyana dogaye masu sheki ,wayuka ta dakko ta shafa mata sannan ta taje ta gyra shi sosai tayi nata kitso daya jelar ta fada gadon bayanta tayi kyau sosai Kayan ta Mika mata bura da fant ta saka sannan ta bata farar rigar ta sa daga bisani kuma tabata wandon wayyo allah kuzokuga yadda NABEHA Takoma baturiya ay bakiga komaiba sai da tasaka hular sak baturiya Haka tazama idan ba ni danasan NABEHA ce ba da Haka zance wata balarabiyar ce ta kawo musu ziyara Masha Allah daman komai Yana bukatar gyra.

Kwallace kwance a idon momy ganin yadda taga NABEHA Takoma sak mufida Babu abin da take tinawa irin ranar da zata rasu kayannan sune a jikinta Daman ita can ba ma,abociyar sa manyan Kaya bace, allahu akbar rungumeta momy tayi Tace" Dan Allah yarinya kizauna tare damu wallahi Ina sonki" kuka NABEHA tasaki acikin zuciyarta Tace"oh wasu suna gudinka wasu Kuma suna sonka " yasunan ki" kalmar da NABEHA taji momy ta fada kenan" uhm sunana NABEHA "Masha Allah suna me dadi NABEHA zo muje kici abinci" atare suka fita falon momy rike da hannun NABEHA ,ashe Ain da suka tafi suka bar genaral yanan a zaune Yana ay kin dayasa ba wato tunanin MUFIDA, zumbur ya Mike ganin yadda yake ganin mufidansa sak ajikin NABEHA kallonta yake kamar zai hadiyeta itako NABEHA kallon sa take cike da tsoro da fargaba .

BAYAN sun ci Abincinne abba ya zo falon suna zaune itama NABEHA na zaune gefan momy sai genaral ma a Zaune ya kuramata ido kamar zai cinyeta.

Gurinne yadauki shuru hakan yasa Abba yayi gyran murya yace " yarinya yasunan ki" sunana NABEHA "Masha Allah sai gashi bakisan muba nasan abin da kikeson sani kenan yanzu suwa ye muko to insha Allah yanzu xakiji takaitaccen bayani akanmu Amma kafin Nan inason ki sanar Mana da wacece ke"wasu zafafan hawaye ne suka Shiga ambaliya aruskar NABEHA jitake zuciyarta na tukuki bakinta yakasa fadar abin da akeso tafada, abbane yasake cewa" ki kwantar da hankalin ki kiyi Mana bayani?" Sallamar Abdul ce ta katse musu maganar da suke abba kuwa juyawa yayi yace wa, alaikumussalam Abdul yanaga kadawo ina fatan andace ko" Abdul karasowa yayi jiki a sanyaye Babu kwari yace", Abba wallahi naje basanan bansan yadda zanyi ba.... Sai yayi shiru da maganar da yake ganin NABEHA a zaune "zaro Ido yayi tare da cewa keee NABEHA mekike anan" Ina su Amrah?" Genaral be yace Kai wannan fa mufida ce kamakance ne" a,a yaya wallahi wannan NABEHA ce ay nataba fadamaka nasan wata yarinya a doguwa me gama da mufida amma ita yarinyace to ay itace wannan" ke NABEHA ina sauran suke?" Kuka NABEHA take ta tashi dasauri ta karasa gaban Abdul Tace Yaya Abdul Ina su Adda Amrah da ummana?" Tayi maganar idonta cike fal da hawaye" tabdijan to kenan idan Baku tare ke Ina kika tafi wai ni ban ma ganeba mené yakawoki Abuja"? Yaya bama tare da su Tun ranar bwai na mahaifinmu ABBO FAHIMNA tatafi Dani da Adda NINEE ,Nan dai takwashe duk abin da yafaru tana kuka tana fadamasu har yadda akai ta baro gidan kuka take tana cewa" Yaya ABBO ta ci amanar zumunci danta ta cutar dani gashi bansan inda Adda NINEE takeba " gabaki daya gurin saï da suka tausaya mata hatta abba saï da ya goge kwalla shiko genaral cewa yayi", Ashe dama' akwai marasa imani aduniyarnan irinsu ABBO tabbas sun aykata babban kuskuren dasai sun karbi laifinsu sunyi shuka Kuma sai sungir ba " Allah sarki bayin Allah kenan wannan kaddara Haka gaskiya kunyi gamo da jarabawa daban daban ammma Allah baya zalinci cewar abba itako momy kara janyo NABEHA tayi jikinta ta rungumeta domin yanzune ma takejin son yarinyar yakara shigarta.

16...
Chapter 7 · 0% Book details