← Book details Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 8

Sashe 5

Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel · about 7 min read

NABEHA kuwa tun da ta bude Ido take kallon saman silif din asbitin cike da mamaki ita dai tasan tana tafi taji kamar an bigeta daga lokacin Bata Kara sanin inda kanta yakeba, kenan a asbiti nake"innalillahi wa'inna ilaihirraju un "afili tare da cigaba da cewa" meyasa baku Bari n'a mutuba dan Allah kukasheni n'a huta meya sa kuka ceci ran yarinyar da bata da kowa batasan inda zataje tasa ranta ba meyasa dan Allah kukasheni "nan danan tashiga cizge ledar ruwan datake hannunta tana sumbatu kamar mahaukaciya ADEENA dake kwance kusa da ita bacci ya dauketa da sauri ta bude idonta Tace"subahanallahi meyake faruwa ne meyasa zakiyi Haka lafiyarki fa ake so aceto kidaina "tana maganar tana rikemata hannu,kuka NABEHA take tana cewa"Dan Allah meyasa baku barni n'a mutu ba mezanyi da wannan bakar RAYUWAR komai nacikinta ya rainamin dadi banason zaman duniyar Nan ancuceni anci zarafina an lalatamin rayuwa narasa komai narasa ummana "yan,uwana yayata duk sun barni kowa baya sona dan Allah ki taimaka ki kasheni kada kiyi tunanin ko za a kasheki idan kika kasheni a,a wallahi Babu Wanda zai kasheki Ni ba kowa bace bani da kowa Ni banzace Mara galiyu Mara tushe kinsan yadda ake kashe cinnaka a zauna lafiya to kamarhaka Zaki zauna lafiya idan kika kasheni" ADEENA kuwa zuba mata Ido Tai tana kallonta yadda taga tana nemowa kanta mutuwa da kanta bayan tasan ita "Yar babban gidace, kallonta sakeyi cikin nutsuwa Tace" haba MUFIDA meyasa kikeson ki kashe kanki kinmanta yadda GENERAL MUS,AF yake sonki kinmanta kwanar da ke tsakaninmu dake da yayanki duk danginki suna sonki kowa Yana kwaunarki to danme Zaki kashe kanki" meee" ta fada tare da zaro ido Tace"Ni wace MUFIDA kuwa eh waye GENERAL MUS,AF ni bansan suba ni ba "yar kowa bace" "kar ki raina min hankali bakece MUFIDA kanwar GENERAL MUS,AF ba ?" A,a ni ba ita bace ni ban sansu ba bantaba jin masu wadannan sunan ba Tun da nake Ni sunana NABEHA Kuma Ni ba Yar kowa bace" runtse ido ADEENA tayi tare da dafe Kai azuciyarta tana cewa "ah God meyake damunane ko dai idonane yake bani kamannin MUFIDA a fuskar wannan yarinyar Kay no sai na Kira KHADEEJA ta ga abin da nake fadamata indai itama taga dagaske ne ba ido n'a bane to dole sai nanemo inda GENERAL MUS,AF yake domin namasa albishir da wannan abin farinciki tayuwu MUFIDA ce ko tasamu tabun kwakwalwa ne bansani ba shiyasa take wannan abin.

Wayarta ta dakko tare da danna numbar KHADEEJA, KHADEEJA kuwa tana daga kangado a kwance taji wayarta na ruri cikin sauri ta Mike tare da dakko wayar taga me kiranta sunan ADEENA taga ya bayyana tsaki tayi ta ajiye batare da ta dagaba tace mtseeeew wannan matar ko Yar kwaya inaga ma ganar MUFIDA ce ance mata yarinyar ta mutu ta mutu takiyar da metseeeeew shegiya yar kwaya kawai" bata karasa rufe baki ba taji karar waya Kiran ya sake shigowa tsaki tayi ta daga tare da cewa "KHADEEJA meyasa kikemin hakane wallahi dagaske nake Miki MUFIDA ce kanwar GENERAL MUS,AF ki taimaka ki zo asbitin nan domin ki tabbatar da gaskiya ko dayake kafin ki cigaba da karyatani maza hau WhatsApp na nuna Miki ta video call ", okay Bari ya tabbatar da karyarki" tana Gama fadar haka ta katse wayar ta kunna data sannan ta hau online ta Kira ADEENA video call ta daga" KHADEEJA kina karyatani kina tunanin abin da nake fadamiki karyane ko to Bari kiga ikon Allah"tajuya cemara wayar baya ta saita wayar daidai kan fuskar NABEHA dake zaune tana faman sharbar kuka, agigice KHADEEJA ta zaro Ido Tace what mezangani ADEENA kodai Ido nane MUFIDA fa nake gani Anya kuwa ADEENA mufida fa ta Dade da mutuwa waini bangane meke faruwa ba" uhm yanzu kin tabbatar ba kwaya nasha na bugu ba ko kinyar da gaskiya nake fada miki?" Tana fadar haka ta katse wayar ta rufe datar ta ta cigaba da kallon NABEHA cikin zuciyarta tana cewa" yanzu kuwa na tabbatar da ba idonane yake nunamin MUFIDA nake gani ba tabbas itace to kenan idan itace meyasameta Haka waya aykata mata Haka meyasa tabar gida ta wace kofa ta iiya fitowa daga cikin rundunar sojojin Nan na gidan su ",Kai to wa Akaje Aka bunne amadadinta aka ce ta mutu "ADEENA dai gani tayi zuciyarta na da kwakwalwar ta na neman fashewa hakan yasa ta nutsu ta sai ta tunaninta Sabi da Kar ta zauce.

*UHM NI Daman nasani Yaya bazaka taba daina tunanin MUFIDA ba meyasa ko su momy da suka hayfeta sun fawwalawa Allah balle Kai dakake yayanta dan Allah yaya kadin ga rage damuwarnan a ranka " uhm Abdul bazaka ganeba ne kamanta nine nayi rainon MUFIDA ba su momy ba meyasa baza kumin uzuri Akan Haka ba mufida kanwatace Kuma Yarinyar da nafi kowa so a duniyar Nan meyasa kakeson takuramin akan Haka" Yaya lafiyarka nake gudu ance karafe yawan tunani da zafin Kai Amma kaki kofa sallamarka ba ayi daga asbiti ba Haka kasaka kafa katafi gurin taron anan ma ka hadu da wata yarinya ka sharara mata maruka har biyu Yaya Wai mece da muwarka ne" bansani ba meyakawoka daki n'a kazo ka isheni da tambayoyi Haka?", Daman inason zan je doguwa domin inason naje Naga halin da su Amrah suke" tofa wacece Kuma amra?" Yarinyar Dana Baku labari lokacin da Inna ta dawo Dani gidannan Yaya naso yarinyar Amma tacemin bazata aureni ba sai ta ga RAYUWAR kannenta ta inganta Tace indai Dan tashiga RAYUWAR farinciki ne ta bar kannenta a wahale do gwara ta hakura da aurena ,shiya naga tun da muna da dukiyar da zamu iya rukesu na fadawa Abba zanje na dakkosu "okay yayi kyau sai kadawo Allah ya kiyaye hanya daga Haka ta juya ya runtse ido tacigaba da tunanin sa , shiko Abdul juyawa yayi ya turo kofa ya sauka kasa tare da yiwa su momy sallama ya dauki hanyar tafiya .

Kai tsaye jirgi yabi Abinka da "yayan masu kudi hakan yasa yayi saurin isa ,Tun da ya nufi hanyar layin gidan su Amrah yaga ko Ina nagidan ya canzamasa komai har ya karasa kofar gidan abin da yaganine ya dagamasa hankali kofar gidan a datse durum gabansa yashiga faduwa to Ina suka shigane ya watsawa kansa wannan tambayar Yana kallon gefe dagefe, wasu mazane samari sukazo hucewa suna tafe suna gurmarsu suna cewa" oh agaskiya wadannan yaran Basu da da,a kuga sai da akamusu korar karnuka sannan masu kudi suke zuwa gidan rannanmafa Naga NINEE ta dawo tab to Allah ya kyauta" shiko abdul rintse Ido tayi tare da budewa jin yadda zuciyarsa ke tafasa da zafin abin da akamusu Nan take yasake maimaita kalmar "korar kare innalillahi wa'inna ilaihirraju un"yafada tare da bude idanuwansa sun kada sun Yi jajur kamar garwashi sannan ya juya yanufi gidan su abokin sa usman wan da yabashi amanar su amra kafin ya tafi chamaru.

Yana Isa gidan yaga wani dattijo a kofar gidan da sallama ya karasa kusa dashi yace" barka da wanan lokacin baba" barkadai yaro ya hanya" lokay kwau Ina wuni?"lafiya Lau sannu dazuwa" yauwa baba Daman Ina neman Usman ne mutanen dake zaune a gidannan saï dai naga kamar bakowa " ayya Allah sarki amma Kai bakone ko?" Eh yau nazo "Allah sarki ay Usman yadade da rasuwa mutanen dake gidanma sun tashi" dasauri Abdul ya dafe kansa tare dacewa" innalillahi wa'inna ilaihirraju un "baba ya rasu kenan wayyo ni to yazanyi kenan " shidai baba besake cewa komai ba sai dai dayaga Abdul Yana kokarin shidewa yace" yaro sai hakuri duk merai sai ya dandani zafin mutuwa yau Kaine gobe ba kaibane" shidai Abdul tashi yayi jiki a sanyaye ya nufi hanyar koma wa inda yafito.

Tun da Abdul ya bar unguwar yarasa inda zai nifa ya ji dadi Gaba kidaya abin duniya ya hadu yayiwa Abdul yawa komai yamasa zafi tinani yakeyi idan ance an Kori su Amrah daga dida to kenan Ina suka nufa shidai yasan kaf cikin garin kano su amra Basu da kowa sai Allah to kodai ADAMAWA suka nufa Anya kuwa haka dai ya dinga tunani ta inda ya shiga batanan ya fita ba zafi da zugi Gaba daya sun vaibayesa ,Babu yadda ya iya Haka ya fawwalawa Allah ya Kama hannya domin yasamu gurin da zai kwana kafin gobe ya huce Abuja .
Chapter 5 · 0% Book details