← Book details Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 8

Sashe 1

Babbar Sakayyah Part 2 Takun Tsakiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

BABBAR SAKAYYAH

*BOOK*2

*SADAUKARWA AL,UMMAR MUSULMAI*
Godiya

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai tsira da aminci Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w da sahabbansa da iyalan gidansa baki daya.
De

* inagodiya da gudummawar da kuka bani har nakawo wannan kan matsayin danake kai ayanzu,ina godiya ga uncle usama,Allah ya bar zumunci,ina godiya musa baffa,Allah ya baka abinda kakeso duniya da lahira,ina godiya ga mahaifiyata abarkaunata,Allah ya sanya ki a aljanna madaukakiya, daduk wanda bansamu damar ambaton sunan shi/ke ba suma ina matukar godiya Allah ya bar zumunci.

NOTE

Wanan littafin mai suna babbar sakayyah narubutashine badan komai ba saidan gera ga al,ummar musulmai,domin fadakarwa , nishadanvtarwa,ilimantarwa,duk acikin wanan littafin mai suna babbar sakayyah kamar yadda rayuwa,da duniya , ta juyamata Baya ,duniya ta ko mamata tamkar ma kabarta a zuciyarta,duk asanadin so' jama'a kada ku bari abaku labari'' kutsaya ku karanta domin sanin me ya aykata mata.

KIRKIRA

Wannan littafin kirkirarran labarine,ban rubutashi dan na muzan ta wani ba kodan na bayyana sirrin wataba, no ba hakabane, littafina kirkirarsa nai kuma nasan hakan tana faruwa, amma duk wadda taga yayi shige da labarin rayuwarta, arashin sanine.

GARGADI

Ban yarda wata tajuyamin littafinaba, kokuma adinga siyarmin da littafi batare da saninaba, banaso, banyarda wani ko wata sukarantamin book ba batare da iziniba muddum kinsan basaya kikayi ba ,wannan littafin paid book ne.

Ban amince wani ko wata akaranta min littafi ,ayi adio dinsa batare da izinina ba sannan ban yarda a sauyamin littafi ko adau wani bangare na jikin littafina ajuyashi ta kowace sigaba馃槨ngd

BABBAR SAKAYYAH

Ep 2

*DORAYI*

Gabakidaya zaratan Mazan haduwa sukayi a Gidan alhaji ABDULHAMID ME NASARA susu biyar ne akawai abdul kanin mus,af saï muhsin shima kanin mus,af ne sai mus,af baisamu damar zuwaba Yana asbiti ba a sallameshi ba jukin nasa yayi tsanani, saï "yayan uncle ABDULHAMID su uku nafarko shine Fahat sai me bimasa zaidu, sai na ukunsu autansu me suna faruq Gaba daya Haka suka rankaya G.G.S.S dorayi domin Kai ziyara mota 15 ne suka tafi dasu motoci biyu suna tsakaiya sune wadda suke ciki.

__________________________________________________________
Tun da akaji jiniya tana tashi aka shiga bude musu get din makarantar nafisa kuwa tun da taji ance ga alhaji ABDULHAMID ME NASARA ya iso ta Kama kanta tashiga kallon inda motocin za su shigo ,kaitsaye parking space sukayi parking .sai da aka yi kusan minti 5 kafin abude motar sufito wayyo Allah jama,a kuzo kuga kallo a gurin dalibai da malaman makarantar mata abin sai wan da yagani wata marainiyar kwallace me cike da so da kauna ta soma fitowa daga idon nafisa tsabar so da kaunar alhaji ABDULHAMID da take Masa tabbas yau Allah ya cika mata burinta taga jaruminta wan da ta Dade tana son gani , fateema kuwa kallon ta ta tsaya tana yi Tace" nashiga uku nafisa wanan wane irin so kikewa wanan mutumin tun kan kisan zaki ganshi zuciyarki takamu da sonshi acikin sakonni kawai sabi da jin labarinsa da kikayi Anya kuwa nafisa wanan so haka?" "Uhm! Bazaki gane ba fateema son sa ajinina yake Dan allah fateema inason na tsaya kusa dashi na tabashi ko zuciyata zata Sami sassauci " "ke baki da hankali tafada tare da zaro ido kinsan saye shi kuwa,nafisa kodai son shi kike kikeson aurensa ?" Aurensa Kuma Baki Gandhi ba me a haihuwar kaji ya haifeni Dan Allah ki bar maganar Nan bakiga yaransa ba ne" au toenene aciki Dan kin soshii da aure " a,a ba Haka nake nufi ba kawai dai BURINA na rungumeshi "suna cikin wanan maganar Basu rufe bakiba suka jiyo karar bindigu suna tashi tako Ina ga jiniya ta motocin sojoji abin dai gwanin Sha,awa gaba daya student din Ido suka zuba domin ganin me su zuwa shiko alhaji ABDULHAMID farinciki ne ya kaashe Sabi da ganin abin kaunarsa ya tashi har ya hallacci taron, parking motocin sukayi tukunna aka bude murfin motar Nan take ya fito da kekkewar kafarsa wadda taji gyra da tsafta kamar madar Dan haske da Kelli batare da ya sake jiraba ya dakko farin glass dinsa ya saka tare da fitowa wow Masha Allah yau Kuma sanye yake da blue din shadda wadda taji dinki babbar riga ta haujikinsa tayi Masa kyau kwarai shi Daman gashi fari ga kyau dan ma ya dan rame jin yar da yayi a asbiti, tin da yafito ake cewa wow wasu ko har da dilalaln yawu wasu kuwa sai neman faduwa suke tsabar kallo kamar sa cinyeshi ,cikin takun kasaita yashiga takowa sojoji n'a biye a bayansa har suka Isa inda alhaji ABDULHAMID yake atsaye Yana kallon abin kwaunar nashi cike da so da kauna, Daga Nan Kuma aka shiga gabatar da abin da ya kawosu bayan angama ne alhaji ABDULHAMID ya musu kyauta ta daban daban tun daga kan malamansu har dalibai .

Daga Haka Kuma suka nufi parking space tare da sauran malaman ,nafisa ce kusa da fateema take cewa" Dan Allah kizo muje kina gani zasu tafi fa kizo ki rakani " ke walalhi bazani ba " ay juyowar da fateema zatai ta hango nafisa har ta Isa gaban alhaji ABDULHAMID ta fada jikinsa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un shikkenan tqjama bala,I cewar fateema " hannu Mus,af ya saka cikin zafin nama ya funciko ta tare da hada ido da ita yace" kina da hankali kuwa ?" Harara nafisa ta watsa masa ta fincike hannunta ta Kara makale wa ajikin alhaji ABDULHAMID Haushin hararar da tamasa ne yasa mus,af ya sake funciko ta tare da tsinka mata Mari jikike Tau luuu, wani gigitaccen Kara ta saka tare da cikukuyo gaban rigar mus'af ta saki kuka ,batare da mus,af yace komai ba sojojin suka karaso suka janye nafisa daga jikinsa tare da yin gefe da ita , afusace mus,af yacire blue din shaddar jikinsa tasama ya fada cikin mota cikin fishi sanan ragowar suma suka Shiga suka ja motar Banda alhaji ABDULHAMID da ya ruko hannun nafisa cike da taisayinta yadda fuskarta tayi kunburi tayi Shari" cikin voice dinsa me dadi yace" yarinya meyasa kikayi Haka kidaina kinji ko Babu kyau kiyi hakuri da Marin da yamiki" kuka nafisa tasaka Tace" Wallahi ni kaunarka nake jinayi bazan iya jurewa ba shiyasa nazo na rungumeka nadade Ina kaunarka tun da naji ance Kai mutumin kirkine" tana Gama fadar Haka tasake fashewa da kuka, shiko alhaji ABDULHAMID rukota ya sakeyi tare da mannata akirjinsa cikin rarrashi yace" to ya Isa Haka kiyi hakuri kinji yarinya ta " Yana Gama fadar Haka da ya tabbatar ta Yi shiru sai ya saketa tare da Bata kudade masu yawa da harta ki karba taga ya hade Rai sai ta amsa tare da yimasa godiya.

*DOGUWA*

Tun da mahaifiyar amra tayi addu,ar Allah ya tashi kafadun amra ,daga lokacin ta Mike tare da dagata suka cigaba da tafiya har suka hadu da me kura ta riban ruwa ya taimaka aka saka umman su amra aciki ya kaisu bakin titi ,suna ta tsaye a bakin titi sunfi awa 5 suna faman neman n'a allah wqn da zai daukesu ya ragemusu hanya ay ko saiga wani tsoho Nan da Yar kurkurarsu ya daukesu suka tafi sai da sukayi tafiya menisa suka iso cikin jejin falgore tukunna ya ajiyesu yace su samu wani ya sake taimaka musu. Alokacin da ya ajiyesu ya tafi amra tashiga tashin hankali sabi da yadda taga jejin Babu kowa tsit ga duhun gaske cikin tsoro da furgici amra tashiga yin addu,a Nan take tsoro ya fita daga cikin zuciyarta ta daga mahaifiyar su suka shiga cikin jejin sai da suka Yi nisa aciki daidai wajan wata bishiyar tsamiya suka tsaya amra ta tsinko ciyayi ta hadasu dayawa akasa yayi tudu sosai kamar gado sanan ta kwantar da mahaifiyar su akai.

10

..
Bayan sun kwantar da itane amra tashiga cikin jejin domin neman abin da zasuci dakuma sassakar itacen da zata hada bukka, tare da sauran "yan uwanta maza su uku da Jafar da Jamal da Abed ,saï da sukayi tafiya medan nisa sannan suka samu bishiyar Mango Nan take suka shiga murna da farinciki Daman rabonsu da cin abinci tun jiya hakanne yasa Abed da yake shine babba ya haukan bishiyar yashiga karkadiwa nunannu masu jaki su amra suna kwasa ,sai da suka dibi me yawa sannan ya sakko suka cigaba da tafiya har suka tadda bishiyar inibi manya manya sunyi marun har wani Baki Baki suke tsabar nuna, wannan lokacin ma abed ne ya au ya debo musu sannan ya sakko suka shiga sassakar ciyayi da itace ,sosai suka loda da yawa sannan suka koma inda suka bar sauran "yan uwansu da mahaifiyar su lokacin da suka koma mahaifiyar su tatashi daga bacci hakanne yasa su jaber suka tsallaka bakin kogin dayake gurin suka wanke abin da suka tsinko sannan suka dawo suka tarar har amra ta fara dasa bukkar agurin Dan Haka suma suka Kai kayan Mango da inibin gaban mahaifiyar su sannan suma suka shiga Taya Amra hada bukka , Masha Allah sai da suka hada bukka uku manya sannan suka sassake ciyayin gurin yayi sarari tukunna suka zauna suka Shiga shan Kayan da suka tsinko, bayan sungama amra suka raka bakin rafin tayi wanka sannan suma sukayi ,suka Sami wata babbar Leda suka zubo ruwan aciki amra ta wankewa mahaifiyar su jikinta daganan kuma Gaba dayansu baccci me dadi yayi awan gaba dasu sabi da dadin iskar da takada tako ina.

*ADAMAWA*
Chapter 1 · 0% Book details