Chapter. 7️⃣ Soyayya Da Ƙaddara 🕊️💔
Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read
Please Follow me on arewapen to read more chapters and also on TikTok for more updates @AmalMusa
"Ga kaunatattun jikokimmu masu daraja, Omar da Aleena. ta fara karantawa da murya mai karfi. "Lokacin da kuke karanta wannan, zaku kasance cikin shekarun da muke ganin ya dace ku fara gina rayuwa tare..."
Kalmar ta sare a zuciyar ta kamar wuƙa tana yanke numfashin ta.
Lokacin da Khan Electronics ta fuskanci rugujewa shekaru da suka wuce, lokacin da kuke yan shekara 4 da 11 kawai, Thorne Comm. ce ta taimake mu. A wannan lokacin, mun yi alkawari; ba yarjejeniyar kasuwanci kawai ba, amma dangantakar da za ta haɗa iyalanmu ta jini..."
No. No, no, по-
"A matsayinku magada, Da ku ne kaɗai magada na gado da tarihin dangi daga kowanne ɓangare… “Ku biyun an ƙaddara ku ne domin ku cika wannan alkawari. Wannan ba wai akan yarjejeniya ce kawai ba. Magana ce ta tabbatar da makomar iyalanmu biyu, Domin tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin ku da zai taɓa zama shi kaɗai ba.”
Numfashin Aleena ya katse, fahimtar ta buge ta kamar jirgin ƙasa mai sauri.
“Saboda haka, a ranar haihuwar Aleena ta 26, wannan alkawari dole ne a cika. Omar Thorne da Aleena Ali Khan za su yi aure..."
Wata irin shaƙa ta fita daga bakin Aleena idanun ta sun yi duhu yayin da nauyin waɗannan kalmomin su ka matse ta.
“Ku biyu, tare da juna, ba kawai za ku girmama alkawarinmu bane, Amma har ma ku kare komai da aka gina tun kafin zuwan ku. Wannan aure zai tabbatar da cewa Khan Electronics da Thorne Comm. sun kasance iyali guda…A haɗe har abada, ba za a iya raba su ba.”
Da ƙyar na ji sauran. Muryarta kamar daga nesa take, kamar daga wani rami mai duhu.
"...Ku yi aure. Ku gina rayuwa tare. Iyalan Khan da Thorne za su ƙara ƙarfi saboda haka..."
“Hannuwan Aleena suka fara rawa da mugun firgici. Jikin ta ya ƙi yarda da kowace ɗaya daga cikin kalmomin da kunnen ta suka ji.”
She can’t take it. Ba zata iya sauraron kara jin wata kalmar ba.
Ba zan yarda da wannan ba. Ba zan taɓa yarda da wannan ba!" Aleena tace tana ihu, ta tashi cikin sauri, Muryarta ta girgiza dakin gaba ɗaya.
“Mahaifiyar Omar ta tsaya a tsakiyar karanta wasikar, fuskarta ta nuna rudani, yayin da mahaifinsa ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya yana goge goshi da yatsunsa.”
She did not even look at Omar. And honestly, ko kaɗan Aleena bata damu da me Omar yake tunanin ta ba.
Granny ta miko hannunta mai rauni, tana jan hannun ta don dawo da ita zaune, amma ta ƙi, ta tsaya cak.
“Aleena dear, ki saurara, don Allah. Wannan abu yana da mahimmanci Wannan wasiyya ce daga marigayi kakanki,” in ji mahaifiyar Omar ta roƙa muryarta kasa sosai. "Aleena, darling, please," granny ta faɗa a hankali, muryarta cike da baƙin ciki da damuwa. “Ba zan daɗe a duniya ba…”
"No, Granny!" Aleena tace, hawaye ya fara zuba kamar fanfo daga idanun ta kan ta yana girgiza da ƙarfi. Muryarta ta karye gaba ɗaya. "Bazan iya zama a nan ba! I am not accepting this! Bazan yarda da wannan ba! Wannan kuskure ne!…A big mistake." Ta fada, ta juya tana ficewa da gudu daga cikin ɗakin, tana yi wa muryoyin da ke kiranta biris. Saboda kalmomin nasu ba su kai kunnenta sosai.”
Guguwar da ke cikin kai na ta rufe duk sauran abubuwa. This is not happening. Wannan ba gaskiya ba ne. Ba zai yiwu ba. Rayuwata ba tawa bace yanzu ta zama wasa kawai, “wannan mummunar izgili ce da aka rubuta tun kafin in samu damar faɗin komai.
Innalillahi!”
Ba zai yiwu ba. Ba zata taɓa yiwuwa ba. Aleena ta ce, tana sauri zuwa wajen karfen benen Emergency ko wane taku yana ƙara nauyi a ƙarƙashinta har seda ta tsaya, Ta riƙe ƙarfen benen da ƙarfi yayin da ta sunkuyar da kan ta. Numfashin ta yana fitowa cikin gaggawa, ƙirjin ta yana matsewa da kowane numfashi da ta ke shaka. Zafin da ke yawo cikin kwakwalwarta ke murƙushe ta, zuciyarta tana bugawa da karfi kamar zata faso ta kirjinta ta tarwatse.
Kakana da na Omar sun tsara aurenmu tun lokacin da muke yara. Ta fada, hawaye suna gangarowa suka zube a kumatun ta kafin ta goge su da sauri. Aleena ta rungume gwiwoyin ta da ƙarfi tana lulluɓe kan ta tamkar takardar da aka murƙushe tana ƙoƙarin ɓoye kan ta kamar babu ita. Sanyin ƙarfen dogon benen yana huda bayanta, yana dawowa da ita cikin gaskiyar da take ƙoƙarin tserewa.
Sautin takun tafiya yana karade matakalan ƙarfen dake karya shirun.
Ta ɗaga kai ta kalli sama. Fushin ta sai kara tashi yake kamar igiyar ruwa. Tashi tayi cikin sauri jinin ta yana tafasa zuciyar ta kamar gobara yayin da taga yana saukowa. Ya tsaya a matakalan kaɗan daga kusa da ita fuskarsa a nutse ba za a iya gane abin da yake tunani ba.
"Why are you here? Me kake yi anan? Me kake so?!” Aleena ta fada da murya mai karfi cike da fushi da raɗaɗin ƙaryayyar zuciya.
Omar ya yi shiru, kallonsa a tsaye, amma ɗan matsewar muƙamuƙinsa ya fallasa haushinsa. Ya sauko a hankali, kowane motsi da gangan, har ya tsaya mataki ɗaya da ita yana fifita ta da wannan nutsuwar da ba ta dace ba.
"You knew about this, didn't you?" Aleena taja dogon huci tana dukan kafaɗarsa da yatsanta, ta kara cewa, da murya mai rawa da tsananin bacin rai. “Karka ka min ƙarya, Omar. Ka san da wannan tun tuni, ko? Wannan wane irin makirci ne! Wannan ai tsantsar yaudara ce—”
"Will you shut up?" Omar ya katse ta cikin tsawa ya kama hannuwanta biyu ya ja ta baya wanda yasa mataki daya tsakanin su. "Shut up, Aleena. Kin haukace idan kina tunanin na san komai game da wannan. Ni ma haka na ke kamar ke—abin ya bani mamaki nima kamar yadda kika ji. Shin da gaske kina tunanin ina son wannan?"
Aleena ta saki wata dariya mai ɗaci, ta na janye hannunsa daga jikin ta. "Oh, really? Ka ji mamaki? Yarda da hakan zai wuya. Iyayenka sun dade da sanin hakan. Granny ta faɗa min da kanta. Don haka kada ka yi kamar ba ka da laifi. You knew Omar. ka yi shiru ne kawai saboda kana jin nishadi ganina cikin kunci."
Muƙamuƙinsa ya matse, Aleena ta lura da ɗan gajeren abu a fuskarsa; Haushi, watakila ma Tausayi? Amma ya ɓace da sauri kamar yadda ya bayyana, fuskarsa ta koma cikin wannan kallon rainin da ya saba sawa.
Aleena ta ce, “You are unbearable” ni da kai? Abu ne wanda bazan taba iya jure shi ba, idan kana tunanin zan iya hakuri ayi muryarta ta karye tare da fesar da fushi. kaga Omar, ta ce “Na tsane ka kuma ka kasance haka tun farko — girman kai, son kanka, kamar duniyar tana juyawa ne don kai. Kuma kasan me?
Abin yana bani haushi.”
"Kina tunanin ina son aure da ke?" Omar ya mai da mata da magana, muryarsa tana ƙaruwa tare da kowace kalma. Idanunsa sun matse sun yi duhu suna tsananta kallon ta. “Kada ki yaudari kanki ki dauka kina da kimar da ba ki da ita, Aleena.” Kina tunanin zan taɓa yarda da wannan? Idan har ma zanyi aure-" yayi dariya yana girgiza kai cikin rashin imani- "Tabbas baza ta zama irin ki ba. Yarinya, Mai tashin hankali. Mai taurin kai. Mai gajiyar da mutane."
"Mai gajiyarwa?" Aleena ta ce, tare da wata dariya mara dadi.
"Ba ka ganin cewa kai ne mai matsala? Kai ne mafi munin mutumin da na taɓa sani Omar! Girman kai da halayyarka, kuma zama kusa da kai cuta ce!"
"At least i am not running away like a small child. Omar yace, Muryarsa tana fita cikin wani sanyi da murmushin da ke kan leɓansa na jifan Aleena kamar zagi. Kamar duk fashewar bala’in da Aleena tayi bai shafe sa ba ko kaɗan. "Ki dubi kanki, kina guduwa da zarar kin ji abin da bakya so. Wannan yarinta ce. Ki girma, Aleena. Ki yarda da gaskiyar cewa kakarki tana cikin matsanancin rashin lafiya kuma—”
"Kai ɗan iska!" Aleena ta yi ihu, ta tura shi da ƙarfi har ya koma da bayan shi yana kusan faduwa daga matakalan. "Kada ka kuskura ka yi amfani da rashin lafiyar granny a matsayin hujja ga wannan! Baka da tausayi."
“Ke wawiya ce sosai, Aleena!” Omar ya ɗaga murya yana taka mataki zuwa gabanta. Kafin ta ankara, ya tura ta da ƙarfi sanyin jikin karfen ya tsayar da ita tare da wani motsi wanda ya fitar da iska daga bakin ta.
“Ba zan taɓa ɗora laifi kan kakarki ba, Wawiyar yarinya!” Omar ya furta da wani irin murya mai raɗaɗi, muryarsa tana rawa da motsin zuciya. “I care about her, Aleena. Na damu da ita, shi yasa na biyo ki! Kin san yadda kika bar ta cikin tashin hankali kuwa? Tana ta rawar numfashi saboda damuwa!”
Kalmominsa su ka buge ni tamkar mari. Girman idanuna su ka kara fadadawa na bude baki amma na kasa furta ko kalma guda. Ina ƙoƙarin wuce shi, amma sai ya riƙe hannuna da ƙarfi, tamkar ba zai sake ni ba.
“Iyaye na suna cikin wannan ɗakin, Aleena,” ya faɗa cikin muryarsa mai matsi amma tsayayye. “Ni ma ban yarda da wannan ba, But they are my family. I love them, kuma ba zan iya bata musu rai ba. Kakarki ma ba za ta iya jure wannan stress da damuwar ba. Idan kina son a soke wannan maganar ki koma kiyi musu magana da kyau. Ba dole bane ki so ni, amma idan kika ƙara tayar da hayaniya ko rashin kunya a gaban iyayena, wallahi sai kin yi nadama.”
Muryarsa a nutse take amma nauyin da ke cikinta ba zai musaltu ba.
Janye hannuna nayi cikin gaggawa daga nashi, zuciyata na harbawa da karfi. Duk second dana tsaya anan tare dashi bata lokaci ne, Kuma ko wane second da granny ke ciki damuwa ne a cikin ɗakin. Ba zan iya barin hakan ya ci gaba ba.
Zuciyata ta fashe tare da ko wane taku da nake ɗauka zuwa ɗakinta, kunya tana kona cikin kirjina, Ta yaya na zama mai rashin hankali haka? Me ya sa na bar ta cikin wahala?” Dole ne in gyara abin da nayi, ko da ko wane bangare na jikina yana son rugujewa.
Ina shiga cikin ɗakin Granny na tsaya cak da ganin abin da ke faruwa. Nurse ce take gyara mata maskar iskar ta, (Oxygen mask) tana lura da numfashinta a hankali. Ganin hakan ya buge ni da ƙarfi. Zuciyata ta nutse, sanin yadda ta yi rauni. Ina garzayawa kusa da ita, ina kama hannunta mai rauni a hankali, kamar riƙe shi zai iya hana komai ɓacewa. Ta yi mini murmushi mai rauni amma mai dumi, yatsunta suna shafa nawa a hankali, A bayyane take tana fama da numfashi, amma nurse ta riga ta kafa mata maskar iska don sauƙaƙa mata. Duk da haka, numfashinta yana da rauni kuma bai daidaita ba, ko wane shaka abin tunawa ne da yadda ciwon dajin ya yaɗu.
"Aleena dear," muryar mahaifiyar Omar ta karya shirun, a hankali da nutsuwa. "Za mu iya yin magana daga baya?"
Ina juyowa gareta, jikina har yanzu yana jijjiga. ina gyada kai, Yayin da na lura da ɗan motsin kan granny tana ƙarfafa ni in yi biyayya. "To Aunty Asiye," nace a hankali da rauni a muryata.
“Zamu jiraki a gidanmu,” ta faɗa da ɗan murmushi mai cike da damuwa. Ta saki hannun Granny da ladabi, Mahaifin Omar ya gyada kai sannan suka fice, suka bar ɗakin cikin shiru mai nauyi.
Naji kamar bana cikin jikina Amma hannun Granny da ke a cikin nawa mai dumi, mai rawa, yana riƙe ni da ƙarfi daga nutsewar cikin wannan gaskiya mai zafi. Gaskiyar da ba na son fuskanta.
Granny ta ɗaga hannu a hankali yatsunta na rawa suna taɓa gefen maskar iska kamar tana so ta cire shi. Amma har yanzu numfashinta bai daidaita ba. Nurse ta shiga nan take, tana gyara maskar iskar a hankali don tabbatar da cewa tana lafiya. Granny ta fitar da wata doguwar hushi daga cikinta jikinta mai rauni yana motsi a kan gadon yayin da take ƙoƙarin gyara kwanciya mai sauƙi. Hannunta ya kai kan nawa yatsu da ƙyar suke shafa ni, Taɓawar a hankali kusan abin shakku, kamar ta san cewa ƙarfinta yana ƙarewa.
“Darling…” muryarta na fitowa ta cikin maskar iska rauni ya lullube ta, amma dumin ƙauna yana nan. “Na san wannan abu yana da wuya a gareki. Amma don Allah... ina bukatan ki fahimta." Ta dan dakata, tana shakar numfashi a hankali ta cikin maskar iska. "Da ban yi imani cewa wannan shine mafi kyau ba, da ba zan buƙaci ki amince ba.”
Kirjina ya matse. Na danne muƙamuƙina, na girgiza kai. "Granny, wannan... wannan ba adalci bane." Muryata ta ragu. "Akwai dalilai da yawa da ya sa wannan aure bai kamata ya faru ba."
Ta fitar da numfashi a hankali, maskar ta dan yi gumi yayin da yatsunta suka ƙara matse nawa. Bata yi ƙoƙarin cire shi ba, amma ina ganin gajiyar a idanunta da nauyin duk abin da bata faɗa ba. “Aleena…” ta kira sunana, kamar iska tana ɗauke kalmarta. Ta dan dakata, kamar tana tattara ƙarfi don ci gaba. “Ba domin na daura miki nauyi bane na yi haka.” Ta kamo hannuna da ɗayan hannunta, ta kai shi bakin labbanta, ta dan sumbace kan yatsuna a hankali, sannan ta mayar da shi saman cinyarta. "Kakan ki da na Omar sun hada wannan shiri ne domin su kare ki. Kin san iyayenki ba su taɓa kasancewa a gare ki ba. Kuma kakan ki... ya san hakan. Ya damu da ke game da abin da zai faru idan na bar duniya.
Ta shaki numfashi mai zurfi, sautin yana fitowa ta cikin maskar iska. "Darling... Ba zan kasance a nan har abada ba."
Kalamanta sun ratsa ni kamar wuka. "I know, Granny," na rada muryata mai rawa. "Amma shin wannan shine amsar? Aure?" Fushi yana turnuƙewa a zuciyata, hannuwana sun matse sosai. "Grandpa ya yanke wannan shawarar lokacin ina shekara bakwai! Bakwai fah granny, bakwai fa! Ta yaya zai iya sanin irin mutumin da Omar zai zama? Idan ya zama mai zalunci fa? Idan ya zama mai duka fa? Idan ya zama mai tashin hankali fa? Idan ya zama wanda ba zan taɓa so bafa?
Shiru mai tsawo ya shiga tsakaninmu.
Granny ta sake fitar da numfashi a hankali, ta dan gyara kanta a kan pillow, yatsunanta masu rauni har yanzu suna riƙe da nawa.
Muryarta ta yi laushi yanzu, "Kakanki yana ganin abubuwan da wasu ba sa gani. Iyalan Thorne sun kasance tare da mu tsawon shekaru.
Ya yi imani Omar zai girma ya zama mutumin kirki.
Kuma Idan bai taba miki kirki ba, to watakila... watakila, saboda kun dade kuna rashin fahimtar juna."
Kallon granny ya yi laushi, yatsunta suna dan matse nawa. "Omar mutumin kirki ne, Darling... idan har kika bar shi."
Na girgiza kai da ƙarfi, ina tilasta hawayen da ke ƙona idanuna su koma. "Ba game da shi kawai bane, granny. Dukkan abin da wannan tsarin ke wakilta ne matsala.” Muryata na rawa yayin da na haɗiya da karfi. "I love someone else."
Hannunta har yanzu yana manne da nawa, amma na ji ɗan shakku a cikin riƙon ta. Idanunta masu rauni suna kallona na dogon lokaci, kafin ta gyada kai a hankali.
“Na sani, Aleena. Amma–”
“Ina son Emir, Granny,” na faɗa a hankali, kalmomin da ƙyar suka fice ta cikin maƙogarona.
Fadin sunansa kamar ina yage zuciyata da kaina.
Rikon granny ya ragu, amma bata saki ba.
Na lumshe ido, kamar hakan zai iya dakatar da zafin da ke huda zuciyata.
Tunanina suka ruga zuwa jiya da daddare. Zafin da ke kirjina ya ƙara zurfafa, yana barazanar fashe duk abin da ke cikina. Idan abinda na gani da gaske ne… idan wannan shi ne shirin Emir, ban san yadda zan fuskance shi ba.
How can i break his heart?…. Yaya zan iya karya zuciyarsa?.
Flashback ( TUNO BAYAN )
Tun da ya iso jiya, bai bar gefena ba koda da mosti. A restaurant muka haɗu lokacin da ya iso ya same ni a can, duk abin da ake bukata ya riga ya umarta. Restaurant din yana kan wani rufin bene mai kallo zuwa ga City Bosphorus a garin Turkiyya. wanda aka yi wa ado da haske mai laushi na fitilun zinari, bangon fararen dutse ne masu walkiya da kujerun azurfa masu kyau - muka zauna. Kamshin kebab dasu abinci ya hade da kamshin turaren oud da saffron yana ratsawa cikin iska. City Bosphorus daya daga cikin mafi tsada da kyan gani a turkey. A gaba na aka jera Sultan’s Platter-wani kwandon abinci mai launin zinari da aka cika da: Kuzu tandir- naman rago ne da aka dafa a cikin tanderu har ya narke.
Balik ekmek – soyayyen kifin Bosphorus mai laushi da aka lulluɓe da ganye da ruwan lemon tsami a cikin bread na alfarma.
Midye dolma – kwakwaƙƙen mussel cike da shinkafa da kayan kamshi irin su habbas, koren albasa da ganyen na’a-na’a.
Baklava na zuma – da aka bushe da ɗanyen almond da pistachio, sannan aka tsiyaye ruwan zuma na musamman daga Konya a kai.
Kuma sha? Ottoman sherbet ne — hadin ruwan pomegranate, ganyen rose, da ruwan kankana mai launin ja kamar soyayya ta gaskiya.
Emir ya riƙe hannuna a hankali, yana shafa babban yatsa a kan hannuna Ki ga wannan view din, Sweetheart?" Ya yi murmushi, yana nufin tagar da ke nuna hasken birnin bursa a ƙasa. "Kamar dai duk wannan anyi ne don mu kawai."
Na dan jingina kaina akan kafadarsa ina kallon shi yana shan ruwan lemu na musamman da ya umarta. "Shin kin san cewa wannan gidan abincin yana da shekaru ɗari a tarihi?" Ya tambaya ni, idanunsa masu haske suna kallona. "Sun fi sanin kayan abinci na asali na Ottoman."
Nayi dariya ina kara makalewa acikin kafadarsa nace mishi to honey taya duk kasan wadan nan tarihin?
Emir ya kara dubana yana murmushi inda banje ba kadan ne sweetheart acikin turkey ba bursa kadai ba, sai ya kara cewa: Sweetheart za mu ci abinci kafin in fara yaƙin da ke ko yaya?
Nan take dukka muka sa dariya ina buge shi da yatsuna.
Ya kamo hannuna, yana sumbatar goshina hankali. Abu ɗaya da nake ƙauna a game da Emir shi ne: bai taɓa nuna rashin mutunci gare ni ba. Ko lokacin da nake zuwa gidansa, har nakan kwana can, Emir bai taɓa tabani ba a hanya da ba ta dace ba. Kullum yana cewa: “Ina so na taɓa ki ne a matsayin halal ɗina.” Wannan kalma ce da ta sa na ƙaunace shi fiye da tunanina.
Ya ƙaunace ni ba saboda jikina ba, sai dai zuciyata da rayuwata.
Na tuna yadda yake yawan mun zolaya, Kamar jiya a lokacin da muke cin abinci a restaurant. Muna tattaunawa ne a kan karatun Alƙur’ani, ya ɗauko wata aya yana ba ni fassara. Na kasa fahimta, sai ya cigaba da yi min dariya. Amma da ya lura na bata rai, sai yace da murmushi: “Haba Sweetheart, ki gafarce ni. ke ce mafi dacewa ki koya mun.” Yadda ya faɗa ya sa naji daɗi sosai, duk da ni na san shi ya fi ni. Amma irin fahimtar da muke yi wa juna, da yadda yake girmama addininsa, su ne abubuwan da suka sa nake ƙara zurfafa cikin ƙaunarsa.
Yayin da Emir ya saka hannu cikin aljihunsa yana neman wayarsa domin aika wani muhimmin saƙo ga ma’aikatansa, sai ya ankara da cewa ya manta wayar a cikin mota.
“Sweetheart, kin ga na manta da wayata a mota, bai gama ba na katse shi ina murmushi, nace bari na dauko maka na tashi da sauri ina nufar sauka kasa inda yayi parking motarsa.
Na shiga motar ina neman wayar lokacin na ji ƙarar vibration din wayar acikin dashboard nasa na bude don dauko wayar, Amma a daidai lokacin ne wani abu ya ja hankalina – wani ja-ja din abu yana leƙowa daga ciki. Ƙaramar kwalbar ta ado ce da red velvet tana shimfiɗe da kyau.
Na dakata, zuciyata ta soma bugawa.
A hankali na ɗaga kwalbar… Zoben diamond ne aciki.
Na sauke ajiyar zuciya da dariya karama. “Emir dai da sha’awar kayan ado yake…” nace a raina Amma… sai na lura da wani abu.
Rubutu ne a jikin zoben. Suna na.
Zuciyata ta harba. Hannuwana suka soma rawa. “Subhanallah… Woww.. wannan zoben… nawa ne?”
Na mai da zoben da sauri yadda na same shi, zuciyata na dukan gangar jiki kamar zata fasa ƙirjina.
Shin zai nemi aurena?
Idan ya tambaya… zan amsa da eh?
Na dawo da wayar na miƙa masa tana rawa a ɗan yatsuna. Na zauna a kujerata ina kallonsa.
Ya murmusa kamar bai san komai ba.
A wannan lokacin ne na tabbatar…
Ina ƙaunarsa.
Ina son in aure shi.
Idan ya tambaya… zan ce: “Yes.”
End of Flashback ( Karshen tunani)….
✍️A/N: Please kuje arewa kuyi liking kuyi commenting and please kuyi sharing 💔🥺….
💘AUREN ALEENA💘
Amal Musa ✍️