← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 29 OF 29

Chapter 2️⃣8️⃣ Rikicewar Zuciyarta ❤️‍🔥‍🔥

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Omar Thorne. The ultimate player, wanda kowa ya sheda shi da babban ɗan shahararen player duk duniya. "How dare him... Ya tura min irin waɗannan hotunan? Har sau biyu?" Mukamukinta suka tamke kam. Ta ja dogon numfashi ta na ƙoƙarin kashe wutar da ta ke ci a ƙirjin ta. Zuciyarta ta na bugawa da ƙarfi yayin da ta jefa wayarta cikin jakarta bayan Omar ya yanke wayar—so damn rudely. Ko kaɗan bashi da manners. "Damn him..." ta furta a ƙarƙashin numfashinta. "Uban me yasa ma ya buɗe maballan rigarsa a cikin mota? A gaban direbansa? Mtssw... har da sakatariyarsa ma tana wajen." Aleena ta lumshe ido tana girgiza kanta. "Wai shi me yake damunsa ne?" Bacin ran da ta ke ji yana kara bayyana a kowace kalma da ta ke furtawa. Komai ya fara ne tun daga daren jiya. Gashi yanzu kuma gaba ɗaya ya mamaye mata tunani. Omar ya san duk wata hanya mai sauƙi da zai shiga cikin kanta. Ya san yadda zai ɓata mata rai. Sannan kuma ya san abin da zai yi ya birkita mata nutsuwarta. Amma sai dai a wannan karon... ba fushi kaɗai ta ke ji ba. Akwai wani abu daban. Wani abu mai zurfi. Wani abu da ya ke ƙuna a hankali a cikin zuciyarta. "God... why am I in this position?" Shi fa Omar ne. Mutumin da ta fi tsana a rayuwarta. "He's the one I hate so much. Omar Thorne." Ta maimaita sunansa a cikin ranta, kamar ta na tunatar da kanta waye shi a wajen ta. "Why am I forgetting who he really is?" Amma duk yadda ta yi ƙoƙarin ture tunanin sa, sai dai ta kasa.

Hoton kirjinsa ya sa ke fadowa a cikin zuciyarta. Numfashinta ya ɗan tsaya. Ta tuna yadda laushin fatarsa ya ke a ƙarƙashin tafin hannunta. Yadda faɗin kirjinsa ya cika hannunta. Yadda tsokokin jikinsa su ke da ƙarfi amma fatarsa ta kasance mai laushi. A lokacin ji ta yi kamar ta nutse a cikinsa. Da sauri ta girgiza kanta. "NO..." Sai kuma tunanin ta ya kuma shudewa a kan lokacin da ya ƙara tura mata hotunan, ya na nuna mata wannan faffaɗan ƙirjin nasa... da waɗannan siraran gashin da su ka kwanta a kansa.... Sai kuma lips ɗinsa. "Damn those lips... " Ta runtse idon ta da ƙarfi. Duk yadda ta ke ƙoƙarin tsanar abin da ya faru... ta kasa. Kuma wannan shi ne abin da ya fi azabtar da ita. Tsaki ta saki cikin takaici, tana naɗe hannayenta a ƙirji. Kallonta ta mai da kan window idonta ya tsaya zuwa kan motocin da suke wucewa ta titi. Cunkoson da ya tsayar da su ɗazu ya warware. Ba jimawa za ta isa gida. Sannan kuma ba jimawa za ta sake haɗuwa da Omar a gida.

Tunanin hakan kaɗai ya sa wani irin zafi ya kara bazuwa a ƙirjinta, shi ba mai ciwo ba, sannan kuma ba mai daɗi ba. Wani sabon yanayi ne da ta kasa ba shi suna. "Me yasa hakan yake damuna sosai? I hate this." Ta furta a cikin kanta. Ta tsani yadda Omar ya samu wani wuri a cikin tunaninta. Sannan kuma ta fi tsanar yadda a kan shi ne take jin hakan.

Rufe idonta ta yi ta na ƙoƙarin dawo da numfashinta daidai. Amma abin ya ƙi. Bugun pulse ɗinta ya na ƙaruwa da sauri. Jininta kamar ya na gudu a cikin kowace jijiya da karfi. "Da ba shi da wannan kwarjinin... kuma ba shi da wannan shegen kyawun... kuma dai, da ace he was mine... Wallahi da tuni naje na sharara masa mari masu zafi saboda bude kirjinsa da yayi." Wani takaici taji ya kara turnuke ta saboda abin da ya yi bai dace ba. "Musamman a gaban direbansa, inda sakatariyarsa ta gan shi haka fah?" Tabbas da sai tayi kusan hauka, saboda yanzu tunanin hakan ma ya kuma sa wata irin wuta ta sake ruruwa a cikin zuciyarta. Wani tunani ya faɗo mata ba tare da ta shirya ba. "Amma... dan me yasa ma zai yi hakan? Omar nawa ne ni kaɗai... Babu wanda ya kamata ya gan shi haka. Ko ya kamata ya taɓa kirjinsa sai ni kaɗai. Nice ce matarsa. Ni ce mai mallakar wannan wajen babu wanda ya kamata ace yana da wannan privalage din bayan ni. Da ace masoyina ne da..." Aleena ta daskare. Idonta ya buɗe da sauri.
Wait...Meyasa ta ke tunanin haka? Meyasa ta ke jin haushi? Meyasa abin yake kamar zai haukata ta? Ba ta ma damu da shi ba...ko? Ta haɗiye yawu da ƙyar. Idan da gaske ba ta damu da shi ba... me yasa zuciyarta take bugawa haka? Me yasa jikinta ya ke rawa saboda tunaninsa kaɗai? Me yasa kalamansa har yanzu suke yawo a cikin kanta? Shit... Ta furta a hankali, tana jan wani dogon tsaki. Amma amsar... har yanzu ta kasa samunta.

Ta ya ya za ta iya ci gaba da zama da shi bayan koda yaushe ya na jifan ta da wannan kallon nasa? Da wannan attitude ɗin na rainin wayon nasa? Da wannan bakin na sa kamar ya na mocking din ta ko challenging din ta dan ta yi losing control? And the worst part, na abin da ya fi komai tayar mata da hankali shi ne... ba ta san ta ya ya za ta yi stopping hakan ba. Sometimes ji ta ke yi kamar ta yi losing ta bar shi ya yi wining. Wani ɓangare na zuciyarta ya na san ta yi resisting ɗinsa da duk wani ƙarfinta. Amma wani ɓangaren kuma... ya na san Omar ya ci gaba da matsa mata. Ya ci gaba da pushing ɗinta. Saboda tana jin cewa... idan har ta sake samun hannunta a kansa, toh wallahi she will make sure to remind him and make him to never forget wace ce Aleena and…-!

Cikin sakanni idanunta su ka buɗe a firgice, kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki. "Ugh! Stop!" Ta furta da ƙarfi cikin takaici, tana girgiza kanta da sauri kamar tana ƙoƙarin wanke duk wani tunanin da ya cika mata ƙwaƙwalwa. A take motar ta taka birki ta tsaya cak, har ta ɗan yunkuro gaba daga kujerarta. Da sauri ta daidaita numfashinta, sannan ta kalli direban. "Meyasa muka tsaya?"

Direban ya waiwayo baya cikin rudani. "Nima ban sani ba, madam. Na ji kin yi ihu kina cewa stop, sai na ɗauka kina son mu tsaya ne."

Dariya ta ƙwace wa Aleena duk da halin da take ciki. Ta girgiza masa kai cikin kunya. "Please, continue. Karka damu. Sorry... I was..." Kalaman su ka mata tsaya mata a maƙoshi.

Alhamdulillah, direban bai ƙara tambayarta komai ba. Ya yi murmushi kawai, ya gyada kai sannan ya ci gaba da tuki.

Aleena ta sake kwanciya jikin kujerarta, tana fitar da wani dogon numfashi. Hannunta ya nufi habarta tana shafawa a hankali, tana ƙoƙarin kashe wutar da ke ci a zuciyarta. “What is wrong with me?” Ta tambayi kanta ko ta fara losing mind dinta ne. A karon farko, ji ta ke kamar ita kanta ba ta fahimtar kanta. Saboda a wannan yanayin... ba ta da tabbacin za ta iya fuskantar Omar. Musamman yanzu da ta ke jin kamar tana gab da fashewa tsakanin bacin rai da kuma rikicewa... da kuma wani irin desire wanda ita ba ma ta taba jin sa arayuwarta ba. And yanzu Aleena idan ta gansa ba lallai ne ta iya rike kanta, kuma Omar ya san exactly abin da ya ke mata. Ya san yadda ya ke anfani da jikinsa wajen burgeta, his sexiness. Da wannan murmushin rainin nasa mai kyau, waɗannan lips ɗin nasa... Those lips... runtse idanunta ta yi da ƙarfi na sakanni sannan ta buɗe su da sauri. "Canza direction ɗin da na ba ka."

Direban ya ɗago kansa ta cikin madubi cikin mamaki. "Zuwa ina, madam?"

"Terrace Cafe," ta faɗa kai tsaye. Sannan ta karkatar da kanta zuwa window yayin da motar ta juya cikin sauri. A wannan lokacin... Aleena abu ɗaya kawai ta sani, shine ta na buƙatar best friends ɗinta. Duk da ta san zuwa wajen su da wannan problem din zai leading ga abu biyu ne kawai, shine ko suyi mata dariya ko su tausaya mata. Amma sanin halin su ta san dukka biyun za suyi mata.

*******

Isowar Aleena kenan Terrace Cafe. Hannunta ta sa ta tura ƙofar glass ɗin ta shiga. Nan ƙamshin shayi iri-iri, sababbin snacks da abinci masu ɗaukar hankali suka buɗe mata hanci. Wurin ya cika da wani ƙamshi mai sanyaya rai wanda ta saba da shi sosai, domin Terrace Cafe na ɗaya daga cikin best friends din ta ne, Nesa.
Sautin waƙa mai laushi ya na tashi a hankali a cikin cafe ɗin, ya na gauraya da muryoyin mutane masu kuɗi da ke ta hirarsu cikin nutsuwa. Kana kallon wajen ka san an gina shi ne domin walwala, hutawa da kuma more rayuwa. Kai tsaye ta nufi floor na biyu, wanda ya ke da indoor da outdoor seating. Ba ta yi nisa ba idanunta suka hango Leila zaune tana jingine da kujera, ta na ta dariya da katuwar muryarta da ta kusan mamaye rabin floor ɗin. A gabanta kuwa Nesa da Mariam ne zaune kan wata sofa mai faɗi, kowacce riƙe da drink a hannunta.

Da suka hango Aleena, gaba ɗayansu suka ɗaga hannu suna yi mata alamar ta ƙaraso. Ba tare da wata magana ba, Aleena ta ƙarasa ta zauna kusa da Leila. Ta ajiye jakarta da ɗan ƙarfi, sannan cikin sauri ta miƙa hannu ta ɗauki wani iced green tea latte da ke kan table ɗin. Ko na waye ma ba ta tambaya ba. Ta ɗaga cup ɗin kai tsaye zuwa bakinta, ta kwankwaɗe shi da wani dogon kurɓa.

"Whoa... Aleena!" Leila ta faɗa ta na fashewa da dariya. "Irin wannan ƙishirwa haka?"

Aleena ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata. Sai da ta shanye abin da ya rage, kankarar da ke cikin glass cup ɗin ce kaɗai ta rage, sannan ta sauke cup ɗin kan table tare da sakin wata doguwar ajiyar zuciya.

Nesa ta girgiza kai tana dariya. "Someone's really thirsty... or restless." Ta ɗan yi murmushi. "Anyway, me kike son sha? Zan sa a kawo miki yanzu."

Aleena ta nuna glass cup ɗin da ta gama shanyewa. "This one, Nesa. Get me this."

Nesa ta sake dariya ta na girgiza kai. "Get this now," ta faɗa wa ɗaya daga cikin ma'aikacin da ya zo kusa da su.

Leila ta ɗan karkata kanta ta na murmushin gulma. "Make it two, Nesa. Banda wani drink ɗin saboda Aleena ta shanye mun nawa."

Mariam ta ɗan matsa kusa da ita ta na murmushi.
"Ni fa na ɗauka gida za ki wuce straight daga office. Kika ce kin gaji, kuma yau ba za ki kwana gidan Leila ba."

Leila ta bugi kafaɗar Aleena da bayan hannunta cikin tsokana. "Sai gaki yanzu... kamar wata wacce duniya ta yi mata zafi." Ta ɗan lumshe ido ta na murmushi. "Emir ne? Saboda ya yi tafiyar sati ɗaya?"

Aleena ta buɗe baki kamar za ta ce eh... Sai kuma ta tsaya. Ta san halinsu sarai. Da zarar ta yi mu su ƙarya, cikin sakan kaɗan za su gano. Sun dade da gama karantar ta da kuma yanayinta fiye da yadda take tsammani. Amma kuma duk da haka... ai kusan hakan ne. Tabbas tafiyar Emir za ta taɓa ta. Za ta yi missing ɗinsa. Musamman bayan ƙaramin saɓanin da su ka samu dazu kafin Omar ya kutsa cikin office ɗinta, ya tarwatsa mata duk wani nutsuwar da ta rage mata.


A/N: Please muyi sharing chapter nan zuwa groups dayawa kuma ayi reacting da comment and if you guys are lucky gobe ku samu wani mai zafi 🔥🔥🔥🔥 Saboda Omar zai drowning ah pool and mai zai faru? Kunsan dai dole ayi masa CPR hada baki da baki wajen ceto ransa amma Omar zai ce bai iya ruwa bane ba??🙄😂😂 mu hadu a next chapter.
Chapter 29 · 0% Book details