← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 29

Chapter. 9️⃣ Auren Da Yazama Dole🖤🔗💔

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read

A cikin lobby din shigowa hotel ɗin, daidai lokacin da kofar lif ɗin ke buɗewa a hankali, Omar cikin sauri ya shiga domin mayar da katin ɗakin ga ma’aikaciyar karɓar baki.

Omar sai ya gansa…Kafafunsa sunyi crossing hannayensa suna kwance a kan kujera yatsunsa suna danna saman itacen kujerar a hankali Idanunsa sun kafe akan shi cike da kallo mai kaifi babu motsi da kuma cike da lissafi.

Ya dan tsaya kadan, sai kuma ya tilastawa kansa ya kau da kai cikin sauri, yana cigaba da kammala tsarin fita daga hotel ɗin kamar babu wani abu da ya faru.

“Mun gode, Mr. Thorne. Muna fatan ka ji daɗin zaman ka, kuma za mu kasance muna jiran dawowar ka,” in ji ma’aikaciyar, tana daga hannu cikin girmamawa.

Gyada kai yayi kadan. Jikinsa kamar ba nashi ba. Komai a jikinsa yana motsi ne kawai ba tare da zuciya ba. juyawa yayi sai kawai ya gansa a bayansa, Omar ya shaki numfashi a hankali, kafin ya hadu da kallonsa.

“Wannan shine kake nufi da cewa kana buƙatar lokaci?” Muryarsa ta kasance mai daidaituwa, wan da ba za a iya gane abin da yake tunani ba.

Omar ya yi watsi da shi, ya wuce.

Ya biyo shi.
Papa mahaifin Omar.

Bai san tsawon lokacin da Papa ya shafe yana jiransa a cikin wannan lobby ba, amma sai ga shi a nan.

Papa ya dafa kafaɗarsa daidai lokacin da yake yunkurin fita waje. Ta gefen ido Omar ya hango direbansa yana matso da mota daga VIP parking space yana nufowa kusa dashi.

"Shin ladabi ne ka yi watsi da mahaifinka yana maka magana?" Papa ya tambaye shi.

Omar ya juyo garesa ya hadu da kallonsa. “Shin haka ladabi ne uba yake bibiyar ɗansa zuwa hotel? Ni fa ba yaro ba ne—”

“To ka daina halayyar yara,” Papa ya katse shi, muryarsa a nutse, amma mai nauyi.

Omar ya dan firgita cike da mamaki, amma yayi saurin rufe shi da rashin nuna damuwa. Motar ta tsaya a gabansa cikin sauri ya shige, Ya mika hannu don rufe kofar sai kawai — Kamar ya sani, Papa ya shiga cikin motar ya zauna kusa dashi kofar ta rufe da wani karfi.

Omar ya lumshe ido, yana sauke numfashi a hankali.

Wato iyayen Omar Mommy da Papa sun kasance mutane biyu daban; Mommy ta kasance mai tsawatarwa Idan ta ƙi duk wani abu da Omar yayi zata nuna, zata yi faɗa. Tun Omar na ƙarami, tarbiyyarta ba ta tsaya iyaka magana ba. Bata tsoron ta buge shi idan ta ga ya kamata duk da shi ne da’ daya tilo abin alfaharin ta.

Amma Papa? Ba ya yawan magana, bai taba yiwa Omar horo ba kamar yadda mommy take yi. Yanayinsa, Fuskar sa, halayensa, yanayin jikinsa, shi ne mutum mafi mai nutsuwa da Omar ya taɓa sani. Papa ba kawai uba ba ne. Shi ne Thorne Senior. Sunansa yana da iko. Shi ne wanda ke ba da umarni. A cikin wannan dangi, a cikin wannan duniyar, duk abinda ya faɗa — doka ce. Baya yawan magana, amma idan ya yi magana, kalmominsa umarni ne kuma suna buƙatar biyayya.

“Bana son irin wannan rayuwar da kake yi Omar,” in ji Papa ya ce a ƙarshe, yana karya shirun.

Ya ci gaba da kallon fitilun birni da ke wucewa a waje. Fitilun neon din bursa suna ta wucewa da sauri kamar bugun zuciyar sa.

"Kada ka yi tunanin ban sani ba, Omar." Muryarsa ta kasance mai daidaituwa, amma akwai wani kaifi a cikinta. "Wannan 'yar fim ɗin? Wadda kafofin watsa labarai ba su daina maganarta ba, ta fita daga lif kafin ka. Kuma mawakiyar nan? Wadda aka yi ta jita-jitai da kai a baya? Ita ce ta fara fita."

Wani dan shiru ya ratsa. Damar yayi ƙarya.
"Ka gaya min cewa ba daga ɗaki ɗaya ba ne suka fito.
Domin ina iya sansanin ƙarya daga nesa."

Yatsun Omar suka fara matsewa a cikin tafin hannu.

Omar ya shafe shekaru yana rayuwa ta rashin hankali, kuma Papa bai taɓa magana akai ba. Mommy ta taba faɗa masa sau ɗaya cewa Papa ya fara lura don har tambayoyi yake akan sa. Amma wannan? Wannan tukumar? Yasan ba game da shi bane. Duk saboda wannan la'ananniyar wasiyyar ce.

Ya fitar da numfashi a hankali, sannan ya yi magana. "Ina yin rayuwata yadda na ga dama, Papa. And that doesn’t give you the right to question me. Ina da ra’ayina — kuma ba zan nemi afuwa akan hakan ba. Kuma eh — ba zan ɓoye ba, dukkansu suna tare da ni ne.”

Kalmomin basu gama fita daga bakinsa ba, hannayen Papa suka kamo Kafadunsa ya ja shi zuwa gare sa. "Za ka daina wannan shirmen Omar." Rikonsa kamar ƙarfe ne, idanunsa sanyi fiye da duk lokacin da ya taɓa gani. "Domin za ka auri Aleena."

Omar ya saki dariyar da bata da daɗi — mai ɗaci.
“Pa, don Allah. Ka daina, wannan ba zai taɓa faruwa ba—”

“Omar Thorne!”
Muryar Papa ta yanka cikin iska kamar bulala.

Omar ya tsaya cak.

Rikonsa ya ƙara tamkewa, Ba ta hanyar ƙarfi ba, amma a matsayin gargaɗin Ƙarshe wan da ya shiga cikin ƙasusuwa sa.

"I was your age once, Omar. Papa ya ce, nasan abin da kake nufi da shagala. da wasa Amma ya kamata kasan lokacin da zaka tsaya." Idon Papa ya kama nasa. Kuma dole ka dena, ya tsaya daga nan a yau, Domin future in ka ba naka bane kai kadai, tana cikin wannan family, da abinda kakanka ya gina da sunan da kake ɗauka.”

Muryarsa ba ta tashi sama ba — ba ta buƙatar haka. Nauyin kalamonsa ke ɗaure sa kamar sarka.

Wani abu ya gangaro a makogwaronsa. Yasan wannan ba tattaunawa bane.
Umarni ne….

Ya tilasta muryarsa ta tsaya tsayin daka. Yace, "Ba zan iya aurenta ba, Papa. Bana ma so in yi aure. Kuma ko da zan yi, ba zai taba kasancewa Aleena Khan zan aura ba."Yatsunsa sun dunkule cikin hannunsa. ya kara cewa "Na tsani wannan yarinyar a rayuwata."

Kalmomin sa sun kasance masu kaifi, masu bijirewa suna yanke tashin hankali kamar takobi.

Amma Papa ko motsi bai ba.

Kuma hakan ya fi komai abin tsoro.

Bayan shiru mai tsayi, sai Papa ya saki rikon da yayi wa kafadarsa. Fuskarsa babu fahimta a cikin ta.

"To me yasa haka?" Papa ya tambaya, Muryarsa ta kasance cikin nutsuwa, amma akwai wani abu a ƙarƙashinta. "Faɗa min, Omar. Menene abin da yasa ta zama abun rashin iya jurewa a gareka? A zahirin gaskiya ita ce mafi kyau a cikin duk matan da na taɓa ganin ka dasu. Kyakkyawa ce. Mai hankali. Tana da wayo. Mai tausayi. Mai mutunci."
Gashin idanunsa suka ɗan ɗaga. "Faɗa min Idan nayi kuskure?."

Mukamukinsa suka matse. Ya kau da kai. Yana cewa, "kayi kuskure, Papa. Ba komai take ba face munafuka."

Wata yar karamar dariya ta fito daga gare shi. “Omar.” Ya girgiza kai, yace, "Idan akwai abu daya da na sani game da kai, shi ne girman kai." Papa ya dube shi na ɗan lokaci, "Yana da kyau ka daga kanka sama, Amma wani lokacin yana makantar da kai."

Omar yaji wani abu mai zafi ya karta a kirjinsa.

"Kana kiran Aleena munafuka, amma faɗa min wannan—"Da me zaka kira mutumin da ke wa'azi akan mutunci amma kuma yana ɗaukar mata kamar abin wasa? Wanda ke tafiya kafin rana ta fito, amma daga baya yana yanke hukunci akan wasu?"

Hakoran Omar suka kara matsewa. ta madubi ya hango direbansa yana dan girgiza kafadarsa. Yana riƙe murmushi. Suna hada ido direban yayi saurin kau da kai yana gyarawa.

"It's not the same-" Papa ba iri daya bane.

"Iri ɗaya ne."Papa ya katse shi, muryarsa mai kaifi kamar takobi. "Ayyuka daban-daban. Ka'ida ɗaya."

Ya shaki numfashi mai zurfi, yana ƙoƙarin rage haushin da yake taso masa.“It doesn’t matter. Aleena ba za ta yarda da wannan auren ba itama, Papa. Don haka — Tunda mu biyun bamu yarda ba, kaga kuwa wannan aure ba mai faruwa bane.

A hankali wani murmushi ya shigo fuskar Papa. Yace, “To me zai faru idan ta ce eh?”

Omar ya juya zuwa gare shi da sauri, bugun zuciyarsa ya dan tsaya. "Ta ce eh?"

"Ba ta da wani zabi." Papa yace.

Omar ya yi hadiya da kyar.

"Kakarta za ta yi magana da ita. Za ta fadama mata abin da ke cikin hadari. Idan ta ƙi, Khan Electronics ba zai shiga cikin Thorne Comm. Kawai bane, zai ɓace. Duk abin da kakanta ya gina, zasu ɓace. Duk abin da ta yi gwagwarmaya a kai, za a shafe shi."

Muryarsa ta kasance cikin sanyi yayin da yake fada.

"Ka ga kuwa, Omar..." Ya ja da baya, yana kallonsa cikin nutsuwa. "Kana iya ƙin ta. Tana iya ƙin ka. Amma ku biyun ba za ku iya ƙin wannan auren ba."

Wani tunani mai kaifi da sauri yazo cikin kan Omar. Ya fitar da wata dariya mai sauƙi, yana girgiza kai. "Hah."

Papa ya ɗaga gira. Da alamar tambaya.

Omar ya fitar da numfashi ta hancinsa, murmushinsa ya faɗaɗa. Yace, "To, don me kake tilasta min, Papa?" Ya jingina da kujera, hannunsa suna shimfiɗe a kan kujerar, yana kallonsa kamar ya riga da ya ci nasara. "Mu bari ta ƙi auren kawai, An warware matsalar. Mun sami Khan Electronics a banza kawai. Babu buƙatar aure, babu buƙatar wani drama ko wayo, ko Papa?"

Shiru Papa yayi.
Sai nauyin da ke cikin iskar ta canza.

Kallonsa ya yi duhu, wani abu mai kaifi da sanyi ya zauna a tsakaninsu.

Omar ya ji kamar ya daskare. Ya tsani kallon da ke idon Papa, wannan kallon ya san ta kuma baya san ta. Ba fushi bane. idan fushi ne zai iya jurewa zai iya yaƙi da hakan.

Amma disappointment? Wannan rauni ne da ba zai iya gyarawa ba.

Papa ya sauke numfashi a hankali, ya kallesa "Yaushe na rene ka don ka zama mara tausayi haka?"

Kallonsa ba riƙe shi yayi kadai ba, danne shi yayi da Karfi. Kalmomin kuwa ba rauni kadai suka mishi ba sun yage shi ne da har suka bar wani abu mai rauni wanda ba zai gyaru ba.

Ya kau da kai, mukamukinsa suna ci gaba da matsewa.

Muryarsa ta yi ƙasa a yanzu, amma duk da haka, ta ɗauki nauyi. "Ta yaya za ka faɗi haka, Omar?"

Ya hadiya da kyar.

"Aleena ba ta taɓa yin amfani da kamfaninta a kan ka ba. Kuma da taso zata iya, Hakane?" Ya bar tambayar ta zauna a cikin haƙarƙarinsa. "Amma bata yi ba. Kuma kar ka tambaye ni ta yaya na sani. I always know."

Omar ya tsani yadda Papa yake iya karanta shi cikin sauƙi.

"Ta shafe shekaru tana guje maka, tana nisantar ka, don tabbatar da cewa Khan Electronics da Thorne Comm. Kar su taɓa yin faɗa. Amma duk da haka, ga ka, kana ba da shawarar cewa mu kwashe mata komai?"

Matsin kirjin Omar ya ƙaru. Numfashinsa ya yi kasa sosai.

"Ko kasan abin da kake faɗa kuwa Omar?" Sautinsa ya yi karfi "Ka manta cewa tun tana yarinya, Aleena bata taɓa samun soyayya daga iyayenta ba? Ko wanne acikin su ya shagala da rayuwarsa bayan rabuwar su, Mutum ɗaya ce kawai da take da ita, ita ce kakarta."

Nauyin kalaman Papa suka matsa masa zuciya yaji tamkar yana shakewa. Amma ba shi kadai ba. Omar ya ga hawayen da basu fito ba a idon Papa. Mahaifinsa mai iko koda yaushe, mai ƙarfin zuciya, yana gab da karyewa.

Omar idan bai fahimta ba a baya, To ya fahimta yanzu. Kuma ya tsani ganin sa cikin wannan hali.

A wajen Omar, radadin iyayensa ya kasance kamar wani abu ne da bazai iya jurewa ba. Wani abu da bai taɓa son ya gani face idan bana farin ciki bane. Duk wani abu ya zama kamar laifi, kamar ya kasa a gare su ta wata hanya to abu ne wan da bazai iya jurewa ba.

Yanzu, gashi yana kallan Papa yana fama da riƙe kansa saboda shi? Hakan ya fasa wani abu mai zurfi a cikin sa.

"Kuma wannan kakar? Wacce ta rene ta? Tana fama da ciwon cancer, tana fama don ta rayu koda na ɗan lokaci kaɗan." Muryarsa ta yi tsauri. "Shin ka tuna halin da taka kakar ta shiga lokacin? Yadda ta sha wahala?"

Cikinsa ya karkace.

"Sannan kake tunanin kawai mu kwashe mata komai?" Kalamansa ba tambaya ba ne. Suna hukunci ne.

Omar ya kasa iya amsawa.

Papa ya fitar da numfashi mai karfi, sautin yana yanke shirun. yace, "Kamfanin nan shine kadai abin da ta rage mata."

"Kuma kar ka manta. Khan Electronics sun tsaya tare da mu lokacin da muka fi buƙata. Sun taimake mu lokacin da Thorne Comm. yayi rauni. Ba tare da neman wani abu ba." Muryarsa ta ɗauki nauyin wani abu mai zurfi fiye da kasuwanci. "Wannan ba kwangila ba ce kawai, Omar. Amincewa ce. Alkawari. Dangantaka tsakanin dangi wanda kakanka da nata suka yi gwagwarmaya don karewa."

Ya bar kalmominsa suna shiga cikin Omar, kafin muryarsa ta yi ƙasa. "Don haka faɗa min, Omar... Ta yaya za ka zama mai mugun hali haka?"

Wani abu mai sanyi ya zube a cikin kashin sa.

"Ta yaya zaka mai da wannan duka game da kai?"

Omar bai taɓa jin sa ya ƙanƙance a gaban Papa ba kamar yadda yake ji a wannan lokacin ba.

Numfashinsa ya katse. Hannunsa masu tsayin daka 'yan lokaci kadan da suka wuce yanzu sai rawar jiki suke yayin da ya miƙa hannu zuwa ga Papa.

"A'a, Papa, ni—"

"Omar." Sunan sa ya fito daga leɓansa a cikin wani sautin da ya sa Omar ya tsaya.

Ya cije ciki bakin sa bugun zuciyar sa yana bugawa a cikin kunnuwan sa.

Muryarsa ta yi taushi kaɗan. Amma ba ta raunana ba. "Ka sani cewa, ina son Aleena. Uwarka ma tana son Aleena, Tun tana yarinya karama, tana da dadin zama, tana da hankali, tana da tausayi, tana mutunta mutane."

Omar yayi shiru. Ya kamata yayi gardama. Ya kamata yayi yaƙi. Amma yadda Papa ke kallon sa, kamar yana karya wani abu a cikinsa, ta yaya zai iya gardama dashi?

"Bata taɓa rashin girmama ni ko uwarka ba." Papa ya ci gaba da Muryarsa ɗauke da wani abu mai nauyi yanzu. "Tana da nutsuwa. Ita ce duk wani abu dana taɓa so maka. Kuma na yi imani da Allah—" kallonsa bai dauke daga kanshi ba"—ita ce kadai wacce za ta iya kawo ƙarshen rayuwar ka ta banza."

Ya fitar da numfashi da rawar jiki.

"Don haka, lokacin da uwarka dani muka ji wannan maganar auren, ba mu taɓa kin hakan ba." Kalamansa suka zama na ƙarshe, "Kakanka ya yi shawarar data dace."

Yatsun Omar suka matse a kan tufafinsa, gwiwoyi suka yi fari. Bai lura da hawayen farko ba har sai da na biyu mai zafi suka zuba akan fatarsa.

Ko saboda kalaman Papa, ko rashin yardarsa, ko nauyin wannan tattaunawa, bai san wanne a cikin ba.

Dumin hannayen Papa suka shafa kumatunsa, yatsansa suna goge hawayen da ke zubowa akan fuskar Omar, hakan ya sa wani abu mai rauni a cikin kirjinsa.

Papa ya manna mishi kiss a goshinsa mai dan tsawo.

"Wannan ba game da kai kadai ba ne, Omar. Game da iyali ne, game da sunanmu. Shin ko ka fahimci nauyin sunan da ka ɗauka Thorne?"
Ba game da aure kawai ba ne. Alkawari ne. Nuna haɗin kai tsakanin iyalai biyu masu girma da iko da suka fi son biyan bashi ta hanyar kara dangon zumunta.

"Kai ne ɗana kaɗai kuma ina son ka sosai. Amma wannan? Wannan shine mafi kyawun hanya a gare ka. Ba zan taɓa zaɓar wani abu da zai cutar da kai ba."

Omar, shiru yayi, ya kasa iya magana.

Omar ya matsa gaba ya kalli direba, sai yace. "Kai mu zuwa gida yanzu."

"Na fahimta, Mr. Omar." Direba ya amsa cikin sauri da rawar jiki.

Omar ya zauna a daskare baya jin komai nasa.

"Yi tunani da sauri, Omar." Muryar Papa ta kasance a nutse.
"Aleena ta riga ta isa gidan tana tare da uwarka. Ka kula da halinka."

Sannan, ya juyo da kansa dan kadan zuwa gare shi, muryarsa ta yi kasa, amma ta fi hatsari.

"Idan har ka kuskura ka furta mata kalma mara dadi ko da sau ɗaya..."

Nauyin kalamansa suka zauna a tsakaninsu.

"Wallahi Omar, sai na sa ka tuna dalilin da ya sa bai kamata ba," ya fitar da numfashi, sautinsa a nutse amma mai ba da tsoro.

Ya goge idanunsa da rigar sa, kallon sa ya faɗa kan hannunsa masu rawar jiki.

A Turkiyya, iyali ba iyali kawai ba ne. Gadon ne. Wajibi ne. Ba kawai kana ɗaukar suna bane; kana ɗaukar kowane alkawari, kowane bashi, kowane yanke shawara da aka yi kafin ka san ma'anarsu.

Har yanzu yana tuna muryar kakansa acikin zuciyarsa, kamar lokacin da yake ɗan shekara sha uku.

"Omar, suna ne mai kyau kamar wanda ke ɗaukarsa."

Yanzu shekara 32 kenan, daya ɗauki nauyin sunansa, Amma yau? Yau sunan ya matse shi kasa irin yadda bai taba yi ba.

Ya shaki numfashi mai zurfi, amma zafin da ke cikin kirjinsa bai ƙare ba. Ko da idanunsa suka rufe, hawayen basu daina zubowa ba. Hannayensa ba su daina rawar jiki ba.

Bai san abin da zeyi ba.

Omar ya shafe rayuwar sa yana ganin yana da iko, zai iya yin duk abin da yake so, ɗaukar duk wanda yaso, rayuwa yadda yaso.

Amma duk da haka, gashi bashi da iko yau, An daure shi da wani abu mafi girma fiye da kansa, Wani abu da ba zai iya tserewa ba.

Shin wannan ne sakamakon sa? Ga kowace mace da ya yi wasa da ita? Ga kowace doka da ya karya? Shin wannan shine abin da ya kamata ya biya na tsawon duk lokacin da yake tunanin ba zai taba iya taɓuwa ba?

Papa shine farkon wanda ya fita daga motar. Bai waiwaya ba, bai yi jinkiri ba; kawai rufe kofar yayi ta bayansa.

Omar ya tsaya a ciki na ɗan lokaci, yana gyara gashinsa, ya share duk wani alamar hawaye da suka zuba a fuskar sa, Allah ya kiyaye Aleena Khan ta gan sa haka. Za ta yi tunanin yana da rauni.
Banza kawai.

Da matakai masu hankali, ya shiga cikin gidan. A cikin falo Mommy tana zaune kusa da Aleena.

Omar ya dubi fuskarta na ɗan lokaci, ta yi kama da wacce aka cirewa duk wani ƙarfi a jikin ta. Kallonta ya tsaya akan cinyarta. Mommy tana zaune a gefenta, tana shafa hannunta cikin shiru.

A gefe guda, Papa ya riga ya zauna a kan kujera. Ya nuna wa Omar wurin zama. Omar yayi biyayya, ba magana.

"Omar." Mommy ta gaishe sa cikin damuwa, idanunta suna kallon tsakanin Omar da Aleena.

Bai iya bada amsa ba. Shiru ya shimfiɗa tsakaninsu har sai da Papa ya yi magana.

"Aleena, kin yanke shawara? Za ki amince da hadin auren?" Muryarsa ta kasance cikin nutsuwa.

Aleena da kyar ta motsa. bata kalli sama ba, bata yi magana ba ko motsi a wurin da ta zauna batayi ba.

Papa ya kalli mommy, mommy ta ɗauki hannun Aleena, wataƙila don ta kwantar mata da hankali.

Omar ya kau da kai yana crossing kafafun sa. Bashi da abin da zai ce bayan abin da Papa ya faɗa masa a mota.

Amma shirun Aleena yana ƙara masa haushi, idan bata so kawai ta fada. Ta wani zauna a nan kamar wata yar tsana, tana sa kowa jira; Abun yana bashi haushi. ji yake kamar yana shakewa.

"Ya Omar ya riga ya amince da wannan hadin, Aleena," Papa ya ƙara, yana karya shirun.

Omar ya rufe idanunsa yana tilasta fuskarsa ta zama mara damuwa, duk da cewa nauyin kalamansa sun matsa shi kasa.

A gefen idonsa, ya ga Aleena tana kallan Papa, muryarta da kyar take fita. "Da gaske, Uncle Mehmet?"

Yadda ta tambaya a hankali, kamar numfashin ta zai tsaya, yasa Omar yaji wani irin takaici.

Omar ya juya zuwa gare ta. Idanunsu suka hadu. Aleena ta ɗaga gira tana harararsa.

Omar ya jefa mata kallon banza. Me take tunani? Tana tunanin ni nafara mika wuya a farko? Tana tuanin rauni gareni? Tana ganin kaman cewa tana da wani abu a hannunta yanzu?

Ah, a'a. Mukamukinsa suka kara matsewa cike da takaici.

Mommy ta yi magana a lokacin, sautinta mai laushi amma mai ƙarfi.

"Eh, 'Aleena. Kin gani? Ya Omar ya riga ya amince. Me na faɗa miki dazu? Bazai taɓa kin yarda ba."

Aleena ta yi humm da baki. Kamar tana tunanin wani abu mai keta. Sai a hankali da gangan ta juyo ta sake kallon Omar.

Tabbas, mommy ta yi magana da tabbaci, kamar amincewata ba tambaya ba ce. Kamar ba ni da cewa a cikin zancen.

Ta ci gaba, Aleena. Ya Omar yana buƙatar ya fara iyali, Kamar yadda na ce miki dazu, zama da matar aure zai sa ya fahimci rayuwa, ya dena wasa da yan mata. girma yake amma bai san yana girma ba."

Omar ya daskare.

Wani irin kunya mai zafi ya fara shiga cikin kashinsa. Kalaman mommy sun yanke shi a gaban Aleena, Mommy ta rasa inda zatayi irin magana haka sai a gaban Aleena? Wannan kawai ta fada ne a fili cewan shi ɗan iska ne da ke buƙatar igiya.

Kuma Aleena, wacce ta kasance tana nuna ita yarinya ce mai biyayya a duk wannan lokacin. Aleena ta ɗan karkata kai, tana kallon Omar ta fitar da ɗan wani murmushin banƙyama a gefen lebanta.

Omar ya tashi cikin sauri afusace.

Dole ne ya fita daga nan. Bazai iya zama a nan ba yayin da iyayensa ke ci gaba da ba wa Aleena kowane dalili don ta yarda da wannan hadin ba, zasu sata ne kawai ta raina shi.

Omar ya nufo wajen Aleena. Ko firgita batayi ba. A maimakon hakan, sai kawai ta dago da kanta sama tana kallon Omar cikin kasala, ta ɗaga masa gira ɗaya kamar shine mai matsala.

"Ke." Muryar Omar ta fito da ƙarfi. "Zo muje muyi magana."

Aleena tana nan zaune inda take, tana kallonsa cikin murmushin rainin hankalin da ya saba mata take masa yau.

Sai yaji Papa ya yi gyaran murya.

Omar ya fitar da numfashi mai nauyi, ya tilasta murmushi da taushin murya. "Aleena. Za ki zo tare da ni? Ina so in yi magana da ke... mu biyu kawai."

Ta ɗauki lokaci kafin ta amsa. Lokaci mai yawa. Da farko, ta kalli Mommy. Sannan Papa.

Sannan tace, "To." Ta fitar da numfashi kamar hakan duk bata lokaci ne, Kamar yarda da hakan wata alfarma ce da tayi masa.

Ohh, Allah…Ya Rabbi… wannan yarinyar munafuka ce. Omar ya fada cikin kasan numfashinsa.


A/N: Gobe ne fah!!!😭💔 Gobe auren Omar da Aleena mun shirya?
I can’t believe yau Omar ke kuka 🥺🤣……


💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️
Chapter 10 · 0% Book details