← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 29

Chapter 2️⃣5️⃣ Raɗaɗin Kalamanta 🥀💔🧍🏻‍♂️

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃


Shigar Omar kenan cikin babban lobby na Khan Electronics. Kamar yadda aka saba, kasancewarsa mutum ne da aka sani a duniyar kasuwanci, nan take wasu daga cikin ma'aikatan reception suka gane shi. Wata daga cikinsu ta miƙe tsaye cikin sauri da girmamawa. "Mr. Omar." Ta gaida shi da murmushi mai cike da ladabi. "Are you going to Mrs. Aleena's office?"

Omar ya gyada kai. "Yes. Is she upstairs?"

Ma'aikaciyar ta sauke kanta tana duba wani abu a cikin computer ɗinta. A hankali Omar ya matsa kusa da desk ɗin. Ya cire sunglasses ɗinsa daga fuskarsa, sannan ya saka su cikin aljihun suit ɗinsa. Bayan wasu sakanni kaɗan, ma'aikaciyar ta ɗago kanta. "Yes, Mr. Omar. Tana office." Sai kuma ta zaro wani ƙaramin key pass daga cikin drawer. Ta miƙa masa. "Please, go ahead."

Omar ya tsaya yana kallon card ɗin na ɗan lokaci. Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa. Key pass? Na musamman? Irin wanda ba kowa ake bawa ba. Irin wanda ke ba mutum damar shiga ba tare da ya tsaya neman izini a reception ba. Ya ɗan yi jinkiri kafin daga ƙarshe ya karɓa.

Ma'aikaciyar ta sake yin murmushi. Kamar tana jin daɗin mamakin da ke fuskarsa. "Mrs. Aleena ta bar umarni." Ta faɗa cikin ladabi. "Idan har Mr. Omar ya ziyarci Khan Electronics, zai iya wucewa kai tsaye zuwa office ɗinta. Ba sai ya tsaya neman izini ba." Ta nuna masa card ɗin. "Saboda haka daga yanzu za ka iya wucewa straight zuwa President's Floor."

Kalaman suka bugi Omar fiye da yadda yake san ya nuna. Aleena? Ita ce ta shirya hakan? Tun yaushe? Ba tare da ya sani ba? "Tun yaushe ta ba da wannan umarnin?" Ya tambaya cikin sanyin murya.

"Tun sanda ta dawo aiki office sati biyu kenan yanzu." Ta amsa. Sai kuma ta ɗan yi murmushi. "I'm sorry idan hakan ya ba ka mamaki, amma... ina ganin hakan ba wani abu bane." Ta ɗan yi shiru. "Tunda ku ma'aurata ne."

Omar ya kasa hana ƙaramin murmushin da ya bayyana a fuskarsa. "Thank you." Ya faɗa kafin ya juya ya nufi elevator. Da zarar ya shiga ciki, ya manna key pass ɗin a wurin da aka tanada. Elevator ɗin ta yi ƙaramar ƙara kafin ƙofofinta su rufe. Nan ne ya samu kansa yana kallon hoton kansa a jikin silver karfen na elevator ɗin. Sai kuma ya sake yin wani karamin dariya shi kaɗai.

Ma'aurata.

Kalmar ta sake maimaituwa a cikin kansa. Ji yayi kamar miji ne da ke zuwa ziyartar matar sa an office. Abin ya yi masa wani irin daɗi fiye da yadda ya kamata. Sai kuma wani tunani ya bugi zuciyarsa. To yanzu... Shima ya kamata ya ba Aleena key pass na Thorne Comm. ko? Ya shafa gefen card ɗin da ke hannunsa. Nan take ya tuna wasu kalaman Papa. "Dole ne ka ba matarka damar shiga rayuwarka ba tare da ƙofa a rufe ba." A lokacin bai ɗauki maganar da muhimmanci ba. Amma yanzu... Ya samu kansa yana tunanin hakan. Sai dai kuma wani tambaya ne daya sake taso masa. Shin Aleena ce ta shirya hakan da kanta? Ko kuwa da sa hannun Papa aciki? Ya kasa samun amsa. Amma abu ɗaya ya sani. Aleena bata taɓa zuwa office ɗinsa ba. Ko da sau ɗaya a shekara. Amma kuma duk da haka... Ya kalli card ɗin da yake hannunsa. A ƙasa an rubuta: SPECIAL ACCESS

Wani murmushi ya sake bayyana a fuskarsa. Ji yayi abun ya masa official sosai. Kuma saboda wani dalili da bai fahimta ba... Ya ji daɗin hakan. Wataƙila shi ma ya kamata ya bata irin wannan damar. Bayan haka, bai dace ace matar CEO ta zo kamfaninsa sannan a zaunar da ita a lobby tana jiran approval ba. Tun da wannan tunanin ya ratsa zuciyarsa, nan take ya hango fuskarta a cikin tunaninsa. Aleena. Tana shiga office ɗinsa cikin isa. Tana zagaye wajen kamar mallakarta. Wani irin yanayi ya ratsa shi. Sai ya girgiza kansa da sauri. Ya gyara suit ɗinsa. Sannan ya saka hannuwansa cikin aljihunsa. A daidai lokacin ne elevator ɗin ta tsaya.

Ding.

Ƙofofin suka buɗe kai tsaye zuwa 15th floor. Omar ya fita. Takun takalmansa suna amsawa a cikin corridor mai faɗi. Ba da jimawa ba ya isa gaban office ɗin. Idanunsa suka sauka kan tambarin da ke jikin ƙofar.

ALEENA ALI KHAN
CEO, KHAN ELECTRONICS

Wani abu yaji ya motsa a cikin ƙirjinsa. Sai ya ɗan juya kai. A gefe guda kuma akwai wata ƙofa.

LEILA
VICE CEO

Ya ɗaga gira kaɗan. Kafin idanunsa su sauka kan desk ɗin da ke kusa da office ɗin Aleena. Desk ɗin Mariam ne, sakatariyar ta. Sai dai babu kowa a wurin. Wataƙila lokacin cin abinci ne. Ko kuma tana wani taro. Omar ya mayar da hankalinsa kan ƙofar da ke gabansa. Ya ɗaga hannu.

Knock.

Knock.

Knock.

Sau uku.

Shiru ya ɗauki sakanni kaɗan. Sai kuma wata murya daga ciki ta amsa.

"Come in."

Murya ce da ya sani sosai. Murya ce da taƙi fita daga cikin tunaninsa tun da safe. Muryar Aleena. Nan take wani murmushi ya bayyana a gefen bakinsa. Kafin ya tura ƙofar ya shiga.

Ƙofar ya murɗa ya shiga ciki. A karo na farko da idanunsa suka sauka kan cikin office ɗin, ya hango Aleena zaune a gefen desk ɗinta. Rabin jikinta yana jingine da teburin, ƙafafunta kuma suna taɓa ƙasa.

Firgita tayi da kyafta do kaɗan. Sai dai cikin sauri ta daidaita fuskarta. Saboda ganinsa ya zo mata bazata. Sannan kuma ba ita kaɗai ce a ofishin ba. Akwai wani zaune a kujerar da ke gabanta. Da mutumin ya juya kansa... Idanun Omar suka sauka a kansa.

Emir.

Nan take fuskar Emir ta haɗe da wani irin bacin rai mai bayyane karara.

A lokaci guda kuma, murmushin da ke kan fuskar Omar ya gushe. Ya ji wani abu ya matse masa ƙirji. Numfashinsa ya ɗan yi masa nauyi. Bai san ko saboda ganin Emir tare da ita bane... Ko kuma saboda ya tarar suna zaune suna magana cikin yanayin da bai so ba. Ko kuwa saboda wani abu daban da shi kansa bai sani ba.

"Omar." Muryar Aleena ta katse shirun da ya mamaye ofishin. Ta miƙe tsaye cikin sauri. Kamar tana ƙoƙarin dawo da yanayin cikin ofinshin daidai.

Omar ya matso kusa dasu a hankali. "Na katse muku wani abu ne?" Ya tambaya cikin sanyin murya. Ya tsaya 'yan inci kaɗan daga inda suke. "Idan haka ne..." Ya ɗan ɗaga kafaɗunsa. "Zan iya jira." Yayin da yake magana, idanunsa suka sake komawa kanta. Doguwar rigar da ta saka tana manne da surar jikinta cikin tsari mai kayatarwa. Ta ɗaure gashinta baya cikin rolling mai kyau. A wani yanayi mai ban mamaki, ji yayi kamar ya ja ta jikinsa kuma ya rungumeta a wannan lokacin. Kawai don ya nuna wa Emir wani abu da ba zai iya furtawa da baki ba. Amma ya haɗiye tunanin. Ya tilasta kansa ya zama cikin control.

"No." Aleena ta amsa cikin sanyin murya. Ta kalli Emir na ɗan lokaci kafin ta mayar da hankalinta gare shi. "Me ya kawo ka nan?" Damuwar da ke cikin muryarta bata ɓuya ba. Kuma hakan ya fi bayyana saboda yadda take guje haɗa ido da shi kai tsaye.

"I need to talk to you about business." Omar ya faɗa. Sannan ya ja kujera ya zauna. Ya haɗa ƙafafunsa. Ya jingina da kujerar cikin nutsuwa. Kamar wani mutum ne da yake da cikakken ikon wurin. Idanunsa suna yawo a tsakaninsu. Shi kuma yana jiran amsa.

"Kuma wannan business ɗin ba zai iya jira ba?" Emir ya katse shirun. Muryarsa cike da takaici. "It's still lunchtime, Omar." Ya ci gaba. "Aleena da ni muna cikin wata muhimmiyar magana."

Aleena ta tsaya a wurinta. Idanunta suna komawa kan ɗaya sannan kan ɗaya. Kamar wacce ta shiga tsakiyar yaƙin da ba ta shirya ba.

Wani ƙaramin dariya ya kubuce wa Omar. Ya ƙara lumewa cikin kujerarsa. "Na riga na faɗa." Ya ce cikin nutsuwa. "Idan ina interrupting, zan iya jira."

Bacin ran Emir ya ƙara bayyana, ya naɗe hannayensa a ƙirji. "To ka fita." Ya faɗa kai tsaye. "Akwai kujeru a waje." Ya nuna ƙofar. "Za ka iya jira har sai mun gama."

Omar ya yi wani gajeriyar dariya. Irin dariyar nan da ke sa mutum ya ƙara fusata. "Eh." Ya amsa. "Na ce zan jira." Ya ɗan karkatar da kansa. "Amma abin da nake nufi shi ne..." Ya nuna kujerar da yake zaune a kai. "A nan zan jira." Ya ɗaga gira sanan ya ɗan yi murmushi. "Feel free, ku ci gaba da maganarku. Zaka iya sawa ma aranka bana nan."

Daga gefen idanunsa ya hango Aleena tana shafa goshinta a hankali. Kamar tana ƙoƙarin fahimtar yadda al'amura suka kai ga wannan matsayi.  "Omar..." Ta kira sunansa. Idanunta suna roƙonsa ya bari. Amma ko kallonta bai yi ba. Sam. Idanunsa sun kafe kan Emir.

Shi ma Emir ɗin kuma kallonsa yake yi, wani irin musayar kallon ƙiyayya suke yiwa juna. Wani irin shiru ne ya cika ofishin mai zafi kamar wuta duk da AC  yana kunne. "I don't understand you, Omar." Emir ya faɗa daga ƙarshe. Ya warware hannayensa. Sannan ya miƙe tsaye. Ya yi taku biyu zuwa inda Omar yake. "Wai ka san ma'anar mutum yana busy kuwa?" Ya tambaya.  "Ko kuma ka rasa duk wani mutunci da ya kamata ka nuna wa hakan?"

Omar ya ɗaga kansa a hankali. Kamar yana nazarin tambayar. "Oh, I understand." Ya amsa. "I really do." Ya ɗan gyara zamansa. "Mutane suna da abubuwan yi." Ya gyada kai. "Kuma ina mutunta hakan." Sai murmushin da ke kan fuskarsa ya dusashe, muryarsa ta yi sanyi. Amma kaifinta ya ƙaru. "But I'm afraid..." Ya kalli Emir kai tsaye cikin ido. "I don't have that same respect for you anymore."

Fuskar Emir ta ƙara tamƙewa.

Omar ya ci gaba ba tare da ya janye kallonsa ba. "Musamman idan maganar tana da alaƙa da matata." Shiru ya sake sauka cikin ofishin. Sai kalmarsa na ƙarshe ya fito a hankali. Mai sanyi, amma mai nauyi. "But hey..." Ya ɗan yi murmushi. "I am sure ka riga da ka san hakan."

Fuskar Emir ta ƙara yin ja. Jijiyoyin da ke gefen wuyansa suka fito fili.

Aleena kuwa ta matsa kusa da su cikin sauri. Idanunta suna aika wa Omar saƙonnin gargadi masu ƙarfi. Amma ba ta ce komai ba.

"Kana buƙatar ka koyi bawa mutane space." Emir ya faɗa cikin zafin rai. "Ba Aleena kaɗai ba. Kowa." Ya fada yana ɗan kara gaba. "It's called boundaries, Omar. Boundaries da ya kamata ka koyi mutuntawa."

Omar ya ɗaga gira. Wani ɗan ƙaramin dariya na takaici ya kubce masa. "Oh, I see... So yanzu kai ne expert akan boundaries?" Muryarsa cike take da zolaya. "To ko zan fara ɗaukar notes ne?" Ya kalli Aleena. Sai ya dawo kan Emir. "Maybe ko zaka koya min yadda ake saka su." Wani murmushi ya bayyana a gefen bakinsa. "Ka san abin da manya suke cewa?" Ya ɗan yi shiru. "Duk wanda bai san yadda zai saka boundaries ba..." Idanunsa suka makale cikin na Emir. "To sune mafi yawancin masu korafin cewa wasu su saka."

Bacin ran Emir ya kai ƙololuwa. Taku ɗaya ya kara zuwa gaba wanda yake gab da Omar.

Nan take Aleena ta shiga tsakaninsu da sauri.. Numfashinta yana fita da ƙyar saboda irin tension ɗin da ya mamaye office ɗin. Ta kuma kama hannun Emir. "Sweetheart, stop." Ta faɗa cikin sauri tana tura shi baya kaɗan. "Enough. Please."

Emir ya ja wani dogon numfashi. Yana ƙoƙarin danne fushinsa. "Bamu gama magana ba, Alee."

"Amma kana buƙatar tafiya airport." Aleena ta katse shi cikin murya mai lallashi. "Ka manta?"

A wannan lokacin ne wani abu ya motsa a cikin zuciyar Omar. Wani abu mai kama da takaici. Ko haushi. Ko kuma wani abu da ya fi haka muni. Ya tsaya yana kallonsu cikin shiru, ba tare da ya motsa ba.

Emir ya kalli Omar na ɗan lokaci, sai ya mayar da hankalinsa kan Aleena. "Alright." Ya faɗa. "You're right, sweetheart." Wani murmushi ya bayyana a gefen bakinsa. "I have to go." Ya ɗan gyara jakarsa. "Za mu ci gaba da magana idan na isa... I will call you, okay?"

Omar ya fara matsowa kusa dasu again, amma kafin ya isa... Takunsa suka tsaya. Cak.

Emir ya ɗaga hannunsa ya kamo gefen fuskarta. Sannan ya manna mata kiss a goshinta.

Wani irin huci ya tashi a cikin ƙirjin Omar. Mai zafi. Mai kaifi. Mai saurin bazuwa. Idanunsa suka buɗe sosai. Yana kallon hannun Emir da ke kan fuskarta. Kallon kiss ɗin da ya manna mata. Kallon yadda ya taɓa beautiful face dinta. Kamar yana da cikakken iko a kanta. Wani irin ƙuna ta taso masa mai ƙarfi fiye da yadda ya kamata. Ji ya hau yi kamar ya je ya janye ta daga wurin. Ya raba su. Ya nuna masa cewa— Sai kuma ya katse tunanin. Saboda bai ma san dalilin da zai yi hakan ba. Abin da yafi ba shi haushi ma shi ne... Aleena bata hana Emir ba. Koda yake ya lura da yadda ta ɗan firgita. Kuma hakan ma yasa Emir ya ɗan yamutsa fuska. Amma duk da haka... Kiss ɗin ya riga ya faru.

"Alright." Emir ya faɗa a hankali. "Zan tafi yanzu." Ya sake kallonta. "I will call you later." Ya juya.

Aleena ta buɗe baki kamar za ta ce wani abu. Sai kuma ta fasa. Ta yi shiru.

Emir ya jefa wa Omar wani mugun kallo na ƙarshe. Sannan ya fice daga office ɗin gaba ɗaya. Ƙofar ta rufe. Gam.

Aleena ta lumshe idanunta. Ta ɗaga hannu tana shafa gefen wuyanta a hankali. Kamar wacce ciwon kai ya fara damunta.

"Da alama soyayyarku ta fara samun matsala, nagani daidai?" Muryar Omar ta fito daga kusa da ita. Ya ƙarasa gabanta, tsayawa ya yi kusa da ita fiye da yadda ya kamata. "Amma kamar na san dalilin ma.." ya dan daga Kansa kadan.

Aleena bata haɗa ido da shi ba, taci gaba da shafa wuyanta. Tana jingine da gefen desk ɗinta.

"What do you really want, Omar? Faɗa min kawai." Ta tambaya cikin gajiya.

"Look at me." Ya faɗa kai tsaye muryarsa cikin bada umarni.

A wannan karon ta ɗago kai. Idanunta suka haɗu da nasa.

"Bazan ƙara magana a kan ke da Emir ba." Omar ya fada.

Aleena ta kura masa ido cikin mamaki. "A yaushe na taɓa buƙatar ra'ayinka akan relationship dina?"

Wani ƙaramin dariya ya kubce masa. "Ba kya buƙatarsu... Of course." Ya amsa, sai ya ɗan karkatar da kansa. "Amma zan iya sa ki buƙaci hakan idan naso." Ya ɗan dakata sannan ya girgiza kai. "But no... i won't do it."

Aleena ta juya idanunta cikin wani salo daya sa zuciyar Omar bugawa da ƙarfi. Sannan ta naɗe hannayenta a ƙirji. "Stop beating around the bush, Omar. Ka daina mun wani zagaye-zagaye."

Gyara tsayuwars yayi, sannan ya ɗan sunkuyo kusa da ita. Idanunsa suka makale cikin nata. Hannunsa ya sauka kan desk ɗin da ke bayanta. Ya matseta tsakanin jikinsa da teburin.

Nan take Aleena ta yi haɗiyar yawu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi. Amma ta dage wajen nuna kamar ko ajikin ta. Numfashinsu ke gaurayewa. Tazarar da ke tsakaninsu kuma tana ƙara raguwa.

"Bazan kara magana akanki da Emir ba, har abada." Ya sake maimaitawa. Muryarsa ta yi ƙasa sosai ta zama very calm, ya ɗan sunkuyo kaɗan."Ya kamata ace kin fahimci abin da nake nufi, akan dokokin da ya kamata ki kiyaye." Idanunsa suka sauka kan nata. "Ina fatan kin koyi darasi daga daren jiya." A lokacin ne ya lura idanun Aleena sun sauka kan leɓunansa na ɗan sakanni kaɗan. Kafin ta yi saurin dawo da kallonta kan fuskarsa. Gira ya ɗaga mata cike da zolaya. Wani mugun murmushi ya bayyana a gefen bakinsa. "You are really enjoying this, don't you?"

Hannayenta suka ƙara matse gefen desk ɗin. Ta yi gyaran murya tana ƙoƙarin dawo da nutsuwarta. "Na riga nayi masa magana. Shikenan abin da kake buƙatar sani." Ta faɗa cikin sanyi. "And you don't need to worry about boundaries." Ta ɗan dakata. "Or your parents." Idanunta suka ƙara kaifi. "Kuma nasan ka tuna abinda ya faru jiya da daddare. Har da maganar da na gaya maka." Ta ci gaba cewa. "Bazan yanke relationship ɗina da Emir ba."

Murmushin Omar ya fara daukewa, tare da wani irin shiru.

"I won't." Ta faɗa kai tsaye. "Bazan yanke ba."

Kalaman suka bugi Omar.

Amma ta ci gaba. "And about December... Ka tsaya a kan maganarka. Bazan iya jira har sai December ba, takardun sakin auren mu daga kotu zai iso bada jimawa ba." Muryarta ta yi sanyi amma babu alamar sassauci a ciki ta kalle shi kai tsaye. "Za su iso. Kuma za ka sanya hannu a kansu."

A lokaci guda sauran murmushin da yake kan fuskar Omar ya ɓace gaba ɗaya. Kalaman nata sun shiga inda bai yi tsammani ba. Har yanzu... Har yanzu tana san sakin auren daman? Daman har yanzu tana tare da maganar December? Wani abu ya taso a ƙirjinsa. Wani abu da bai taba ji ba arayuwarsa.

"Sannan kuma abu na karshe." Muryarta ta sake katse tunaninsa. "Daren jiya." Ta haɗiye yawu. "Ka manta da shi kamar bai taɓa faruwa ba." Ta faɗa cikin sanyi.

Idanunsa suka tsaya a kanta, sai kalamanta gaba daya suka zo masa kamar mari.

"Thinking about it made me sick all night. Taya ma na bari hakan ta faru?" Ta girgiza kai. "I don't understand it, abin tsantsami ne." Ta lumshe ido na ɗan lokaci. "Tunaninsa kaɗai yana sa ni jin kamar zan yi amai."

Omar bai motsa ba ko kaɗan, saboda wani abu ne ya matse masa ƙirji. Da ƙarfi.

"Don haka..." Ta faɗa a ƙarshe, muryarta cike da yanke hukunci. "Omar, bana san na kara magana akai har abada. Ka manta ya faru kamar yadda nima na manta. Mubar komai a baya." Ta ɗaga idanunta suka sauka cikin nasa ta fada, cold and final. Duk da tasan... Ko ita kanta ta san kalamanta sun yi masa rauni saboda a bayyane yake a idonsa.


💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️
Chapter 26 · 0% Book details