← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 27 OF 29

CHAPTER 2️⃣6️⃣ Wani Zafi Mai Daɗi ❤‍🔥💑😂

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃


Omar ya kwashe da wani irin dariya mai sanyi kamar fanko. Dariyar iyaka leɓunansa kawai ta tsaya ba taje cikin zuciyarsa ba. Ya gyara tsayuwarsa sannan ya ja baya kaɗan daga inda ya tsare ta tsakanin jikinsa da teburin. "Of course," ya faɗa cikin wani murya mai ɗauke da baƙar magana. "Tsantsami, ƙyama, amai... Ina mamakin ta yadda kike jin hakan akan daren jiya, bayan cewa kinji dadinsa sosai."

Idanun Aleena suka zaro kaɗan. Ta ƙyafta su cikin sauri tana kallonsa. "Kada kayi tunanin cewa zaka iya faɗa min duk abinda kaga dama, Omar. Saboda ko kaɗa ban ji daɗin abinda ya faru ba. It was a mistake. Kuma bazai sake faruwa ba."

"Na yarda bazai sake faruwa ba." Ya amsa ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kanta ba, sai ya ɗan karkatar da kansa kaɗan. "But you enjoyed it. Kuma koda zaki ci gaba da musanta hakan, ba zan yarda ba. Saboda nasan yadda mata suke reacting idan na taba su. And the way your body reacted to my touch? Hahaha... You enjoyed it. So, tunda kin ji daɗinsa, Aleena. Kada mu tsaya musu akan abinda mun sani. Saukin ki ne kema kuma hakan zai rage miki ciwon kai, Just a suggestion."

Tsaki ta saki a fili. "Ofcourse, you do." Muryarta cike take da takaici.

Omar ya ɗaga gira. Amma daga kallon da take yi masa ya san cewa bata gama magana ba.

"You speak like a real player." Kalaman suka fito da sauri, masu kaifi kamar wuƙa. "Kamar wani wanda yasan exactly yadda zai sa mata fadawa cikin tarko, kamar abun alfahari ne. Or part of your daily routine." Idanunta suka ƙara cika da takaici. "Kuma kasan wani abu?" Ta nuna shi da yatsa. "Wannan halin naka shine abinda yafi sani jin ƙyama akanka fiye da komai." Shiru ya sauka na ɗan lokaci. "Idan na tuna cewa na bari wani abu ya shiga tsakaninmu..." ta haɗiye yawu. "Jina nake kamar mara lafiya." Sai ta girgiza kai. "And no, I'm not lying." Muryarta ta yi sanyi amma cike da tabbaci. "I'm telling the truth. Ban ji daɗin abin da ya faru ba. Ko kaɗan."

Omar ya tsaya anan yana kallanta yana kwashe bakaken maganar da take zuba masa, yana kallon yadda fushinta ke feshi. Yadda nadama ke yawo a cikin idanunta. Da kuma wani abu daban... Wani abu da ya kasa fahimta.

Tsoro?

Rikicewa?

Amma duk da haka, kalamanta basu girgiza shi ba. Ko kaɗan. Sai dai ya lura da wani abu atare da ita, Aleena ta shiga cikin wasan game din da yake yi ita sai dai banbancin kawai bata san tana playing ba.

A hankali ya sake matsawa kusa da ita. "Kina yawan magana game da yadda kike ƙina," ya faɗa cikin wani murya mai laushi kamar shagwaba, sunkuyo wa yayi kaɗan gab da fuskarta. "Amma bana ganin hakan a idanunki, Aleena. I see something else."

Aleena ta firgita amma taki motsawa.

Omar ya ci gaba da kallonta.

"What?... Me kake nufi? Kana tunanin ina jin daɗin wannan banzan game din naka da kake playing? No, Omar. I hated it."

Omar Kara sunkuyowa kasa sosai gab da gab yanzu, don taji dumin fitar numfashinsa akan fuskarta. "Jikin ki yana yaudararki," ya fada cikin rada sannan da gangan. "Shine matsalar, kina ta cewa hate, hate . Amma jikin ki yaki boye min abinda kikeso koda kuwa kinyi ta kokarin boyewa."

Aleena ta tsaya cak bata motsi sannan kuma Omar ya kara ganin yadda hannunta ke ƙara matse gefen teburin. Shirun da tayi ya bazu a tsakanin su. Ya lura da yadda take ƙoƙarin riƙe kanta. Ya lura da yadda idanunta ke gujewa nasa na wasu sakanni kafin su sake dawowa. shirun da tayi ya fadi komai fiye da duk wata kalma da zata fito daga bakinta.


Amma Omar bai tsaya iyaka nan ba, ya cigaba da wani ƙaramin mugun murmushi da yake bayyana a gefen leɓansa. "Let me guess," ya faɗa a hankali. "kin tsani hakan saboda kin tsani cewan inada gaskia koh?. You hate how much you want to deny it, saboda duk lokacin da kika ganni sai kin ji wani abu, hakane?" Hannunsa ya kai yana matsar da wani siririn gashi dake taba fuskarta. Yatsunsa suna shafa fatarta ahankali.

Nan take Aleena ta daskare anan numfashinta ya yanke na yan sakanni. Sannan tayi hadiyar yawu cikin sauri. "You think you can just play with me?  You think you know me?" ta fada tana zaro idanunta.

Dariya yayi sannan yaja baya kadan daga kusa da ita tare da jefa hannayensa cikin aljihunsa. "I don't play, Aleena. Saboda bana bukata. Ni ba irin sauran mazan nan bane masu kokarin yaki da fadan kalamai don samun soyayyaki.. saboda na riga na sameta." Muryarsa ta kara fitowa ahankali cikin rada. "Ina ganin kece har yanzu baki fahimci hakan ba."

Dariya yayi sai yaja baya kaɗan, ya saka hannayensa cikin aljihun wandonsa. "I don't play, Aleena. Saboda bana bukatar yin hakan." Muryarsa ta fito cikin nutsuwa yana kafe ta da ido. "Ni bana daga cikin sauran mazan da suke yaki da ɓata lokacinsu wajen fadan kalamai don samun soyayyar ki, saboda na riga na sameta." Muryarsa ta kara fitowa ahankali cikin rada. "Ina ganin kece har yanzu baki fahimci hakan ba."

Aleena ta buɗe baki zata yi magana amma kalmomin suka makale mata. Tunani iri-iri suka fara yawo akanta. "Bazan bari kaci gaba da tunzura ni ba, Omar," ta faɗa daga ƙarshe muryarta tana ɗan rawa kaɗan idanunta suna nuna abinda take fada basu kai zuci ba. "Kana tunanin kawai saboda ka tabani, kayi kissing dina, shine kayi wining zuciya ta? You're wrong." Ta girgiza kai.

Murmushinsa ya ƙara faɗaɗa. "Ba maganar nasara bane, Aleena." Ya ɗan matsa kusa da ita. "It's not about winning. It's about understanding power. Understanding how it shifts, how it flows." Kafe ta yayi da ido. "And right now, Ina tunanin kin fara fahimtar cewa kin riga kin bani wannan control din akanki fiye da yadda ya kamata kuma bakyasan yarda da hakan."

Wani walƙiya na fushi ya ratsa idanunta. Amma duk da haka, bata kau da kallonta ba. Omar yaci gaba da kallonta, sai kuma ya lura da tsananin damuwar da ta shigeta da kuma yadda take kokarin yaki da kanta don nuna babu abinda yake gaskiya akalamansa.

Fuskarsa yanzu tana kusan gab da fara gogar tata muryarsa a wani irin  karamin sanyi yace. "You can keep pretending, Aleena. Zaki iya cigaba da cewa duk wannan bai dameki ba, amma daga ni har ke mun san ya dameki." Ya daura hannayensa a gefen waist dinta daga jikin teburin dake kusa da ita yana cinye duk wani space tsakaninsu. "Kuma ki sani bazan daina ba har sai ke da kanki kin fadi duk abinda na fada gaskiya ne.."

Kafe shi tayi da ido itama ta kasa numfashi idanunsu sun makale cikin juna lips dinsu suna gab da taba juna."Me zan fada da kaina?" Ta tambaya muryarta tana fita da kyar, yawunta yana makalewa a makogwaronta.

"Cewan karya ne yanzu baki tsaneni kamar da ba, cewan wani abu ya canza tsakanin mu, and kuma kema kina san abinda yake faruwa tsakaninmu fiye da yadda nakeso." Ya amsa mata murya cike da tabbaci. "Kuma kina sha'awata kamar yadda nake sha'awar ki. Duk da bakya son ji amma kina ji." Na wasu yan sakanni Omar ya dauka zata karaya kuma ta fada masa cewan eh hakane tana jin duk abinda yace, amma kuma batayi hakan ba amaimakon haka ja baya tayi tana girgiza kanta kamar tana kokarin fisge kanta daga tarkon da yayi tsakanin jikinsa da ita da take manne jikin desk din.

"I don't know why I am even entertaining this," ta faɗa tana juya idanu cikin rainin hankali.

"You don't have to entertain it," ya amsa kai tsaye, muryarsa cike da wani nishaɗi. "You can fight it, amma daga ni har ke mun san gaskiyar kuma hakan shi yafi komai dadi. And trust me, Aleena, bazaki dade ba zaki yarda dani."

Ta ciji leɓenta tana kallonsa ido cikin ido. Omar kuwa ya dauka finally she's breaking and giving in. Amma batayi ba, instead. Gyara tsayuwarta tayi tare da naɗe hannayenta a ƙirji. Hakan yasa gefen hannunta ya dan goga da ƙirjinsa saboda kusancin da ke tsakaninsu. "I'm done playing games with you, Omar." ta faɗa cikin murya mai kaifi kamar wacce ta kawo ƙarshen tattaunawar gaba ɗaya. "Na gaji da wannan wasan naka. I still hate you. Kuma a fili yake. Babu wani abu da zai canja hakan."

"Are you sure?" ya tambaya a sanyaye. Yaja baya kaɗan daga gare ta, wani murmushin rainin hankali yana kwance a gefen leɓensa. "Saboda nasan kiyayya ta kan komawa so."

Bata amsa masa ba amma Omar ya lura da tension dake tare da ita daga yadda kafaɗunta suka motsa. She was fighting it, fighting him, Wannan kaɗai yasa wani murmushi ya sake bayyana a fuskarsa tare da yanke shawarar ƙyaleta haka don ta samu space din yin numfashi saboda abayyane take yaki take da kanta. "Alright, Mu bar maganar nan. Saboda bana son ki kumbura ki fashe akan zancen nan." Ya fada yana kallon idonta dake kallan gefe. "Dalilin zuwa na nan shine, saboda nasan yaushe zaki samu free time da zamuje Antalya."

"Zaka iya jirana a gida, zan baka amsar, Omar." tayi wani tsaki muryarta cikin haushi. "Baka buƙatar kazo nan kayi ta fadawa saurayina magana kamar yadda kayi dazu."

Omar ya ɗan yamutsa fuskarsa. "Taya zan san ko zaki dawo gida? Na fada miki tun safe, Aleena. Dalilin da yasa na tambayi number dinki kenan, saboda gujewa abubuwa irin wannan ne. Amma kika ƙi bani. So... yanzu ga ni nan."

Ta buɗe baki za ta yi magana. Sai ya katse ta. "By the way..." ya faɗa cikin wani murya mai sauƙi. "Key pass ɗin da kika sa reception suka ba ni, That was cute."

"Uncle Mehmet ne yace na baka." ta fada tana cukune fuska bakin ta ya turo gaba kadan. "So, karma kaji dadi ka dauka nice na shirya hakan."

Omar ya saki wani ƙaryaryar dariya ahankali. "So... Papa ne kenan ya hada hakan? Amma meyasa banyi mamaki ba?" Ya dakata yana daga kansa kadan yana tambaya. "So, yanzu akwai mutane biyu da suke da exclusive access zuwa wannan floor ɗin?"

"Saurayina ya dade yana dashi for 2 years now. So, ba wani abun mamaki bane, right?" Ta amsa Muryarta flat cikin sanyi kamar kankara. "Kuma kamata yayi daman ace shi kadai ne mai wannan special access din. Kuma bana buƙatar yi maka wani ƙarin bayani. Ina ƙoƙarin sauƙaƙa abubuwa ne kawai. Ba complicating su ba..inda badan Uncle Mehmet ba, bazan taba baka wannan special access din ba."

"Fine, zan yi kamar banji abinda kika faɗa ba," yace yana daga kafaɗa cikin wani sauyin yanayi. Ido Aleena ta zaro masa tana aika masa wasu arshashi zuwa idanunsa. "Yanzu bani phone number dinki," ya kara cewa muryarsa babu barin waje na gardama.

Aleena ta juya idanunta sama, wani kallon rainin wayo ta aika masa.

Shi kuwa ya ci gaba. "Idan har ba kya son na riƙa zuwa office ɗinki ba tare da sanarwa ba... amma ruwanki ne. Kar ma ki bani number ɗin," ya fada yana wani dariya kasa kasa. "After all, yanzu ina da key pass zan iya shiga da fita ko yaushe naga dama." Ya jefa hannuwansa cikin aljihun wandonsa.

Aleena ta kafe shi da ido, sai ta kalli desk ɗinta. Sai ta sake kallonsa. Kamar tana lissafi a ranta, kamar zatayi magana kamar kar tayi. "Bani wayar ka," ta fada daga karshe.

Omar ya danne murmushin da ya kusa kubuce masa, ya zaro wayarsa daga aljihu ya miƙa mata.

Ta fisge wayar daga hannunsa da ƙarfi. Cikin haushi. Irin haushin da mutum yake yi idan ya san anci galabarsa. "Kuma karka kuskura ka gwada tura min wani abu da bai dace ba, idan ba haka ba zanyi blocking dinga kafin ka kyafta ido." Ta fada tana danna masa harara.

Wani haske na nishaɗi ya bayyana a idanunsa. "Ko mafarkin hakan ma bazan yi ba, Madam." Ya faɗa cikin murmushin nasara.

Idonta ya sake aikawa Omar wata harara mai nauyi yayin da ta miƙa masa wayarsa.

Yatsunsa suka gogi nata na ɗan sakanni kaɗan. A hankali. Da gangan.

Da sauri Aleena ta janye hannunta kamar ta taɓa wani abu mai kuna.

"Easy, Aleena," Omar ya faɗa yana kallon reaction ɗinta da wani murmushi a gefen bakinsa. "Bazan shafa miki komai ba don yatsunki sun taɓa nawa."

Harara kawai ta sake aika masa kafin ta juya ta nufi kujerarta. "Banda tabbacin hakan," ta faɗa tana zama. "Watakila yatsunka sun riga da sun shafawa wasun matan naka dayawa."

"Ouch.!" Ya dafe ƙirjinsa cikin wasa kamar kalamanta sunyi masa zafi. Amma kamar hakan kara kular da ita yayi. "No need to worry. Idan baki yarda ba, na tabbata ai kin yarda da harshena koh? Because it works perfectly-" yace  cikin nishaɗi.

"Zaka iya tafiya yanzu, Omar?" Ta tambayeshi tana sakin wani tsaki.

Dariya yayi yana gyada kai cikin jin daɗi da nasara. "Yes. Ai na samu number ɗinki. Don haka ina ganin babu anfanin na tsaya anan din. Enjoy your day, Miss Khan." Ya ɗan yi mata salute na tsokana. Ya juya zai fita har yaje kofa sai kuma ya tsaya. Ya ɗaga gira ya juyo ya kalle ta.. "Wait. Na kusa mantawa. Yaushe ne exactly zamu tafi Antalya?"

Aleena ta kwanto kan desk ɗinta ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. "Tomorrow."

Murmushi yayi sannan shima ya jingina da jikin ƙofar yana kallonta. "Perfect. See you at home then."

Wani ƙaramin murmushi tayi mai kyau amma yafi guba daci. "Yes, darling. Wait for me at home. Kuma karka manta kasa kayan da suka fi maka kyau." Ta amsa cikin wani salo mai cike da rainin hankali.

Omar ya juya da sauri yace, "Oh, I will." But please... ki daure kada ki sake lumewa cikin kallon lips ɗina kamar yadda kika yi ɗazu."

Idanunta suka buɗe sosai. Ta miƙe zaune. "What? Yaushe na kalli—"

"Na ganki." Ya katse ta. "Aleena Kar ki damu. Ba abun kunya bane." Sai kuma ya ƙara rage muryarsa ƙasa-ƙasa. Cike da tsokana. "Zan sa wani abu mai kyau idan kika dawo gida anjima, amma fa ina kara tuna miki kiyi kokarin kame kanki saboda bazan so ki suma ba idan kika ganni."

Mukamukinta suka matse wanda ya nuna tana daf da balbala masa masifa. Wanda hakan shi ne abin da ya fi ba shi nishaɗi. "Get. Out. Omar." Ta fada tana juyawa neman wani abu anan don jefa masa.

Yaga yadda take neman wani abu da zata jefa masa. Hakan yasa ya kwashe da wani irin dariya mai sauti. Mai cike da jin daɗi. Ya buɗe ƙofar cikin sauri ya fice. Kafin ta samu damar jefa masa komai. Ƙofar ta rufe a bayansa.

Bayan ya shiga elevator, ya lura da cewa murmushin da yake fuskarsa yaƙi gushewa. Har kumatunsa sun fara masa ciwo. "Aleena ba wuya an hura ta." Ya furta a hankali yana dariya shi kaɗai.

Sai kuma ya tsaya cak yana kallan fuskarsa ajikin karfen elevator din. Murmushin da yake fuskarsa na daban ne, bana koda yaushe da ya saba ba, bana tsokana bane, ko najin dadin narasa bane, na wani abu daban ne kuma mai zurfi wanda yasa akaro na farko har dimples ɗinsa sun bayyana. Murmushin ya fito daga zuciyarsa ne.

Nan da nan  ya goge shi daga fuskarsa da sauri. "No." Ya girgiza kansa. "No, Omar." Yaci gaba da kallon kansa. Why are you smiling like that? Saboda ka samu number ɗinta? Ko saboda ka ɓata mata rai? Ko saboda zata dawo gida yau? Tambayoyin suka fara yawo a kansa. Zuciyarsa kuwa taci gaba da bugawa. Da ƙarfi. Da sauri. Fiye da yadda ya kamata.

Aleena yau zata dawo gida. Zasu kwana ƙarƙashin rufi ɗaya. Zata zauna a inda yake zaune. Zata shaki iskar da shi ma yake Shaka. Kuma kawai tunanin hakan... Ya isa yasa zuciyarsa kara gudu.

"What is this?" Ya furta a hankali. Wani irin zafi mai daɗi ne yake yawo a ƙirjinsa. Ba ruɗani kaɗai bane, kuma ba sha'awa kaɗai bane. Wani abu ne daban. Wani abu da yake ƙara girma. Wani abu da ya fara tsorata shi. Idanunsa suka buɗe sosai. Yana ƙoƙarin daidaita numfashinsa. Amma hakan ya gagara.

"Tabbas bani da lafiya." Ya faɗa wa kansa. Muryarsa kusan rada. "Maybe ina buƙatar naje asibiti." Ya dafe ƙirjinsa. Saboda zuciyarsa taƙi rage gudu. "Heart palpitations?" Ya haɗiye yawu. "OMG..." Ya lumshe ido. "I'm too young for heart palpitations."


💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️
Chapter 27 · 0% Book details