← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 29

Chapter. 1️⃣4️⃣ Saki? A’a. 🔒🌫️

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃


Aleena tana tattara kayan ta a hankali cikin dakinta na Thorne family, Kawai sai taga ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, babu knocking, idanunta suka kafe kan kofa.

Omar ya shigo cikin dakin kamar iska, ya rufe kofar a bayan shi. ƙarar ƙofar na bada wani irin sauti mai nuna ƙarfin iko da ɗan tsoro. Bai ce uffan ba. Kuma bai buƙatan hakan. Saboda tsayuwar sa kadai ta cike dakin kamar wani mai ba da umarni, ko irin wanda ya mallaki wajen – eh, watakila ya mallaka, tunda na iyayensa ne.

Ya zura hannu daya cikin aljuhun wandon sa, tsayuwar sa cikin nutsuwa tare da wani abu mai nauyi a cikin idonsa. Idonsa kamar dutsan kankara, masu sanyi, masu kaifi.

Aleena ta tsaya cak, yatsunta suna kan kayan da take ninkewa. Wani bacin rai ta ji ya tokaro kirjin ta. Ta daga ido ta kalleshi, muryar ta flat tace, “Me kake so?”

Bayan wasu yan second sai yace, “Ina za ki?”

“Gidanmu zan koma,” Aleena ta ce tana hade rai ta cigaba da aikin da take yi tana kin hada ido da shi. Ta kara cewa, “Na riga na yanke shawara zan zauna a can.”

Wani dariyar ba’a ta fito daga bakin Omar. “Kuma kina tunanin zan yarda da hakan?”

“Yarda?” Aleena ta fada tana mikewa da sauri. Ta kalli cikin idonsa da ke cike da sanyi ta ce, “Yaushe na fara bukatan yardar ka kafin na yi abu, Omar?”

Bai motsa ba, bai firgita ba. Wani dan karamin dariya ya sake fitarwa. “Watakila bakya bukata. Amma iyayena fah?” Ya daga idonsa kallon sa kamar yankan wuka. “Ya kamata su san inda matar dansu za ta koma da zama. Ba kya tunanin hakan, Aleena?”

Ya yi shiru yana barin maganar ta ratsa sararin tsakaninsu, sannan ya kara da cewa, “Besides… sun riga sun siya mana gida. Matsayin wedding gift.”

Aleena ta juya idanunta cikin rashin kunya ta wuce ta gefen shi ta nufi wajen wardrobe din kayan ta. “Za ka iya zama anan amma ni ba zan zauna ba.”

Kafin ta dauki riga, hannun Omar ta ji ya fisgota cikin wani karfi yana rike kafadarta da har ta yi tuntube. Fuskokin su kusa yanzu, numfashin sa yana sauka akan fatar ta.

“Na fada maka kar ka kara taba ni,” Aleena ta ce tana jan kafadarta, amma ya rike ta gam. Jikin sa ya kara matsowa kusa yana rufe space din tsakaninsu tare da wani sanyi mai kaifi a idonsa da ya sa zuciyar Aleena ta fara harbawa da sauri.

Idonsa yayi sanyi kamar kankara. Ya rufe cikin kallon Aleena. “Look, “Bari mu fuskanci gaskiya—ba ma kaunar juna. Ya fada a hankali amma muryarsa kamar reza. “Kuma hakan afili yake haka ne? Mun yi aure saboda ba mu da zabi, amma hakan ba yana nufin zan barki ki dinga raina ni ba.”

Aleena ta yi shiru na yan second. Amma badan bata da amsa ba—sai don kallon da ke idanunsa ya firgita zuciyarta – ba fushi bane amma wani abu… wani abu da ya nuna mata ba da wasa yake ba.

Sai ya saki hannunta amma bai matsa ba, ko dauke ido daga cikin nata bai ba. Aleena ta fara shafa wajen a hankali saboda tsananin rikon da ya yi mata.

“Ko kina so, ko ba kya so, Ke…matata ce,” Omar ya cigaba da magana, muryarsa a hankali kusan kamar rada kusa da fuskar ta kamar wani mai tuna mata sai kace ta manta.
Muryarsa ta sake yanka shirun. “Kuma yanzu ke Thorne ce.
Kuma Thorne family sun baki gida. Dole ki zauna a ciki… Kuma ki bi abinda nace, kin fahimta?”

Aleena ta yi wata karamar dariya a cikinta tana jan baya cikin girgiza kai. “Ka ga Omar, biyayya? Ba abu bane da zaka tilasta min. Kuma magana akan zama Thorne?” Ta girgiza kai. “Ni ba Thorne bace. Kuma ba zan iya pretending ina jin hakan ba. Saboda ba Thorne bace ni.”

Aleena ta ga reaction dinsa – lips dinsa suna matsewa, murmushinsa ya mutu cikin fushin da bai fito ba amma yana tashi da sanyi kamar iska mai kaifi.

“Wannan auren fake ne a wajena.” Aleena ta fada tana daga murya. “Kar ka kuskura ka zata na amince da shi koda da zuciyata. Ba komai bane a wajena.” ta tura shi da ƙarfi don ta wuce, amma bai motsa ba. Tsayuwarsa kamar dutse.

Omar ya saki wani dan dariya mai cike da mugunta cikinsa. Ya ɗora yatsunsa cikin gashin kanta yana kallonta kamar yana karantar ta. “Fake koh? Maybe,” ya ce a hankali. “Ba ma son juna nida ke wannan na yarda. Amma igiyar dake kanki fa? Suna? Shaida?” Ya matso kusa muryarsa ta sauka a hankali da gangan. “They were real, Aleena. Wannan duk gaskiya ne, kakarki ta zauna a wajen, ta ga komai da idonta.” don haka kar ki kara ko da sau daya raina ni ko ki fada mun maganar da ba ta yi min ba.”

“Karka ƙara saka sunan Granny a cikin wannan, Omar!” Aleena ta katse shi. tana ja da baya, numfashinta na saurin fita.

“Zan ci gaba.” Muryarsa cikin sanyi kamar reza. “Idan hakan zai sa ki tuna cewan yanzu ni mijinki ne. Kuma yanzu ke Thorne ce. Kuma baki da ikon yanke shawarar barin gidan nan ba tare da yardata ba.”
“Me kike son in ce wa iyayena? Me kike son dangina su ce?” Omar ya ɗaga murya kaɗan. “Iyayena basu yi komai ba sai son ki. Fada min kin kuwa damu da yanda zasu ji ko kadan, Aleena?”

Aleena ta juyar da kai da sauri ta kasa iya hada ido da shi. kallon da ke idonsa yana razanata. A karon farko Aleena ba za ta iya cewa idan tsoron shi ta ji ya shiga zuciyar ta ba ko kuma kawai ta gaji ne da kasancewar sa anan. Amma abu daya ta sani eh tabbas… Da gaske ta damu da iyayensa—suna nuna mata ƙauna sosai fiye da yadda take tsammani. Kuma a ko yaushe tana musu godiya da kasancewar soyayyarsu a gareta.

“Dukkan maganganunku da Emir… na ji su.” Muryar Omar ta sake shigowa. Muryarsa yanzu ba tare da tsawa ba, amma kalmomin suna da kaifi kamar wuka a zuciyar Aleena.

Aleena ta dago kanta sama cikin firgici tana kallonsa kirjinta yana matse mata da karfi.

“Kuma ba zan ba ki hakuri saboda na tsaya ji ba,” ya cigaba muryarsa kamar ya gaji da zancen.“ Na fahimta karara. Kina son shi kuma kina bukatan shi, kuma kina son in sake ki.”

Aleena ta kyafta ido zuciyarta tana bugu maganar sa kamar anjefe ta da kankara. Bata san mai zata ce ba.

Ya daga kansa yana nada hannunsa a kirji. “I don’t care Aleena idan kina san rayuwa tare da shi. Amma ki barshi sirri. Kada ki bari iyayena su sani. Sun san Emir kuma suna ganin shi da mahimmanci…” idanunta suka kara budewa. “Sun san Emir? Mai kake nufi?” Omar ya daga idonsa cikin gargadi. Wanda bai bata ansa ba ya cigaba da maganar sa. “Papa ya fara tambaya—menene alaƙarki da Emir? Na ce musu friend dinki ne. Don haka ki tabbata hakan ya tsaya anan. Kada ki sake bari wani abu ya fito fili.” Keep whatever it is to yourself.

Aleena ta sankare na yan second kamar wacce aka tsayarwa da numfashi taji kalamansa suna dukan ta fiye da yadda ta zata. Tunanin ta ya fara juyawa zuwa baya ga lokacin da komai ya fara rikicewa sanda ta gudu tana bin Emir. Kunyar kanta ta fara ratsa jikinta har ta rasa inda zata buya. Kamar ta nutse—ta bace gaba ɗaya.

“Sai da nayi bayani,” Omar ya cigaba da magana cikin sanyin murya, “Na tsaya nayi defending dinki, nace musu ke da Emir babu komai tsakaninku. Friends ne kawai. A yanzu sun yarda dani. Amma ina kara tuna miki…” ya dan dakata idanunsa suka ƙafe nata, “…ke matata ce. Duk da auran baki dauke shi a bakin komai ba. ya fada Idonsa cike da sanyi kamar kankara. Amma ki fahimci wannan: Ya kamata ki fara bada duk wani hakki dake kanki na matsayin matar aure.”

Aleena taji kalaman sa kaman duka a fuska. Maganganun sa sun doki zuciyarta. Sai da ta shanye wani yawu mai zafi kafin ta iya magana.

“Omar,” ta furta a ƙarshe, muryarta cike da juriya da ɓacin rai. “Idan kana neman wani abu fiye da igiyar da aka daura a kaina wallahi na rantse maka bazan iya. Kar ka fara tsammanin hakan.”

“No.” Ya katse ta da sauri, muryarsa kamar reza tana huda iska. “I have zero interest in you. Ko na second daya bana jin wani abu a kanki. Kin ji?” Idanunsa sun cika da girman kai da wani irin ɗaci da ya saki a fili. Aleena taji ta kamar wata ƙaramar mace a gaban sa. Ta ja dogon numfashi ta matso kadan tana cewa: “Masha Allah. Tunda duka muna layi daya. ko?” Ta murɗa lips dinta cikin ƙyama. “Fine. Zan ajiye relationship dina da Emir cikin sirri. Zan kuma yi biyayya ga iyayenka. Amma kada kayi tsammanin zan maka biyayya kai, Omar. That’s not happening. Kuma wannan biyayyar ma, saboda iyayenka kawai nake yi.”

Omar ya ja baya kadan motsinsa da gangan yana kallonta cikin sanyi da mugun nutsuwa. Ya ce da wata murya mai sanyi: “Kin samu abinda kikeso—rayuwa da Emir. Ni kuma na samu abinda nake so—biyayyarki ga iyayena. That’s enough.” Sai ya dan ciza lips dinsa. “But Aleena…” yace, muryarsa ta sirƙe kamar ta sare itace. “…bazaki taba samun sakin da kikeso ba.”

Aleena ta tsinci kanta tana matsawa kusa da shi ta jawo rigarsa.
“Me yasa?” ta tambaya cikin fushi. “Sakin yana da mahimmanci. Ba ma kaunar juna. Wannan auren ba komai bane illa show. Kawai ka sake ni, Omar!”

“No.” Ya sake katse ta da sauri. Ya ɗaura hannunsa a kirji. “Idan zan sake ki ma, ba yanzu ba. Na baki ’yanci kiyi abinda kikeso, amma banda wannan, saki Aleena? Banda shi.”

Aleena ta bude baki zatayi magana cikin fushi amma Omar ya daga mata hannu yana dakatar da ita kamar mai mulki.

“Zaki rasa Khan Electronics idan baki cika matsayin matata ba kafin ki cika shekara 26.” Ya furta a hankali kamar yana yanke hukunci. “Bari na tuna miki, har yanzu baki kai shekara 26 ba. Munyi aure da wuri ne saboda kakarki. Don haka, ki zauna a matsayin matata har zuwa December 21st. 7 months.”

Idon Aleena ya kada bakin ciki na taso mata kamar ruwa mai dafi. “I don’t care about that Omar, ban damu da company din ba. Kawai ina so na fita daga cikin auren nan.”

Omar ya saki dariyarsa ta ba’a, mai sa zuciya ta ɓaci. “Baza ki iya jiran 7 months ba? Emir zai jira ki, Ai yana sonki ko? Idan ba haka ba, kin san me zai faru.”

Aleena ta jefa masa harara mai cike da gargaɗi. “Karka ƙara fadin sunan sa.”

Omar ya kwashe da dariya yace, “Ke da shi kuna cikin relationship da shari’a bata yarda da shi ba. Ni kuma mijinki ne. Don haka—ina da ikon magana akan shi.” Ya matso kusa sosai yana sauke numfashinsa a gefen kunnenta. “Zaki samu masoyin ki da company din ki. Amma… bayan 7 months. Kuma zaku more. Saboda bazaki rasa komai ba.”

“Why?” Aleena ta tambaya muryarta tana rawa kamar ganyen bishiya cikin iska. “Meyesa ka damu sai bayan 7 months? Sai kace ka damu dani? Mene damuwar ka Idan duk da hakan ina son ka sakeni yanzu?”

Murmushinsa ya kara girma - murmushi mai dauke da mugunta da rashin jin tausayi. Wanda ya karawa Aleena takaici fiye da murmushinsa na ba’a.
“Duk bai shafi damuwa dake ba ko kuma abinda kikeso ba,” yace kallonsa cikin sanyi. “Kawai ina bukatan iyayena su kasance cikin farin ciki. Koda na 7 months ne. Suna farin ciki da auren nan, kuma bana san abinda zai kwace musu farin cikin nan. Kuma bana san wani matsala kafin fito war T-phone gen 6.”

Aleena ta dan daure fuska tace, “Kafin fitowar sa? Ai sai October.”

Omar yayi murmushi yana shafa kafadarta kadan, amma Aleena taji kamar shocking ya ratsa jikin ta gaba daya. Duk wani gabobi na jikinta taji suna matsewa. Hannunshi ya tsaya nan kafadarta zuciyarta tana mata ihu ta ture shi ta matsa amma jikinta ya kasa bin umarnin zuciyarta.

Sai Omar ya matso kusa da ita sosai yana fesar da numfashi a kunnenta ya ce, “I have delayed it, princess. Har sai December. Zanga yadda za a yi da Khan Electronics. Na riga na sanar da Leila da Mariam. Ina tsammanin basu fada miki ba tukunna… watakila saboda sun ga har yanzu kina cikin damuwa ta rasuwa.”

Ya tsaya kadan numfashinsa yana fesa akunnenta. “Trust me, ina yin hakan ne saboda inada tausayi - CEO din tana cikin damuwar rashi.”

Aleena taji kalmominsa suna shiga zuciyarta suna sa kirjinta nauyi mai ciwo amma jikinta ya tsaya cak ta kasa motsi. kuma ta rasa control akai wani tsoro taji mara suna yana shigar ta. Kuma ta tsani yanda yake kusa da ita yanzu, da kuma yanda yake sawa take jin tsoronsa yana harbawa cikin zuciyarta kamar kibiyar wuta.

Ya ja da baya kaɗa don ya kalle ta kai tsaye cikin idanunta. Kallonsa ya kasance mai tsanani dake huda ta.

“Ga yarjejeniya, Aleena.” ya ce, muryar sa sanyi kamar ƙanƙara amma mai umarni. “Be a good daughter in-law awajen iyayena kuma ki zama matar gida mai biyayya agaban iyayena. Ban damu da cewa kina ƙin ganina ba. I don’t care if you hate me. Amma za ki samu komai. Zaki samu rabin dukiyar da nake da ita idan hakan kike so.” Kawai… watanni bakwai. Kafin ƙarfe goma sha biyu na dare, ranar 22 ga December, zan baki sakin da kike nema.”

Ya sake matso kusa muryar sa ya sauketa ta zama mai duhu. “Amma idan baki karɓi wannan sharaɗin ba… fine. Sai dai kakarki…” Ya kara matsowa kusa sautin muryarsa ya yi ƙasa kamar wani murya daga cikin mafarki mai firgitarwa.
“Tabbas kakarki tana can sama tana kallan ki cikin bacin rai cewan baza ki iya ko gwadawa na watanni bakwai ba..Ni kuwa?”
Numfashinsa ya kasance mai dumi a fatarta, lips din sa sun kusance har kusan tana jin su. “Zan mayar da rayuwar ki kamar jahannama, Aleena. Zan ɗauke komai daga gareki. Komai.
Kar ma ki yi tunanin rayuwa cikin farin ciki da Emir bayan kin yi hurting iyayena. Za ki ga ainihin irin dodon da zan iya zama miki.”

Kasancewar sa kusa da ita haka ya kasance kamar yana shake mata numfashi tare da nauyi mai yawa da ya matse ta ƙasa. Jikinta ya tsaya cak. sai zuciyarta ta fara bugawa ba daidai ba. Jininta yana ambaliya cikin jin tsoro da ruɗani. Sai wani abu mai wahala ya mamaye ta—ba fushi kadai ba. Ruɗani. Sha’awa. Cike da zafi. Cike da rikicewa. Aleena taji kanta ya fara juyawa… Me yasa nake jin irin haka?

Omar ya janye kadan, amma idanunsa ko na dan second guda ba su kauce daga nata ba. Cike da sanyi. Cike da iko. Babu laushi.

“Ki yi magana da Emir game da wannan,” ya ce muryar sa har yanzu mai tsanani ba kauna ko tausayi. “Idan baki yi ba, ni zan yi. Kuma ki tabbata hakan ba zai yi kyau ba idan ni na yi. Kina bukatar ki sani, ya gaya min kwanakin baya cewa ba zai dawo gareki ba, saboda mutunta iyayena.
Yanzu da ya yarda ya kara baki dama?
Zan yi amfani da wannan a kansa. Fada ba makawa.

Ya riga ya tsaneni. Kuma gaskiya, Aleena, Nima na fara jin hakan.”

Omar bai jira amsa ba. ya juya ya bude kofa da ƙarfi ya rufe da ƙwanƙwasa mai ƙarar da ta katse numfashinta.

Ta tsaya a nan, ta daskare a wurin bugun jini ya cika kunnuwanta.
Tunanin ta ya koma ruɗani. Fushi. Kunyar kai. Takaici. Amma a ƙarƙashin duk wannan—akwai wani abu da baza ta iya fassarawa ba. Wani abu mai zafi, mai daɗi, mai haɗari. Kamar wani abu da take son ta ƙi. Kamar wani abu da bata so ta yarda da shi.

Ta kai hannunta cikin gashin ta, tan ƙoƙarin kawar da komai. Duk wannan lamarin ji take kamar ya fita daga control din ta. Omar ya bata watanni bakwai - 7 months for this twisted waiting game.

Kuma yanzu, tana jin cewa watakila wannan shine zaɓi mai kyau. Saboda bata so ta iyayensa bakin ciki. Sun kasance ba komai ba sai kirki gare ta. Kuma zata samu sakin da take so bayan ranar haihuwar ta. kamar hakan shine hanyar da ta dace, duk da tana jin kamar hakan zai kawo matsala gaba.

Ta ɗauko wayarta, yatsanta ya sami sunan Emir da sauri. Idanun Omar sun gaya mata cewa bada wasa yake ba- yana nufin kowace kalma. Idan ta dage da kin bin wannan sharaɗi, zai gaya wa Emir da kansa. Kuma hakan zai jawo rikici—rikicin da ba zata iya jurewa ba.

Amma tana danna sunan, sai wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ƙirji. Guilt. Jin laifi.

Emir ya dawo gareta. Ya amince zai jira. Zai tsaya…

Ya Allah, ka sa ya fahimci wannan kamar yadda na yi. Ba zan iya bari na kuma rasa shi ba.


💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️
Chapter 15 · 0% Book details