← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 21 OF 29

Chapter. 2️⃣0️⃣  Har Yanzu Ta Tsane Shi 😶‍🌫️ 💔🔥

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃


"Dan Allah ki faɗa mun idan Ya Omar ya dawo gida, kin ji dear."
Surukar Aleena ta faɗa da murmushi mai dumi tana tafiya zuwa hanyar kofa.

"In shaa Allah, Mommy," ta amsa tana gyada kai tare da tursasa murmushi tana jin kalaman suna mata nauyi a harshenta.

"Ki faɗa mishi nace... kar ya ƙara zama a waje haka har dare. Shi bai san yanzu ya ajiye mata agida bane?" Papa ya ce cikin murya mai ɗauke da ɗan zafi yayin da ya buɗe ƙofar gidan suna shirin tafiya.

"In shaa Allah, Papa. Ka daina damuwa. Na san ba zai daɗe ba zai dawo."
Aleena ta amsa, tana jin karyar da take zubawa kamar guba mai sanyi tana ratsawa cikin jijiyoyin ta.
Baki ma san inda yake ba, Aleena... ko idan ma zai dawo gidan yau da daddare... ta furta cikin ranta, tana riƙe murmushin dole, tana ci gaba da aikinta a matsayin matarsa — duk da cewa zuciyarta ta san wannan auren tamkar wasan kwaikwayo ne kawai.

Papa ya gyada kai, yana murmushi sannan ya shige cikin motar da driver yake jiransu.

Yauwa Aleena, ci gaba... ki tabbatar komai ya yi kyau. Ba dole sai iyayen Omar sun gano gaskiya ba, Aleena ta faɗa wa kanta a zuciya.

Mommy ta rungume Aleena, ta manna mata kiss a goshinta cikin so da kulawa.
"Alright, my dear... zamu tafi yanzu," ta faɗa da murmushi mai dumi.

"Thank you for coming. Next time, dan Allah, ku faɗa mun za ku zo, yanda ba za ku tsaya a waje ba kamar yau," Aleena ta ce, tana sake rungumar Mommy na ƙarshe. Murmushin ta ya yi faɗi — wanda kawai acting ne, ba na gaskiya ba.

Yauwa Aleena, karki daina murmushin nan... ki tabbatar sun yarda komai lafiya lau ne, ta sake ce wa kanta, tana jin kumatun ta na ɗan zafi saboda tsawon wage-baki.

Mommy ta gyada kai tana murmushi, ta wuce wajen motar.
Aleena ta daga musu hannu tana yi musu bye-bye har sai da motar ta bace daga ƙofar gate. Sai a lokacin ta sauke dogon numfashi, zuciyarta tana sauka a hankali.

Ta juya ta koma cikin gida tana rufe ƙofar gidan a hankali.
"Ohh my God..." Aleena ta ce ƙasa-ƙasa muryarta tana vibrating a cikin falon da ta shiga yanzu, Ta tura hannayenta cikin gashinta, tana jin nauyin abinda ya faru yana dannawa a ƙirjinta.

Ta ja ƙafa tana tafiya zuwa backyard tana son gujewa ƙamshin karya da ta cika palon yanzu. Palon da ta shafe hours tana yin acting a cikinsa — karya akan Omar, karya akan su biyun.

A cikin gazebo ta zauna, ta jingina bayanta, idanunta suka hango moon da stars a sama. Sanyin iska yana shigarta yana rage zafin takaicin dake cinta a zuciyarta.

Tun lokacin da ta bar office yau, Aleena ta nufi gidan Nesa — best friend ɗinta. Suka yi girki tare, suka ci abinci tare, suka zauna suna kallon wani film. Sai bayan awa da awanni ne ta ɗauki wayarta. Nan taji guilt ya mamaye ta. Missed calls da messages daga iyayen Omar sun taru a screen ɗin wayarta. Da sauri ta kira Mommy, wadda ta ce suna tare da Papa a waje, sun zo musu ziyara amma suka tarar gidan babu kowa. Nan take Aleena ta fice zuwa gida, ta same su a waje kan kujeru kusa da flowers, fuska cike da rudani. Babu Omar. Sun kira shi baya dauka, Aleena itama hakan bata dauka ba dazun. Sai yanzu.

Iyayen Omar sun yanke shawarar zuwa ne bayan sun fito daga gidan tsofaffin abokan su wanda suke makota dasu omar. Sun yi kewar Omar da Aleena ne, kuma su ziyarce su tunda basu taba zuwa sabon gidan nasu ba. don haka sun zo su ga ko sun gama settling.

Hakan yasa Aleena taji wani guilt mai nauyi. Zuwansu gidan ba matsala bane, infact, zasu iya zuwa duk lokacin da suke so — kawai rashin sanar musu da wuri da kuma rashin samun Omar, ga tsayuwar da suka yi a waje, yasa ta ji kamar an kifa mata wani zafaffen mari.

Har yanzu kalaman Mommy suna yawo a kunnenta: "My dear, kuna tare da Ya Omar  ne. Ganin dare ya yi, mun zo amma ba mu tarar da kowa ba."  Har hakuri Mommy ta bata a waya kafin ta iso tana cewa idan suna tare karsu takura musu.
Sai Aleena ta amsa musu dazun awaya da Aa, ba tare muke ba, amma gani nan ina kan hanya. Sai kawai Papa ya karɓe wayar da murya mai iko ya ce:
"Ina kikaje 'yata Aleena? Kin san inda Omar yake yanzu?"

Tohfa... daga nan Aleena ta fara gina ƙarya cikin gaggawa.
Ta ce, Omar ne ya kai ni gidan Nesa, sai ya bar min mota. Ali da Kemal suka zo suka ɗauke shi suka fita.

Papa ya ce ta kira Omar yanzu ta tambaye shi yana ina...  kuma ya dawo gida. Aleena nan da nan ta kira Mariam tana neman number din Ali ko Kemal su kira mata Omar, amma babu wanda ya dauka cikin su biyun. Ta karbi number Omar shima ta kira shi amma bai dauka ba kuma bai biyo baya ba duk da tasan bashida number dinta.

Yanzu... Aleena tana zaune a gazebo, idanu kafe kan swimming pool. Tana riƙe da pillow a ƙirjinta, tana jin numfashinta na wahalar fita. Rashin amsa kiran ta da suka yi — ya bar wani abu a ranta. Wani abu mai haɗin zafi da sanyi. Relief... da kuma damuwa.

Aleena ta ji wani irin relief sosai, saboda da duk alamu sun yarda da abin da ta faɗa musu — cewa Omar da su Kemal suna tare, kuma watakila ba su ji kiran ba.
Amma duk da haka, wani abu ya makale a zuciyarta, yana damunta, ta rasa dalili.

Ina Omar ya tafi? Kuma da gaske yana tare da su Kemal da Ali?
Meysa na kasa samun wani daga cikinsu.
Mey Omar yake yi yanzu?

Sai Aleena ta dan yamutsa fuska tana dukan kanta a hankali.
Meysa nake tunanin yana ina? Ko kuma me yake yi? Wannan ba matsalarki bace... stop it, Aleena.

Ta girgiza kai tana matse pillow a kirjinta, ta zauna kan gazebo chair din. Wani bacin rai ya shiga cikin kirjinta yayin da ta nufi stairs tana hawa zuwa room din ta.

Ta buɗe kofa ta shiga cikin room din ta ɗauki wayarta daga kan madubi — sai ga message daga Emir:

Emir: Sweetheart, are you alright? Zamu hadu gobe? Zan tsaya a office ɗinki... what time?

Aleena tayi shiru, yatsunta suna shafa screen ɗin wayar. Idonta ya sauka kan babban photo frame ɗinsu ita da Omar, wanda aka ɗauka bayan daurin aurensu a asibiti.
Ta kuma duba lokaci — 12:50 am.

Omar yana ina haka? Aleena ta tambayi kanta a hankali.

Tunda suka tare, Aleena bata cika kwana a gida ba sai wajen Leila ko Nesa ko Mariam — kuma Omar bai taɓa kwana a waje ba. Wannan yasa ta fara tambayar kanta, Toh ina ya tafi?

Aleena tayi shiru — ta zauna a dakinta tana tunanin ko kuma ta koma kasa ta jira dawowar Omar.
Ba saboda komai ba, kawai tana so suyi magana akan abin da ya faru dazu a restaurant.

Tun lokacin da ta haɗu da Omar a wurin, zuciyarta ta ki samun nutsuwa.
To be honest, wannan ne ma yasa ta tafi gidan Nesa gudun haɗuwa dashi.

Tabbas na yi ba daidai ba, ta fada a ranta.
Na wuce layin da ya zana min. Kuma babban laifina shine na bari Emir ya rike hannuna.

Hankalinta ya ci gaba da komawa akan kallon da Omar yayi mata dazu — irin wutar da ta gani a idanunsa da bata taɓa gani ba.
Kamar kallon da ke haɗe da bacin rai, kiyayya, rashin yafiya, da wani abu daban da bata gane ba.

Kuma a karo na farko, fushin Omar ya dameta. yasa ta kasa nustuwa duk da bai kamata ya dameta ba, tunanin sa ko actions dinsa, ko kalamansa bai kamata su dameta ba, Aleena da Omar sun tsani juna kuma hakan gaskiya ne.

Amma wannan karon, kamar warning ɗin Omar ya ratsa ta yana shiga jijiyoyinta har kashin bayanta.
A nan Aleena ta ƙara fahimtar cewa, tabbas ta yi laifi. Idan iyayensa suka ji ko suka gani—especially yau da suka zo ba tare da wani sanarwa ba to da lamarin ya yi muni. Zuciyarta ta buga da ƙarfi. Har yanzu tana jin nauyin karyar da ta zuba musu akan Omar, akan rayuwar su ita dashi, da kuma cewar ta san inda yake. Da sun san cewa ashe bata ma zama gidan sosai ba... duk wannan tunanin na yawo a cikin kanta.

Ya Allah... dukkan su suna danne mata kirji.

Aleena ta kwanta kan gado, amma sai maganganun su da Emir suke dawo mata cikin kai.

Flashback

Idon Aleena ya makale a ƙofar fita ta restaurant lokacin da Omar ya fice. Kalamansa na ta yawo cikin zuciyarta, suna sa ta tunani iri-iri.

"Da gaske ne? Idona ya rufe kan tsanar da nayi masa da har ban lura cewa wani abu ya canza tare da shi a kaina ba?" Aleena ta ce wa kanta.

"Kin tabbata ke da shi babu wani serious abu da ya faru tsakaninku?"
Emir ya tambaya bayan Omar ya fice, idonsa shima har yanzu na kan ƙofar da ya bi.

Aleena ta kyafta ido, ta juyo zuwa gare shi, tana ɗan yamutsa fuska. "Me kake nufi?"

Nauyin maganar Emir ya tsaya cak, kamar ya toshe duk wani iska a cikin restaurant ɗin.

"Nothing," Emir ya ce yana murmushi kamar wanda ba ya son nuna komai.

Aleena ta ja baya tana kallonsa, bata yarda ba.
"Kana nufin Omar yayi wani abu da ni? Are you serious, Emir? Yaushe ma nake kwana a gidan? Kusan koda yaushe ina tare dasu Leila—yaya zai ganni bare ma abin da kake tunani ya faru?"

"I know," Emir ya ce yana ɗan murmushi kadan. "Sweetheart, ba haka nake nufi ba. Kin san dole na damu. Nasan kin dade da sanin Omar, kun dade kuna kiyayya ke da shi. Amma baki san waye shi ba. Ni na san shi tun shekaru baya—mun yi karatu tare a Princeton University. Nasan halinsa akan mata, bare yanzu da ya aure ki. Bazai rike wannan kiyayyar har yanzu ba, koda ke kin tsane shi. Ki saurare ni—nasan waye Omar. Kuma ina gaya miki—kishi yake, saboda nagani a idonsa dazu."

Aleena ta kyafta ido tana murza idonta da hannu.
"Me kake ta cewa ne, wai kishi yake? Wait... kun san juna? Ya akayi bansani ba? Omar bai taba fada min ba—wait, kaima baka fada min ba?!"

Ta hade rai tana kallonsa.

"Wato kun san juna, kuma ya aureni, duk ku biyun kuka yi shiru? God..." Aleena ta kwashe da wani dariya mai daci.

"Aleena, I'm sorry. Na so na fada miki, amma sai na ga babu amfani. Already kema baki fada min za ki aure shi ba."

Aleena ta kara dariyar bakin-ciki.

"Auu Allah? Wannan ne maganar da kake so mu yi yanzu?"

"Sweetheart, ki saurare ni," in ji Emir. "Ina fada miki nasan halinsa—wallahi, Omar kishi yake. Rayuwarsa ya dade yana wasa da zuciyar 'yan mata, bai taba daukar mace seriously ba. Amma yanzu ya aure ki. Rantsuwar da ya dauka—ya dauke ta seriously. Shiyasa kawai nake jin insecure, bare kuna zama gida daya. Ki yi hakuri, karki ga laifina."

Aleena ta jefawa Emir harara.

"Abu daya kawai zan iya yarda shi ne—Omar yana damuwa ne saboda kada iyayensa su gano komai. Amma ba don yana kishi ba, ko abinda kake tunani."

Emir ya dena murmushi, ya gyada kai.

"Eh, naji. Amma ki yarda—harda kishi."

Aleena ta sake wani harara tana jan tsaki.

"Har yanzu maganar kishi kake? Wannan ai abin dariya ne. Ni da Omar, ko magana bamuyi sosai a gidan, bare haduwa. Kuma kishi ai sai da feelings. Idan kana nufin Omar ya fara sona ne—wannan hauka ne. Daga ina hakan zai fito? Taya hakan ma zai faru? Wannan baya making sense."

Emir ya yi dariya mai daci.

"Feelings? No. Omar yana da taurin kai—bazai taba admitting hakan ba."

Aleena ta daga kai tana kallonsa, bacin rai karara a fuskarta.

"Ya isa haka, sweetheart, kafin kuma abincin ya bar raina."

Amma Emir bai hakura ba.

"Kawai ina fada miki ne—baki san yadda brain din Omar yake aiki ba. Shi baya bukatar deep feelings kafin ya ji yana son mace. Idan abu ya kama idonsa—baya bari sai ya tabbata ya samu. Shiyasa na tambaye ki—idan akwai wani abu da ya faru tsakaninku, ko da ba dole kin yarda ba. Shi da kansa zai nemi ya biya bukatarsa—koda kuwa bakya so. Na gaya miki—Saboda na ganshi yana kishi, amma yana rufe hakan da maganar iyayensa. Kuma ni nagani karara—ba hakan bane."

Emir ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce:

"Amma tunda kika ce babu wani abu da ya faru—Toh hakan yana nufin abu daya ne kawai. Omar ba kishi kadai yake ba—sha'awarki yake. Yana jin kamar ya mallake ki, saboda igiyar aurensa da aka daura miki. Na gani a idonsa lokacin da ya yi ta bragging da rantsuwar aurensa a kanki. Ba anan kadai ba—amma lokacin da ya rungume ki yayi miki kiss agoshin ki a asibiti, lokacin rasuwar Granny. Har ma a lokacin zaman makoki—yadda ya dinga sama da ƙasa akanki. Omar baya wahalar da kansa akan mace—sai idan wannan yarinyar tana da wuri a cikin ransa.

Kuma ki yarda ko karki yarda, Aleena—wannan hadin auren naku ya zama masa kamar wani sabon abu da yake ji ya samu. Kamar wanda aka ba shi dukiya ya kula da ita. Kuma ko kina so ko baki so—aikin gama ya gama, tunda kika yarda kika aureshi."

Aleena ta kyafta ido, yatsunta suka kame, ta kasa motsi. Kalamansa sun zuba a kirjinta da nauyi, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin numfashinta ya rikice. Da gaske ne? Da gaske ne Omar ya ɗauki wannan auren amatsayin wani babban abu mai muhimmanci a ransa? Ni kuwa, wannan auren ban ɗauke shi a bakin komai ba. But why? Me yasa zai damu da auren? Aleena ta tambayi ranta, tana kai idanuwanta zuwa ƙarshen table ɗin.

Ta shaki numfashi da ƙyar, ta juya tana kallon Emir tace a hankali:
"Sweetheart, bari in faɗa maka abu ɗaya. Ni da Omar muna ƙin juna, kuma babu abin da zai canza daga hakan. Komai yake tunani, bazan taɓa bari ya faru ba. Don haka mu bar maganar nan haka, please."

Emir ya kalleta na ɗan lokaci kamar yana karanta fuskarta, sannan ya juya, ya ɗauki drink dinsa ya kurɓa kaɗan. Sai yace:
"Akan kiyayya ne kawai komai? For him? For you? Kin tabbata har yanzu kiyayyar da yake ji miki tana nan... bata fara gushewa ba?"

Aleena ta yi shiru na ɗan lokaci, kamar ba za ta amsa ba. Sai kuma tace a ƙasa:
"I still hate him... kuma hakan bazai canza ba."

Emir ya gyada kai, bai ce komai ba. Ya juya kawai ya ɗauki spoon ya fara cin abinci.
Aleena ma ta ɗauki nata spoon, tana kai abinci bakinta, sai taji muryarsa ta sake fitowa a hankali:
"Allah yasa."

Hannunta ya tsaya cak a tsakiyar hanya, daidai bakin nata... amma bata ƙara cewa komai ba.

End of flashback.


A/N: Idan comments suka yi yawa, update ma zai zo da wuri. Na gode sosai ❤️📖


💘AUREN ALEENA💘

Amal Musa ✍️
Chapter 21 · 0% Book details