← Book details Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 29

Chapter. 4️⃣ Katon Banza 😤

Auren Aleena Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

SHARE SHARE SHARE 💃💃💃💃💃


Jiya ne karo na farko da wannan ’yar mai kibar ta yarda ta hadu da ni fuska da fuska. Na shafe shekaru ina jiran wannan rana.

Shekara hudu kenan.

Shekara hudu tayi tana guje haduwa dani kamar wata matsoraciya. Na yi tunanin cewa daukar nauyin kamfanin danginta zai iya tilasta mata ta girma a zuciya, ko ta fara yin aiki da kwarewa kamar yadda ya kamata.

Amma a’a. Har yanzu tana nan dai da halinta. Wata yar mulkin girman kai. Mai son Zama gimbiya a idon jama’a. Kuma ganin yadda ta fusata jiya, yadda na hargitsa mata tunani da zuciya? Na ji dadi fiye da yadda zan iya misaltawa.

Bazan iya tabbatar da daidai lokacin da na fara jin kiyayyata a gareta ba, amma nasan tabbas cewa ya samo asali ne daga munafurcinta da halinta. A lokacin da na fahimci yadda take nunawa duniya wani fuska daban da ainihinta. Duniya na ganin ta da ido na alheri, na kirki da kawaici. Amma ba haka take ba.

Saboda ni? Na shaida ainihinta.

Tun muna yara nasan wannan ba irin yarinyar da zan taba so in yi shiri da ita bace. Ko da kuwa nima din ina cikin yaran da ba su da mutunci a wancan lokacin.

Maybe it all started when she was 6 years old. Lokacin da suka dawo Turkiyya daga Ingila, bata ma iya furta kalma guda ta Turkiyya ba.

A lokacin, danginmu na ziyara wajen su Khans. Kakana marigayi yana da alaka ta kut-da-kut da kakanta.

At the time, everything was fine. Ni kuwa ina da shekara goma sha uku a lokacin—kuma, a gaskiya, har yanzu dan butulci ne.

Na tuna da lokacin da cikina ke cike da fitsari, iyayena da kakanni na suna ta hira da danginta, har suka manta da ni. Don haka, sai na dauki kaina da kafafuna, na fara yawo a cikin masarautarsu ina neman bandaki. Na bude kofa daya bayan daya amma babu sa’a. Sai na tarar da wata kofa a bude kadan, na tura ta.

Can naga karamar yarinya ta zauna ita kadai tana wasa da ’yar tsana. Da ta gann ni, sai ta fara fushi ta fara yi mini ihu cikin harshen da ban gane ba. Ta tashi tana nuna ni da yatsa kamar wata sarauniya tana zargi na. Yanzu da nake tuna baya na fahimci abin da ta ce. Na roketa da ta gaya mini inda bandaki yake, amma a maimakon haka, Sai tafara yin taurin kai kamar gimbiya ta ci gaba da mun tsawa sosai. “Meyasa ka shigo dakin sarauniya ba tare da ka kwankwasa ba? Koma daga inda ka fito, talaka kawai!

Na yi kuka cikin zuciya, ina fama da ciwon fitsari. Na roketa da harshen Turkiyya, “Don Allah! Ina ne bandaki? Na ce fitsari nake ji!” AMMA BATA TSAYA BA. Ta ci gaba da yi kamar muna cikin wasan sarauta.

RASHIN FAHIMTA. a lokacin ya kasance bala’i; ni ban fahimci ko kalma ɗaya ba, balle ma batun Turkanci nata mai kauri, ita kuma ba ta da masaniyar Turkanci ko kaɗan.

Sakamakon hakan kuwa? Na yi fitsari a wando. A gabanta.

Iyaye na sun yi mini kaca-kaca. Mommy ta mare ni tana cewa ni abin kunya ne. Papa kuwa ya tsaya yana dariya a gefe.

DANGIN KHAN KUMA? Sun kalle ni cikin tausayi. Kuma ni bana son tausayinsu. Haka kuma ban son zama abin kunya.

Ina mutuncina? I was just 13 years old. Amma ina da girman kai tun a yaro? Ni Omar Thorne ne fa! kuma magajin gadon Thorne.

Amma wannan yar lukutar yarinyar? Ta kalle ni da murmushin nasara. Sai ta daga gira kamar ba ta da laifi yayin da nake kokarin fadar cewa ita ta yaudareni. Na gaya musu cewa ita ta hana ni zuwa bandaki, amma mommy ta ce na daina karya. saboda ansanni da dorawa mutane laifi.

HAR MA NA FADI, “Ta yaya ba ta gane cewa ina bukatar yin fitsari alhalin ina rike wando na ina bouncing gwiwoyi?” A zahiri, Mommy ta kara fushi, tana cewa ina kara dagula al’amarin.

Wannan shi ne tunanin farko da na yi, cewa zan tsani wannan yarinya har abada. TUN DAGA WANNAN RANA, ”Every time I see her, I feel angry and hate her.” ina jin wani babban sha’awar hallakata.

I hated her.

Duk abinda ya shafeta Inaso naga na shiga ciki kawai don na lalata mata shi saboda inaso in ga ta ragargaza.

Kuma yanzu, Sai gashi ’yar lukutar yarinyar nan na sake fuskanta jiya. But the difference now is that, she is now slim more taller and more beautiful. BAYAN SHEKARU… da tayi tana guje gujen haduwa dani. Sai gashi jiya ba ta da wani zabi face ta fuskance ni kai tsaye. Taron gaggawa da na kira ya takaita mata lokaci. Ba ta samu damar tura mataimaki ko sakatariya ba. Sai da tazo da kanta.

Aleena Ali Khan.

Shugabar Khan Electronics.

Kamfanin da ya zama ginshikin kayayyakin lantarkin da muke amfani da su a Thorne Communications. dangantakar ta samo asali ne daga kusancin danginmu.

Shekaru da yawa, Khan Electronics ta kasance muhimmiya, tana tallafa mana a lokutan wahala kafin in karɓi wannan kamfani. “ If not because of them, ” Papa ya taba fada, “ da kamfaninmu ya yi rauni sosai.” SUN KASANCE. ɗaya daga cikin ginshiƙan nasarar Thorne Communications, abin alfaharin dangina.

SHEKARA 10 DA SUKA WUCE, na karbi Thorne Comm. bayan mahaifina ya sauka, ya ba ni mulki a lokacin mafi duhun lokutan kamfanin. Khan Electronics sun taimaka mana har zuwa lokacin da na hau shugabanci—lokacin da muka kusa durkushewa. Yayin da sababbin kamfanonin waya daga China suka mamaye kasuwa. Bashi yana yi mana katutu.

A matsayina na babban dalibi daga Jami’ar Princeton, na ki barin kamfaninmu ya ruguje.

Dalilina sun kasance a sarari: Ina da buri, ina da son kudi, kuma ban amince da faduwar arziki ba. Ban taba yarda da faduwar daraja ba. Girma cikin alatu, kasawa zai kasance abin kunya ga girma kai da mutuncina. Amma abinda yafi komai damuna shi ne iyayena.

Lokacin da kamfaninmu ya fara durkushewa, mahaifina—mutumin da na dade ina ganin jajirtaccen shugaba ne—ya soma nuna kasala. Mahaifiyata kuwa bata da wani karfi. DON HAKA, na yi aiki tukuru na tsawon watanni.

TARE DA TAIMAKON abokaina na Princeton University wanda mukayi karatu tare. Kemal da Ali, mun kirƙiro wani sabon abu mai ban mamaki: wayar fasaha mai saukin gwiwa, T-Phone.

Har yanzu ina tuna ranar da na gabatar da samfurin T-phone ga mahaifina. Ya rike wayar yana kallon ta kamar zai karanta sirrin rayuwa a cikinta.

Wannan lokacin har yanzu yana cikin ƙwalƙwalwata kamar jiya ne ya faru.

“Please say something, Papa. Koma mene,” na furta cikin nutsuwa, ina tsaye a gaban teburinsa, samfurin wayar T-Phone Gen 1 na kwance tsakaninmu.

Bayan wani dogon shuru mai cike da tashin hankali, sai ya miƙe, ya ƙaraso gare ni, ya dafa kafaɗata da hannunsa.

“Look at that, Omar,” ya ce cikin murya mai ƙarfi. Na kalle shi, sannan na dawo da idona kan wayar. “Wannan ce za ta zama ginin farko naka. Ita ce za ta ceci danginmu, kuma ta buɗe maka ƙofa ba don ka mamaye kasuwar Turkiyya kaɗai ba, har duniya gaba ɗaya. Duniya bata san wanene Omar Thorne ba tukunna. Amma za ta san shi.” Muryarsa cike da tabbaci, amma idanuwansa na cike da alfahari da kauna. Wannan kallo da wannan lokaci, ba zan taɓa mantawa da su ba.

Tun daga wannan rana, mahaifina ya gabatar da ni ga kwamitin kamfanin. Sun rungumi ra’ayina da hannu bibbiyu, kuma ba da jimawa ba, T-Phone Gen 1 ta fara fitowa kasuwar Turkiyya.

Kemal da Ali suka zama hannun damana, yayin da mahaifina ya yi ritaya, ya koma rayuwa mai nutsuwa da mahaifiyata a gidanmu.

Shekara da shekara, kamfaninmu na ƙaruwa. Sunanmu yana ƙara daraja. Har ma muka zarce wani shahararren kamfanin Amurka, muka zama mafi mashahuri a kasuwar waya tsawon shekaru biyu a jere.

Tsarin talla namu ya kasance mai gwaninta matuƙa.

Thorne Comm. ta haɗu da manyan kamfanonin kafafen yaɗa labarai a Turkiyya, hakan ya ƙara mana daraja da amincewa a idanun jama’a.

To, da yake muna amfani da manyan jarumai da samari da ’yan mata masu kyau a tallanmu—na T-Phone, rayuwata ta sirri kuwa sai ta rikice.

Let's face it, A gaskiya, mata su ne raunina na ƙarshe. Dukkan abokaina sun sani. Ina da wani suna da suke fada mun player. Shin na yi nadamar zama dan yaudara? A'a ko kaɗan. Na yarda da hakan. Mutanen da suke sukar halina su ne ko dai masu kishi ne ko masu bakin ciki. Ko ta wace hanya, ban damu ba.

Sai dai iyayena suna da korafi akai. Musamman Mommy. Ita ce irin wacce take tsawata wa mutum kamar ƙwararriya. Ta iya shiga rigima. wata rana ta zo ba tare da sanarwa ba a gidana na babban bene (penthouse). Abin takaicin shine, wata mace da na kwana da ita ce ta bude ƙofa. Yayin da nake kwance a kan gado tsirara ina bacci. Mommy kawai ta juyar da idanunta ta roƙi yarinyar cikin ladabi da ta shirya yanzu ta fita. Na farka daga bacci sai kawai na tarar da wannan labarin. Mommy ta sanar da ni da kanta, da dukkan cikakkun kalmomin da ta faɗa.

Game da tsawatarwa da ta biyo baya. Haka de kullum tsohuwar lacca game da rayuwata ta sirri, da kuma tabbas, Aure.

Zan iya cewa kunne na har yanzu yana zafi saboda tsananin fadan ta.

“Wato ba za ka iya zama da hankali ba ko?…” "You're not in America anymore, Omar! Kana nan Turkiyya!”

"Oh my God, Omar yarinyar da fa ta buɗe min ƙofar ba ta sanya komai jikin ta ba face wata rigar zanin gado! Ban ma san ko ta sanya wando ba! Inda wani ne yazo ba uwarka bafa?

Na ɗauki rigar wanka daga ƙasa, na sa da sauri domin gudun wutar kallon mommy. Saboda tun da ta tada ni daga bacci da safe, har yanzu faɗa take.

"I sent her home, of course," ka naji ko? Na tura ta gida, ta ci gaba da cewa, cikin haushi. "Na tsufa kuma nagaji da wannan rayuwar da kakeyi. don wannan shirme ne. Ba zan iya ci gaba da jurewa ba!"

Da na gama ɗaura rigar, na miƙe, na fita daga ɗakin. Ta biyo ni, Mun isa falo, amma fadan na ta bai tsaya ba. “Ka kusa kai shekara 33 yanzu, Omar. Ba zaka fara ɗaukar rayuwa da muhimmanci ba ne? Kowa kuwa ba za ka fara tunanin yin aure da wata ba?”

Oh God, I was going to lose my mind. But I loved her so much. Na juya don fuskantar ta, na lura fuskarta ta zama ja saboda haushi. Na ji tsoro sosai kada ciwan ta ya tashi. Na dora hannuna a kafaɗarta, na yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

"Mommy, take a deep breath," shaƙi numfashi," na faɗa da ƙarfi, na hada idanuna da nata. "Omar, ban gane tunanin ka ba-" I really don’t understand what you want with your life..” "Mommy, ja numfashi," na katse ta, ina nuna numfashi a hankali. "Fitar dashi." Ta juyar da idanunta, tana ƙoƙarin ɓoye wani ɗan murmushi. Na rungume ta, na shafa bayanta a hankali.

"Ki huta, Mommy. Zan saurara. If not, zaki iya fashe wa idan kika ci gaba da yin ihu kamar haka. Mu zauna."

Na ji tashin hankalinta ya ragu yayin da ta janyo ni kusa da ita ta sumbaci goshina da ɗan murmushi, Na zata komai ya lafa… sai kawai ta ɗaka min tsawa ta buge hannu na!

“Mommy!” Nayi ihu, ina shafa inda ta bugeni. yayin da nake komawa kan kujera. Ta zauna a kusa da ni, tana kallona da idanun gargaɗi.

“Ka daina raina min hankali, Omar. Ka girma. Kana bin mata kamar wasa ne. Har mahaifinka da baya yawan magana ma ya koka.”

Na dafe goshina.

“Mommy, me kike so in yi? In zama mutumin kirki daga nan? In daina more rayuwa? Ai zai zama kamar na mutu. Duniya hanya ce, ni kuwa ina jin daɗi.”

Ta dafe kirji. “Jin daɗi ba yana nufin canza mata da daddare ba. Ko mahaifinka ya gaji da labaran ka a jaridu! Kwana ɗaya, da wata actress. Washegari, wata daban. Me kake yi ne, Omar Thorne?”

Na kara shafa goshina, ina ƙoƙarin kwantar da hankalinta. Tun da ta riga ta fara kirana da sunana na cik - alamar cewa tana gab da kara fashewa.

“Gossip ne kawai, Mommy. Kuma ban da haka, idan akwai wanda zai zama mai laifi, shi ne Papa. Na gaji wannan kyau daga gare shi. Mata suna sona, ba laifina ba ne dana yo kyau."

Ta bude baki, cikin mamaki, tana kokarin daure dariya. You are unbelievable Omar.

Na daga kafada. "Kawai ina faɗin gaskiya ne."

muryarta ta yi sanyi kadan. "Shin za ka iya aƙalla daina canza abokan zamani kowane lokaci? Wataƙila ka gwada neman budurwa ta gaske? Duk rayuwata ban taba ganinka da wata ba - balle ma ka gabatar da wata gare mu. Hakan yana sa na yi tunani... shin saboda ba ka taba samun wata bane, ko kuma saboda kawai ba ka so ka gabatar da ita gare mu? Hmm?"

Na matso kusa da ita. "Mommy, ban taba samun wata ba. Kuma ki yarda da ni, duk matan da na yi... ba irin waɗanda zaki so su zama budurwata bane. Na yi muku alkawarin haka."

"Ba za ka sani ba sai ka gwada," ta mayar.

Na koma kan kujera. "Ba na son gwada abubuwan da ba su da tabbas."

"Ba su da tabbas? Me kake nufi da hakan, Omar?" Ta tambaya, tana ɗaga gira. "Gina dangantakan ne abu mara tabbas ko tsarin yin wasa? to Shi ne ainihin ɓarnar lokaci. Ba ka ganin hakan ne?"

Na kalle ta da murya mai mahimmanci. "Mommy, don Allah bari. mu bar maganar budurwa. Ki san abin da zai biyo baya - bayan budurwa sai aure. Kuma ba zan iya yin hakan ba."

"Omar Thorne! Why? Of course the next step is marriage. What do you mean by you can't'? Can't what?" Ta tambaya, girarta ta ƙara zurfi.

Na sunkuyar da kai. "Ba zan iya ba kawai. Kuma a gaskiya, ba na so. Wataƙila ba zan yi aure bama ni-"

Ta buɗe ido sosai. “Omar Thorne! Ka ce ba zaka yi aure ba?! Me kake nufi?” "Kada ka kara faɗin irin wannan abin banza! Kai ne ɗana kaɗai! ka dinga yin tunani kafin ka sake magana. Ta yaya za ka faɗi ba za ka yi aure ba? Toh baka isa ba-"

“Na yi duk abin da kuke so, Mommy. Na ceto kamfani, na kawo nasara, na saka kowa farin ciki. Shin hakan bai ishe ku ba? Duk rayuwata, na yi duk abin da ku da Papa kuka so, kuma na yi shi da kyau. Me ya sa za a tilasta mini abin da ba na so?

"Kai abin alfahari ne, Omar. Tabbas, haka ne. Amma wannan ba game da alfahari ba ne. Mahaifinka da ni ba za mu kasance nan har abada ba. Kana bukatar ka yi tunanin makomarka. Samun wani a gefenka zai sa rayuwa ta fi kyau."

Na danne ƙoƙarin juyar da idanuna, ina sauraron laccar da ta saba. A ƙarshe ta daina, ta ɗauki numfashi mai zurfi, ta shafa goshinta.

"Ba za mu yi maka auren dole ba," ta faɗa bayan ɗan lokaci, "mahaifinka da ni ba mu ne za mu yanke shawara ba, aƙalla."

Na daga gira, cikin rudani. "Me kike nufi da hakan?"

"An riga an yanke shawara. Tun lokacin da kake yaro."

Girata ta kara zurfi. "Me kike magana? Ban gane ba-"

"Never mind," ta katse ni, "Za ka gane wata rana," ta ci gaba da cewa. "Mahaifinka yana da gaskiya; ko da yake halinka yana sa mu hauka, yin aure wajibi ne idan lokaci ya yi. Za ka yi aure a ƙarshe, duk game da lokaci ne. Kuma yana kusantowa. Kuma za ka ga dalilin."

Na shiga cikin rudani fiye da kowane lokaci, amma na bar hakan yayin da nake kallon mommy tana buɗe firiji ta fara shirya mini abinci.

Na zauna akan stool. na dube ta a shiru, ina ƙoƙarin watsi da kalamanta. Na rufe idanuna na ɗan lokaci, na girgiza kai, na kawar da tunanin. Gwara in bar wannan. Ba shine karon farko da ta faɗi irin wannan ba.

Amma ko da yake na yi ƙoƙarin yin watsi da shi, ba zan iya kawar da ji ba. Akwai wani abu da iyayena suka sani, wani abu da ba su faɗa mini ba.

Kuma ko ma mene ya kasance, na tabbata ba zan ji daɗinsa ba.


💘AUREN ALEENA💘


Amal Musa ✍️
Chapter 5 · 0% Book details