← Book details Afnan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Afnan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AREEF tun da yafice Bai tsaya a ki Ina ba sai acikin gidansu ,BAYAN yayi parking ya fito yanufi takin su, Kai tsaye bathroom ya nufa ya watsa ruwa ya fito daure da towul a kirjinsa, Yana tafe Yana faman tinani iri daban daban har ya karasa bakin durowar da,si lokacin ta kula da rigar daya saka wa AFNAN ,ashe jallabiyar sa ce fara ya saka mata,shima jallabiyar ya dakko yasaka sannan ya karasa bakin bed ya kwanta domin ji yake mayma ba zai iya sakawa ajikinsa ba, wayarsa ya janwo yashiga dannawa Yana kokarin Kiran numbar da doctor yabashi,BAYAN ya Nemo number ne ya shiga Kiran number Kuma yayi da,a tashiga Amma an ki dauka,sai da yakira number yafi so 30 Amma shiru ba a dauka ba, hakanne yasa ransa ya Soma baci waushi da tsanar likitan ya kamashi ,tsaki yayi yace"mtseeeew ace Dan ma iya ayki shine saika dauki girman Kai ka dorawa kanka "wallahi idan banda na damu da aykinnan bazan zauna inaji Ina gani adinga wulakanta Ni ba"mita yake tayi sosai domin yarasa abin da yake Masa dadi Dan Haka ya zauna yashiga tunani can sai ya tunano wata da bara , murmushi yayi yace "yauwa Bari n'a tura message kawai muga" kan number ya shiga tare da Hawa Jan message yashiga rubutu kamar Haka"Assalamualaikum barka da wannan lokacin doctor ya kake ya aiki da kokari dautane, Daman ni sunana AREEF Ina zaune ne a *KOGI LAKWAJA* ina da kanwa karama yar shekara 12 zuwa sha 3sai dai an haifeta da *Dick*n'a Maza kuma na tambaya ance Kai kadaine zaka iya wannan aykin Dan Allah inason kataimaka kayiwa kanwata ko nawane Zan biyaka AFNAN tana cikin hadari katai maka doctor". AREEF Yana Gama tura message d'in yatabbatar da ya tafi sannan ya ajiye wayar Yana tsammanin Kiran doctor ,mintina kalilan zai dauki waya ya duba ko doctor yakira Amma har lokacin shiru.

Gajiya yayi da jira Dan yaga alamun doctor ba shi da alamar Kira,Dan Haka ya Mike tsaye ya dauki takalinsa yasaka sannan ya dau wayarsa da mukullin mota ya nufi waje.

AFNAN kuwa tun da ta farka take faman razana tana tsorata abin dai sai wan da yagani ,momy dake zaune a gefanta sai faman tofa mata addu,a take Amma AFNAN takasa nutsuwa sai faman furgita take tana cewa" wayyo Yaya AREEF ga tanan "wallah kasheni zatayi ,Yaya ga anty fadeela Nan zata kasheni"shikkenan takamani Yaya zata ciremin gabana Yaya kataimaka zata kasheni" wasu wasu zafafan hawaye ne masu dumi da zafi suka Shiga zirya a cikin idon momy ,kallon Yar Tata take cike da tausayi ,tabbas Allah ya jarafci AFNAN da wata kadda wadda cinye zarabawar ta sai Mai imani,Allah katsaremin ita aduk inda take "ya Allah kada ka samata abin da bazata iyaba "allah ka kiyayya daga sharrin mutane dama aljanu "kukane me karfi yakara CIN karfinta Har da majina,jitai an dafa kafadar ta ta baya ,afurgice ta juyo domin ganin waye, AREEF ne tsaye a kanta, hannunsa yasaka Akan fuskarta yashiga gogemata wahaye Yana girgiza mata Kai Yana cewa" momy kidai na bana so "idan kina kuka muma saiki sakamu mufara kukan Dan Allah kidaina insha Allah AFNAN zata samu lafiya kuma ta kasance kamar kowa ce Macé" son Zan daina Amma ban da wannan lokacin shin bakaga halin da take ciki bane Taya za ay ruwan hawaye na yakasa zuba?" Yanzu ya maganar doctor kasameshi a wayar"? Ajiyar zuciya AREEF yasaka sannan yace "momy nayar da da maganar doctor dayace samun wannan likitan wahalane tun dazu nake Kiran wayar tashiga Amma ba a dagawa ,sannan har message nayi Masa Amma shiru kukeji "bazan gaji da rokon Saba sannan bazan gaji da kiransa ba har sai lokacin da yafahimci AFNAN tana tsananin bukatar likita irinsa "shikkenan AREEF Allah ya maka albarka Bari bane waje gurin Abban ku Kai ka zauna a nan Naga tun dazu furgita take" tom shikkenan momy sai kun dawo"

Zama yasamu yayi a kujerar dake kusa da AFNAN ,bayan ya zauna ne ya kura mata ido Yana kallonta cike da tausayawa, hannunta ya kamo ya rikeshi cikin nata ,Nan take tajuyo a hankula ,itama kallonsa take kamar yadda yake kallonta sai dai ita idanunta yacike da kwalla ,rintse Ido AREEF yayi ya bude Dan jiyake idan Yana kallonta zai iya sakin kuka, sai Kuma ya daure ya bude idonsa tare da sakar mata murmushi yace "sannu kanwaty" batare da Tace yauwaba ta jefo Masa tambaya"Yaya bakason ganina ne?"" To AFNAN me kika gani ?" "Naga kana rufe idonka ko kaima kafara guduna me?" "A,a AFNAN Ni n'a isa ina tare dake har karshen rayuwata" "Yaya Dan Allah kayi hakuri" "hakurin me Kuma AFNAN"? "Yaya bani nakirawo anty fadeela ba ka hanani na biye mata Allah Yaya ba laifina bane Dan Allah kada kayi fishi Dani" Kai kadaine wan da yake fahimtata Kuma kaikadai ne wan da yafi sona da nuna min kauna dan Allah yaya kayi hakuri "tana karasa maganar tare da fashewa da kuka, "ksh oh God AFNAN Ni ba Zan taba fishi dake ba Kuma bakimin komai ba Dan Haka kidai na damuwa kinji kanwaty" "Kai ta dagamasa sannan ta kakaro murmushi Tace" Yaya Dan Allah ka rungumeni" zaro ido yayi yace" AFNAN a asbiti fa kike ko kin manta nanfa ba gida bane" eh Yaya Ni kawai sonake najini ajikinka Dan Allah Yaya" AFNAN tasake marai Rai cewa, kasan cewar bayason da muwarta yasa ya Mike tsaye yayi Dan tattaki zuwa inda take ya sa hannu ya dagota zaune sannan shima ya zauna a kan gadon ,tallafo kanta da bayanta yayi zuwa kirjinsa yashiga jinnigata Yana Dan bubbuga bayanta har bacci yafara dauketa, sai da sukayi mintina kusan 20 a Haka sannan AREEF ya tabbatar baccinta yayi nisa tukunna ya kwantar da ita a hankula ,sai da ya tabbatar yagama gyra mata kwanciyar sannan ya yimata addu,a ya shafa kanta ya durkusa yayi mata kiss a goshi sannan ya fito waje.

Kai tsaye office din doctor ya nufa Yana zuwa ya kwankwasa kofar doctor ya bashi izini ya shiga, BAYAN yashiga ne yasamu guri ya zauna a kujerar dake fece din doctor,gaysawa suka Yi sannan AREEF yace" doctor wannan numbar da kabani tana shiga ba a dauka sannan namasa message still shiru "ko zaka taimaka ka bani number wannan abokin naka nakasar *Faris* Dan Allah doctor kada kace a,a"shiru doctor yadanyi na Dan wani lokaci sannan yaja dogon numfashi yace"A.R samun doctor abin da matukar wahala nabaka shawara kaki ka yar da , da hakura kayi da yafiye maka sauki kada kaje garin ceto ran yarinyar nan kasaka kanka a wani halin " hmm bazaka gane ba likita wannan yarinyar itadin kamar rayuwa Tace inason na cireta daga wannan halin bakasan ko ta sanadiyyar Haka Allah sarya samu a aljanna dagani har kudin Ni dai BURINA kabani number" shikkenan "doctor ya dakko wayarsa ya fadawa AREEF numbar abokinsa alhji ilu dake zaune a kasar *Faris* bayan ya fada masa ne AREEF yayi godiya sannan ya tashi ya fita daga office din, dakin da AFNAN take yakoma still dai haryan zu Bata tashi ba ,Dan Haka yasamu guri ya zauna ,numbar yashiga Kira tana ringin Amma ba a daga ba sai da yayi Kira yakai hudu ana diyar din aka daga , Ajiyar zuciya AREEF yayi tare dayin handala yace" ASSALAMUALAIKUM" wa, alaikumussalam" aka amsa cikin dattako daga can kasar, "yakake nasameka lafiya "AREEF yafada, "lafiya kalau alhamdulillah kaifa"? Nima lafiya kalu yauwa kana magana da AREEF ABDULLAHI daga *KOGI LAKWAJA* "Masha Allah malan AREEF meke tafe dakai?" Daman Ina neman wani bawan Allah ne ko zaka taimakamin ka hadani dashi" wakenan?" Likitan *Dick* " ban fahimci inda ka dosaba kamun cikkakken bayani akan sa?" Ayadda akacemin shi doctor ne kuma shi lauya shi sojane" zumbur alhji ilu yatashi tsaye tare da zaro Ido yace " Wai *Lion*kake nufi" to sunansa lion ?" Koma dai mene nidai shinakeson gani" agaskiya ganin *lion* zai maka wahala dan koni Tun da nake sodaya na taba ganinsa ,ranar danagansa kuwa sai Dani kwana da kwanaki cikin tuaninsa bazan maka karya ba ka hakura da ganin doctor indai Babu damuwa "meyasa kace na hakura"? Sabi da nasan har aba da bazaka taba ganin Saba" Wai shi wanene wannan mutumin ba Dan Adam bane kamar kowa?" Tabbas mutum ne kamar kowa saï dai Shidin na dabanne ,Zan tura maka number sa ta kasar *AMERICA* ka jarra ba kira" ki Allah zaisa ka sameshi Amma dai Zan baka numbar wani abokina idanma baka samu doctor ba mebi shi zai iya taimaka maka wajen samun sa ,shima Yana zaunene a America" Okay Tom nagode sosai AREEF ga katse wayar tare da dafe Kai Yana sauraron atura masa numbobin .

___ 💋 *AFNAN* 💋______
*Chptar 6*

💃💃*TO!! TO!! TO!! Shhhh*😌 *KUNA INA MASOYA LITTAFIN*💋*AFNAN*💋WANAN LITTAFIN DABAN YAKE DA SAURAN AFNAN FA AKA FADA MUKU KUNSAN YADDA KUKAJI WANNAN LITTAFIN ZA A KWASHI ROMON DADI ACIKINSA AFNAN LITTAFINE MECIKE DA TARIN ABIN BAN AL,AJANI FADAKARWA NISHADAN TARWA DUK ACIKIN WANNAN LITTAFIN ME SUNA 💋 *AFNAN* 💋.
*NICE TAKU HAR KULLUM MARUBUCIYAR *✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*AFNAN*_
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
_And now_
💋_*AFNAN*_💋
*BOOK one*

*Chapter 6*

______mintuna kalilan saiga shi alhji ilu ya turomasa numbobin guda biyu data abokin sa data doctor,can Kuma sai ga kiransa ,dagawa AREEF yayi tare da yin sallama yace"Assalamualaikum" wa, alaikumussalam"AREEF ya amsa tare da cewa" Naga sunshigo yanzu nagode kwarai dagaske"a,a Babu damuwa anzama daya ,sai dai kakula fa domin sunan danasan shi dashi amatsayin *lion* ba lallai shi ake kiransa dashi a *AMERICA* ba "okay tom nagane nagode kwarai dagaske "daga Haka kuma sukayi sallama.
Chapter 6 · 0% Book details