← Book details Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 34 OF 61

   PART 2        

Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 13 min read

                          _PAGE  3️⃣6️⃣89

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]

     
          
         

   
          _MY FIRST NOVEL _

Da sauri ta dauki hoton tace "Wannan wacece?"
Karba yayi ya duba sannan yace "bakisan wannan ba? Kakarkuce wadda ta haifi su Abba"
"Wannan ai kakar su Hanan ce"
"kamar yaya?" ya tambayeta cikin rashin fahimta, nan ta kwashe komai tagaya masa na zuwanta bauchi jinjina kai yayi yace "masha Allah, nina san wannan kamar da kuke ba'a banza ba, tabbas abunda kakar Hanan tagaya miki haka yake, Sun baro garinsune saboda hari da ake kaimusu, amma yanzu karkiyi saurin fada, Abba yakamata kifara samu da wannan maganar, ya dade yana bincike ko Allah zesa yasamu wani daga dangin iyayensa, tunda basu san kowa ba daga family dinsu, Inna kawai suka sani da baba"
"Allah yasa gaskene Su Hanan 'yan uwan su Abba ne, inda suke sunada yawa sosai estate ne guda gaba daya family dayane"
"' yan uwankune Insha Allah, bari in mayarda hotunan nan se in maida ke"
Ta gyada masa kai ta jirashi ya mayar ya dawo, ya kalleta yace
"muje ko"
Ta wuce gaba ya biyo ta abaya ta tsaya ta wigo ta kalleshi "dan Allah karkayi wannan tukin, dan Allah" bece komai ba ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga ya kunna motar, aka bude masa gate ya fita, masu gadi nata daga masa hannu amma yayi musu banza,
"Suna maka magana amma kayi musu banza ba dadi fa"
"to mezan musu? Ko sokike in sauka in tsaya ina surutu?"
"A'a bahakaba at least ko daga musu hannu kayi"
Be kuma kulataba ya cigaba da tukinsa,
Sarkar wuyansa ta kalla, sekace ba ďan musulmi ba, "Kafasa tafiyar dai ko?"
"baki yadda dame na fada bane?"
"A'a ni banceba, Amma dan Allah kadena yi wa Mummy abunda kake mata, dan Allah"
"Waike ba Adda tagaya miki komai game da rayuwata ba mekikeso inyiwa Mummy?"
"Bahaka bane ba, inka mutu tana fushi da kai Allah ma zeyi fushi da kai, kila sanadiyar yafemata kaga Allah ya daidaita maka Al'amuranka, mutane zasu dena kyamarka"
"Anya Al'amurana zasu gyaru? Mutane bazasu taba sakin jiki daniba kowa ya riga ya gujeni se kalilan din mutane"
"Al'amuranka zasu gyaru inkaso mana"
"Ta yaya?"
"I will help you do that, sekowa ya dawo yana sonka"
"how?" ya tamabayeta a takaice
"Just believe me, you Can change, I will help you change your life, trust me"
Kallonta yayi sannan yai murmushi "I have trust you already, ko iya haka you bring a lot of changes in my world, Thank you"
"kasan wani abu daga lokacin da ka kasance tareda abunda kakeso lokacin kake kara samun nutsuwa da kusanci zuwa gareshi, Iyaye abun sone, dakana kokarin ka manta abunda Mummy tayi maka ka kyautata mata wataran zaka manta da komai"
"bazan manta ba kuma ni yadda take kara cusamin Ilham ke batamin rai"
"wai me Ilham tayi maka haka?"
Kallon Jalila yayi irin kin rainamin hankali
"kinsan komai amma kina rainamin hankali, lokacin dana kwanta a Asibiti kikace musu ina bacci, sunsaki baki itada mahaifiyarta naji duk abunda suke cewa kuma kina tambayta me tayimin bansaniba"
Dauke kai tayi ta danyi murmushi.
Suna shigowa bakin layin suka ga wani dattijo yanata tattare ledojin da suka dan bata layin, da Sauri tacewa Jalal ya tsaya
"me zakiyi?"
"Kaga dattijon can zamu tsaya mu gaisar kaimasa Alheri"
"saboda me?"
"Maganar me mukayi dazu, you want change"
Hade rai Jalal yayi "Wannan mutumin ba irin zagin dabemun ba farkon fara shaye2 na"
"kayi hakuri ka nuna masa ka manta please"
Jalal yaja motar suka karasa inda dattijon yake suka gaisa sukayi masa sannu da aiki, sannan Jalal ya dakko dubu daya ya bashi yasa hannu ya karba ya dinga godiya sannan suka wuce,
"Kiduba Ajiyata dana gaya miki"?
Ya jefo mata tambayar, Jalila bata son rigimadsa tasan intace Ilham ta dauka fada zasuyi dan haka tace
"Wace Ajiyar fa?" ta tambayeshi irin ta manta din nan
Ya gano so take ta raina msa hankali dan haka ya kyaleta yayi parking Akan idon Ilham Jalila ta fito daga motar Jalal.
Ilham aranta tace "dama tazo dazan bakantawa Jalila insa a tsanate" dan haka Ilham da gudu ta shiga cikin gida tana kwalawa Mummy kira ta samu Mummy a daki idonta yayi Ja saboda kuka tana lazimi
"Mummy wallahi Jalal bashida mutunci bashida Imani, duk yadda kikayi kina kuka bakyason ya tafi seda ya tafi, gashinan a banza mace tasashi ya dawo yafasa tafiyar, wallahi gaskiyar daddy Jalal neman mata yakeyi"
Cikin rashin fahimta Mummy tace "Ke bangane me kike nufi ba"
"Mummy Jalal yadawo be tafi ba saboda Jalila"
"Kamarya saboda Jalila?"
"Oho musu dai, wallahi gashi can shida Jalila sun dawo, saboda ita yafasa tafiyar"
"ke ya akayi kikasan saboda ita yaki tafiya?"
Ilham ta gyara zama tace "Mummy nifa shiru kawai nakeyi, Allah kadai yasan abunda nake gani a tsakaninsu, bana son yawan bata miki raine"
A fusace Mummy tace "Ilham bana son shirme da shashashanci, kimin bayani yadda zan gane, ban fahimci ke kadai kika san abunda kike ganiba kimin bayani"
"Wallahi Mummy ba tun yauba akan yarinyar nan bakiga rashin mutuncin da takemin ba, kuma wallahi ita take ziga shi yakemiki wani rashin mutuncin, har dakinsa take zuwa gurinsa, Allah kadai yasan me sukeyi"
Mummy tayi shiru tace "lallai yarinyar nan makira ce, agaban idona take bude baki tacewa Jalal mara tarbiyya, Ashe itama mara tarbiyya ce, tunda take biye masa suna lalacewa, wallahi bata isaba dole in nesan tata da dana, dan bazan zuba ido yana ta'amalli da itaba, akan me na yadda da ita  ina mata kallon mutuniyar kirki amma zatayi min haka? Gaskiyar dsddynsa yana neman mata kenan inbahakaba uban me take zuwayi dakinsa, kema banda rashin mutunci ubanme ya hana ki gayamin abun tun farko"
" Mummy dan Allah kiyi hakuri, kawai nidai bana son ki tayara da hankalinki ne a zatona zan iya shawo kan abun, tunda naga abunda yafaru yau kalli banbamin dayake miki dankice kar ya tafi, Amma dayake akwai abunda sukeyi ai baze iya hakura ya tafi ba, yanzu ki kwantar da hankalinki kawai dai kiyi kokari ayi mana Aure da shi a wuce gurin "
" Ke kina batun inyi kokari ke wani kokarin kikayi?, tsawon shekaru kina gidan nan amma kinkasa janyo hankalin sa, Amma kanwar kanwarki wannan 'yar yarinyar hartasan taja hankalinsa duk taurin kansa, da uwar me tafiki? Niba ina nufin ki zubar da mutuncinki ba amma abun ya dauremin kai, ace har taci mutuncinsa agabana amma dayake bashida zuciya har tasamu kusanci dashi fiye dani da kema gaba daya Kinga tashi kibani guri ni raina ya gama baci"
Ilham ta mike ta fita tana zunbura baki, Amma dai tayi Nasara tunda har Mummy tafara daukar zigarta ta harzukata haka yanzu saura next plan dinta.

Jalila ta tsaya ta kalleshi tace "to ni zan shiga gida, Amma kabawa daddy hakuri"
"Hakurin me zan bashi? Jiya da daddare ya tafi U.K ai"
"to Mummy fa?"
"mezan mata, akanta nake kokuma wani abun nayi mata? "
"Ohh God kanada taurin kai, Just recently kace you want change, kuma yanzu kana wata magana, she's your Mother, komene halinta kuwa, Aljannarka tana karkashin kafarata, ko kanaso kashiga wutane?"
Tayi masa tambayar kaman tana tambayar karamin yaro
Kallonta yayi amma bece komai ba
"Kadinga zuwa inda take, kayi hakuri da duk yadda take, kadena bata mata rai, kaji dan gidan daddyn sa, your Mum is so kinda, she loves you, you have to show her love too, batun Ilham kuma babu dadi kace baka son mutum agabansa kaji"
Tai maganar tana murmushi sannan ta shige gida.
Sumar kansa ya shafa yayi murmushi shima.
Gida ya shige yayi wanka ya ci Abinci ya tafi gurin Jawwad, Jawwad na ganinsa yafara dariya "mutanen Dubai ya akayine?"
Jalal ya dan hade rai "naga alama da hadin bakinka kanwarka tasa aka hanani tafiya"
"niba hadin bakina, amma nasani daddyn Hanan tagayawa, tun a lokacin nasan za'a soke visa dinka, amma nayi shiru ban gaaya maka ba, Amma ya akayi kasan itace tasaka, ina fatan zakayi hakuri karka hukunta ta"
"Hmm Jawwad kenan, yarinyar nan nasan halinta sarai, tun ana gobe zan tafi take dariya tace taga ta inda zan tafi, kaga inba itaba babu memun haka, akwai abunda tayi da har yanzu yake bani mamaki shiyasa akwai abubuwan da idan tayi bazan mamaki ba. Sannan yazan mata ta riga tayi, ban mata komaiba tare muka dawo ma"
Murmushi Jawwad yayi yace "zoka bani Labari, yaushe kuka dena fada ne? Ya akayi ka sakko da wuri haka? Nazata inka gano itace semunzo ban hakuri kar a hukuntata hukunci me tsanani"
"ta fini gaskiya ne, a da dinma abubuwan da take fada akaina gaskiya take fada, nina nake fadan rashin gaskiya, sedai tafiya tsiwa a gadarance take gayamin magana abunda yake harzikani kenan"
"to yanzu fa?"
"Bansaniba babana kasani agaba se antayamin tambayoyi kake, sekace EFCC, kaje ka tambayeta mana"
Dariya Jawwad yayi tareda dan jan kunenen Jalal dake cin Abinci ta sigar wasa yace "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade nidai tunda baka hukunta taba kagama min komai"
Murmushi Jalal yayi sannan yacigaba da cin Abincin sa.
Sunata hirarsu shida Jawwad gwanin sha'awa,

Naja tana gaban mudubi, tasha kwalliya kaman zata gasar rawa, duk tabi ta tsuke jikinta, ta feshe jikinta da turare se taunar chewing Gum takeyi
Nana tace "Ehemm su hajiya Naja ko anyi sabon kamune wannan wanka haka?"
"bawani Sabon kamu, gurin Masoyina zanje tunda shi bezoba ai gara inje inda yake"
Jalila kallin Naja take kawai dan ba karamin tausayi take bata ba yanzu, rashin sani yafi dare duhu, da Jalila zata fadi wani abu data rusa duk wannan rawar kan da farincikin Naja har karshen rayuwarta, abunda ita kanta Najar bata san dashi ba "Allah ka kiyayemin Yaya Jawwad dina ka tsaremasa Imaninsa tareda dukkan Musulmi, dan a wannaan shigar da Naja tayi tana wannan masifaffen Kamshin indai Lafiyayyane namijine da wuya ya iya shallake wannan mugun tarkon na shedan.
Nana ko cewa tayi" kekam dan rashin aji dan yaki zuwa ke sekije inda yake, Sannan kalli shigar ki bata daceba kayan sun matseki"
"A'a ke kyaleni, A haka zanje irin wannan shigar da ita ake kama zuciyar masoyi kuma tana kara kusanci da kauna"
Itadai Jalila batace komai ba har Naja ta fice, sedai girgiza kai datayi tana cigaba dayiwa Jawwad addu'a.

Jalal yagama cin Abincin sa ya dakko system dinshi yana dubawa yace

"Jawwad next month fa zaka tafi Abuja gurin Aikinka"
Da sauri yace
"Saboda me?"
"Saboda nima haka na shirya maka kafin intafi, dan haka seka tafi"
"haba Jalal meyasa, Abba na kokarin bude mana store ne muyi ruining dinsa da kanmu kaga base nayi aikin gwamnati ba mun huta"

Dan tsurawa Jawwad ido yayi a ransa yace "mezanmaka a rayuwa Jawwad in biyaka kauna da alherinka, Sarai Jawwad yasan Jalal yanada tarin dukiya a kasa, Amma bayason ya kashe masa zuciya kar ya nemi na kansa"

"Kaga idan ka tafi nika barni da harkar kasuwancin zanyi mana, Amma seka tafi fa"
"Amma Jalal hakan......
" Salam Alaikum "
Muryar Naja ta katsesu gaba daya suka juyo suna kallonta
Wato har wani pink take saboda tsabar bleaching, saboda daganin wannan farin banata baneba, ga gaba daya dakin ya gauraye da kamshin turarenta tareda karnin mayukan da take Amfani dasu, tasaka riga da skirt na material dasuka kama jikinta matuka duk saman kirjinta a waje.
Dauke Kai Jalal yayi, yacigaba da danna system dinsa
"Masoyina gurinka nazo fa"
Tai maganar tana kokarin zama a kusada Jawwad, Jalal kam mikewa yayi ya shige bedroom din Jawwad, yana tunanin meyasa wasu matan basuda kunya basu san ciwon kansu ba, ace mace budurwa kaman wannan amma tana nanikar namiji haka ba kunya ba tsoro, hakama Ilham take masa wani lokacin, To Amma meyasa ita Jalila bata haka? Shidai yasan ba ruwansa da mata hasali yana gudun taba macen daba maharramarsa ba, Amma ita Jalila bayajin komai dan ya tabata, yana jin kaman hakan shi a gurinsa ba laifi bane, sannan duk lokacin da hakan tafaru a tsakanin su yana ganin matukar tsoro da rikicewa a idonta. Haka yacigaba da zancen zuci yanata tunani daban2.

"Haba masoyin, Meyasa baka zuwa inda nake Yaya Jawwad, wallahi banajin dadin abunda kakemin sam baka nunamin soyayya"
Matsawa yayi daga kusada ita yace "Naja soyayya daban Aure daban a yanzu keba halalina bace ba meyasa zakimin irin haka? Ke ko kunya ta bakyaji ne haba Naja kidinga kama kanki mana"

Matsowa takumayi jikinsa tana kashe murya tace
"meye wani kama kai, Aurena fa zakayi dan Allah kasaki jiki ka nunamin soyayya haba Jawwad" takai hannu tana shafo fuskarsa

Gaba daya jikin Jawwad rawa yakeyi Tsaki yayi yana kokarin mikewa, tunda ya fuskanci bazata ganeba
Riko hannunsa tayi tana kokarin Rungumeshi, A fusace ya hankadeta kasa yana kokawa da numfashi,
Tashi takuma yi tace "bazanyi zuciya ba" sekace mayya take kuma shanye ido kamar tana maye, ta rungume shi.
"Ke!!!" ya daka mata tsawa a fusace wadda seda yasa Jalal fitowa a sukwane yayi jifa da ita
"ki tashi kibarmin dakina, Allah ya shiga tsakanina dake ban taba aikata mummunan sabo ba bazan fara akanki ba, get out from my room ko in illataki" idon Jawwad yayi jawur jikinsa yana rawa, gaba daya ta kasa gane dama Jawwad yana fushi haka? Jalal ya karaso ya rike Jawwad yace 
"Jawwad kyaleta yi hakuri, calm down"
"bazanyi hakurin ba ka kyaleni, wallahi takuma zuwarmin daki sena bata mamaki, bata san a bisa umarnin Maama zan Aureta ba, in bahakaba me zanyi da ita? Me take dashi daza'a kalla a ce wannan mace tagari ce ya dace a Aureta? Itada mahaifiyarta sun shiga sun fita sun rabani da kanwata shekara da shekaru suna uzzuramata suna bata mata rai suna cimata mutunci, na hakura, ance sena Aureta na hakura nayi biyayya, be isheta ba seta nemi tasana aikata laifi me muni"

Kallon Naja Jalal yayi, kaddai ace wannan yarinyar ya yadda ze aura, Amma Jawwad hakurin nasa yayi yawa. Naja ba karamin mamakin abunda Jawwad yayi mata tayi ba, ita babban mamakinta bata taba ganin yana fada ba, saboda tasan mutum ne me kunya da kawaici.
Jalal yace "Naji kadaiyi hakuri"
"bazanyi hakurin ba Jalal"
Jalal yace "da nine da yanzu kacemin masifaffe, haba dan uwa Aliyu Haidar zakin Allah, katangar sikari na Hanan kowa ya jingina da kai seya lasa, fari me farar aniya kai a cikin masu sunan ma na dabanne kayi hakuri" Jalal yana lallaba Jawwad ne saboda yasanshi be iya fushi ba, seya shafe shekaru be fushi ba amma idan yayi abun baya kyau.
Naja tace "kagama duk masifunka, wallahi nidin dai ni zaka Aura kuma zaka gane baka da wayo, bari Maaman ta dawo zaka gane ka taka tarkon mace.
Jalal ya hanashi magana, suka kyaleta a gurin yaje ya dinga rarrashin Jawwad, ana haka Hanan ta kira wayar Jawwad, Jalal yai murmushi yace "kaga ka daga wayar nan ayi maka kalamai, zaka huce"
"A'a ka kyaleni, am not in mood"
Aikuwa Jalal ya daga wayar suka gaisa yace "Hanan ga mutumin naki, Amma ransa a bace yake fa"
"Subhanallah dan Allah wayakai min zuciyarsa bango har akasamin shi fushi, dan Allah ka bashi wayar"
girgiza masa kai Jawwad yayi alamar baze karba ba
"kiyi hakuri, baze karba ba fa, ransa a baci yake"
Hanan a shagwabe  tace "Shikenan tunda baze karba ba amma zuciya ta bazataji dadi ba, Allah kuka zan tayi duk daren nan, wallahi har naji tawar zuciyar tafara nauyi"
Ai tuni Jawwad ya zare wayar a hannun Jalal yasa a kunnensa yace
"Hello Hanan kina jina?"
"haidar dina me akayi maka?"
"wani little issue ne, kuma yanzu komai yayi settling"
"little issue baze bata maka raiba"
"ki manta kawai, kar inga abunda yasamin ke kuka"
Jalal yaji Jawwad ba kunya anataya masa kalamai agabansa. ya minstili kafar Jawwad yace "dan rainin hankali kawai"
Jawwad yai murmushi
Jalal ya daga masa hannu ya wuce gida.
Yanayin maganar Hanan kaman Jalila, tuno moments dinsu yayi dazu dayake ta dage bilhakki tana masa fada, da yadda take da ido idan batada gaskiya murmushi ya dingayi shi kadai, har ze kwanta ya tuno maganganun Jalila game da Mummy.
Mikewa yayi ya nufi cikin gidan, babban palourn Mummy yasa hannu ya bude kofar. Salla takeyi yanemi guri ya zauna, rabonsa da dakin  nan harya manta yana jiranta yana sake2 a zuciyarsa mema ze ce matane?.
Ta idar tagama lazimi, ba karamin mamakine yakamata ba ganinsa a part dinta
Ta kalleshi tace "Lafiya kuwa? Ashe baka tafi ba, uwarka wadda tafini, wadda take baka abunda bana baka ka fasa tafiya saboda ita.
" Wakenan? "
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
Chapter 34 · 0% Book details