← Book details Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 61

   PART 2        

Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 12 min read

                          _PAGE  2️⃣0️⃣73

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]

     
          
         

              _MY FIRST NOVEL_


Da sauri Saudat tace "Salma lafiya kuwa? Wai meya faru ne?"
Cikin kuka tace "dole kicemin meyafaru Saudat, kuncuceni ina zaman lafiya da mijina, amma ku yaudareni keda yar uwakki wallahi bazan yafe muku ba Saudat, kije da Allah nabarku da Allah daga ke har khadija" cikin rashin fahimta Saudat tace "bangane me kike nufiba Salma, dan Allah kimin bayani"
"Au saboda baki da kunya har bayani kike nema inmiki, Azzalumai kawai, wallahi bazan yafe muku ba na yadda dake kun hada kai da yar uwakki kun cutar dani cuta mafi muni kuda Allah" ta kashe wayarta, ta dora hannu akai ta fashe da wani irin matsanancin kuka me tsuma zuciya
"Na shiga uku ni Salma, menamuku kuka kwacemin miji, mijina mafi soyuwa a gareni shi zaku auremun Habibin nawa, shi zaku auremun na shiga uku ni Salma, meyasa nasanki Saudat" haka tacigaba da kuka tana surutai.

A salube Saudat ta sauke wayar, takasa gane inda maganganun Salma suka dosa, meye alakarsu da Auren mijin Salma. Tana cikin wannan tunanine taji ana shelar ankai lefen khadija gidan kanin babansu, akwati ashirin da hudu, gida ya dau sowa da hayaniya
"Akwati ashirin da hudu"? , Saudat ta maimaita, "itakuwa khadija ina tasamo Attajirin mutum haka? Waye wannan ze Auri khadija haka, shiyasa take boye shi, to tabbas idan har bansamu Auren Habib ba, sena shiga na fita naraba khadija da Auren nan koda tayishi, dan bazeyuwu tayi Aure tasamu Attajiri haka, nikuma ina gararanba ba"
Tafito tsakar gida yan gida nata surutu, wasu na san barka wasu na kushewa, suna agarin kwashe2 kil dan yankan kaine, inbahakaba akwati ashirin da hudu sekace wata yar gwal, yayinda bakin mahaifiyar khadija yaki rufuwa dan murna.
Khadija bata gida dan sedare ta dawo, yauma Saudat gurin khadija ta tafi
"Khadija nikam dan Allah ki gayamin waye mijin nan ko a hoto ki nunamin shi, akwati ashirin da hudu dozen biyu fa, sana'ar meyake haka"
"mekike ci na baka na zuba, har gidan nan zezo ranar daurin Aure kijira zaki ganshi ai, koma sana'ar meyake ni ina ruwana"
"sewani Boyeshi kike kaman ciwo, zamu ganshi dai muga meye ake boye mana, nace wai yazakiyi da kabir ne"?
Tsaki khadija tayi "Kabir din banza, nabashi katin daurin Aurena, yagama zage zagensa da kumfar baki, uwassa ma tayi tagama, nace yaje yai duk abunda yaga ze iya"
"hmm khadija manya, amma Kabir be cancanci haka daga gareki ba, ya miki wahala be kamata ku rabu baran baran ba"
"to ko zaku daidaitane keda shi?"
"Allah ya kiyaye ke ki auri me kudi nikuma ki hadani da matsiyaci Allah ya kiyaye"
"yo kuma ni sekiga laifina"
"to abar wannan zancen dazu tela ya aiko miki da dinkinki"
"Aiko ya kyauta, dama nagama biyansa kudinsa"
"Khadija munyi waya fa da Salma dazu" wani mummunar faduwar gaba ta ziyarci khadija amma ta dake tace "Allah sarki"
"Amma wasu magamganu ta dingayi da bangane musu ba"
"kamar ya kenan"
"ni kaina ban gane me take nufiba, Amma zankuma kiranta, yadda take maganar tana cikin damuwa"
"Saudat duk wanda za'ayiwa kishiya ai dole yashiga damuwa, mussaman bw san da wacce kishiyar zata shigo ba, kibata shawara cewa ta mike tayi tsaye, dan duk wata mace a yanzu musamman wadda zata shiga gidan me mata toda shirinta take zuwa"
"bata tsaya ta saurareniba balle in bata wata shawara, bari dai ayi bikinki agama, nikuma zan mike inyi fafatuka nima inshiga a ta uku" dariya sosai khadija ta dingayi mata "lallai Saudat yakamata kema seki dage Allah yabawa me rabo sa'a"
Yau Habib yadawo daga tafiyar da yayi, dan satin biki yakama, dan gidansu khadija har sunfara wasu events din da mamakinsa koda yadawo Salma bata gida, yakira wayarta amma taki dagawa. Yasan bata da wasu kawaye ko gurin zuwa a kano dan haka a ranar ya shirya ya nufi maiduguri, aikuwa yanazuwa tana can gidansu gaba daya bata hayyacinta banda aikin kuka babu abunda takeyi, dayake shima gidansu ne be jira amma sa isoba ya shiga gidan ba kowa se ita kadai a palour a kwance akan doguwar kujera idonta duk ya kumbura saboda kuka
"Salma meyasa kika taho kekadai baki gayamin ba, inata kiran wayarki kinki ki dauka hankalina ya tashifa"
Banza tayi masa ta dauke kanta, "haba Salam meyake faruwa ne?"
"dan Allah ka rabu dani Habib karshen wulakanci kayimin shi, karasa wadda zaka Aura se yayar kawata duk matan dake garin nan, bakasan wacece khadija ba, amma ka rubuta ka ajiye sekayi danasanin wannan auren kuma bazan koma gidanka ba nagama Aurenka Habib, am really disappointed on you " mikewa tayi zata bar palourn ya riko hannunta amma ta fizge ta wuce dakinta ta kulle kofa, jiki  a sanyaye yanemi guri ya zauna ya dafe kansa a gurin, Salma tanada mahimmanci a rayuwarsa baze taba bari kishinta ya rufemata ido ta rabu dashi ba, amma me take nufi daze auri yayar kawatta dama tasan khadija ne? Mikewa yayi ya nufi part din mahaifin Salma.
Amma yana zuwa ya tarar yanada baki dan haka yajira ya gama sannan yashiga, mahaifin Salma na ganinshi yafara murmushi "Ango kasha kanshi, saukar yaushe haka ba Labari" dan sosa kai Habib yayi ya samu guri ya zauna yace "Abba dan Allah ka tayani bawa Salma hakuri, duk na rasa gane kanta, munyi sallama lafiya na tafi na dawo na tarar bata gida ta taho nan, nace tazo mukoma tace bazata koma gidana ba" Ajiyar zuciya mahaifin Salma yayi sannan yace "Mata se addu'a, ni na dauka kasani kai ka batta tazo ai, kuma mahaifiyarta batacemin yaji tayo ba, tashi muje yaudin nan zaku koma kano tare Insha Allah"
Suka mike suka tafi dakin Salma, Abba yace ta bude masa shine, haka ta taso ta bude,
Nan ya dirar mata da fada ta inda yashiga bata nan yake fita ba, yaimata kaca2
Cikin kuka tace "Abba kayi hakuri amma yayar kawatace fa, meyasa yaya Habib zemun haka"
"ko kawartaki ce aiba haramun bane ba, kuma daba'a Aure daba a Aureki ba" daga nan ya yakoma yimata nasiha da rarrashi, ya hadasu gaba daya yai musu nasiha yai musu Addu'a, Abba be bari maman Salma ta dawo ba yace ta shirya tabi Habib sukoma Kano.

Da magariba Saudat tanata safa da marwa a daki, tarasa meyake mata dadi, khadija zatayi Aure ta batta, gashi khadija tasamu me kudi itakuwa ko oho, ga Salma na wasu maganganu da bata gane kansu ba, "gaskiya yakamata inyi wani Abu, bari inji in Salma na gida gara tamin kwatancen gidanta inje inji komai, sannan inyi fafutukar haduwa da Habib"
Wayarta ta dakko da sauri ta dannan lambar Salma, aiko a fusace Salma ta daga wayar "me kike nema a gurina kuma, kun kwacemin miji, hakan yayi sanadiyar samun sabani da iyayena, kun rabani da farinciki na, shine kika bugo kiji kona mutu ko? To ban mutu ba da raina"
Cikeda mamaki Saudat tace "dan Allah Salma kiyi hakuri bangane mekike nufi ba"
"dole kice baki ganeba, maciya Amana kin hada kai keda yayarki zata Auremin miji, Saudat kurasa wanda zaku cuta seni Habib dina yayarki zata Aura, nagode Saudat karki kara kirana a waya, kuma ko a lahira bana fatan Allah ya hadani da ireiren zuri'arku" Saudat bata karasa gane me Salma take nufi ba, dan kojinta bata gamayi ba, dan tuni ta saki wayar a kasa, kokari take ta tabattar da bacci take kokuma idonta biyu, kaman wadda aka tsinkula tayo waje da sauri daga dakin.

Khadija tana kwance tana wayada Habib
"Hayatee dan Allah kazo inganka mana, tunda satin biki yakama banaganka ba kuma kacenin kadawo daga tafiyar"
"kiyi hakuri Dijart, wallahi Salmace duk ta birkicemin, kuma bata da lafiya dole ina tareda ita kiyi hakuri, Tana bukatar kulawa ta mussaman"
"nibana bukatar kulawarka kenan?
" bahakabane ba deejart, ita daza'ayiwa abokiyar zama tana bukatar rarrashi da kulawa, yawwa nace dama kinsan Salma ne? "
" Meyasa ka tambayeni"
Saudat ce ta fado dakin bako Sallama tayo kan Khadija, da sauri khadija ta tashi zaune ta kashe wayar
"Khadija wane Habib din zaki Aura?
Waye Habib din?" dama khadija tasan wannan ranar zatazo, dan haka ta mike da sauri ta rufe kofar dakin, saboda yan biki sunfara zuwa gidan da mutane, ta dawo ta kalli Saudat tace
"ina jinki, mekike cewa?"
Cikin fada tace "tambayata ma kikeyi? Waye Habib din dazaki aura?"
Cikin dakewa tace "Habib Kamal me Gwal, mijin Salma kawarki shi zan aura" A razane Saudat ta kalleta "ke yanzu khadija bakji kunyar gayamin haka ba, macuciya Azzaluma, na yadda dake kici amanata, mijin kawata, wanda nakeso nazo nagaya miki matsalata, kikace zaki temakamin ashe cuta ta zakiyi khadija, na yadda dake amma kimin haka"
"ke dalla dakata, mekikace mijin kawarki, aigara ace nina aureshi akanki abun kunyar seyafi sauki, ni abun kunya gaba na bashi ba bayaba, kekikace ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba, kema Auren cin amana kikaso kiyi ai, Saudat na dade ina mafarkin Auren miji irin Habib tun ranar da naganshi naji nakamu da sonsa amma abun mamaki, kika rigani gayamin kema kina sonshi, a lokacin nan dana gayamiki ina sonsa nima toda biyu babu za'ayi, shiyasa namiki shiru, na gargadeki da kinemi wani karki tsaya jiran Habib amma kimayi bris dani, kisani mutuwa ce kadai zata iya hana Auren nan, duk wani shige da fice dazakiyi a yanzu aikin gama ya gama baki isa kiyi komai ba, dan ba karamin shiri nayi ba"
Fashewa da kuka Saudat tayi tace "khadija da tun farko kin sanardani kina son Habib, dazan iya barmiki shi, da ban wahal da kaina haka ba, amma kika bari na dinga lalube kina rainamin hankali, tun tasowarmu kaf cikin yan uwana uwa daya uba daya dake na yadda, amma kinmin cutarwa mafi muni khadija!!!! Kinsa na zubda hawaye kin bakantamin rai kinmin tabo me muni da bazan manta ba, kin kwace abunda na kallafa raina aki, shikenan ki shirya ki rubuta ki Ajiye idan harni Saudat yar halak ce haihuwar uwa da uba, wallahi senamiki mummunan tabo kema ki Auri Habib ga daula nan kinsamu, amma ki saurar zakiga nima abunda zan iya" ta juya da sauri fuskarta duk hawaye zatayi waje khadija ta rikota, karo na farko dataji tausayin Saudat amma ta basar tace
"Saudat ki fawwalawa Allah lamarinki, kiyi wanka da fetur, sannan ki hau risho da wandon leda yafimiki sauki akan hana Auren nan, kisawa zuciyarki salama kibi a sannu kema sekiga kin samu ko wanda be karasa Habib bane, kinfi kowa sanin hatsarina karkije garin daukar fansa kikuma ruftawa wani tarkon wanda bazanso hakan ba, har yanzu ina kaunarki yar uwata, kar abunda nayu miki ya shafi zumunci da kaunar dake tsakaninmu"
Fizge hanunta tayi da karfi ta bude dakin ta fice, Ajiyar zuciya khadija tayi ta koma ta zauna tayi murmushi tace "Saudat kenan, na dade ina ankarar dake amma baki gane ba, naciki wasa se hakuri"
Tundaga lokacin nan Saudat tafara rashin lafiya har akayi gama bikin khadija, tarasa nutsuwarta gaba daya, banda tunani babu abunda take, so take ta samu hanyar dazata turawa khadija bacin rai dan ta huce, tarasa mezatayi danta huce, kasa samun mafitane yasata takara shiga damuwa da halin rashin lafiya, yayinda khadija ko a jikinta hidimar bikinta kawai takeyi, anyi hidima sosai a bikin khadija anci an sha, anyi watsi da nera yadda yakamata.

Kabir yashiga matsanciyar damuwa gameda Auren khadija, yayi kuka, yayi kukaba adadi, ga fushi da mahifiyarsa keyi dashi, ga basussukan mutane saboda yadda yakecin bashi yana kashewa khadija, gaba daya duniya tayimasa zafi, yarasa meyake masa dadi.

Tunda Allah yasa khadija ta shiga gidan Habib komai yafara rushewa, gaba daya hankalin Habib yakoma kanta, Salma dama bata da surutu, khadija tafita baki, dan haka ta shiga hadasu fada, dama khadija bata kaunar dangin Habib tunda taji labarin basa son Aurenta, da Habib baya wata guda cikakke beje maiduguri ba amma tunda ya auri khadija seyayi watanni bejeba, Salma sedai ta zauna tasha kuka, ya shirya musu tafiyar wata daya Dubai shida Salma da khadija, Salma tace bazataba, ya dauki khadija suka tafi basu dawoba seda sukayi wata uku, gaba daya Salma ta zubawa sarautar Allah ido.
Idan yan uwan Habib sukazo gidan ta dinga rashin mutunci kenan tana habaici
Tunda taje dakin miji Saudat bata taba zuwa gidanta ba balle takirata a waya, hakazalika seda ta shekara guda cif sannan ta yadda tabi Habib maiduguri ta gaida mahaifiyarsa, tunda mahaifiyar Habib taga khadija taji sam bata kwanta mata ba dan sam babu alamar kunya ko kara a tareda ita, tunda ya aureta shekara guda sannan tazo ta gaishesu. Ta lura khadija a tsaye take ga Salma ta rame matuka tayi duhu, dan bata gayawa kowa meyake damunta, kota fada ba a goya mata baya sedai ace tayi hakuri kishine ke damunta.
Maman Habib ta kirashi dakinta, ta dinga masa fada, akan yadinga adalci tsakanin matansa, in bahakaba seyayu danasani, dan taga alamun wannan tsagerar daya aura kamar suna cutarda Salma, dan ita sam wannan yarinyar batayi mata ba, banda rashin mutunci shekara guda da aure sannan sukazo yakawota gida sugaisheta shi kansa ya canza gaba daya,
Haka yaita bata hakuri, yace insha Allah ze gyara amna yana kokarin yimusu adalci.
da kyar khadija ta hakura ta kwana biyu a garin tace ita ya maida ita gida ta fuskanci danginsa basa kaunarta.
Watan khadija biyar a gidan ta fuskanci tanada ciki, koda tagayawa Habib yayi murna matuka, tunda ya auri Salma shekara biyu kan na uku amma bata taba ko batan wata ba, sunje Asibiti ance lafiyarta kalau, dan haka yayi murna da wannan cikin
"Habib kadena murna da wannan cikin zubar dashi zanyi wallahi!"
Cike da mamaki ya dubeta "kamarya ya? Ina neman abu in samu kice zaki zubar khadija why?"
"ban shirya haihuwa yanzu ba wallahi, da kuruciyata bazan tsufa ba wahalar yaya ta kasheni ba, tun kafin muyi Aure kasan burina inason yin karatu me zurfi a kasar waje, tayaya zanyi karatu da ciki, kwata2 yaushe nayi Auren zanyi ciki, wallahi sena zubar"
"khadija kiyimin rai dan girman Allah kiyi hakuri, kibari ki haifamin cikin nan seki tafi karatun"
"sekuma kayi, in kanason cikinka seka dauka ka maida shi jikinka ka haifa, amma indai a jikinane bazezo duniya ba gara ka hakura inkun matsu kaje kaimata cikin ta haifa maka"
Saroro yayi yana kallonta, ba kunya take gasa masa wannna maganganun.


.
A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu 'oinku
Sannaan masu rokon adinga posting a Facebook insha Allah za' a fara posting din Littafin ABDUL JALAL  Facebook tundaga farko
Insha Allah, za'afara posting a group din
AISHA HUMAIRA NOVEL FANS (Daddy's girl) dakuma sauran groups nagode sosai ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
Chapter 20 · 0% Book details