← Book details Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 61

   PART 2        

Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 14 min read

                          _PAGE  2️⃣4️⃣77

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]

     
          
         

              _MY FIRST NOVEL_


Sosai Jalila take Hawaye, tareda surutai a hankali, Nana ce ta shigo dakin, da sauri Jalila ta goge hawayenta, zuwa tayi ta zauna ta kalli Jalila
"Jalila lafiya kuwa, meyasameki? Meyasaki kuka kuma ina kika shiga tun dazu nake nemanki" Jalila bata san wace tambayar yakamata ta fara amsawa Nana ba, Jalila ta dan girgigiza kai tace "Bakomai karki damu"
"Yazakicemin ba komai, kuka fa kikeyi"
"Nana bakomai"
"Shikenan tashi muje, Bakin su Jalal zasu tafi, taso Anty Amina tace inkiramata ke" se yanzu Jalila tasan sunan Antin Jalal dinma, ba musu ta mike suka fito tare, suna shiga gidan suka tarar dasu sunfito zasu tafi, Mahmud ya kalli Nana yace "Nana gashi zan tafi bangama ganinki ba" murmushi Nana tayi "Nima bangama ganinka ba, kaje kayi zamanka a England, memakon kadawo Nigeria muma mu amfana da iliminnaka, kaje se wani uban kumatu kakeyi"
"Allah hajiya Nana, ke bakiga yadda kikakoma bane, kinzama wata madam, yanzuma Anti Amina mukayi waya, zasu zo nan kano, shiyasa nadawo nace nima suzo dani zan dade a Maiduguri kafin inkoma England" ya kalli Nana yayi kasa da muryarsa yace "Nana wannan ce Jalila ne?"
"itace kasanta ne?"
"A'a na tambayekine kawai, naga tana kama da wata ne, just forget, bani lambarki"
"Seka biya tukuna" murmushi Mahmud yayi, "Yimata kudi ko nawane imbiya" Nana tai dariya ta karbi wayarsa tasamasa lambarta, Suna tsaye suna jira Jalal yafito suyi Sallama amma tunda Jalila taimasa abun nan da safe, ya shige daki yaki fitowa ko sallama suyi, Jawwad yanata masa magiya amma yaki bude kofar nan.
Anti Amina takamo hannun Jalila tayi gefe da ita, ta kalleta tace "Jalila kuka kuma? Meyasa? Munasa ran samun nasarar daidaita rayuwar Jalal ta hanyarki amma muga karaya a taredake, karkimana haka Jalila, banbaki labarin Jalal dan isaki damuwa ba" kaman ta ziga Jalila takuma fashewa da kuka, Rungumeta Anti Amina tayi tana sharemata Hawaye cikin kuka Jalila tace
"Anty dana san haka Rayuwar Jalal take daban zama daya daga cikin masu kara rusa farincikinsa ba nasan na dade ina bata masa Rai amma.......
" Jalila kina yimasa hakane dan inyaji haushi ya dena abunda yake nasani karki damu kinji kidena kuka"
Jalila ta jinjina kai, suka musu rakiya har mota suka daga suka tafi.
Jalila jikinta a sanyaye takoma gida, daki takuma komawa ta kule akan gado tayi shiru nan ta shiga tunani daban2,
"Kenan Kabir shine Oga Kb? , Jeje yataka Rawa gurin lalacewar Jalal, menen alakar Kabir da Jeje?" dafe kanta tayi tai tagumi hannu bibiyu tai shiru sekuma wani abu yakuma fadomata a rai
"Saudat tabawa Jalal turare, aranar yadinga karkarwa cikin dare yana firgita, kenan Saudat ma wani abun tayi masa kokuma mene? To wa zangayawa? Mema yakamata inyi ne? "
"Yasalam" Jalila ta furta da karfi tareda dafe kanta, da Hanzari Nana ta shigo dakin ta tarar Jalila ta dafe kai tana kuka
"Jalila lafiyarki kuwa? Tun dazu nake tambayarki meyasameki amma kinki gayamin se kuka kike kinga yadda idonki yayi Ja kuwa?"
Murmushin dole Jalila ta kakalo, "Karki damu kaina namin ciwo sosai, allow me to rest" ta ture Nana ta kwanta, Nana ta dade tana mamakin meyake damun Jalila haka?
Yadda Jalila taga Rana haka taga dare, banda zunzurutun tunani da tambayoyi ba abunda ke kai komo a zuciyarta, ga wani irin tausayin Jalal dake ratsa zuciyarta, antarwatsa Rayuwarsa akan abunda lokacin da ake laifin baya duniyar, gaskiya Mummy bata cancanci zama uwa ba, ta fifita duniya akan Rayuwar danta. Har gari ya waye Jalila idonta biyu,
Halima da Nana ne suka hada breakfast, nanma sukayi sukayi taci Abinci takici, Abun yafara bawa Nana tsoro, dan haka taje tagayawa Maama halin da'ake ciki
"Nono kikeso inkamota in bata ko goyata zanyi inta jijjigata?"
"Maama bahakaba, at least yakamata musan meyake damunta, kartayiwa kanta illa, tun jiyafa bataci Abinci ba tanata kuka, kinsan batada cikakkiyar lafiya fa?"
A fusace Maama tace "fita kibarmin daki, kar Allah yasa taci, inta kashe kanta aita huta"
"Amma Maama....
" Bazaki fita ba sena makeki" ba shiri Nana ta fito, ta nufi part din Jawwad amma bayanan, takira wayarsa harta katse be dauka ba, daki takoma tazubawa Jalila ido data kwanta ta rufe ido, amma hawaye nabin gefen idonta
"Jalila dan Allah kitashi kici Abinci, wallahi gaba daya zuciya ta babu dadi, na damu matuka, dan Allah kici wallahi inbaki ciba nima bazanci ba" A hankali Jalila ta bude ido, ta mike zaune ta kalli Nana tace "zubo muci, banason kizauna da yunwa"
Nana ta zuba Abinci amma Jalila ta dan cakala ta barshi.
Wunin Ranar Haka Jalila tayi duk surutun nan amma yau tsit kakeji, Nana tayi tambayar harta gaji ta samata ido.

Da daddare Jawwad ya shigo yasamu Maama a palour yake gaya mata Ankai Jalal Asibiti. Da sauri Jalila ta mike ta fito palour ta labe
Maama tace "meysameshi haka?"
"kinsam jiya yan maiduguri sunzo, kuma dai kinsam babu jituwa tsakaninsu da Mummy, andai bata masa rai yaje ya kulle kansa a daki, yafasa abubuwa sosai sannan cikinsa da yunwa ya sha wani abun bansan meyasha ba, da kyar na bude dakin dazu, naganshi a sume shine muka kaishi Asibiti, yanzu can zantafi zan kwana dashi"
Maama ta kalleshi "ohhh Jawwad Allah yayemaka wannna Jaraba, wannan yaron Jalal kullum seyajanyo abun daze hanaka hutawa, sekayi tayi ai wahalalle"
Murmushi Jawwad yayi yace "Maama kenan, ai duk dan halak baya manta alkhairi, bari in tafi seda safe" ko kallonsa bata kumayiba, har ya juya ze fita Nana tace "Yaya Jawwad amasa sannu dan Allah, kuma wallahi Baby ma inaga wani abu na damunta tunjiya kuka takeyi, taki cin Abinci da kyar nasata taci kadan"
"Haba dai? Kuma kin tambayeta meyake damunta?"
A fusace Maama tace "fita katafi inda zaka, bazasu hadu sukasheka ba kowa  ya kwaso iskancinka akanka ze sauke, kaidabaka san ciwon kanka ba"
Jiki a sanyaye Jawwad ya juaya yafita, Jalila takoma daki ta kwanta tai shiru tamarasa tausayin wa yakamata taji.
Jin batun Jalal na gadon Asibiti abun yadameta.
Har gari yawaye Jalila nata kasa kunne taji wanda zeyi zancen halin da Jalal yake ciki, har wajen azahar shiru, Jalila tace "Nana naji kaman yaya Jawwad yace an kai Abokinsa Asibiti?"
"Eh acanma ya kwana, har yanzu kowaya beyoba, dazu Maama takirashi a waya amma bata shiga"
"to ya jikinnasa?"
"Nima bansaniba wallahi, amma bari mujira zuwa anjima"
Jalila ta gyada kai, ta dakko wayarta tana dubawa taga missed calls rututu
Call logs dinta tashiga tatarar da missed calls na Zahrah, Jalila ta kirata a waya bugu biyu ta dauka
"Salam alaikum, Jalila ina kika shiga tun jiya nake kiran wayarki amma ba kya dagawa"
"Am sorry ina wani mahimmin abune, se yau na dakko wayar, ya akayine?"
"Hmm Jalila sarkin Sabga, dama gayamiki zanyi anbada belin Baban Samir Fa shida duk wanda aka kamasu, shine nace kina ganin ba abunda ze faru kuwa insuka ganomu"
"Zahrah karki damu babu abunda ze faru, koda anganomu muka shirya wannan abun, to ki zame kibanni ba ruwanki balle baza'a gane ba, Burina ya cika na tonawa duniya asirin ya da Uba, duk wani cin zarafi da wulakanci dasu Saleema sukeyi dole sudena, saboda wannan mummunan abu. Kunya dasuka aikata, Amma tabbas zankuma gauraya dasu, Alhaji Kabir da Jeje, Nagode kigaida Umma" Jalila ta kashe wayarta, tacigaba da duba kiran da akayi mata takuma cin karo dana Hanan, da sauri ta kira Hanan, seda takusa tsinkewa sannan Hanan ta dauka, tace "Se yanzu zaki kirnaiko? Tun jiya nake kiranki amma kinki dagawa yar wulakanci kawai"
"Yi hakuri Hanan, lokacin bana tareda wayar se yanzu na duba nagani"
"To na hakura Allah ya temakeki, dama zamuje Bauchi nan da 2 weeks, Daddy yace zamuzo mu tambayi Abba inya yadda mutafi dake Inna taganki"
Jalila tace "Hanan zanyi murna da zuwanki, ina cikin matsala inason inganki"
"Matsala kuma Jalila? Meyafaru?"
"Hanan na dade ina tafka kuskure, yanzu ina nadamar abunda nayi, abun baze yuwu ta waya ba, nafison mu hadu"
"Subhanallah Jalila nadamar mekuma? Zaki banni cikin damuwa da tunani, ki gayamin menene?"
Jalila ta dan share Hawaye tace "Hanan for all this time i have hurting Jalal, calling him with different bad names, he is innocent, Hanan an gayamin tarihinsa, Jalal abun a tausaya masane, inajin kunyar hada ido dashi, Hanan ban kyauta ba"
"Is ok kidena kuka, ai duk dan adam baya wuce aikata kuskure, Calm down, abunda na dinga nunamiki kenan a baya amma baki ganeba, baka yankewa mutum hukunci kai tsaye akan abunda kaga yana aikatawa, idan nazo zamuyi maganar, amma ya akayi kikasan ba laifinsa bane?"
" Ai baze yuwu a waya ba, se mun hadu"
"Amma yakamata ki wanke lefinki"
"Hanan tayaya, tunda na riga nayi"
"Hakuri zaki bashi mana"
"Hakuri kuma?"
"Eh mana, yakamata kinemi ya yafe miki"
"mhmm Inasu Yaya Abdallah? Inason ganinsa ma ina neman yamin wata Alfarma inze iya"
"Wace Alfarma kenan?"
"Ina ruwanki semun hadu nida shi, ki gaida Baba"
"Hmm shikenan zeji Insha Allah" sukayi Sallama
Jalila kasa jurewa tayi ta dau waya takira Jawwad amma baya dauka, haka ta hakura.
Washegari shiru2 Jawwad be dawo ba. Har bayan Azahar gashi baya daga waya, hakan yasa Jalila ta kara shiga damuwa, ta fito harabar gidan, dan tasamu ta kadaice tayi tunani, tana nan Zaune tayi nisa sosai a tunanin tarasa ta ina yakamata ta fara, gaba daya abubuwa sun hargitse mata.
Motsi taji abayanta yasatayi saurin waigawa, Jawwad ta gani a tsaye tai sauri ta mike tsaye.
"Baby meke damunki hakane? Tun dazu nake magana amma kinyi shiru, gayamin meke faruwa?"
Murmushi Jalila ta kakalo, "Yaya Jawwad bakomai kawai dai banji bane, ina ka shiga bana ganinka nakiraka a waye baka dagawa"
"Jalal ne ba lafiya, na kaishi Asibiti na manta wayata a gida"
"Meyasameshi?"
Ajiyar Zuciya Jawwad yayi sannnan yace "jininsa ya hau, yana damun kansa dayawa, Jalal baya iya controlling bacin Ransa, yanada saka abu a ransa, ga kinsan shan taba yana kara saka hawan jini, amma Alhamdilillah jikinsa da sauki an sallameshi tare muka dawo gida" jinjina kai Jalila tayi "Allah yabashi lafiya"
"Ameen Baby, meyasamin ke kuka kika kasa cin Abinci Nana ta gayamin"
"Nikuma ai kaina ke ciwo kawai itakuma tabi ta damu, amma na warke ai"
"Anya kuwa, karya ba halinki bane, fuskarki ta nunamin kina cikin damuwa"
"bana cikin wani damuwa ni, kako ci Abinci naga kaman a gajiye kake"
"Hmm wato ba kyason incigaba da tambayarki ko?"
"bahaka bane, banaso ka zauna da yunwa ne"
Murmushi Jawwad yayi, "Ina jin yunwa kam, samomana wani abun, Jalal ma beci Abinci ba, yaki cin Abinci wallahi, nayi2 amma yaki, Yana cikin damuwa sosai, anyway samo mana abunda yasamu in lallabashi koze ci" gyada kai Jalila tayi ta juya da sauri ta tafi cikin gida.
Tana shiga palour ta tarar da Maama tana mata wani irin mugun kallon banza, Jalila ta dauke kai kaman bata san meke faruwa ba tai kitchen abunta. Ta dafa masa jallof spaghetti, ta hada da juice bayan tagaama take tunani yanda Maama ta zauna a palou  tana mata kallon banza, yanzu in tace zata kaimasa Abinci wani bacin ran zata jawa kanta dan haka ta kirashi a waya tace yazo ya dauka, befi minyi bakwai ba sega Jawwad yaje kitchen ya dauki Abincin. Har yazo ze fita Maama takirashi, yadawo ya zauna a gabanta yace "Maama gani, Allah yasa ba laifi nayi miki ba"
"laifi kuma tun yaushe kake sabawa umarnina, minyi magana akan muna son hada Aurenka Naja amma har yanzu baka kumabi takan zancen ba, sekara shigewa wannan algungumar yarinyar kakeyi, ban isa ingayamaka magana kajiba ko?"
"Maama dan Allah kiyi hakuri, na yadda in Auri duk wadda kikeso, amma bazan iya Auren Naja ba"
"Jawwad kake kallon tsabar idona kake cemin bazaka iya Auren Naja ba"
"Maaama Naja yar uwata ce bazankita haka kurum ba amma...
" Yimin shiru badai akan waccan hatsabibiyar kake rawar kaiba, idan ina raye ayi ingani, tashi kabani guri"
Jiki a sanyaye cike da damuwa Jawwad ya mike yabar palourn.

Tunda yan maiduguri suka tafi Jalila bata kara saka Jalal a idonta ba dan sam yadena zuwa gidansu, ga Jawwad yanata complain akan Jalal bayacin Abinci yana damun kansa sosai, ga matsalar da Jawwad yake ciki shima Maama nata tursasa shi tace se ya Auri Naja, amma ita Nana ta tirje tace bazata Auri faruk ba an kyaleta, Jalila tarasa yadda zatayi taga Jalal, duk abun yafara damunta. Ga yaya Jawwad dinma ta dena ganinsa ko waya basa yi, yadena shigowa cikin gida. Zaman cikin gida ya isheta dan haka ta fito danta sha iska, ta fito ba dadewa Jawwad ya shigo yayi parking, duk taga ya dan rame, yafito ya kulle motar, takarasa inda yake "Yaya Jawwad wai meyake damunka hakane, ka rame kuma tun shekaranjiya ban kuma ganinka ba" cike da damuwa yace mata "Baby Jalal, yana nema ya kashe kansa"
"Kamar yaya?"
"Ankuma kwantar dashi a Asibiti, tun shekaranjiya ina can, banason inkira Daddy kar adaga masa hankali, idan Mummy taje gurinsa, seyace seta tafi bayason ganinta yanzu haka jikinsa yakuma rikicewa, yanzu haka tun jiya yana ICU, maybe yau zasu fito dashi" nan da nan jikinta ya hau rawa, cikin rawar murya tace
"Subhanallah Allah yabashi lafiya, if you don't mind zan rakaka in dubashi"
"Shikenan naji amma kibari seda safe in Allah ya kaimu zanzo muje" ta jinjina masa kai takoma cikin gida

Yau Hannah har gidan Jeje taje nemansa tayi sa'a kuwa yana nan, Jeje yayi mamakin ganinta sosai "yau kece da kanki a gidana"
"Eh nice amma kasan duk lokacin daka ganni bukatace ta kawoni, almost one week ina nemanka, bana ganinka layinka baya shiga, amma naji ana rumors ankamaka kai da megidanka a gidan karuwai meye gaskiyar lamari" shiru Jeje ya danyi ya kalli Hanna
"Ni ina zargin dasa Hannunki akan abunda yafaru dani, shekara da shekaru inawa Oga Kb aiki inasamun rufin Asiri a gurinsa, ina hutawa da 'yarsa ba tareda yasani ba lokaci daya aka masa cunen gidan danake zuwa yakamamu, yanzu ya sallameni tareda cin alwashin seyaga bayana, wallahi Hannah indai dasa hannunki a wanna cin zarafin da' akamin bazaki tsira daga sharri na ba"
Murmushi Hanna tayi sannan tace "Aidama karshen alwa kasa, kuma ramin mugunta kurarrene, Jeje idan har zanmaka wannan manakisar yan sanda suka maka kaida uban gidanka to wallahi da duk yadda zanyi bazaka fita daga hannun yan sanda ba daga kai harshi, dara ce taci gida kawai, kakoma kayi tunani ka sake nazari waze iya aikata maka haka, kasan innice nayi maka wannan aikin bazanji tsoron gayamaka bako? tunda irin tarbar danasamu daga gurinka kenan shikenan nagode ni na tafi, amma kakiyaye shiga hanyata, kasanni ban da kyau"
tanagama fadin haka ta juya tanufi motarta, yayi Yunkurin ya biyota amma ta tashi motar tabar gurin.
Yauma Jalila ba bacci, saboda tashin hankali da damuwa, se addu'a da takeyi, Nana kam ta gaji da tambayar ta meyake damunta. Da Asuba Jalila tai wanka tai salla ta shiga kitchen ta dama kunun gyda da dankalin turawa, karfe bakwai tagama shiryawa tsaf tana jiran Jawwad, Nana tai juyi akan gado ta kalli Jalila
"wai shirin mekikeyi hakane?"
"Asibiti zan raka Yaya Jawwad muduba Yaya Jalal" dan zaro ido Nana tayi, sannan tai murmushi
"Yaukuma da kanki kike cewa Yaya Jalal" takuma murmushi tace "Zanso inje nima induba shi, amma wallahi bacci nakeji, kuyi masa sannu in an sallamoshi naje in duba shi, kokuma in Maama zata semuje tare" Nana ta juya tashige bargo, Jalila na nan zaune, wajejen karfe takwas Jawwad yakirata a waya yace tafito su tafi, da sauri ta dakko kwandon kayan Abincin ta fito, Jawwad ya kalleta yace "Baby hada hidima haka, Abinci kika mana"
"Eh Yaya, koba kwaso?"
"haba mu mun isa, taho mutafi" ta shiga mota suka tafi, suna zuwa Jawwad yaimata jagora har dakin da Jalal yake, suka tura kofa suka shiga ta tsorata da ganin Jalal, yana kwance akan gado dagashi se dogon wando da singlet, yanata sauke numfashi a hankali, ya rame matuka gashi yayi duhu se dogon hancinsa yakara fitowa sosai, drip yana shiga jikinsa a hankali, hawaye yafara bin idon Jalila a ranta tace "idan har Jalal ya mutu ina da alhaki, ninakara assasa bata masa rai"
Jawwad ya dora hannunsa akan gadon da Jalal yake ya sunkuyar da kai, Yana dago ido Jalila taga kwalla a kwance a idonsa
"Yaya karka karaya mana, zeji sauki" Jawwad yai murmushi yace "Baby Jalal wani bangarene na rayuwata, inajinsa a raina kaman wani bangare na rayuwata, banason rasashi, banason wani abu yasameshi da inada yadda zanyi in kawar masa da damuwarsa, danayi amma ba yadda na iya kaddara tariga fata, haka Allah ya kaddara masa, ina fatan Allah ya musanya masa da kyakyawar kaddara " Jawwad yai ajiyar zuciya yace "Bari inje gurin doctor inji meze ce, kizauna anan anjima su Ilham zasuzo nima yanzu zan dawo, inkuma ya tashi kafin in dawo kikirani beci Abinci ba" ta jinjina kai, Jawwad yafita yabar dakin guri ta samu ta zauna akan kujerar gaban gadon Jalal, Hawaye tacigaba da sharewa lokaci zuwa lokaci tana dorawa kanta alhakin wannan rashin lafiyar da yake,
A hankali Jalal yai juyi, da sauri ta goge idonta ta tsaya tana kallonsa bude idonsa yayi a hankali ya saukesu akan Jalila dake goge hawaye, kura mata ido yayi ko kyaftawa ba yayi.


Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
Chapter 23 · 0% Book details