← Book details Zumah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 9

Sashe 9

Zumah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A gidan megari kuwa, kowa na faɗar, albarkacin bakinshi domin kuwa ba wanda kuluwa bata addaba ba. Suna hangosu tafe tana kuka jadda na masifa gawani kyakkyawan saurayi ya taso ƙeyarta gaba suka fara murna. Domin dayawa sun ɗauka wani abun ne tayiwa Umar yadda suka ganshi tafe kamar wani zaki. Yana isowa ya durƙusarda ita gaban me gari kafin ya tsugunna cikin girmamawa yace "ranka ya daɗe ance kana neman ƙanwata ne shiyasa nakawota dakaina, naji ko wani abinne yafaru. "Tofa ƙanwarka ta ina? Da alaƙarme? Kuluwar jadda ce ƙanwar taka sabida tsabagen renin hankali. Cewar wani saurayi dake tsaye gefe yana gatsar rake. Ɗagowa kawai Umar yayi ya kalleshi sekuma yamaida dubanshi gun me gari yace "ranka yadaɗe koba kaine kake nemantaba? Naga ina magana kamin shiru, yafaɗa aɗan ƙufule domin har yafara gundura da taugonon. "Humma nine ɗan samari wato ina duba girman kuluwa ne dakuma girmar ta asar datayi, yanzu fisabilillahi wannan yarinyar dudu nawa take? Amma itace da wannan ta asar har aka abun kamar zata tada gari. Cikin takaici sarkin fada yace, "humm ai ɓarnar kuluwa sedai Allah ya kyauta kawai amma abinta ya zama annoba....cikin tsawa Umar yace wai mitayine haka? Ku gaya mana koma minene mana, amma kun satasu agaba da wani zantuka na shirme. "Relax Umar mana relax please, cewar canal Yusuf yana riƙo hannun Umar ɗin domin shima sunfara bashi haushi wannan zantukan dasukeyi. Jadda kuwa tacika tayi fam abinda yasa tayi shiru batayi magana ba gudun batasan abinda kuluwa tayiba kuma batasan hukuncin da megari zeyiba. "Hattaradai yaro ka iya bakinka kafin mu gyara maka zama anan kasan ko agaban waye kake, me garine dakansa basawaba, cewar wani zagi dake wurin yana mazurai. Wani mugun kallo Umar ya watsa mishi amma bece komaiba domin Yusuf ya hanashi. Limanne yayi gyaran murya kana yace "yaro ƙarar wannan yarinyar kuluwa aka kawo nan gaban megari, mutanen gari kowa da abinda yazo dashi, amma bara kaji kaɗan daga ciki. Anan liman yabashi labarin duk abinda kuluwa tayi, tabbas wannan abin yagirgizasu dagashi har canal Yusuf, domin tayi ta addanci dayawa. Liman na gama magana megari ya ɗora da cewar "to ina fatar kunji laifin data aikata, sabida haka bayanke hukuncin miƙawa hukuma ita abirni domin abiwa waƴannan bayin Allah hakkinsu, kai dogari maza kusakata gaba har birni kumiƙawa hukuma ita kuce injini ni megarin shuwarim nace ahukuntata dede da laifinta. Ah haf ai koma minene akayiwa wannan yarinya ba'ayi maganinta ba wlh yarinya tazama annoba acikin gari ta koma kamar haifar rana, shegiya jarababbiyar yarinya, cewar sarkin fada. Afusace Umar yamiƙe tare da riƙo hannunta yace "shikenan duka munji ƙorafinku kuma zamuyiwa tufkar hanci, duk wanda tayiwa ɓarna ko wani ta adi zamu biyashi kana zan tafi da ita base ankaita ko inaba. Cikin tijara saurayin ɗazu yace "zakaje da ita ina? Ohh yanzu naganoka kace kai kwartonta ne shine zaka bige dacewa wani yayanta bayan tun haifar kuluwa muna nan da ita agari bamu santa da wani yayaba, kaide kace zakuje kaɗora daga inda ka tsaya, to bamu yadda ba wlh dudda kuwa takoma kotifar gardawa ayanz...ɗosss sukaji ƙarar bindiga lokaci ɗaya batare da sunsan a ina akayi harbinba kafin ihun wannan saurayin yakaraɗe ilahirin wurin yafaɗi ƙasa wanwar riƙeda ƙafa yana rusa uban ihu...cikin faɗa canal Yusuf yace "what subahanallah miyasa Ka harbeshi Umar? Kalli kaga yadda yake zubda jinifa. "Yagodewa Allah da ƙafarsa na harba ba kansa na fasaba yaa Yusuf kuma wlh sena nuna masa shiba shegen kowa bane, dan ubanka ƙanwata zaka aibata agabana sabida tsabar iskanci kuma wai dani zaka alaƙanta iskancin naka? Hum zakaci ubanka wlh, kusaka minshi mota captain., yafaɗa cikin bada umurni wa sojojin dasuka biyosunan domin wasu sunbisu faruk asibiti, "Okey sir suka amsa mishi suna ɗaukar wannan saurayin. Kallon megari yayi kana tace I'm Marcial Umar khamis damsak, nine Zan yanke hukuncin daya dace da ahalina bakuba, kana kusani ahalin khamis damsak sunfi ƙarfin tozalci a ko ina cikin faɗin duniya bawai iya wannan ƙauyenba dako sunanshi babu acikin tasurar Nigeria. Yana gama faɗar hakan yafigi hannun kuluwa kawai yajefata a mota shima ya shiga. Ajiyar zuciya canal Yusuf yasauke kafin ya shiga bawa me gari haƙuri akan abinda Umar yayi dudda shima yaji haushin abinda sukayi sosai, kafin ya cire kuɗi kusan rafa huɗu da dubu dubu ya ajiye masu kana yariƙa hannun jadda itama yasakata amotar Shima ya shiga sukabi bayansu Umar domin tuni motar daya shiga ta ɗaga, jadda kam shiru kawai tayi tanajin kamar zuciyarta zata buga sabida yadda akaci mutuncin ahalinta kuma agabanta amma bata ce komaiba. Suna ɗaukar hanya wayar canal yusuf ta ɗauki ƙara, cikin sauri ya ɗaga ganin me kiranshi, wato FARHAN. "Hello My bro good morning. Shiru yayi kamar baze amsa ba kusan minti biyar kafin yace "morning too Yusuf how is he's feeling now? "Alhmdllh but suna hospital tareda faruk yanzu zamu samesu acan mun tsaya kashe wani case ne...shiru babban yaya yayi bece komaiba hakan yasa Yusuf yagane yana neman ƙarin bayani ne, labarin abinda yafaru ya shiga bashi from AtoZ. Har Yusuf yagama bece komaiba, harya fidda ran zeyi magana kana yaci ɗaukar muryarshi yana cewa "Do not leave her in town, take her to Abuja, I am also on my way, our plane is leaving in 10 minutes. "Okay Farhan ai sunwuce tun ɗazu Umar ya tafi da ita, yanzu nima gani tareda jadda. Bece komaiba illa yanke wayar da yayi.........acan cikin motar su Umar kuwa, tunda suka shiga kuluwa kuka takeyi har suka isa asibiti, buɗewa yayi yafito, kana yadaka mata tsawa yace ta fito. Hakan tafito tana tunzura baki, gaba yayi tabishi baya, tare da buɗe baki cikin tsiwa tace "wlh bashi kaci kuma seka biya.. da sauri Umar yajuyo yana kallonta cikin rashin ɗaukar reni yace....!

To alhmdllh
END OF BOOK 1

semun haɗu a book 2 wanda yake paid ne in sha Allah. Idan kinaso kibiya kuɗinki kikaranta cikin salama.

Book ɗin ZUMAH paid book ne 1k kacal 👌zaki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneypoint sha'awanatu kasim. Idan kuma a Niger kike zaki turawa anan 👉 +2347037092176 My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp 🙏

Autar alheri✍️
Chapter 9 · 0% Book details