CHAPTER 16
Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel · about 6 min read
بسم الله الرحمن الرحيم.
Sanu a hankali zuciyar Fateema Abbas ta fara ƙeƙashewa, ta koyi mugunta da son abin duniya kamar mijinta Lawan, yanzu wani lokacin atare suke gudanar da aiki idan oganninshi sun saka shi, ta na yawan yiwa Anty Wasila mahaifiyar Fateema Abbas, yanzu Sadiya da Fateema sun sake ɗinkewa sun zama abokai kamar can baya, musamman da yanzu Fateema kan siyi ƴan abubuwa na sha'awa ta kaiwa Miemie a matsayin kyauta, ance me ɗa wawa, nanda nan Sadiya ta sake amincewa da Fateema ɗari bisa ɗari, ana ahaka ne Fateema ta fuskanci Sadiya nada shigar wani cikin, batai ƙasa a gwuiwa ba ta sanar da mijinta Lawan, inda Lawan ya garzaya ya sanarda ubannin gidanshi, nan suka ɗunguma suka tafi wajen boka, boka ya sake tabbatar musu da wannan damar ce suka daɗe su na jira, nan ya basu umurnin su je su jira har ranar da za'a haihu, su tabbatar bayan kwana uku sun kawar da jinjirin daga duniya tare da ɗayar yarinyar da aka haifa wato Miemie.
Kyautar maƙudan kuɗaɗe suka yiwa Lawan akan ya san ta yanda za'ayi ya salwantar da abin da za'a haifa, ba tare da sanin oganinsa ba ya bawa Fateema Abbas akan ta tabbatar da ta sato jinjirar Sadiya Abbas ko ta kashe jinjirar, abinka da ido a nera nan da nan Fateema tai na'am da zance ta kuma amshe kuɗaɗen.
Zuciyar Fateema Abbas ta fara karyewa ne lokacin da tai arba da Alhaji Umar ɗauke da kyakkyawar jinjirar da matarshi Sadiya ta haifa ma shi, farin cikin da bata taɓa gani akan fuskarshi ba shi ta gani, yanda yake ririta jinjirar kaɗai ya isa ka gane cewa lallai ƙauna marar adadi ta wanzu ga wannan uban.
Karo na farko da jikin Fateema Abbas yai sanyi, sai ta ji zuciyarta ta karaya, kasancewar haryanzu Allah bai bata haihuwa ba, gashi kuma Allah ya ɗora ma ta son yara, idan taga anyiwa Miemie kwalliya kamar ta sace yarinyar haka take ji.
Cikin sanyin jiki ta zauna tare da gaisar da Sadiya da jiki, gaida Alhaji Umar ta yi tare da satar kallon jinjirar wacce idan ba gizo idonta ke ma ta gani ta yi kamar jinjirar ta saki murmushi, miƙa hannu ta yi akan ya bata jinjirar, sai da yayi ɗan jim sannan ya miƙa ma ta, amma kuma bai daina ziro hannu ba yana ma ta wasa, tunda jinjirar ta shiga hannun Fateema Abbas, zuciyarta ta tsinke, ta sauke makaman yaƙinta tare da ɗaukar ɗamarar tseratar da rayuwarsu, ranar sukuku ta koma gidanta, jikinta duk a mace, sai ta ji bazata iya akinba amma kuma ba zata nunawa Lawan ba, zata sake sabon tsari wajen ganin ba'a salwantar da rayukanda basu da alhakin kowa akansu, tafi tausayawa Miemie wacce tasan daɗin iyaye kan jinjirar, sabon shiri ta sake ta yanda zata taimakawa ƙawarta ba tare da Lawan sun gano ta ba, asirin da Lawan yai ma ta yanzu ya karye shiyasa take danasanin aurenshi, har gobe ta na mamaki akan yanda ta aureshi bayan sam bata sonshi ita Sir Umar ɗinsu take so.
BAYAN KWANA UKU.
Gudu take tsalawa akan tinti ta na yi tana kallon jinjirar da ke kwance ta na wasa da hannayenta, hawaye na kwara a idonta take faɗin. "Ki yafe min ƙawata bazan iya zuba ido ina kallo a raba ƴarki da rayuwarta ba, hakan da zanyi shine daidai, zan tseratar da ƴarki in nisanta ta daga gareki, hakan ne kaɗai zai ba ƴarki damar rayuwa cikin salama."
Saida tabar cikin mutane sanan ta fara shiga cikin daji sannan ta yi kira a wayarta, babu jimawa sai ga wani mutum sanye cikin jemamun kaya, cikin sauti ta ɗauko wa ta baƙar jaka sannan ta fito, sai da ta tabbatar da babu me ganinsu sannan ta buɗe jakar, kuɗi ne shaƙare a cikin jakar nan ta bawa mutum tare da bude ma shi inda ta aje jinjirar sannan ya ɗauketa, harta tada mota za ta tafi sai kuma ta juyo ta kalli mutumin ta na faɗin.
"Ka tabbatar da ka bar garinan yau ba sai gobe ba, sannan kuma idan kana buƙatar wani abu ka kira layin dana baka, sunanta MUBARAKA amma naji mahaifinta na kiranta da MUBEENAH, idan kun isa legos ɗin ka kira ni zan haɗa ka wanda zai samo muku masauki." ta na gama faɗin hakan ta juya tabar wajen da mugun gudu, akan haryar komawarta ne ta kira Lawan ta sanar da shi duk inda yake yanzu ya kasance tare da Alhaji Umar ta aiwatar da aiki na farko yanzu za ta gama na biyu.
Cikin sauri Lawan ya shiga motar Alhaji Umar da ya tada zai je shopping, bayan sun gaisa ne ya nuna zai raka shi inda zasu je, babu musu ya amince dan yana cikin farin ciki yanzu da kowa fira yake yana faɗar yanda yake bala'in son jinjirar da aka haifa masa, cikin farin ciki yake zuzuta kyawun yarinyar harma ya nuna photon ta, su na tafiya su na firar yanda taron sunan zai ƙayatar, yayinda Lawan ke murmushin ƙeta a zuciyarsa, a fili kuma ya na ƙara bawa abokin nashi shawarwari akan yanda za'ayi gagarumin taro, da wannan damar Fateema Abbas tai amfani wajen zuwa ta ɗauko Miemie daga school, kai tsaye ta nufi hanyar ƙauyukan da ke kan hanyar Abuja, wani ƙauye ta samu ta tsaya akan hanyar shiga garin, babu jimawa wani mutum ya zo da mashin zai shiga garin, nan ta tare shi tare da bashi jaka cike da kuɗi ta ce so take yakai Miemie gidan me gari yace akan hanya ya tsinceta anyi accodent, mota da mutanen cikinta duk sun ƙone, dama mutumin mayen kuɗi ne, nan take ya amince da buƙatar Fateema Abbas ya ɗauki Miemie ya shiga da ita cikinngarin, gudun samun matsala sai ta kunnawa motarta wuta ta taka a ƙafa harta fita bakin hanya ta samu ɗan mashin ya kaita inda zata samu motar shiga garin Abuja.
CI GABAN LABARI
Fateema Abbas na zuwa daidai nan a tunaninta ta fashe da matsanancin kuka har jijjiga jikinta ke yi.
Yayinda Lawan shima ya tsaya a daidai nan sai ya fara zarya ya na tunanin kodai amanarshi Fateema Abbas ta yi bata kashe ƴaƴan Alhaji Umar ba, sai yanzu ya tuna da ai bega gawar yaran da idonshi ba, kiranshi tai akan ta gama aiki, shi kuma ya sanar da su Muhammad Bello daga nan su kuma suka fara aikn da boka ya saka basu.
LEGOS.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK TWO