← Book details Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 16

CHAPTER 15

Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel · about 4 min read

بسم الله الرحمن الرحيم.

Sosai Alhaji Abbas ya jinjinawa ƙoƙarin da sirinkinshi sir Umar ya yi wajen samawar da Malam shago, tun tuni Alhaji Abbas ke fafatukar sama ma shi shagon amma sai hidimomi suka shan kanshi, takanas Alhaji Abbas ya je har gidan mahaifin sir Umar Alhaji Ibrahim yai godiyar ban girma akan babban abin alkairin da ɗansa ya yi, hannu bibiyu Alhaji Ibrahim ya tarbi sirikin ɗan nashi.

Bayan biki Sir Umar ya aje aikin koyarwa ya tsunduma tsama-tsamo cikin harkar manya-manyan kasuwanci da taimakon mahaifinsa, a gefe guda kuma ya na tare da Lawan yanda ya zama abokinshi ta ƙarfi da yaji, dan dole yake saka Lawan ɗin a harkokinsa saboda yanda yake shige masa kuma yana yawan bashi shawarwari akan business da sauran harkoki, Muhammad Bello najin daɗin yanda Lawan ke gudanar mashi da aiyukan da yake sakashi, ganin irin kwazon da yake ya saka ya gabatar da shi wajen abokanshi su Ale Dikko Zaki da sauran manyan abokanan shi da suke gudanar da harƙalloli ta ƙarƙashin ƙasa.

Lawan ya fara fantamawa da manyan kuɗaɗe da kuma motoci, dan yanzu sosai yake ɗaukar kasada ko wace iri ce, aiki na biyu da ya gudanarwa su Ale Dikko shine kisan kai, wani ɗan kasuwa da yaƙi basu goyon baya akan buƙatar da suka gabatar ma shi, shine suka gwada Lawan ta hanyar bashi aikin sheƙe mutumin, aiko babu ko ɗar Lawan ya haikewa mutum har sai da ya rabashi da duniya, sannan ya kawar da suk wa ta sheda da zata iya fallasa shi.

Zaman lafiya gami da zazzafar soyayya Sadiya da Umar suke gudanarwa, Sadiya bata rufe shekara ɗaya ba ta samu ciki, inda bayan watanni tara ta sintilo kyakkyawar ƴarta mace ta ci suna Maryam su na kiranta da Miemie, sosai sir Umar yai farin ciki da samun ƙaruwar, bayan haihuwar maryam da watanni kaɗan ƙofafin arziƙi suka sake buɗewa sir Umar, inda yake gudanar da kasuwanci me tsafta anan gida Nigeria da sauran ƙasashen ƙetare, babban abin da ya sake haskaka tauraron sir Umar shine sauki da kayanshi suke da shi, indai daga compnynshi abu ya fito to za'a sameshi tsaftatacce me kyau gami da sassauƙan farashi, ganin yanda lokaci ɗaya sunan Sir Umar ya zagaye Nigeria ya saka su Muhammad Bello juyowa takanshi, dan sun nemi tattaunawa tare da shi akan ya shiga cikinsu su dinga gudanar da haramtattun harƙallolin kasuwanci a tare, amma ya taka musu burki, bazama sukai wajen malama da bokaye akan a disashe tauraron Sir Umar, amma duk inda suka je maganar ɗaya ce, babu wanda zai iya dakushe hasken da ke tare da shi, nan suka shiga neman rayuwarshi ta mabanbanta hanyoyi, amma sai Allah ya ku ɓutar da shi, ganin haka sai suka koma tada wuta ga companys ɗinshi da shaguna, sosai sukai ma shi ɓarna amma abin mamaki, a maimakon ya durƙushe kamar yanda suke so, sai ya daɗa yin sama, inda manyan jiga jigan ƴan kasuwa suka tallafa mashi ya sake bunƙasa kasuwancinshi, harma ya zarce na baya, ga ƙananun customers da suka dinga tayashi da addu'a domin faɗuwarshi tasu ce suma, tun wajenshi suke samun kaya a farashi mai sauki da rahusa, sake bazama su Muhammad Bello sukai wajen manyan bokaye inda suka samo wani boka da zai musu aiki akan sir Umar wanda yanzu ya zama Alhaji, amma yace ba yanzu aikin zai yuwu ba, suɗan jira kaɗan zuwa wasu ƴan shekaru da matarshi zata sake haihuwa, zata haifo yarinya ƴar baiwa wacce taurarinta zasuyi daidai danashi, ita ce zata zamo rauninshi, da ƙarfin soyayyar da zai mata ne zasuyi amfani wajen durƙusar da shi, sunji daɗin wannan bayani sosai, inda suka sake saka Lawan aiki akaro na biyu yasan ta yanda zai shiga jikin matar Alhaji Umar wato Sadiya, a wannan karon yai amfani da Fateema Abbas ne ta hanyar auenta badan tana son shi ba, ta amince da shi ne da ƙarfin asirin da yayi ma ta, bayan aurensu ne ya sake haɗa ta da Sadiya suka koma ƙawancensu, sam Fateema Abbas batason Sadiya yanzu musamman yanda ta ga irin daular da ta ke rayuwa a ciki, ga kyakkyawar ƴarta gwanin sha'awa sannan Alhaji Umar kan ririrta matarshi a gaban kowa, hakan ya saka ta sake ƙullatar Sadiyar a zuci, sannan kuma zugarda Lawan ke ma ta akan yanda yanzu Sadiya ke nuna ita ɗin matar manya ce taf ƙarfin Fateemar ya sanya ta amince da aikin da yace zai bata sannan kuma za ta samu maƙuden kuɗaɗen da harta gama rayuwa ba za iya ƙarar da su, nanfa Fateema Abbas ta sake ruɗewa dan akwaita dason abin duniya kamar yanda ta tashi ta ga uwarta Wasila na martaba kuɗi.....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘


WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.


MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK TWO
Chapter 14 · 0% Book details