CHAPTER 13
Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel · about 9 min read
بسم الله الرحمن الرحيم
Sauke wayar Sadiya ta yi, tana jin wani ƙarfin gangar jiki da zuciya na zuwa ma ta lokaci ɗaya, sai ta tashi zumbur tare da kama hanun Alhaji Umar ta nufi toilet da shi, alwala ta ɗauro shima ta taimaka ma shi yayo alwalar suka fito a tare, sallaya ta shimfiɗa musu, nan suka shiga jero salloli babu ƙaƙƙautawa, yayinda take sauke dukkan buƙatunta idan tai sujjada, duka rauninta da gazawa take tattarowa ta roƙi ubangiji ya yaye musu wannan wahalhalun rayuwar da suke fuskata, ya sauƙaƙa musu ƙaddarorin da ke sake kutsowa cikin rayuwarsu.
AGEGE
ABBA
Tun ranar da Umma ta satarwa Abba kuɗi ya canza salo, yanzu baya zama da kuɗi a jikinshi, banki ya je ya buɗe account har guda uku, ya zuba rabi da kwatar kuɗin, sannan ya bazama wajen malamai ya na neman fassarar mafarkan da suka addabi rayuwarshi, muddin zai kwanta ya rufe ido da sunan barci, to sai yayi mafarki akaina, kuma ya bada sunan Mama akan a karkato da hankalinta gareshi, dan yanzu ta zage sai ɗibar albarka ta ke ma shi, bata ragawa kowa ba yanzu, bata barin bashin magana, sannan kuma ya na so a rufe mashi bakin Umma aka kuɗin da yake so ya bawa Mama wanda Alhaji Abdallah me gwalagwalai ya umurta akan a bata, duk da ba duka zai bata ba amma yasan dole za'ayi rigima da Umma akan kuɗin.
Ranshi fes ya dawo gida ya ci gaba da gudanar da sabgogin gabanshi, yau dai shiru kukejin bakin Umma, ko ƴan kudaɗen da ake damfarar Abba ba'a amsa ba, sai faman kaiwa da komowa take ta na shafce gumi, aikin girki ta ke, amma idan kukaga zanin jikinta kamar me yin aikin ƙuli zanin dawan-dawan da shi kamar tsuman sauke tukunya, takalmi gamin bauta ne ta saka a ƙafarta, sai faman zarya ta ke daga ɗaki zuwa inda ake girki, duk bayan mintuna uku sai kaga ta kamo haɓar zani ta fyace majina, sai ta buɗa tukunya ta jujjuya sannan ta rufe ta koma ɗaki.
Mama ma yau ta na ɗaki zamanta ta ci kwalliya tana girki a gas ɗin sai ƙamshi ke tashi gwanin daɗi, yanzu Mama idan ba alwala ko shiga bayi ba ba ta fiye fitowa waje ta zaunaba, tafi zamanta a ɗaki ita kaɗai abin ta, duk wanda tsautsayi ya saka yai ma ta ba daidai ba zai fuskanci ɓacin rai, bata shayin kowa yanzu ta zama masifaffiyar ƙarfi da yaji.
ABUJA LAWAN.
Zaune ya ke a gaban wani rami, hannunshi a zura tare ɗauko wa ta ƴar tsana wacce aka ɗaure ƙirjinta da wa ta yar tsoka, jikin tsokar an caccaka allurai, wani jini ya ɗauko cikin ƴar ruba ya shiga kwararawa a jikin ƴar tsanar ya na diga cikin ramin, maida ƴar tsanar yayi tare da mayarda ƙasa ya rufe sannan ya maida grass carpet a wajen kamar ba'ayi komi ba, kakkaɓe hannunsa ya yi tare da zuwa gaban tap ya wanke tsa sannan ya fice daga gardeng ɗin.
Manyan mutane ne zaune a babban parlon su uku su na, ko wannensu da ƙaton tunbi a gaba, ga gemunansu duk farin gashi alamar anfara kwana biyu, fuskokinsu a murtuke babu fara'a ko kaɗan.
"Barkanku da ƙarasowa manyan giwaye, yanzu nike...."
"Dakata Lawan, ba zuwa jin tatsuniyar da ka saba shirya manah ya kawomu nan ba, zuwa muka yi jin muye dalilinda yasa baka cika aikin da muka umurceka da shi ba tun shekaru ashirin da ɗaya da suka shuɗe, mufa ba yara bane da zaka zauna kana tsara mu da ƙarairaki, munzo ne muji ta inda ka bari aka samu matsala." Ɗaya daga cikinsu ya faɗi tare da cafar tufa ya gatsa a baki babu ko basmala.
"Muƙuttt" Lawan ya haɗe yawu me kauri, hasashe ya ke wane aiki ne nasu bai cika ba, tun da har suka yo tattaki suka suka zo har inda yake a daidai wannan lokacin babu sanarwa yasan ƙiyamarshi na daf da tsayawa, sake bin su da idanu yayi yana ƙare masu kallo a zuciyarshi yana furta.
"Ale Dikko Zakin fama, Alhaji Balarabe Basani ba sabo, Alhaji Mas'ud Cinnaka bakasan na gida ba, sai na ƙarshensu oga kwata-kwata Alhaji Muhammad Bello Kuraye, manyan mutanenda ake damawa da su a fannin siyaya da kasuwanci, mutanen da al'umma ke yiwa kallon shuwagabanni na kwarai, har talaka na yi musu laƙani da baya goya marayu, saboda yanda suke hidimtawa jama'a da aljihunansu, sai de kash, su ɗin kura ne lulluɓe da fatar akuya, sun kasance masu taka muhimmiyar rawa wajen ƙuntatawa talakawa ta ƙarƙashin ƙasa, suɗin taurarine masu wutsiya ganinsu sam babu alkairi.
Saita kanshi ya yi tare da sake sunkui da kai ya aro bangon nutsuwa ya yafawa kanshi, sannan ya rausayar da murya yana faɗin.
"Kuyi min aikin gafara, nidai a iya sanina ban bar ko ɗaya daga cikin ayyukan da kuka taɓa saka ni, niɗin tamkar ƙasƙantacen bawa ne a gabanku, na kasance ina jiran umurninku dan biyanku akan halaccin da kuka taɓa yimin, kuyimin aikin gafara saboda ni ɗan Adam ne kuma ajazi, ko zan iya sanin aikin dana kuskure akanshi idan da hali in gyara shi yanzu-yanzu."
Wa ta dalleliyar baƙar harare Ake Dikko ya dallawa Lawan, yana jin kamar ya murɗe wuyanshi ya raba shi da numfashinsa, sabosa tsabar fusata da abin da ya yi musu.
"Shin ko kasan cewa ƴaƴan tsohon amininka Alhaji Umar su na nan raye a duniya, shin ko kasan cewa rayuwa da burikanmu su na dab da rushewa ta sanadiyyar sakacinka, shin tayaya yaranda ka tabbatar manah d sun mutu suke a raye, ta ina wanda ya mutu zai dawo, shin ko za ka iya faɗa mana ta yanda akai haka ta faru." Cewar oga kwata-kwata Muhammad Bello.
Wani irin ƙugin tashin hankali ne cikin Lawan ya yi, yayin da idanuwansa suka firfito waje cike da tashin hankali gami da firgici, zufa ce ta shiga karyo ma shi daga cikin kai ta na tsiyaya har cikin rigarshi, sau bakwai ya na buɗe baki zai yi magana amma sai maganar ta maƙale ta gagara fitowa sakamakon numfashinshi da ke barazanar ɗaukewa.
Babu ko tausayi a fuskokinsu suka shiga zayyano ma shi kalolin uƙuba da tashin hankalin da zai fuskanta matsawar bincike ya sake tabbatar musu ƴaƴan Alhaji Umar su na raye, tsallake shi sukayi ba tare da ko tausayi ba suka fice suka barshi a halin firgici da ɗimauta.
Zarya ya ke tsakanin bango zuwa bango, ya na lissafa ta yanda za'ayi ace yaranda Fatima Abbas ta tabbatar masa da mutuwarsu za'ace su na raye.
"Wait, shin wai ma wacece Fatima Abbas, kuma wacece Sadiya matar Alhaji Umar."
Ya jefawa kanshi tambayar tare da tsallakawa tunanin abubuwanda suka shuɗe acan baya.
Alhaji Abbas ɗan kasuwa ne babba, ya na kasuwancin siminti da buloluwa, tun farko ya fara ne da gina gidan bulon ƙasa, kafin daga bisani zamani ya zo aka fara yin ginin bulon siminti, a wancan lokacin za'a saka Abbas cikin jerin ƴan kasuwa masu faɗa a ji, babu inda simintin Abbas bai zagayaba a Nigeria, yayi aure tun ƙuruciya inda akai masa auren haɗi shi da ƴar uwarsa Hadiza, kasancewa Hasiza nutsatsiyar kamilar yarinya ya saka Abbas fara sonta, dan shi yana son mace me kamun kai da kunya, bayan aurensu sun gina rayuwa me tsari dabin turban addinin musulinci, su na girmama junansu sosai hakan ya sake ƙarfafa soyayyar tsakaninsu ta rikiɗe ta koma zazzafar ƙauna, sun ɗauki lokaci basu samu albarkar aure ba wato haihuwa inda iyayen Hadiza da kansu suka matsa akan ya ƙara aure gudun kar ace matsalar daga Hadiza ne, da farko yaso yai tiejiya amma da suka bashi kwararan hujjoji sai ai na'am da hakan ya kuma basu wuƙa da nama akan su zaɓa ma shi wacce ta dace, sunji daɗin karamcin da yayi musu hakan yasaka mahaifiyar Hadiza ta nema ma shi auren ƙanwar abiyar zamanta, itama ta na da nutsuwa sosai ga girmama mutane sannan ta na da addini dan kusan tare suka taso da Hadiza, ba'awani ɗauki lokaci ba aka saka ranar aure Abbas da Karima, inda Hadiza ta shiga sahun gaba wajen masu murnan haɗin wannan auren da iyayenta sukai, bayan anyi auren Karima da Abbas suka haɗe kansu da Hadiza suka samar sa wanzajen farin ciki a gidan Abbas.
Bayan shekara ɗaya da aure Karima ta haifawa Abbas ƴa mace, wace taci sunan mahaifiyar hadiza ana Fateema ana kiranta da Inno, Hadizama ba'aɗauki lokaciba ta santalo ƴan biyu kyawawan gaske waɗanda suka biyo ta, tsakanin Karima da Abbas aka rasa gane wanne yafi farin ciki, dan su suka raini ƴaƴan iyakar Hadiza da su shayarwa.
Rayuwa na ƙara gaba Abbas na sake samun dukiya da arziƙi me tarin yawa, inda ya baro garin Katsina ya dawo Kano da zama yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hadiza nada yara uku yan biyu Hassan da Husaini sai gambonsu Aama'u, ita kuma Karima tun haihuwar Fatima ba ta sake samun haihuwa ba, bayan an yayeta yayar Karima Wasila ta ɗauketa daga yaye ta riƙe ta ce tayi ƴa, bayan dawowarsu kano da shekara biyu Hadiza ta haifo sntaleliyar ƴar auta, wace ta biyo ainahin kamanin maaifinta Abbas, fara me dogon hanci da manyan idanuwa haɗi da sisilkan baƙin gashi, aka saka mata suna Halimatus Sadiya, shaƙuwa me tsanani ce ta shiga tsakanin Sadiya da mahaifinta, inda ya je ririta ta, sosai Karima ke nunawa Sadiya soyayya ta gaske, komi ta samu Sadiya ahankali ta janyota tadawo da ita ɗakinta da kwana.
Shekaru sun ja da dama, yanzu Alhaji Abbas ya zama babban mutum, kuma ɗan kasuwa wanda ake damawa da shi ta harkar kasuwanci, Allah yayiwa Hassan ɗanshi rasuwa sai Husaini da sadiya da Asma'u ne kawai ƴaƴansa, tuni ya barwa Anty Wasila Fatima kyauta halak malak saboda Allah bai basu haihuwaba ita da mijinta, Karima kuma bata ce komi ba akan hakan dan yanzu ida ba sa ni kaiba ba zaka ce ba ita ta haifi Sadiya da Asma'u ba.
Hussaini yayan Sadiya ya taso d son ilimin islamic, inda ya gaji Kakanshi Malam Iro ta fanin sanin magungunan gargajiya da likitanci a musulunci, sannan ya na tare da baiwar gane sihiri ko sammu, wannan yasaka ace kiranshi da Malam, Malam na matuƙar ƙaunar Sadiya, bayason duk wani abu wanda zai ɓata ma ta rai, idan ka ji hayaniyarshi to akan an taɓa Sadiya ne.
Sadiya ta gama secondary school Alhaji Abbas ya turata Zaria gidan ɗan uwa kuma babban abokinshi ta yi kadatu a A B U, a canne Sadiya ta haɗu da Fatima Abbas wacce itama tazo karatu a fanin kasuwanci, ba tare da sanin suɗin ƴan uwa ba ne suka ƙulla ƙawance, koda yaushe su na a tare, duk inda kaga Fatima to zaka ga Sadiya a wajen.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK TWO