CHAPTER 11
Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel · about 7 min read
بسم الله الرحمن الرحيم
Shirun da Fauzan ya yi min ya saka na tashi tare da rufe maganin nai tafiyata nabar shi, bai san zuciya na yi ba a tunaninshi wani abin zan je inyi, amma sai ya ji shiru ban dawo ba, har kowa ya hallara wajen yin azkar amma ni shiru babu ni babu alamuna, duk wanda ya zo sai ya tambayi ina naje yau ban fito ba, ko lafiya, amma sai Fauzan yai musu nuni da maganin da na kaɗa na bari, har suka gama azkar aka hau hira cikin raha da mutunta juna amma bandawo ba, Sulaima har dubo ɗakina ta yi danta duba ko wani abu ya tsaida ni amma ta je ta iske wayam babu kowa.
Ni kuma garding ɗin gidan na nufa wanda ya ke a bayan ɗakin Fauzan, can nai zamana ina shaƙar dadaɗar iskar wajen me saka nishaɗi, ina zaune a wajen na ji wa ta iska me tsananin sanyi ta taso, lumshe ido na yi ina shaƙar iskar da kyau ina kuma ƙanƙame jikina saboda sanyi.
A hankali na shiga buɗe idona amma mizan gani, sai na ganni a tsakiyar wani tanƙamemen teku wanda ke ɗauke da ruwa masu haske farare tas gwanin sha'awa, firfito da idanuwa na yi waje ina kallon ruwa kuma ina kallon kaina asaman wani dutse da ke tsakiyar ruwan, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya baibaye ni, kafin insan abin yi kawai naga wani abu dunƙulalle na fitowa ta ƙasan ruwan da nike, a hankali abin yayo sama gaba ɗaya sai kuma ya shiga shimfiɗe kanshi kamar tabarma, kafin in dawo daga suman mamakin da na yi sai kawai naga wani haske me fitar da tartsatsin ruwa na bayyana akan abin, kafin insan abin yi wa ta zankaɗeɗiyar kyakkyawar hallita fara sol ta bayyana ta cikin haske, zaunawa ta yi ta na fuskanta ta farar fuskarta faɗaɗe da murmushi, cikin wa ta irinyar murya me sanyin gaske ta ce da ni.
"MUBEENAH!!! INA MIKI BARKA DA ZUWA FADA TA, MI KIKE SO INSAKA A KAWO MIKI, KI FAƊI DUKKAN ABIN DA KIKE BUƘATA."
Ta yi maganar tartsatsin ruwa na fitowa daga bakinta.
"Wa,,,,,,wah,,,,wa,,wa,, wace,,,,wacece ke!!!!!!."
Na faɗi da ƙyar cikin inda-indar murya.
"NI CE SARAUNIYA ZUBUDIYYA, ƳAR SARKIN RUWA, NI ƊIN ME TAIMAKONKI CE, INDAI INA TARE S KE BABU MAHALUƘIN DA ZAI CUTAR DA KE, INA BAKI KARIYA DA ƘARFIN IKON UBANGIJI, INA TSAYA MA KI TA INDA BAKI TUNANI, NI ƊIN MAI TSANANIN TASAYINKI CE."
Ta faɗi ta na ziro dogon farin hannunta zuwa inda nike ta shafa kaina, nan take wani irin sanyi me tsayar da numfashi ya mamaye ilahirin jikina, sai na faɗi a sume, lokaci ɗaya ruwan ya ɓace ɓat, hakan yayi daidai da zuwan Mommy ita da masu aiki wajen ta na kwalla min kira, ɗan turus ta tsaya ganina a kwance ƙasa ina barci, a hankali ta duƙo kaina ta na kiran sunana.
"Mubeenah! ke Mubeenah lafiyarki ƙalau kuwa da za ki zo nan ki kwanta da sanyin marice."
Tai maganar ta na ƙoƙarin ɗago da ni ganin na buɗe idona, ji na yi kaina yamin nauyi sosai dan haka ban samu damar cewa komi ba na shiga kiciniyar miƙewa tsaye, ganin ina tangaɗi sai Mommy ta taimaka min ta ɗago da ni tare da taimaka min muka bar wajen.
Ɗakin Hajjo ta kai ni, sai da ta kwantar da ni akan gado ta rufamin blanked sannan ta fice ta barni.
Nannauyan barci ne ya ɗauke ni wanda ban farka ba sai ana gab da tada sallar magrib.
A hankali ya tura ƙofar ɗakin jin shirun ya yi yawa, sannan ya kira wayatshi amma bai ɗaga ba har sau biyar, tsayawa ya yi yana bin ɗakin da kallo ganin yanda yaɗan hargitse, ga wani wari marar dadi da ke tasowa, da sauri ya ƙarasa shigowa ya na faɗin.
"Innalillahi bee mi ke damunka haka, lafiya ƙalau fa muka rabu."
Yai maganar ya na kai hannunshi jikin Al-hassan, da mugun sauri ya janye hannun jin wani irin azababben zafi da ke fitowa daga jikin Hassan ɗin, bai daddara ba ya sake miƙa hannu da niyyar birkito da shi, amma sai ya sake jin wani irin zafi wanda yafi na farko, ɗago da hannu shi ya yi yana kallon yanda nan take hannun yai jazur alamar ƙonuwa, cike da firgici ya ke kallon ɗan uwan nashi sannan kuma ya kalli hanunshi, da wani irin gudu ya nufi wajen freezer ya buɗe ya shiga jido kwalaben ruwan sanyi, ɓalle murfin kwalaben ya shiga yi lokaci ɗaya ya shiga juyesu a jikin Hassan idonshi na tsiyayar hawaye, amma mi lokacin da ruwan ke sauka jikin Hassan wani irin "Cuuuuuuuuw" kake ji kamar anzuba ruwa a tafasashen mai.
Cike dafirgici Hussain ya ja da baya ya na fashewa da kuka me tsananin ƙarfi sannan ya tashi da mugun gudu ya fice daga ɗakin.
ABUJA.
"Wannan wace iriyar rayuwace, wannan zalincin yayi yawa, rashin iymanina bai kai nanba, ya kake so inyi da girman haƙƙin da ke ɗawainiya da ni, anya kuwa akwai sauran ɓirɓishin imani a zuciyarka Lawal, wallahi tallahi ka ji na rantse ba zan sake biye maka inyi abin da zai idasa tarwatsa ɗan ɓirɓishin farin cikin da ya ragemin ba, na gaji!!! na gaji Lawan, bazan iya ba."
Hamshaƙiyar matar ta faɗi ta na jijjiga kwalar rigar mutumin da ta shaƙe ta na masa magana cikin ihu fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye.
Wani makirin murmushi wanda ta kira da Lawan ya saki tare da kai ma ta shura da ƙafa, nan take ta faɗi akan ƙafafuwanta, duƙowa ya yi tare da tallabo haɓarta ya matse da ƙarfi, sannan ciki sanyin sauti ya ke faɗin.
"Fatima Abbas, dolene ki idasa abin da aka fara da ke, idan kin san ba za ki iya ba tun farko mi yasa kika fara, na daɗe ina maimaita maki cewa duk wanda ya shigo wannan aiki to babu fita, matsawar kuma kika matsa akan za ki bar aikin, to kema kin san makomarki, mutuwa ita ce makomarki Fatima Abbas." Ya faɗa tare da hankaɗa ta kan kujera sannan ya bita ya ɗora ƙafarshi ɗaya akan hannun kujerar fuskarshi a murtuke ya sake faɗin.
"Na baki awanni biyu rak, kar ki kuskura ki ƙara koda minti ɗaya akai, maza ki je ki haɗomin waɗancan tsinanun ƴaƴan da Sadiya ta sake haifawa Umar, alƙawari na yi akan muddin ina raye to jinin Sadiya da Umar ba zai taka a doran ƙasa ba, sai dai idan na mutu na bar wannan duniyar, kai wallahi koda mutuwa zanyi to sai na tabbatar da naga bayan Umar da dukkan dukiyar da ya tara, wannan alƙawarina ne."
Ya faɗa ya na murje yatsun hanun Fatima da ƙafarshi sannan na fice ya barta a wajen.
Wani irin kuka ta ke tare da gwara kanta da jikin ƙarfen da aka dasa dan sarƙafe labule, jini ne ya soma tsatsafowa daga goshinta amma sake gwara kan nata take ta na faɗin.
"Kaicona da wannan ƙazamar rayuwar wacce na zaɓawa kaina, Allah wadarar rayuwata, gashi na biyewa son zuciyata nayi abin da tsawon shekaru masu yawa ya hanani sakewa, haƙiƙa na aikata aikin dana sa ni wanda ya kulle ƙofofin farin cikina, Sadiya ki yafe min, haƙiƙa na cutar da rayuwarki cutarwa me muni, na azabtar da ke ta hanyar bin son zuciya d kyale-kyalen duniya, Allah ka ɗauki rayuwata kozan huta da wannan baƙar azabar wacce na janyowa kaina da waɗannan hannuwan nawa."
Tai maganar tana dukan kanta da hannayenta tare da sake fashewa da kuka wanda ya kusa saka numfashinta ɗaukewa.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK TWO