← Book details Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 16

CHAPTER 14

Zafin Wuta Part Two Complete Hausa Novel · about 11 min read

بسم الله الرحمن الرحيم

Kowane lactura yasan da zaman Fatima Abbas da Sadiya Abbas, kasancewarsu masu ƙoƙari da maida hankali sosai akan karatu, lacturas na alfahari da su sosai saboda ƙwazonsu.

A makaranta ne Sadiya ta haɗu da wani kyakkyawan matashi me ji da naira, ba dalibi bane lactura ne shima, shike ɗaukarsu a fanin kasuwanci, tun ranar da ya ɗora idanuwansa akan Sadiya matsananciyar ƙaunarta ta mamaye shi, sam baida sukuni sai yaga Sadiya, gashi ya rasa ta hanyar da zaibi wajen sanar da ita yana sonta, ganin zaiwa kanshi illa sai ya shirya takanas ya je har ƙofar shiga hostel ɗinsu ya nemi a kira ma shi Fateema Abbas, sosai Fateema Abbas tai mamakin jin cewar sir Umar Aminullah na nemanta, saboda zumuɗi kasa tsayawa tai Sadiya ta fito daga wanka ta sanar ma ta tai, sai kawai ta shiga gyara fuskarta ta na fatan ace yazo wajenda da wani abu me kama da soyayya, cike da ɗauki ta fita ta nufi wajen da aka kwatanta mata, da zuwanta ta taras da shi tsaye kusa da tsadaddiyar motarsa ya na jifarta da tsadaden murmushi, da kyar ta saita kanta ta dan karta kwafsa, dan sai yanzu ta sake nutsuwa ta na ƙarewa halitarshi kallo, wa ta kibiyar ƙaunarshi ce ta soke ta a ƙahon zuciyarta nan take, murmushin da yake sakar ma ta ya sake ingizata ta afka cikin kogin ƙaunarsa.
Ta na maida ma shi da martanin murmushin ta tsaya tare da yin sallama cikin saura ainahin sautin muryarta wanda itama batasan ya aka yi ta samu kanta da sauya murya ba.

Sai de kash, Umar yayi nasarar dugunzuma tunani da zuciyar Fateema Abbas ta hanyar faɗa ma ta yazo ne ta shige mashi gaba wajen samun soyayyar ƙawarta Sadiya, inda ya warware ma ta yanda yake fama da gyambon sonta a zuciyarsa, yanzu yakai matakin da ko barcin kirki baya samu.
Wa ta zufar tashin hankali ce ta tsatsafowa Fateema Abbs, yayinda ta ke kokowa da harshenta wajen ganin bata dannawa Umar manya-manyan ashariya ba, ta daɗe bata ce komi ba, shiko ganin shirun yayi yawa ya saka shi tunanin ko Sadiyar na da wanda take so, tunanin hakan kaɗai sai da ya dugunzuma nutsuwar zuciyarshi, amma yai ƙoƙari wajen saita kanshi.

Fateema bata da wani zaɓi a lokacin sai cewa da tayi karya damu zata tuntuɓi ƙawarta akan zance, duk abin da kenan zata sanar da shi.

Sosai Sir Umar ya ji daɗin wanan zance hakan ya saka yaiwa Fateema kyautar kuɗi masu kauri waɗanda suka sake karyar ma ta da zuciya ta kuma sake jin soyayyarshi na yunƙuron ma ta da ƙarfin gaske.

Bayan tafiyar Sir Umar Fateema ba ta koma
hostel ba ta nemi wani ɗan tudu ta zauna ta na sharce hawayen baƙin ciki, ta na nan zaune wasu ƴan class ɗinsu gungu guda suka zo wajen, ashe duk abin da ya faru tsakaninta da Sir Umar akan idonsu ne, hakan ya saka suka taho dan suji gulma, har musayar yawu sukai akan zuwa yai wajenta ya ce ya na sonta, dan Fateema Abbas babu laifi kyakkyawa ce itama, gata doguwa kamar Sadiya.

Kuka ne me sauti ya kubcewa Fateema Abbas lokacin da suke tambayarta abin da ya faru suka ga ta na hawaye ga kuma kuɗi a hanunta, sanna kuma duk sunga zuwan Sir Umar wajenda.
Fateema Abbas sam bata da sirri, tanan wajenne kawai ake jin kansu ita da Sadiya, kwashe komi ta yi ta faɗi ma su tana sakw fashewa da kukan takaici da hassada, aiko nan suka zagaye ta suka dinga famfata akan karta yarda ta barwa Sadiya Sir Umar, da ita ya dace ba da Sadiya ba, sannan suka hanata faɗawa Sadiya yana sonta, aiko Fateema Abbas tahau kan zugarsu ta zauna, a maimakon ta koma hostel sai kawai ta bisu nasu hostel ɗin can suka shantake su na ta firar duniya, da yawa daga cikinsu sun daɗe su na jiran wannan rana da zasu samu damar shiga jikin ɗaya daga cikin ƙawayen, kowa na son mu'amula da su saboda baiwarsu ta karatu, amma Sadiya sam bata bawa mutane fuskar, har gara ma Fateema Abbas ita takan ɗan kula wasu dan ta na da son mutane.

A ranar Sadiya ta nemi Fateema Abbas amma bata ganta ba, ta yi ƙoƙarin kiranta a waya amma bata same ta ba, haka ta ƙarashe wunin sukuku da ita, sun saba duk inda zasu je su na tare, koda fita ta kama ɗaya to dole ƴar uwarta za ta sa ni, Fateema Abbas bata dawo ba sai can cikin dare, lokacin har Sadiya ta kwanta barci saboda ta n tashi tayi karatu cikin dare saboda tunkarowar exam, harara Fateema Abbas ta aikawa Sadiya sannan ta juya baya tai kwanciyarta cike da tunanin Sir Umar har barci yai awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da asubahi shima Sadiya ce ta tada ita, lokacin da ta buɗe ido tai arba da innocent face ɗin Sadiya tunanin yanda Sir Umar ya karkace ya saki baki ya shiga karanto ma ta yanda yake ƙaunar Sadiyar, nanda nan ta haɗe dai ta kuma daina ganin kyawun fuskar Sadiyar sai wani muni da baƙi da take gani, a yatsine ta tashi ba tare da ta kula Sadiya ba ta shige toilet, koda ta fito ta iske har Sadiya ta gama shirinta ta na shirin ɗaura girkin abin kari, dakatar da ita Fateema Abbas ta yi akan karta haɗa da ita idan ta tashi ta haɗa iya nata, Sadiya bata damu da hakan ba dan tanada fahimta sosai kuma bata damuwa da abin da ba'a saka ta ba.

Daga ranar Fateema Abbas ta daina shigewa Sadiya sai ya zama dole, yanzu komi da suke yi tare Fateema Abbas ta ware kanta gefe ita da sabbin ƙawayenta su Zee baby da Ayush ƴar wanka.


Wa ta rana Sadiya na zaune a bakin bishiya ta na karatu gabanta lemo da ruwa ne ta na kurɓa a hankali, Sir Umar ne ya gifto ta wajen sai ya hangeta zaune ita kaɗai, bai yi wata-wata ba ya isa wajen tare sa sallamarshi a baki, amsawa Sadiya ta yi tare da ɗago ido ta kalli mamallakin wannan muryar, karaf idonta ya sarƙe a ciki nashi idon, inda ya hanata janye nata yayi amfani da damar ya fara aika mata da sakonin da ke cikin zuciyarshi ta idon, cike da kunya Sadiya ta sauke kanta ƙasa tana jin wani yanayi haɗi da faɗuwar gaba a lokac ɗaya, a taƙaice dai ranar Sir Umar yai nasarar jefa kwallon soyayyarshi a zuciyar Sadiya bai yarda ya bar wajen ba sai da ya ɓata lokaci ya kuma tabbatar da ya samu karɓuwa sannan ya rabu da ita cikin shauƙin ƙaunarta.

Soyayya me tsafta ce ta shiga tsakanin Sir Umar da Sadiya, yayinda Fateema Abbas ta koma gefe ta na jinyar zuciyarta tare da ɗaukar shawarar su Zee ta nesanta kanta da Sadiya, sai de kuma hakan ya bawa Sadiya damar sakewa da Sir Umar, babu me takura ma ta, sannan yanzu tafi jin daɗin karatun saboda kusan duk weekend su na zama ita da Sir Umar su yi lesson, yayinda kaidin basirarta ya daɗa ƙara soyayyarta a zuciyar Umar dan ya fahimci ita ɗin daban take da sauran mata.

Lokacinda aka yi hutu ne Sir Umar yabi Sadiya har gida Kano ya gaisa da Alaji Abbas tare sa gabatar mashi da kanshi a matsayin siriki, anan ne Alhaji Abbas ya fahimci Sir Umar ɗan gidan Babban ɗan kasuwa ne wanda ake ji da shi a lokacin, bai yi wata-wata ba ya amince tare da bashi damar turo magabatanshi dan a tsaida magana tunda yanzu Sadiya na ajin ƙarshe.

Babu ɓata lokaci Sir Umar ya sanar da mahaifinshi komi da kuma yanda sukai da Alhaji Abbas, bincike Alhaji Ibrahim ya saka akai ma shi akan Sadiya sa mahaifinta, ya ji daɗin sakamakon bincike inda anan ne ya fahimci Sadiya ɗiyar Abbas me siminti ce, babu ɓata lokaci manya suka shiga maganar aka tsaida lokacin aure bayan Sadiya sun yi candy, bayan Sadiya ta koma makaranta bata sanar sa kowa saka ranarta ba, amma ta kusan dayawa sun fahimci soyayya suke ita da sir Umar, hakan sam baiyiwa wasu dayawa daɗi ba, ana cikin haka kwatsam wani mutum ya shigo rayuwar sir Umar, inda ya fara da bin diddiginshi, ananne ya gane ansaka mashi rana da ɗalibarsa, baiyi wata-wata ba ya tsananta bincike akan Sadiya da waɗanda take mu'amala da su, Fateema Abbas ita kaɗaice ƙawa ga Sadiya hakan ya saka ya je ya sanar sa me gidanshi ansamu mutum ɗaya da take da kusanci da matar da sir Umar zai aura.

Sosai Muhammad Dikko ya jinjina ƙoƙarin sabon yaron da ya taimaka ya kuɓutar da rayuwarshi daga hannun ƴan fashi da makami wato Lawan.

Lawan dai almajiri ne wanda tun yana shekara shidda mahaifinsa ya kawoshi almajiranci, amma tunda ya dire shi a Kano bai sake waiwayarshi ba, Lawan ya taso cikin matsi da ƙyara daga sauran ƴan uwanshi almajirai, da yawa kanyi ma shi gori akan rashin sanin asalin garinshi ko ƴan uwanshi, tun yana damuwa harya daina damuwa dakanshi ya sanar da su cewa shi ɗan shege ne baida uba, hakan ya taka rawar gani sosai wajen sake ƙyamatarshi, babu me raɓarshi bare yayi abota da shi, ana cikin haka ne wata raba bayan ya girma ya zama tantirin ɓarawo kuma marar ji ya fita sata cikin wata unguwar masu kuɗi, akan hanya ƴan fashi suka tareshi, har sun sait harsashi akanshi zasu tarwatsa ma shi kwanya saiga Muhammad Bello ya zo wajen tare da jami'an tsaro, nan take ƴan fashin suka watse kowa ya shiga gudun ceton rai, saboda ruɗewa sai da Lawan ya suma a wajen, amma sai Muhammad Bello ya bawa securty umurnin su ɗauke shi, nan aka ɗaukeshi aka kaishi asibiti aka duba lafiyarsa, washe gari ya dawo daidai dama kawai ya shiga ruɗu ne amma babu abin da ya sameshi.

Muhammad Bello ya nemi jin tarihin Lawan, nan lawan ya faɗa ma shi komi, aiko Muhammad Bello ya ɗaukeshi aiki, aka bashi wajen zama a gidan aka kuma wadatashi da komi, har malamin da zai dinga yi mashi lesson aka samo ma sho, cikin shekara ɗaya ya waye ya goge ya zama gaye, ahankali Muhammas Bello ya fara janshi cikin ƴan kasuwa da kuma ƴan siyasa, duk da cewa Muhammad Bello yana gaba da sir Umar a wajen kasuwanci, kuma yafi bada ƙarfi a siyasa, amma da yaga yanda tauraron sir Umar ke haskawa, mutane kuma na yinshi sosai duk da baɗan siyasa bane sai hakan ya tsayawa Muhammad Bello a yuwa, ya dinga shege-shigen malamai akan a durƙusar da sir Umar amma sai aka tabbatar ma shi yaron yanada baiwa me ƙarfi kuma farin jininshi daga Allah ne, sannan kuma bazai yuwu ya koma ƙasan Muhammad Bello ɗin ba kamar yanda yake sakawa ana mallake ma shi sauran ƴan kasuwa da ƴan siyasa su dawo ƙasanshi, sosai abin yai wa Muhammad Bello tsaye a rai, ana nan kwatsam sai ya ji labarin akan wata babbar cibiyar kasuwanci da Alhaji Ibrahim zai buɗewa sir Umar, hakan ya sake tunzura tunzurarren ya shiga neman yanda zai samu dama koda sau ɗaya ne akan sir Umar, tofa nan ne yafara amfani Lawan ya tirashi ya shiga jikim Sir Umar amma sai hakan bai samu ba, yayi masara tunda har su na ɗan gaisawa amma daga hakan sir Umar bai bashi wata damarba, nan ne suka juya alaƙar Lawan ya koma ya shiga jikin Fateema Abbas, shine ya sauketa daga shawarar su Zee ya sake maida ita cikin rayuwar Sadiya, a karo na biyu Sadiya ta sake amsar Fateema Abbas, sai de bata sake da ita sosaiba, sai Fateema ta ji kamar ta rabu da Sadiyar sai kuma ta yi haƙuri tuno irin maganga da Lawan ya tsara ma ta.

Haka rayuwa taci gaba ta gudana Lawan ya samo kan Fateema Abbas inda yai ma ta alƙawarin zai mallaka ma ta sir Umar harma ta aureshi, toko ta yarda saboda gaban idonta sunsha gaisawa sa sir Umar ɗin anan ta sake tabbatarda lallai Lawan dagaske ya ke zai haɗata da masoyinta harma suyi aure.

Bayan an yaye Sadiya da Fateema ko wace ta koma gida, anan ne aka shiga shirin biki gadan-gadan dan dama takowane fanni ashirye suke kuma auren ƴan gata za'ayi shi yasa kowa ya shirya tunda wuri kafin zuwan lokacin, auren Sadiya Abbas da Umar Ibrahim ya ƙayatar sosai, biki ne akai irinna ƴaƴn gata masu ji da naira, Karima ta shiga ta fita wajen sake gyara Sadiya, sai da ta maida ita ƙayatacciyar mace sannan kuma a ɓoye Hadizama na nata aikin gyaran ba tare da sanin Karima ba.

Ansha shagulgula sosai a bikin, inda tun a lokacin Malam wato Hussain ya gano irin baiwar da sir Umar ke sa ita, nan ne yayi ƙoƙari wajen bashi wasu surrukan tsarin jiki wanda basu kaucewa hanya ba, sir Umar ya sake da Malam sosai inda ya nemi yazo suyi aiki a tare amma sai ya nuna ma shi shiyafi son harkar Islamic medicine kasuwanci sam bai dameshiba, aiko sir Umar ya taka rawar gani wajen Malam, dan shago ya buɗe ma shi ƙato a nan kano sanan ya cika ma shi shi da ingantattun magunguna waɗanda akayo order su daga ƙasar Saudiyya.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘


WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.


MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚


PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK TWO
Chapter 13 · 0% Book details