Sashe 7
Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
shuru Kawu Habu ya yi yana tunani, yar wajen shi Nu’aima, allah ya sa ba wani abun Nu’aima ta janyo mai ba,
“kana tare da ni ko Malam?.”
muryar Daddy ya yi nasarar yenke mai guntun tunanin da ya fara,
“eh eh Nu’aima ko?, ‘ya ta ce, ince dai lafiya ba wani laifin Nu’aima ta yi ba ko?.”
“Aa kada ka damu alkairi ne insha Allah.”
“to to masha Allah ya yi.”
sai da Daddy yadan ja fasali sannan yace,
“to ina nema wa ‘da na auren ta, in ba damuwa.”
kwalalo ido Kawu Habu ya yi ya na dafe kirji, jin maganar Daddy kamar saukar guduma a kanshi, gir-giza kai ya shiga yi, kafin da kyar ya iya furta,
“Aure? Aure fa kace Alhaji,? kuma wai Nu’aima?.”
“eh aurenta nike nemawa ‘dana Afif.?
Daddy ya dan yi shuru, kafin yace,
“amma akwai wata masala da muke fatan ta zama ba masala ba insha Allah, sai dai ku ban san ya zaku dauki abun ba, duk da insha Allah yar ku bazata cutu ba.”
“ai kada ka damu Alhaji, yadda kuka dauke shi muma haka zamu dauka dan haka karka damu.”
(“ shikenan fa,? tunma bai ji menene masalar ba,”) Daddy ya yi maganar a zuciya mamaki na bayyana a fuskarshi,
“owk, to yanzu idan ba ta da wani tsayayye kuma kun amince sai ayi magana.”
Daddy ya yi maganar yana kawar da tunanin da ke zuwa kanshi,
“Ah haba Alhaji wani irin tsayayye kuma,? ai kawai ayi magana, ina ma laifin ka fito a shirye da sai ka biya kudin tambaya da na lefe ga ba dai ko?.”
Kawu Habu ya yi maganar da fatan samun kudade a wajen Daddy,
“wannan ba masala bace, zaka iya fadin nawa za’a biya.”
“eh to, ku biya miliyan biyu.”
ya yi maganar yana kar-kata kai yana duba motar Daddy ,
(“da ganin wannan motar ba ita kadai bace, kuma akwai yan canji a bayanta.”) ya kare maganar a zuciya yana dawo da kallonshi ga Daddy da ya kafe shi da ido,
“Alhaji kasan sayayyan da yawa, kuma komai ya hau yanzu abunda ka sani biyar idan ka taba shi yanzu sai dai dubu.”
ya yi maganar da tunanin ko dan yawan kudin da ya kira ne yasa Daddyn ke kallon shi,
“Ah kada ka damu, zan bada miliyan biyar amma banda lefe da kayan daki, wannan mu zamu mata.”
“ehhh, me kace Alhaji ban ji da kyau ba kamar miliyan biyar kace, ko kunnuwana ne?.”
murmushi Daddy ya yi, jin abunda Kawu Habu ke fadi
“ka hada ni da wanda zai dauko kudin dan ban fito da cash ba.”
jin maganar Daddy yasa Kawu Habu sake gaskata maganar, cikin rawar baki ya furta,
“Ah ah Alhaji yanzu har ina yaddan da zai sa da ranka da lafiyar ka ka wakilta wa ni amsan kudi, ai kasar mu yanzu ba tsaro, gani ni zan bika na amso su hannu da hannu yadda kaima zaka fi jin amincewa, yawwa kuma nace me zai hana a daura auren yanzu kaga hankali kwance.”
ba wani dogon zance Daddy ya amince, dan shi ta lafiyar Afif ya ke,
a masallacin anguwar bayan sallan la’asar sirarun mutanen da suka yi salla cikin masallacin suka shaida daurin auren AFIF BADAMASI da amaryarsa NU’AIMA IBRAHIM ……….✍
#zabinkaddara
#queenmk
#08089884996
WhatsApp only
————————————————————
typing 📲
🌙ZABIN KADDARA 🌙
Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻