Sashe 3
Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AFIF POV,
ahankali ya ke bude idanun shi, har ya ware su akan fankar da ke juyawa ahankali, kafe fankar ya yi da ido ko kyaftawa bai yi, ya na sauraren manyan masifun da ke yawo acikin jikin shi, ya na jin yadda naman jikin shi ke rawa, rawa bana wasa ba , wanda hakan kuma bai bayya na fatar shi ba, wani zafi yake ji yana tashowa daga jikin shi,
bude baki ya yi, da niyar ya ambaci sunan allah, amma sai yaji ya kasa sarrafa harshen shi, ya ji wani nauyi akan shi, kamar an daura mai dutse,
mase jikin shi ya yi, ya dunkule waje daya, ya na jin yadda idanun shi ke rufewa, ba fatar idon ne ke rufewa ba, wani farin abune ke rufe bakin kwayar idon,
kuma hakan bawai ya hana shi gani bane, sai ma wani karfi ganin ya kara, kunnuwan shi kuma sun sake bude wa, dan har wayar da Mommy ke yi daga falon kasa ya na jiyo wa,
da sauri, ya tashi zaune ya na bude ramun hancin shi, ya fara shinshine-shinshine, alamar ya na jin kamshi ko warin wani abu,
takon tafiya da ya ji ne, alamar za’a shigo dakin, ya sa shi gane warin jini ya ke ji,
duke ya tashi irin dukin nan da birai ke yi, yana fuskantar kofar,
da sallama, Anty Jayyada ta turo kofar,
amugun rikice, hadi da firgici, ta mayar da kofar ta rufe, rufe kofar da ta yi, ya yi, daidai da tumowar da Afif ya yi,sai dai kafin ya iso ta mayar da kofar hakan ya sa ya bugu da kofar, ya fadi kasa ya na wani gurnani mai rikitarwa.
“Mommy, Mommy, Anty Jalila,” a mugun rikice Jayyada da ke rike da kofar da Afif ke duka, take kwala kiran sunayen su Mommy.
da sauri su Mommy, suka hawo suna tambayar meya faru,
har lokacin Anty Jayyada na rike da kofar,
ganin haka ya sa su Mommy saurin isa inda take, dan basai ta fadi ba, sun fahimci me ke faruwa, ga gurnanin Afif dake tashi da karar fashe-fashe, alamu sun nuna wasi ya ke yi da kayan dakin.
cikin kukan da ya kwace ma Mommy tace,
“Jalila kira Daddyn ku, Innalillahi’wainna’ilaihirraju’un, wannan wani irin masifa ne, dama wannan lalurar bai bar Afif ba, oh ni, kaddara zabin da kika yi mai kenan, wannan shine ZABIN KADDARArka Afif, allah ya baka karfin zuciya, da imanin da zaka iya, canye wannan jarabawan.
( “ kai, kai, kai, toh shi wannan Afif din, maye ne ko horro, bari dai inyi shuh, muje zuwa.”
★...........★
LOCOST AREA
NU’AIMA POV,
Nu’aima , kwance take a kan tabarma , kallon Na’im tayi,twins brother dinta dake kwance a saman tabar mar shima.
yayi filo da katifar da Ummy ke kwance,hausa novel ne a hannunshi yana karanta wa.
Nu’aima ; sai boye dariyar ta take yi, dan bawai iya karatun hausa yayi ba.
Na’im ;ajiye littafin yayi akan cikin shi,ya juyo yana kallon Nu’aima yace,
``wai Habibty fadan me na tarar Kawu nayi ne``.
Nu’aima ; tace,
``na me ko, bayan wanda suka saba``.
Na’im ; yace,
``allah wadaren naka ya lalace, ace mutane kullum aiki daya masifa dai masifa``.
``banson rashin tunani fa,Habiby, da hankalin ka kake fadin irin wannan maganar``.
Na’im ; yace,
``sorry Habibty, mutanen gidan nan ne, ko baka son ka fadi mumunan kalma akansu, sai kayi dan abun nasu kullum gaba-gaba yake sakeyi``.
Nu’aima ; tace,
``sai addu`a``.
``ke kici gaba dayi musu addu`ar, nidai na gaji, zama gidan ma ya ishe ni wallahi``.
Nu’aima ; tace,
``to ya zamuyi, ZABIN KADDARAR MU kenan, dole mu rungumeta``.
Na’im ; yace,
``to allah ya shige mana gaba``.
``amin ``.
ya dauki littafin yaci gaba da karantawa,
duk abun da suke yi Ummy na jinsu, amma bata tankasu ba.
★...........★
“ Malam Ado, magana daya ba kari, kazo ka kwashi yaran nan da uwar su, shikenan.”
baki sake wanda aka kira da Malam Ado ke kallon Kawu Habu,
“ Aa Habu kadai manta, ai cewa zakayi inzo in dauki yaran, amma ba da uwarsu ba, ai uwar taku ce, ni meye alakata da Nuratu, kuma ma ai, in baka manta ba Nu’aima da Na’im ma nace na barmuku.”
Kawu Habu, yace,
“ ji wani maganar banza, alaka sakanin ka da Nuratu kam ai an dade da samun ta, tunda har dan uwanka ya aure ta, ta haifa muku yara, dan haka kazo ka dibe su, dan na gaji da ciyar da su.”
“ to bari kaji, Habu, su Nu’aima dai ko?, to bazan dauke su ba, kuma duk ranar da zan sake ganin kafar ka, kofar gida na, wallahi sai na maka abun da baka taba tunani ba.”
Kawu Habu yace
“Aa ai bazata kai mu ga haka ba, ina amfanin cin mutuncin juna, ni dama tafe nike da wani zance mai mahimmanci.”
ya dan sagaita dan jin ko, Malam Ado zai ce wani abu, jin ya yi shuru, sai kallon shi daya ke yi yasa shi ci gaba da fadin.
“ dama nace me zai hana mu aurar da Nu’aima, kaga dukan mu nauyi ya sauka kammu, sannan tunda mu zamu samo mata miji, zamu iya hada ta da uwarta, su tafi can ko ya kace?.”
Shuru Malam Ado ya yi, kafin yace
“zanyi shawara.”
Yana fadin haka ya shige gida ya bar kawu habu anan
tsaki kawu habu ya yi yana fadin
“ mutum sai fadin ran tsiya da girman kai, kamar wani shege, du shi Nu’aima ta biyo, yoh ina hadin talakka da fadin rai .”
barin kofar gidan ya yi yana surutai dan ba haka yaso ba, yaso Malam ado ya amince mai da gobe goben nan zai daura mata aure da Malam buba kowa ya huta …….✍
#zabinkaddara
#queenmk
————————————————————
typing📲
🌙 ZABIN KADDARA 🌙
Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻
Page 5&6
GRA AREA
AFIF POV.
kwance ya ke a saman gadon , ya daura kan shi a kafafun Momy, idanun shi a lumshe suke amma ba bacci yake yi ba, Daddy na zaune a bakin bed din, Anty Jayyada kuma na goge dakin da Afif ya hargisa,
“sweetheart open your eyes are you okay.”
Mommy ta yi maganar ta na shafa kanshi,
“yeah, Mommy I am okay.”
ya bata amsa ba tare da ya bude idanun shi ba.
“good, oyah open your eyes.”
ta sake fadi tana leka fuskarshi.
“ no Mom.”
“wani abun ne a idon .”
“No.”
“to oyah bude idon.”
a hankali ya fara bude idanun, har ya bude su tar, a fuskar Mommy dake kallon shi.
zaro ido Mommy ta yi, da sauri ta sa hannun ta ta mayar da idon shi ta rufe, ganin har lokacin bakin kwayar idon bai dawo ba, yana nan fari.
“ya ilahi, har yanzu?, kana jin wani abune son?.”
“Daddy ya ce, bar shi ya tashi ya shirya, lokacin juma,a na wucewa .”
mikewa Afif ya yi zaune, ya na fadin,
“Anty Jayyada, my sun glasses please .”
dauko wa ta yi ta mika mai,
amsa ya yi, ya sa, sai lokacin ya bude idanun shi, akan Anty Jayyada idon shi ya sauka, kafe ta ya yi da su, yana kallon yadda, jini ke gudana a jikin ta, gaba dai abun da ke cikin ta ba wanda bai gani,
ganin yadda yake kallon ta, yasa Daddy, isa inda take ya kama hannun ta, jan ta ya yi suka bar dakin.
sai lokacin Afif ya dauke idon shi daga kallon kurillan da yake mata, ya tashi, ya shige toilet.
★......
“Daddyn Kamilat,meye mafitar wannan lamarin, wallahi abun ya fara ban tsoro, idan wannan labarin ya fita, da wani suna mutane zasu kira shi.”
kallon Mommy,Daddy ya yi, ganin yadda ta zama kalar tausayi,
“wa zai fitar da labarin, daga ni sai ke, da yaran mu, ba bare, wa zai kai labarin waje?.”
“to ko zamu fitar da shi waje ne.”
“a karo na nawa kenan zamu fitar da shi, a kalla mun fitar da shi kasashe fin sau asherin 2, amma maganar daya ce, lafiyar shi lau, ko wani Doctor haka ya ke fada muna, yanzu ma zamu je ne, dan su sake fada muna bai tare da wata masala, bayan mu ga masalar nan muna gani.”
shuru Mommy ta yi, kafin ta dago ta kalle shi,
“to Daddynsu, mu gwada na hausa, ko allah zai sa a dace.”
a wannan karon sosai Daddy ya juyo yana kallon ta, ganin kamar ta manta lalurar Afif din wani iri ne, maganin hausan da ko an karbo ba a iso wa gida da shi, ko ma an iso dashi, an bashi ya sha to wanda ya bashi, shi zai ji jiki,
mikewa ya yi, bai ce mata komai ba ya bar dakin,
da kallo Mommy ta bi shi, dan shurun nashi ya tuna mata da abun da ta manta,
Daddy na fitowa babban falo, Afif ya sauko, sanye ya ke da shadda light blue dunkin rigar iya cinyar shi ya tsaya, hannun rigar ma guntuwa ce, kan shi na sanye da bakar hula, takalmin kafar shi da sadadden agogon da ke hannun shi na hagu, duka bakake ne,
ya yi kyau sosai, kayan sun amshi farar fatar shi, har lokacin bakin glass din na nan a fuskar shi.
kama hannun Daddy ya yi, ya daura a kumatun shi, ya karkata kanshi, ya matse hannun Daddy sakanin wuyan shi da kafadar shi.
kallon shi Daddy ya yi, ganin yadda ya turo small-small lips din shi da ya sha lipstick, sai kyalli ya keyi.
murmushi Daddy ya yi ya ce,
“me kuma wannan karamin bakin ke bukata daya ke son ya kara tsawo?.”
sake turo bakin ya yi, bai ce komai ba.
rike hannun shi Daddy ya yi, suka fita compound din gidan, motar da Baba Bala direba ya fitar, Daddy ya bude mai, sai da ya shiga, sannan Daddy ya zagaya, Baba Bala ya bude mai ya shiga, suka bar gidan.
★......★