← Book details Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 7

Sashe 6

Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nu’aima kin ci abinci ko,?”
kallon Ummy ta yi, “ eh “ ta amsa ta na nade sallayar da ta idar da sallah, ta daura kan jakar kayansu,
kallon ta Ummy ke yi, ganin yadda ta yi zuru-zuru,
“i ya abincin da suka baki kenan kika bani, ko?”
jin bata ce komai ba, Ummy ta sake fadin, “zo ki gyara ni, in ti fitsari.”
isa inda Ummy take ta yi, ta gara ta, ta mike tana fadin, “ bari in daura ruwan zafi, in gyara miki jiki.”
Ummy, tace. “ aa Nu’aima, ban son abun magana, ki yi min da ruwan sanyi.”
“amma Ummy yadda baki da lafiyar nan, ruwan sanyi ba alkairi bane a jikin ki, kada mu jawo wata masalar kuma.”

“kada ki damu, ba’abun da zai same ni Insha Allah.”
fita ta yi, ta debo ruwa a buta, ta dawo dakin, koda ta fita tana ganin iya shegen da su Badi’a ke yi asakar gidan, ita da Munira da Mukaddas, da wasu abokan Mukaddas biyu, wai suna buga wort, sai ihu suke yi.
karamin kyalle ta samu, ta fara goge ma Ummy jiki da shi, bayan ta shirya ta saf cikin wasu kaya, ta mike tana tambayar ta ko akwai abun da take bukata,
“aa ban bukatar komai, allah ya yi miki albarka.”
da amen ta amsa, nan taji shewan su Badi’a,
“Oh ni bahba, yariyar nan ta kama wannan guy din sosai fa, ba dare ba rana, ko gajiya baya yi da zuwa wajen ta.”
tajiyo muryar daya daga cikin abokan Mukaddas na fadi.
Badi’a ce ta amshe zancen da fadin,
“ai baka ga komai ba sai kaga irin wankan da yake dibowa.”
Munira da Mukaddas suka kwashe da dariya suna tafawa,
“ashe yau na zo a daidai kenan, muje in ganshi.”
cewar abokin Mukaddas din da ya yi magana dazu,
tana ji suka tashi dukan su, suka nufi kofar gidan inda Zaidy ke saye,
hijabin dake jikin ta take kokarin cirewa, Ummy ta tare ta da fadin,
“cire hijabin zaki yi, bayan kin san ana jiranki a waje.”
kallon Ummy ta yi, ta tura baki, “ to Ummy ni me zan mai.”
“walakanci ba kyau, Nu’aima, kuma ma ai wanda yace yana sonka ai ya gama maka komai, tun da ya zo bai kamata ki ki fita ba, je ki saurare shi.”
“uhm naji.” tana fitowa su Badi’a suka kwashe da dariya, bata kula su ba ta fita,
Suna saye a kofar gidan, kanta na sunkuye ta nade hannun ta a kirji, shikuma Zaidy yana saye a gefe hannayen shi cikin aljuhu yana kallon ta.
ZAIDY, yace,
``Nu’aima, kiyi hakuri da shishshigin da na miki, banyi hakan da wata manufa ba, sai dan na kare ki daga auren malam buba, kuma ni da gaske nike yi zan aureki inkin amince``.
Nu’aima, shuru tayi har lokacin bata dago kanta ba.
Zaidy, yace,
``baki ce komai ba, kada ki damu idan har ban miki ba zaki iya fada min ``.
Nu’aima, dagowa tayi ta kalle shi, tace,
``a`a wallahi, aitunda Kawu ya amince da kai, shikenan, nima na amince``.
Badi’a , dake fitowa daga cikin gida tace,
`` auh haba ashe saboda Baba ya amin ce ne ke ma kika amin ce, munafuka dama dai kina sonshi``.
Zaidy, yace,
``haba Badi’a , meya kawo wannan maganar harda zagi, kuma in dama tana sona menene``.
Badi’a , tace,
``kaga, zaidy kake ko wa, ni ban sakoka cikin Magana ta ba, da wannan abar nake``.
Badi’a , ta juya ga Nu’aima da kanta ke sunkuye tun lokacin da Badi’a ta fara Magana , tace
`` ke kuma maza ki shiga gida kiyi wancan wanke-wanken da kika bari yana kallon mutane``
ba musu ta juya , ta shige gidan, dan ta san idan ta saya to , walakancin da zata dauka wajen Badi’a ba kadan ba .

★……
a hankali ya zuro jikinshi waje sai da ya tsaya da kyau sannan ya maida marfin motar ya rufe bakin glasses dake idon shi ya gyara yana kare ma farfajiyar gidan kallo akalla shekara daya da watanni biyar kenan bai kasar yau kuma gashi ya dawo cikin ta a bisa umarnin mahaifiyarshi dan ba abisa radin kanshi ya dawo ba,
“oyo yo Bro Muhris finally bayan hijiran shikaru yau dai an dawo.”
kallon Makaddarasiya dake maganar tana nufo shi ya yi,
har yau tana nan da halinta kenan anyi dai-dai kenan dan shima yana nan a yadda ya ke,
murmushi ya yi ya bude mata hannu alamar ta yi huge din shi,
“Ah haba dai Bro Muhris wannan fa Makaddarasiya ce haka zalika kuma wannan kai ne ai kasan ba haka sakanin mu.”
ta yi maganar tana yatsina fuska “a tafi kawai a yadda aka saba.”
“good girl kin kyauta ma kanki.”
ya yi maganar yana nufar cikin gidan, itama bayan shi ta bi………✍

#zabinkaddara
#queenmk

————————————————————
typing 📲
🌙ZABIN KADDARA 🌙

Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻

PAGE 11&12

“innalillahi Khalil me ya same shi, lafiya lau fa kuka fita, Afif, Afif meya same ka?.”

cikin kuka Khafilat ke maganar tana jijjiga Afifi dake kwance bayan motar Khalil ba alamar numfashi a tare da shi,
da sauri ta juyo ga Khalil din da kallo guda za ka mai ka hango sansar tashin hankali a tare da shi,
kwalarshi ta rike tana jijjiga shi,
“Khalil can u tell me what’s totally happened to my brother, idan ba haka ba kuma wallahi summa billahi zan aikata abunda zai dami kowa.”

“Khafilat is something that I can’t explain to you, because ko ni ban san ta ya hakan ya faru ba, kawai fa gani na yi ya fadi, amma idan zaki lura da kyau zakiga ai yana numfashi.”

“Will you shut that your dirty mouth up Khalil, kana hauka ne ko me, baka mai komai ba kawai ya fadi kana nufin ciwon farfadiya ne da shi ko me, eh Khalil explain, ka yi min baya ni nace.”

cikin kuka da daga murya take maganar, wanda hakan ya yi nasarar jayo hankalin mutanen gidan,
Umma da Muhris ne suka fara fitowa sai Makaddarasiya a bayan su, ganin yadda ta ci kwalarshi yasa Umma karasawa wajen da sauri tana fadin,

“Aa menene haka, ke Khafilat ya zaki rike mai kwala lfy?.”

“Umma can you please wait for a second.”

Khafilat ta yi maganar tana kallon Umma da ke kokarin rike hannunta da ke rike da wuyar rigar Khalil, juyawa ta sake yi ga Khalil da rufa ya gana jika mai jiki sai zaran ido ya ke,

“kai nike saurare Khalil, dan wannan shurun bazai fidda mu ba.”

inda Afif ke kwance Muhris ya isa, kallon shi ya shiga yi kafin ya tara dan yasan shi ga hanshin Afif, nan ya ji zafin numfashin da Afif ke fitarwa a hankali ya daki yasan shi, zura jikinshi cikin motar ya yi ahankali ya tallafo Afif jikinshi ya fito da shi,

“ina zaka dashi Muhris?.”

Khafilat ta yi maganar tana juyowa inda ya ke,

“Asibiti dan ya na numfashi.”

da sauri ta nufi cikin gida dan dauko car key, har lokacin kuma su Mommy ba su san me ke faruwa ba, sai bayan shigan Khafilat suka sani,

★…….

“Badamasi, tun farko sai da na sanar da kai laluran Afif bana asibiti ba ne, bakin sihiri ke aiki a jikin shi, kuma danganta shi da maganin asibiti ba zai taba zama maslaha ba sai ma dai ya sake bata lamarin.”

shuru dattijon da Daddy ke zaune a gabanshi ya yi,

“Malam to yanzu me ne abun yi?.”

“to bana ce ba, amma dai yanzu ka fara mayar da shi gida dan jinyar bana asibiti ba ne.”

“Insha Allah, amma akan laluran ba abun da za’a iya yi bakin ruhin ya bar jikin shi, ina nufin gaba dai.”

shuru mutumin da Daddy ya kira da Malam ya yi, kamar mai tunani kafin yace,

“Badamasi bazan ce maka ga abun da za’a yi ba dan ni ba boka bane kuma ba Malamin tsibbo ba, duk wani kokari da zamu yi zamu yi ne ta fannin adddini, to shi Afif din kuma bai karban magani,
duk da ina tunanin wannan ce damar mu ta karshe da zamu yi amfani da shi wajen yi mai amfani da duk wani ruwan rubutu, amma masalan wanda zai mai amfani da su.”

cikin dhoki da kosawa a lokaci daya Daddy ya kalli Malam jin ya yi albishir kuma ya kawo masala a ciki,

“ban tunanin hakan zai zama masala, ga ni ga mahaifiyar shi da yan uwan shi, ko wani daga cikin mu zai iya tsayawa dan samun lafiyar Sardauna.”

“no Afif not a younger da zaku kula da shi irin haka nan, ina nufin da a Kwai damar yi mai aure da abun zai fi zuwa da sauki.”

dan jimm Daddy ya yi yana nazarin maganar, shi ko kusa bai taba kawo ma Afif tunanin aure nan kusa ba amma indai hakan zai zama silar samuwar lafiyar shi to zai yi, amma sai dai wa za’a aura mai bai tunanin Afif din na da budurwa balle yace ita,

“to amma Malam wa za’a aura ma Sardauna a wayan nan kananun shekarun na shi, kuma ga jinya yana fama da shi, dama ace yana tare da wata ne da sai ince zata aure shi kodan son da take mai.”

“wannan ba masala bane a Kwai wanda zan tura ka wajen shi, everything will be alright Insha Allah.”

★…….

bakin Kawu Habu kamar zai bare saboda farin cikin jin Babban mutum irin Dady ya nemi kebewa da shi suyi magana,
cikin hanzari har yana tun-tube ya bi bayan Daddy da yanufi inda ya yi parking motar shi kasan bishiya tsayawa Daddy ya yi yana kallon Kawu Habu da sai sussunne kai yake yana zabga murmushi,

“Amm dama ba komai yasa nace mu kebe ba, wata alfarma nike nema wajenka in zan samu.”

“haba Alhaji, ai kawai ka fadi abunda kake so Insha Allah ka samu muddin dai ina da shi.”

kai Daddy ya jin-jina yana gyara tsayuwa kafin yace,

“magana ne akan yar wajen ka,”

Daddy ya dan ja numfashi, kafin yaci gaba,

“Nu’aima ta ke ko?.”
Chapter 6 · 0% Book details