← Book details Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 7

Sashe 5

Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

`` wayyo allah Umma,zai kasha ni, mugu kawai azzalumi``.
Safraz, yace
``ok baki saduda ba kenan`` yaci gaba da lafta mata belt.
Umma , ce ta shigo palon da gudu tana fadin,
``me yake faruwa ne, muryar wa nike ji kamar na Makadda.``
sauran kalamanta suka lake, ganin yadda, Safraz ke dukan ta, kamar ya samu jaka.
Umma , da sauri ta nufi inda suke tana isa ta ture Safraz,ta durkusa ta jawo Makaddarasiya jikin ta tana tattaba ta, tana fadin
``innalillahi, Safraz kana da hankali ko, jaka ka samu ne, nashiga ukku ni Sadiya,ke mikika yi mai , ya miki wannan shegen dukan.”
Safraz, yarda belt din yayi, ya koma ya zauna.
Makaddarasiya, tana kuka, tace
``wallahi ban mai komai ba Umma , kawai muguntar shi ce ta mosa, mugu kawai sai allah ya saka min``.
Umma tace,
“tashi muje.”
ta dagata, kallon Safraz da yaci gaba da aikin shi tayi, tace,

``wallahi kaci bashi, dan kalan dan gi kawai.``
taja tsaki, suka fita.
Afif, fitowa yayi daga daki, yana daura agogo, ba tare da ya kalli Safraz yace,
`` mi yasa kake biye ma waccan yariyar, kasan ba hankali ne da ita ba, gashi kasa ta rainaka``.
Safraz, dagowa yayi yana kallon shi da murmushi yace,
“kace min kawai, kana son kayi min fada dan na daki, matar ka ta gobe``.
Afif, harara ya wasa mai , yaja saki, yace
``idan ka tashi ka fito muje.”
ya nufi kofa.
Safraz, mikewa yayi , yarufe system yabi bayan shi

★…….★

AFIF POV
saye ya ke a harabar makarantar hannuwanshi na zube cikin aljuhun farin wandon makarantar, shige da ficen dalibai ya ke kallo ta cikin farin glass din da ke idon shi.
dafa shi aka yi ta baya, bai juya ba dan yasan Safraz ne,
“ kana lafiya ko?, tun da ka shigo makaranta yau baka ci komai ba.”
leben shi na kasa ya sa cikin baki ya tsotsa, kafin ya turo bakin, ya na daga kafada.
“Yeah.”
“Ok muje in sauke ka, na kwana biyu ban ga Mommy ba,”

kallon Safraz Afif ya yi, ya tabe baki.
dariya Safraz ya yi, yace
“kada kace komai please.
“ai dole kace in yi shuru, tun da kasan wajen Momy Kamilat zaka .”
Afif ya yi maganar ya na yin gaba.
bayan shi Safraz ya bi yana fadin,
“kai ban son iskanci wai ba Antyn ka bace.”
“to sai aka yi me in Anty na ce.”
Safraz da ya bude motar da Afif ya shiga, yace.
“Anty zaka kira ta mana.”
tsaki Afif ya ja.

★……

tura kofar dakin ya yi, ya shiga, yana sanye da threequeter black, da ya tsaya mai iya guiwa, da t-shirt mai guntun hannu, itama black.
kwance take asaman bed, da waya a kunnen ta, bata ji shigowar shi ba, to dama bai yi salama ba,
hawa bed din ya yi, hannu ya kai a hankali ya fizge wayar,
a firgice ta tashi zaune, tana fadin.
“wani dan islamiyan ne wannan.”
tsayawa ta yi tana kallon shi, ganin ya kara wayar a kunnen shi, shuru ya yi, yana sauraren Safraz dake fadin.
“Ayya Baby, yau sati daya fa kenan ban ganki ba, nazo kina jina kika ki fitowa, kuma kin san dan ke nazo,.”
“wallahi Safraz ka guji ranar da zaka shiga hannu na, dan iska kawai.”
Afif ya yi maganar yana lasar lebenshi na kasa.
daga daya bangaren Safraz ya ce.
“to sannu Ubana, dalla malam bama Baby wayar ta.”
kashe wayar ya yi, ya kalli Kamilat dake kallon shi, ya ce.
“yanzu Anty Kamilat, mekika gani wajen wannan yaron mai kama da aljanu, gashi kin ja min raini.”
ya yi maganar a shagwabe har yana shushshura kafa.
tsaki Kamilat ta ja, tana fadin.
“mika min wayata malam, ina wayon da za’a raina a nan, kuma da kake kiran shi yaro, bai girmeka bane?.”
make kafada ya yi, ya na kokarin sauka daga bed din,
da sauri Kamilat ta sauko ita ma tabi bayan shi,
har ya bude kofar, sai taga ya saya, ba tare da ya juyo ba.
isa inda ya ke ta yi tana fadin.
“ban wayata shugaban yanson girma kawai.”
ta sa hannu da niyar zare wayar da ke hannun shi.
bata ankara ba sai ji ta yi, an yi sama da ita, an buga ta da wed rope, ihun azaba ta saki tana dafe kanta da taji wani abu mai dumi na bi, kallon hannun ta yi, ganin jini yasa ta sakin kuka.

Afif dake tsaye ya na kallon ta, idanun shi sun rikide, sun koma fari, ganin jini na bin hannunta yasa shi, nufo inda take,yana gurnani da bude bakin shi, wanda haka ya bayyana hakoranshi da suka kara tsayi.
jin gurnanin shi ya sa ta dago kanta,ganin ya nufo ta ya sa ta mike da kyar, amma kafin ta yi yunkurin barin wajen ya riko wuyanta, hannunta da ke da jinin, ya riko yana kokarin kaiwa baki,
da sauri ta dunkule hannun, dan sauran karfin da ya rage mata tasa, tana kokarin fizge hannunta daga nashi, ganin ta kasa fizge hannun ta saki kuka tana sulalewa kasa dan ta sadakat yau kwananta sun kare,
babban tashin hankalin ta, kada Afif ya lashi jinin, dan anfada musu idan aka bari ya sha jini, to karfin ruhin da ke jikin shi zai nunku,
Gurnanin Afif da taji ya cika dakin da sakin hannunta da taji ya yi, yasa ta bude idanun ta, ta take gani dushi-dushi, Daddy ta gani rike da shi ya na kokarin fitar da shi daga dakin……✍

#zabinkaddara
#queenmk

————————————————————
typing📲
🌙 ZABIN KADDARA🌙

Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻

PAGE 9&10

Umma , tana saye gaban Abba dake zaune, tace
``gaskiya alhaji bazaiyu ba wannan ai maganar banza ce, taya yaro zai kama diya da duka kamar wani uban ta, sannan kace kada na dauki mataki, ko shi ya haifar min ita ne``.

Abba , da mamaki yake kallon ta, yace
``Sadiya nine nike maganar banza, to wallahi bari kiji, duk ranar da naji kin tayar da wata hayaniya agidan nan ranki zaiyi mugun baci, sannan ki sani zanin aro bai rufe katara``.
Umma , kanta ta nuna, tana fadin,
``alhaji nikake yi ma gori , har kana fadin raina zai baci akan wani dan kalan dangi``.
Abba , yace
``saboda naga kina manta halin yarki ne, idan ba ta wannan hanyar na yi miki magana ba, bazaki fahimta ba.”
Umma, shuru ta yi, kafin ta jah kwafa, ta juya ta fita.

★★…….

LOCOST AREA
NU’AIMA POV.
Nu’aima ,tana durkushe gaban Kawu abu ta rike kafar shi tana kuka,
Kawu abu, na saye da shirin shi na zuwa daurin aure, Mamammu,tana saye agefen su ta rike kugu tana kallon su.

Nu’aima , tana fadin,
``dan allah, Kawu , kamin rai,ka dubi maraici na, kada kamin auren dole, wallahi bana son malam buba, dan alla karka daura auren nan``.
Kawu abu, jan kafar shi da Nu’aima ta rike yake yi, amma ta mai rikon kwarai, yace,
``ke bana son shirmen banza, bazaki mayar dani karamin mutum a anguwa ba, inkika ga anfasa auren nan to ki tabbatar ni, ko ke, daya baya duniyar nan``.

Nu’aima , kuka takeyi sosai, tana girgiza kai, tama kasa fadin ko kalma daya.
Mamammu, tace ,
``ato, wannan shine maganar, inba haka ba kana kallo akan yariyar nan, sai ka zama sohon banza a anguwa``.
Nu’aima , da sauri ta saki kafar Kawu abu ta juya wajen Mamammu, ta hade hannayen ta waje daya tana girgiza mata kai, alamar a`a.
Da wannan dammar Kawu abu, yayi amfani ya fice daga gidan, batare da Nu’aima ta ankara ba.
juyowar da zata yi da niyar ta sake rokon Kawu abu, sai ganin tayi babu shi awajen, da sauri ta mike ta nufi hanyar waje .
Mamammu, da sauri ta yunkura , ta rike ta, tana fadin,
``ke wai bakida hankali ne, binshi zakiyi wajen,dalla shige daki kafin ranki ya yi mummunar baci, shashasha, kawai``.
ba musu ta nufi dakin tana kuka,


Nu’aima, durkushe take a gaban su Kawu abu, da Mamammu, da ke saye a sakar gida.
Kawu abu, yace,
``ki gode ma allah, ke mai sa`a ce Nu’aima, aure dai sakaninki da Malam buba, babu shi``.
Nu’aima, arikice ta dago tana kallon kawu abu, da murmushi a fuskarta.

Kawu abu, yaci gaba da fadin,
``an samu wani dan albarkan daya, fanshi auren ki da naira dubu dari biyu, yace shi zai aure ki``.
Nu’aima, nan dan guntun murmushin da ke kan fuskar ta ya bace, tashiga girgiza kai, hawaye na bin kuncin ta, nan ma ta kasa cewa komai.
Mamammu, tace,
``ai Babansu, wannan yaron ZAIDY, dan arziki ne, allah dai yasa ayi damu.
Kawu abu, yace ``amin dai Lami”

★………★
Afif POV
tun fitowar Afif daga gidan ya kafe shi da ido, har ya iso inda ya ke jingine ga motarshi,
“Yaya Khalil.”
Afif ya kira sunan shi yana bata fuska ganin irin kallon da Khalil din ke mai,
“muje ko?.”
Khalil ya yi maganar yana nuna mai gaban motar da ya bude alamar ya shiga,
da wani kallo na alamar tambaya Afif ya bishi ba tare da ya ce komai ba,
fahimtar hakan da ya yi yasa shi yin murmushi yana fadin,
“come on wai Khafilat ba ta fada maka zamu fita bane ba jimawa ma zamu yi ba owk.”
ba musu ya shiga motar Khalil ya rufe motar yana sakin wani shu’umin murmushi, har suka yi nisa da tafiyar hankalin Afif na kan hanya, wato idan da mutane zasu san waye shi da sun bar boye mai abu dan saff yake iya karatun tunanin mutum kuma izuwa yanzu saff ya karance tunanin Khalil din kuma ya gano me yake shirin yi amma dai bari ya bari ya ga iya gudun ruwan shi,
wayar Khalil dince ta fara kara duba wa ya yi sannan ya dauki kiran yana fadin “ I am on my way tare da shi zamu iso yanzu.”
yana gama fadin haka ya yanke kiran kallon Afif ya yi da har lokacin hankalin shi na ga window

★……
Nu’aima POV
Chapter 5 · 0% Book details