← Book details Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 7

Sashe 2

Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“su adalci manya.”
kallon inda maganar ya fito saurayin ya yi.
budurwa ce wacce bazata haura shekara ashirin 20 ba,
kwance take asaman wata katifa wadda ko riga bata da, duk ta yakuce, waya ce ahannun ta wadda itama ta yi raga-raga.
“da uban wa kike.”

wurgi ta yi da wayar akan katifar, kamar mai jira, ta mike tsaye tana gyara daurin kirjin da ke jikin ta, tace.
“da uban ka nike, kaga Mukaddas ka fita idona in rufe, iya shegenka ya fara isa ta agidan nan, wallahi zan yi maganain ka.”
shekeke, saurayin da ta kira da Mukaddas , ya kalle ta.
“Muwwwst, kin ga Badi’a ni, yanzu bana cike da iskanci , amma ki bari in yi lokacin naki zaki basu bayani.”
“dan allah ka yi lokacin nawa yanzu, ni ina cike da iskanci.”
Badi’a , ta yi maganar tana nufo shi.
“wai wani irin, iya shege ne ke damun ku,ba zaku bari muji da na uban ku ba, zaku daura naku, to tun kafin in shigo dakin nan, Badi’a ki fito ki yi wanke-wanken dake gaban ki.”

wata bakar mata mai kama da Badi’a, ta yi maganar tana dage labulen dakin.
“ kutt, Allah ya ki ya ye, ni Badi’a, ni ce zan yi wanke-wanke, tabb wallahi ba uban da zan ma wannan aikin , wai ma Innarmu jaka ake son mayar da nine a gidan nan, ba ga Sabira nan ba, ku sata mana.”

Badi’a ta yi maganar tana koma wa kan katifar da ta tashi, ta kwanta ta jawo wayar ta taci gaba da dannawa.
daga waje ta jiyo muryar Mamammu, tana fadin.
“ai kin san ita Sabirar jakar ce, da zata yi ta zaman yi muku aiki.”
muryar Goggo suka sake ji tana fadin.
“ ohh ashe ita wadda ke kichin tana girki, shugabar jakuna ce kenan?, ke Munira fito nan, dan uban kowa agidan nan yau a wini da yunwa.”
fitowa daga dakin matar da Badi’a ta kira da innarmu ta yi, tana fadin.
“Halima idan zaki yi magana ki rinka kula da abun da kike fadi, tun da ba ubanki ya kawo abincin ba, baki isa ki hana a dafa ba.”

“ai kam za’a dafa, amma dai ba Munira ce zata dafa shi ba.”
cewar Mama tana kama kugu.
“ni dan allah Mamammu ban hanya in wuce, ban son hayaniya, idan mutum na gidan nan ba shi ba natsuwar zuciya, bari na barmuku gidan, in ya so ku cinye kan ku.”
masawa, Mamammu ta yi, wata budurwa ta fito daga dakin, sanye take da riga da sket na wata atamfa da ta gama kodewa , dinkin yakama jikin ta sosai mayafin da ke jikin ta kuma ko kafadar ta bai sauko ba,
fara ce amma da ka kalli farin kasan na shago ne,
“Sabira ina zaki ?.”
yaron dake rike a hannun Mamammu, ya fadi ya na kokarin barin hannun Mamammu,
“ in da uwarka ta aike ni, zani.”
ta yi maganar ta na ficewa daga gidan.

★...........★

“ina zaki je Nu’aima.”
dakatawa ta yi daga kokarin dage labulen da take da niyar yi, ta ju yo tana kallon mahaifiyarta, dake kwance akan katifar da ita kadai ce acikin dakin sai jakar kayan su.
“duk zagin da kika sha wajen Yaya Habu bai ishe ki ba, zaki fita a kara miki ko?.”
“ Ummy,dama jina yi sunce baza su iya yin wanke-wanken ba, shine zanje inyi.”
“dawo ki zauna, kema ba zaki yi wanke-wanken ba.”
ba musu ta koma ta zauna a kasa gefen katifar,
sare ta Ummy ta yi da ido, ganin yadda ta zuba ma yasun hannun ta ido, tasan tunani take yi, wanda dama ya zamar mata wajibi ta yi shi, duda ta yi kankanta da yin shi, amma yin tunanin wajibi ne a wajen ta, tun da ta tsinci kanta a cikin wannan gidan da basu san me ake nufi da zaman lafiya ko tausayi ba, kowa kanshi yasani, to ya zata yi, nan ne inda KADDARA ta zabar mata ta yi rayuwa.

shekarun ta sun yi kankanta da daukar wahalhalun rayuwa irin wayan nan, duka-duka fa sha biyar 15 take yanzu, ga rashin mahaifi ga rashin kulawar dangin shi, gakuma dangin mahaifiyarta data ke cikin su, gara ace babu su baki daya, zai fi.
“ki yi hakuri Nu’aima.”

da sauri ta dago kanta, ta kalli Ummy, hannunta tarike tana girgiza mata kai.
“dan allah Ummy, ki daina bani hakurin nan, da ban san dalilinki na bani shi ba.”
murmushi Ummy ta yi, tana kallon fuskar ta da ta yi fayau kamar babu jini a jikin ta, lips dinta sun sake yin red, idanun ta sun yi haske sosai har sheki suke yi,
hakan alamu ne na tana jin yunwa, dan idan ta na jin yunwa ga ba dai fita hayyacin ta take yi,
hannu tasa taja dogon hancinta da saman shi ya yi jah, saboda yanayin sanyin da ake ciki.

“ Nu’aima baki hakuri, nauyi ne da ya rataya a kaina, dan babu wani hakkin ki da na sauke amasa yi na na mahaifiyar ki.”
ba tace komai ba, sai kantar da kanta da ta yi akan hannun Ummy,

“kin tabbata kina lafiya, ba abun da kike boye min.”
dagowa ta yi ta kalli Ummy da ta yi tambayar , ganin ta kafe jikin ta da ido, ya sa ta kalli jikin nata, murmushi ta yi, da yasa dimple din ta na hannun hagu lubawa, ba yau ne karon farko da Ummy ta saba yi mata irin wannan tambayar ba,
ko ita ta kan yi ma kanta wannan tambayar, idan ta kalli jikin ta , anya ko lafiya lau ta ke, a zahirin gaskiya jikin ta ya yi ma shekarun ta kankanta, dan idan ka kalli jikin ta ko fuskarta zaka yi zaton yar sha uku 13 ce,

kuma bawai
rama bace, ko yana yin wahala, suka mayar dajikin ta haka , halittar ta ce haka.
“Ummy lafiya ta qalau fa.”

ta yi maganar ta na murmushi.
ita ma Ummy murmushi ta yi,tace.
“to masha allah, allah ya karamiki lafiya.”
“ameen Ummy na, ke ma allah ya baki lafiya, ya nuna min ranar da zanga kin mike akan kafafun ki.”
“amen ameen, insha allah sauki ya kusa zuwa, dan ina jin sassauci sosai cikin jiki na.”
“to allah ya baki lafiya.”…..✍

#zabinkaddara
#queenmk

————————————————————
typing📲
🌙 ZABIN KADDARA 🌙

Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻

Page 3&4

GRA AREA
tana zaune a gefen gado, Abba kuma na saman gadon ya jin gina da kan gadon da system akan kafan shi.
UMMA , tace, ``alhaji, wai nikam yaushe MUHRIS zai dawo ne,[ ayi ta ta kare dan na gaji da jiran gawan shanu],[ anata min gafara sah ban ga kaho ba,]wallahi dan baka san yadda na tsani wannan Afif din bane``.
ABBA ; duk maganar da takeyi bai dago daga danna system din da yakeyi ba,sai da ta dasa aya sannan ya dago yana fadin, `` ina ga kin manta wannan gidan na SARDDAUNA ne, ko kin manta da bazarshi muke rawa ne``.
UMMA; cikin yar fusata ta fara magana, `to wai alhaji, sai me dan da bazarshi muke rawa, sai mu saya muna kallon dukiya , ba mai ci, a`a wallahi bazai yu ba , ina dan mafari bare dan dalili, maganar gaskiya zan ci dukiyar nan ne , tunda mai ita bai damu da ita ba, ah`ah``.

MAKADDARASIYA ; duk maganar da sukeyi, tana labe a kofa, tana jin su, kai ta girgiza tana cizon yasa,ta rike kugu tana fadin,
``ok wato abun da su Umma ke kulla wa kenan, to lallai sai dai in ban kusa, amma da raina da lafiya na ba, wanda zai cutar da, Saddauna`` kai ta sake girgizawa, ta bar kofar dakin.
Palo ta fito, Nasiba na zaune tana kallo, juya wa tayi tana kallon ta , har ta samu waje ta zauna.
sannan tace mata,
``meya faru ne``.
Makaddarasiya, tace `meko zai faru bayan maganar Saddauna, ni na kasa gane meyasa Umma ke son ganin bayan shi, bayan tasan duk duniya babu wanda nike so sama das hi, bansan ko so takeyi na kasha kaina ba, dan idan na rasa Sardauna, mutuwa zanyi``.
Umma , dake saye abayan su, batare da sun ganta ba, tace, ``sai me to in kin kasha kan naki, wakeda hasara, insha allahu kuma burina saiya cika``.

Makaddarasiya, tana tura baki da hararar inda Umma ke saye,tace ``ba amin ba wallahi, Saddauna yafi karfin ki`` .
Umma , duka ta kawo mata, tana fadin, `ke, kishiga taitayinki dani ina wasa dake , wallahi zanyi mugun saba miki``.
Makaddarasiya, da sauri ta mike saye ta kauce ma dukan da Umma ta kawo mata, tana tura baki, ta bude baki da niyar tayi Magana.
Umma tace, `ki bace min da gani, kafin na sauya miki kamanni, shashasha kawai, kuma ki sa aranki keda Afif sai dai hange, dan ban haifi `yata dan naba wani dan iska aurenta ba``.
Makaddarasiya, daki ta nufa tana gunguni.
Umma , kallon ta ta mayar kan Nasiba dake kallonta hankali kwance kamar batasan suna palon ba, kai Umma ta girgiza, ta zauna.

★...........★
Chapter 2 · 0% Book details