← Book details Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 7

Sashe 1

Zabin Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Typing 📲
🌙ZABIN KADDARA🌙

Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻

MARUBUCIYAR

📔TSUGUNNO BATA K’ARE BA:free
📙KABILATA :free

And
Now
🌙ZABIN KADDARA 🌙

Page 1&2

BISSIMILLAHIR RAHMANIRAHIM

GRA,zuru kebbi state Nigeria

Zaune suke, a yalwataccen dainin table din da ke ,dauke da kujeru goma sha biyu 12, wajen ya yi shuru, ba kajin komai sai karar haduwar plate da spoons.

Alhaji Badamasi, dago kanshi ya yi. ya bi yaran nashi dake zaune a dainin din su biyar 5, duka mata, kallon karamar cikin su ya yi, wadda ke zaune kusa da shi.
“ ke Kamilat, je ki duba min sweetheart shurun ya yi yawa.”
“Owk Dad.”

wadda ya kira da Kamilat ta amsa, tana mikewa cikin falon ta nufa, wanda ya gaji da haduwa an kawata shi da tokish sopa golden color set biyu 2, duk abun da ke cikin falon golden ne,

kafar benen ta nufa, wani karamin falo ta shiga, wanda kayan ciki suka kasan ce blue color ne, akalla kofofin da ke cikin falon, zasu kai shidda 6, kofar da ke tsakiya ta nufa, da sallama ta tura kofar .

lumshe idanuta ta yi, sana diyar sanyi, da dadda dan kamshin da ya daki hancin ta, ahankali ta fara bin dakin da kallo, daki ne madaidaici. pentin dakin white ne,sauran kayan da aka kawata dakin dasu kuma pink, kama daga madaidaicin royal bed, da labule da senter carpet da study table duka pink ne, kallon ta ta kai kan merrow, cike yake da kayan shafa kala- kala, kallon ta ta mayar kan gado inda rabin gadon duk teddy ne suma pink,

Waro idanu ta yi, ganin ba kowa a kan bed din, taka wa ta yi, ta isa gaban bed din, lokacin ne hankalin ta ya kai kan kafafun mutum dake ta saman kan bed din, sun leko daga cikin bedsheet, wanda hakan ke nuna kan koma waye, to yana ta kasan bed din kenan, karasawa ta yi, ta kama kafafun duka biyu ta jawo su.

jaye kafafun aka yi, zuwa cikin bedsheet din, ganin haka yasa ta jan bedsheet din da karfi ta ajiye gefe, tana fadin.
“Wannan wani irin iskanci ne, a garin ku da bedsheet ake lullubewa, ko duk kauyancin ne?”.
da wata ‘ yar tsiririyar murya mai kama da ta yara aka ce.
“why why Anty Kamilat, meya sa kike da damuwa ne? fisabilillah barcin ma bazaki bari mutum ya yi cikin salama ba?”.
“ kaniyar salamar , ba abun da ka iya sai barci, kaci ka kwanta shine aikin , to ka tashi Daddy na jiran ka a dainin.”
tashi zaune ya yi, yana musussuke ido.
matashin saurayi ne, wanda ba zai haura shekara sha takwas 18 ba, kyakkyawa ne irin kyawon nan da kallo daya zaka yi ma mai shi, kasan ya amsa sunan mai kyau.
fari ne, irin farin nan mai surki da yellow, dogo ne yana da yar jiki dan baza a kira shi da ramamme ba, yana da dogon hancin, da yadace da sarin halittar fuskar shi, mai dauke da manyan idanuwa masu yalwar gashi, yana da yalwar gashin gira wanda suka hade da juna ta goshin shi, lallausan sumar kanshi mai yawa sai kelli take yi alamar tana shan gyara, ahankali yake motsa labban shi da suke pink dasu masu dan fadi,
kasan cewar fuskar shi babu ko tsillin gashi yasa ya yi shar dashi ,
turo baki ya yi cikin shagwaba ya ce .
“gaskiya Anty, sakani na dake, sai allaha, ba dai mutum ba, dan kina shiga hakki na sosai”.

tsaki Kamilat ta yi tace.
“idan ka ga dama ka tashi, kiran Daddy ne ba nawa ba”.
tana fadin haka ta dauki teddy daya, ta buga mai a kai ta juya ta bar dakin.

da harara ya raka ta yana sake turo baki, kamar anyi mai dole ya sauko kan gadon yana kunkuni,Bathroom ya faɗa wanka ya yi me rai da lafiya ya fito sanye da blue bathrobe a jikinsa, farar fatar nan sai walƙiyar kyau da tsantsar jin daɗi take. tsaye ya yi gaban ƙaton mirror'n Hand dryer dake saman mirror sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da sumarsa da tafi kama data ƴan India, lotion ɗin dake jere saman mirror'n ya shiga shafa wa jikinsa da spray's nashi masu ƙamshi, sannan ya nufi gaban wardrobe nashi.tsabbb ya shirya cikin white t-shirt da blue jeans, phone's nashi kaɗai ya dauka yana nufar main Parlour,

“aina kika baro shi kuma”.
Daddy ya yi tambayar yana kallon Kamilat da ta dawo dainin din .
zama ta yi, tana fadin,
“ barci na tarar yana yi, amma ya tashi”.
dan karamin tsaki Momy ta yi, tana fadin,
“wannan kayan aman har ina, ga ya kuma zuciya ta ki tashi, allah ka muna magani, tsoro na allah tsoro na kada Afif ya zama dan daudu”.n
“subhanallah, malama wannan wace irin magana ce, dan daudu ana zaune lafiya, insha allahu bazan ga dan daudu ba.
“nima ba fatan ganin nike ba Daddyn su, amma lamarin Afif ne sai du’ai, gaba ki dai bai da dabi’un maza.”
Daddy yace,
“ki yi la’akari da yanayin da ya taso, acikin mata ya tashi, dole za’asamu wasu yana yin nasu a tare da shi, amma da ya kara girma zai bari, kuma ma kwana nawa ne sun bar gaban shi, sai dai in ya kai musu ziyara.
jin takun tafiyarsa da baya taɓa ɓuyewa ne ya sanya su kallon stais din,
taku ya ke cikin nasuwa hannun shi daya na cikin aljuhun wandon shi, dayan kuma na cikin lallausar sumar kanshi, sai yamutsa fuska ya ke yi kamar wanda ke shirin yin kuka,
yana iso wa dainin din, ya rungume Jalila ta baya, yana fadin,
“good morning Anty Jalila.”
“morning Saddauna, haw was ur night.”
Anty Jalila ta amsa tana shafa kanshi,
“sohhh sweet big Anty.”
sakin ta ya yi, ya isa inda Anty Afiya take, itama ya rungumeta hadi da gaisuwa, cike da kulawa ta amsa , tana tambayar shi yau bazai je makaranta ba?.
“No sai Monday insha allah.”
yadda ya yi ma su Anty Afiya, haka ya yi ma su Anty Kafilat da Anty Jayyada, ko kallon inda Kamilat take bayyi ba, haka ita ma bata kalle shi ba.
isa ya yi inda Mommy ke zaune, ya rungume ta ya manna mata kiss a kumatu.
Daddy dake kallon su yace,
“ sweetheart, nifa nace a tashe ka, amma ni zan zama na karshe?.”
“no Daddy, naka gaisuwan na musammam ne, ya yi maganar ya na isa gaban Daddy.
kawai sai gani sukayi, ya durkusa gaban daddy, baki sake suke kallon shi, har Daddy da aka dukama, da mamaki Anty Kafilat tace.

“tohh yau kuma.”
tana rike baki, sanin bai dukawa gaida kowa, acewar shi ciwon baya zai kama shi, gara ya mika gaisuwar daga tsaye.
mikewa ya yi, ya koma kujerar dake kusa da ta Anty Jalila ya zauna, ya na fadin ,
“to menene kuma.”
ganin yadda suke kallon shi,
mikewa Daddy ya yi, ya musu sallama ya fita, Anty Afiya da Anty Kafilat da Kamilat, suma mikewa sukayi suka yi musu sallama, Anty Kafilat da Anty Afiya zasu je wajen aiki, ita kuma Kamilat zata makaranta.
shima Afif mikewa ya yi, yana yamutsa fuska, kallon abincin da aka zuba mai Anty Jayyada ta yi, taga bai ci ba.
“ ina zaka tafi Saddauna?.”
hanyar sama ya nuna mata, yana langabar da kai gefe hadi da turo baki, tashi ta yi, ta kama hannun shi suka nufi bene.
Mommy da tun dazu take bin su da ido tace.
“ba dai kai shi zaki yi, ya kuma kwanciya ba, bayan yanzu ya tashi?.”
“Mommy ba da yawa zai yi barcin ba, tare ma zamu fito ko Saddauna?.”
ta yi maganar tana kallon fuskar shi, da ya kwantar kan kafadar ta, duda kasan cewar ya fita tsayi nisa ba kusa ba, kasancewar shi dogo ne.

kai ya jinjina mata yana lumshe ido.
“kada ka manta yau Juma’ah.”
Anty Jalila tayi maganar ba tare da ta kalle su ba.
hannun shi ta ja suka haye, Mommy dai da ido ta raka su tana girgiza kai.
suna shiga dakin, ya sake hannun ta, ya zare rigar jikin shi da wando ya rage daga shi sai guntun wando, haye wa gadon ya yi, ya jawo teddy daya ya rungume.
“Saddauna, wai wannan dakin macce ne ko na namiji ?.”
Anty Jayyada dake kare ma dakin kallo ta yi tambayar.
bude idanun shi, da ke rufe ya yi ya zuba mata.
“Anty Jayyada, wannan ai cin fuska ne.”
ya yi maganar rai a dan bace kuma cikin shagwaba.
takowa ta yi ta isa in da ya ke kwance, ba tare da tace komai ba ta fara shafa kanshi.
Rufe idanun shi ya yi, tun ya na sauraren yadda hannun ta ke sauka saman sumar shi, har barci ya yi awon gaba dashi.
sai da ta tabbatar da ya yi nisa da barcin, sannan ta mike ta rage gudun Ac ta fita.

★...........★

LOCOST AREA

“dan uwar yariyar nan, ni zata mayar dan iska, ina magana ta shige daki, to ki jini da kyau, duk ranar da zaki kuma fita da yaron nan cikin rana, wallahi sai na lahira ya fiki jin dadi, yau naji iskanci, fatar shi irin taki ce, ko shegen yawon nan naki kike son ki koya mai.”

Tsaye dattijon ya ke, a tsakar yamusassen gidan da ko ina raggogi ne, alamar an kare gidan dan ba Katanga.

“wai dan allah, mutanen gidan nan meyasa baku san yadda ake barin bawa ya huta ba, yanzu barcin ranar ma baza’a bari mutum ya yi cikin salama ba, haba, wannan wani irin rayuwa ne , to wai kai Baba me ma ya dawo da kai gidan da ranar nan.”

juyawa dattijon ya yi, ya kalli inda matashin saurayin da ya yi maganar ya ke tsaye,
saurayi ne wanda bai yuce sha shidda 16 ba.

“ uban ka ya dawo dani gidan, shege mai kama da halittun ruwa, gidan ka ko nawa.”
“naka, amma dai ba adalci cikin irin wannan dawowar da za’a takura ma mutane.”
saurayin ya yi, maganar yana juya wa, dan komawa cikin dakin da ya fito.
Chapter 1 · 0% Book details