← Book details Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 7

Sashe 5

Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

YARINYAR BABA
[07:23 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 121-130
Haka rayuwa tacigaba da tafiya da ilham, dan
yanzu ilham ta wuce duk 'yanda me karatu ke
tunani yau kimanin shekarunta hudu cikin
'Kungiya likafa taci gaba, dan yanzu 'kungiya
tafara sakar masu kud'i suna fantamawa a gari,
sa6anin da, da ba'a basu kud'i saidai suna abinda
sukaga dama batare da wani ko wata ya takura
rayuwarsuba.
Yayinda kullum 'kungiyarsu ta _*AJI DADIN
RAYUWA*_ take 'kara ha66aka dan yanzu Abigael
ta'kara samo masu salon tsafi, Inda arana sai
susha jinin mutum a 'kalla biyu ko ukku.
Ilham tasaki jikinta cikin 'kungiya, fantamawa
take cikin Gari tana yanda taga dama batare da
wani ya takurataba, dan yanda ilham ke hawa
manyan motoci masu tsada da yanda take fita
gari ko d'an gwamna Albarka, ko kad'an dadynta
bekawoma ransa kome akan hakan ba, dan
atunaninsa kud'i sane ilham ke amfani dasu,
besan ilham ta dad'e da barin amfani da
'kud'insaba sai wanda 'kungiyar aji dad'i ke basu.
Momy kuwa har yau har gobe tana son
tsawatama ilham amma takasa, addu'a kullum
take Allah yayimata maganin abin, kuma ya
ku6utar da ilham daga sharrin shaid'an.
**********************
_BAYAN AHEKARA UKKU_
Yau 'kungiya tayi taro na musamman wanda ba'a
ta6ayin irinsaba, su ilham ne duddur'kushe gaban
Abigael wacce ke zaune kan wata katafariyar
kujerar tsafi, sanye take da ba'ka'ken kaya sai
wani jan kyalle data d'aure 'kugunta dashi.
Yayinda duk matan dake gurin suke d'aure da
wani yadi me sil6i me zanen jikin maciji, iyakar
d'aurin be wuce gwiwarsuba, sunyi d'aurin gaba
dashi an d'aure daga baya.
Mazan kuma sanye suke da gajerun wanduna
kalar ja.
Sun nutsu suna sauraren bayanin da Abigael
kemasu na yanda 'kungiya zatasamu cigaba.
Bayan ta gama ne taro na shirin tashi tace
"sannan bayani na 'karshe 'kungiya na bu'katar
jinin mahaifin ilham,.......
Wani mummunan fad'uwar gaba ilham taji cikin
tsananin firgici ta d'ago da dara-daran idanunta
takai dubanta ga Abigael tana fad'in "no
impossible bazan ta6a bayar da jinin dadyna ga
'wannan 'kungiyarba, kunsan kuwa yanda yake
nunamin so.....ta fashe da wani mahaukacin
kuka, dan gabanta yan 'kungiyar ke sadaukar da
iyayensu ko 'yan'uwansu dan suji dad'i kuma da
ita ake cin moriyar abun, yau kuma abun yafad'o
kanta anya tanada hujjar hana jinin dadynta,
"Nooooo...... Tafad'a da 'karfi, hakan yayi dai-dai
da dawowar ruhinta jikinta,
Momy tagani tsaye kanta tana tofa mata addu'o'i
duk illahirin jikinta yajike da gumi kamar wacce
aka watsama ruwa.
Love u all
Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:38 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 141-150 washe gari da misalin 'karfe tara
na safe, Zaune suke kan dining suna breakfast
Kowa naci hankalinsa kwance Amma banda
ilham wacce taketa juya spoon d'in cikin cup d'in
tea ba abunda ke zuciyarta sai tunanin yanda
zata ku6utar da daddy daga hannun shugabar
'kungiyarsu Abigael. Duk abinda ilham keyi daddy
na kula da halin datake ciki Saboda haka shima
duk sai yaji yashiga damuwa lokaci guda Ya
maida dubansa ga ilham yace _*"YARINYAR
BABA*_ meke damunki? Da sauri takai dubanta
ga daddy sannan tasaki fuskarta ta 'ka'karo wani
busashshen murmushi Wanda zamu iya kira da
ya'ke Wanda yafi kuka ciwo tace "Ba kome, cikin
damuwa daddy Yakama hannunta ya had'e
danashi cikin sigar rarrashi yake magana "Haba
ilham ashe akwai wata damuwa dazata sameki ki
6oyemin. Ilham ta wasance tace wallahi daddy
ba kome, kawai hakanan naji jikina ba dad'i
amma yanzu ma naji kome ya wuce. Duk abinnan
Momy na zaune tana kallonsu, bata sanyamasu
bakiba, illah wani irin 6acin rai dake addabar
zuciyarta Ganin yanda daddy kullum yake 'kara
shagwa6a ilham Gashi itakuma yanzu bata iya
hana kome. Cikin jin dad'i dady yace "yauwa
ilham d'ita kinsan banison 6acin ranki ko kad'an,
wani murmushi ilham tasaki wanda bekai cikiba.
Dady yace "yanzu dai ki shirya mufita shan ice
cream, ko kin washe dan banison kina shiga
damuwa, 'Kila idan muka fita muka d'an zaga
gari kin warware. Su Hassan da hussaina dake
zaune sunajin duk yanda daddy ke rarrashin ilham
kamar wata 'karamar yarinya, Wanda kosu
beyima haka, suda suke 'kannenta wacce tabasu
kusan 9 Year's, sukace "daddy muma muna
zuwa.... Kafin su ida fad'a ya tari numfashinsu
tare da d'aga masu hannu yace "kubari anjima
driver ya kaiku banison 6ata lokaci.... Sunajin
haka suka nufi d'akinsu suna turo baki dan sun
dad'e da sanin yanda daddy ke nuna banbanci
tsakaninsu da 'yar'uwarsu. Bayan sun wuce ne
daddy ya kalli ilham yace bari inshiga toilet inyi
wanka, Kema kije ki shirya, bejira jin amsar
dazatabashiba yanufi toilet d'in Ilham tayi saurin
binshi takamo hannunshi idanunta na zubar da
hawaye tace dan Allah daddy kada kayi
wankannan...... Dady yace dan me? Ilham tarasa
amsar dazata bashi sai hawaye dake zuba daga
idonta. Ganin batada niyyar yimashi magana yasa
ya zare hannunshi daga nata tare da saka
'kafarshi toilet d'in. Love u all Zee Elkaseem

YARINYAR BABA
[07:45 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 131-140 lham lafiya mike damunki,
tundaga d'akina nake jiyo ihunki kina fad'in
impossible, meye baze yiyuba? Cikin tsananin
rud'ewa jikinta na 'kyarma tace "ba kome kawai
nayi wani mafarkine wanda ya tsoratani, Cike da
damuwa momy tace ilham dole kiri'ka muyagun
mafarkai ilham baki damu da addininkiba, baki
damu da sallah ba barantana addu'a Nidai sai dai
ince Allah kyauta. Haka momy tabar d'akin ilham
zuciyarta cike da tunani barkatai, al'amarin ilham
yana matu'kar tsoratata, gashi ko kad'an bata iya
tsawatar mata. A ranar haka ilham ta wuni
sukuku ba 'karfi jikinta ko kad'an tana tunanin
yanda zata tseratar da daddynta daga sharrin
Abigael, Bakin iya tunani tayi amma batasamu
wata mafitaba. Washe gari kuka ilham tayini
tanayi ta kulle kanta cikin d'aki, dan jiya 'kungiya
ta tabbatar mata da kada ta kuskura tawuce
kwana biyu bata bada jinin daddyntaba. Haka
tayi kuka tagode Allah batare da wani yasaniba,
har kanta yafara ciwo. _*BAYAN KWANA BIYU*_
Yaune kungiya ta ibarma ilham kada ta wuce
bata kawo jinin mahaifintaba, _*Misalin 'karfe
3:00am na dare*_ Taron 'kungiyane kamar yanda
suka saba, saidai yau tsai-tsaye suke yayinda
Abigael ke zaune kan katafariyar kujerarta, ilham
kuma tana dur'kushe gabanta tana sharar
hawaye, Cikin tsananin 6acin rai Abigael ta kalli
ilham tafara magana tare da mi'kewa tsaye tana
nunata da sandar dake hannunta "Kisani ilham
baki isa kisha jinin iyayen wasu ba kuma kiyi
arzi'ki da kud'in kiji dad'in rayuwa kekuma kice
baza'aji dad'i da jinin iyayenkiba. Tunda kika
shigo cikin 'kungiyarnan yau tsawon shekara
bakwai bamu nemi wani kwa'kkwaran Abu daga
garekiba sai yau, saboda haka dole kibi umarni
ko kinso, ko kin 'ki. Sannan kisani guri na'kara
kure mana kinaso ki kawo mana cikas, tokisani
gobe da daddynki yashiga toilet da niyyar yin
wanka baze fito da raiba, dole ne musha jininsa
yanda akasha jinin iyayen Kowa cikin wannan
'kungiya. Abigael nagama fad'in haka taro
yatashi, ilham na dur'kushe inda take takasa ko
motsin 'kirki sai wasu hawaye masu yaji ke zuba
daga idanunta. 'Dago kan dazatayine taga wayam
ba Kowa gurin ba Alamr mutane sun zauna,
hakan ya tabbatar mata duk sun tafi, Wata uwar
'kara tayi sannan tafd'i gurin tana birgima, Jitayi
andafata Hakeem tagani, cike da tausayawa yake
rarrashinta, har a zuciyarshi yakejin ilham besan
6acin ranta amma yazasuyi dokar 'kungiyace dole
tabi, haka Kowa yayi. Sai gab da dallar asuba
sannan ilham da Hakeem sukabar gurin. Love u
all Zee Elkaseem
Chapter 5 · 0% Book details