Sashe 3
Yarinyar Baba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
[04:48 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 61-70
Wani 'katon fili aka jiyeta tskiyar wasu mutane
wanda ganinsuma abin tsoro ne, su duka sanye
suke da jajjayen kaya sunyi d'amara da wani
ba'kin kyalle sannan sun d'aura wani a
kawunansu, fuskokinsu anyi wani zane a
goshinsu da farin Abu, sannan bakunansu
ba'kikkirin kamar sun shafa ba'kin tukunya.
Wata mace ce zaune kan wata katafariyar kujera
wacce akayima kwalliya da zanen kwarangwal
d'in kan mutum, matar tana ri'ke da wata farar
yazga a hannunta, koda ganin matar basai ka
tambayaba kasan itace shugabar wannan
mutane.
Ilham na durkushe tsakiyarsu takasa d'ago da
fuskarta barantana ta kalli mutanen dake gurin,
saida wannan matar ta taso tazo gaban ilham ta
nunata da wata sanda take wani haske yafito
daga jikin sandar yashiga jikin ilham, lokacin
ilham taji duk wani tsoro ya kawar daga cikin
zuciyarta ta d'ago da manyan idanuwanta tari'ka
bin mutanen dake gurin da kallo, abinda yabata
mamaki shine mutum na farko data fara tozali
dashi shine Hakeem best friend d'inta sannan big
boy sai kuma Leena sai sauran class mate d'insu
sunkai su goma sai sauran mutanen dabata
saniba.
Wannan matar wacce itace shugaba ta kalli
ilaham tace barka da shigowa wannan 'kungiya
tajin dad'in rayuwa, my name is Abigael, nice
shugabar wannan 'kunhiya tajin dad'in rayuwa
yawanci duk wanda kikagani a nan suna cikin
wannan 'kungiyar ne kuma sun shigetane dan
sunason jin dad'in rayuwarsu batare da sun samu
takurawa daga gurin iyayensu ko waniba.
Nasan jiya zakiyi mamakin yanda Momy takasa
aiwatar da kome a kanki lokacin dakikayo dare
gurin birthday d'in Hakeem to wannan 'kad'an
kenan daga cikin aikin wannan 'kungiya tajin
dad'in rayuwa idan zaki lura cikin wannan
'kungiya duk yarane yan kimanin shekaru sha
takwas sha bakwai zuwa ishirin, zakiga a zahiri
suna aikata abinda sukaga dama ba tare da
iyayensu sun takurasuba duk da wasu daga
cikinsu basuda iyayen kuma hakan besa sun
shiga cikin gararin rayuwaba, to daga yau kema
kinzama member ta wannan 'kungiya.
Sannan Abigael takoma kan kujerarta ta zauna
bayan tagama ma ilham wannan bayani, ilham
kuwa zuciyarta tagama dakewa da 'kungiyar
lokacin tagama amicewa da zama yar 'kungiyar.
Abigael ta d'aga sandar tsafinta sama take wani
haske ya mamaye gurin duka yan 'kungiyar suka
had'a baki sukace
*AJI DA'DIN RAYUWA*
Abigael ta kalli ilham tace gobe munason jinin
momynki koya yake kiyi kokari yazuba 'kasa.
Ba'a jira jin abinda zata fad'aba Abigael ta
sallami taro Kowa Yakama gabansa.
Love u all
Zee Elkaseem
YARINYAR BABA
[04:52 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR*
*BABA*
_*Written & Edited*_
_*By Zee Mmn Khady*_
*```Just a short story```*
*Page* 71-80
Washe gari ilham ta tashi jikinta ba kwari ko
kad'an, ba abinda take tunawa sai abinda yafaru
da ita daren jiya, a zuciyaryta tace _(Ashe dama
shiyasa su Hakeem da Leena da big boy basuda
wata matsala a rayuwa kullum zaka gansu cikin
farin ciki, basuda wata damuwa a rayuwa abinda
sukeso shi sukeyi,)_
Ta numfasa tace _"to ay nima banida matsala
kan kome tunda duk abunda nakeso dady
yanayimin kuma bayason 6acin raina, matsalata
dai Momy, kuma itama yanzu tazama labari
tunda Abigael ta tabbatar min bazata 'kara yimin
fad'aba zanyi duk abinda nakeso_.
Cike da 'karfin gwiwa ta tashi tafad'a toilet tayi
wanka sannan takira Ameeno ta kawomata break
fast, bayan ta gama shirin tsaf cikin kayan
makarantarta, sannan tayi kalaci tagama ta
tsallake ta wuce, bayan fitarta Ameeno tazo ta
d'auke kayan ta maida kitchen...
d'akin su hassan da husaina ta wuce ta iske me
aikinsu tagama shiryasu takamo hannunsu suka
fito, falo suka iske Momy da daddy sun kammala
nasu kalacin, dady cikin shigar manyan kaya
yana shirin fita gurin aiki, ganin fitowar su ilham
yasashi washe baki yana dariya yace "Ilham
*_YARINYAR BABA_* yau zakije school d'in, cikin
sanyin jiki tace "eh dady zanje, cikin fara'a yace
to kuzo muje in saukeku, ilham tace "to amma
dan Allah dady inaso kabani 10k zanba wata
friend d'ina gudummuwa zatayi birthday, dady
yace "ba damuwa kije d'akina ki bud'e loka ki
d'auko 20thausand ay dubu goma me
zasuyimaku a gun birthday, wani irin farin ciki
yakamata tace 'thanks my dear dad, tanufi d'akin
cikin rawar jiki a zuciyarta tanata godema
dadynta da yanda yake biya mata duk wata
bukata data kawomashi.
Harta kai bakin 'kofar d'akin, Momy ta daka mata
tsawa
Ke Ilham dakata.....
Jiki na 'kyarma ilham ta tsaya cak inda take bata
ko 'kara taku d'ayaba.
Momy tace kada ki kuskura ki d'auki
kud'innan......
Love u all
Zee Elkaseem
YARINYAR BABA
[04:59 PM, 01-Oct-16]
by ZAINAB ELKASEEM
*YARINYAR* *BABA* _*Written & Edited*_ _*By
Zee Mmn Khady*_ *```Just a short story```*
*Page* 81-90 Ke Ilham kada ki kuskura ki d'auki
kudinnan..... Ke yanzu dan kina hauka zaki d'auki
dubu ishirin ki kaima wata dan zatayi birthday
dan bakisan ciwon kankiba, ke shikenan kullum
aikinki kenan daga biki sai birthday fatty, haba
ilham kiyima kanki fad'a mana, Sannan Momy ta
juya gurin daddy tace "haba dadyn ilham
bekamata ace ka d'auki kud'i kamar hakaba kaba
ilhan takaima wata 'kawarta dan zatayi birthday
fatty, ga mutane nan masu Neman taimako da
yawa kaje ka basu mana Allah zebaka lada.
Daddy ya fusata da maganar Momy yace
"banison abinda kikemun kibarni inyima 'yata duk
abinda takeso idan banyimataba waye
zanyimawa, ilham itace farin cikina kuma itace
nafara sawa a idanuna amatsayin 'yarda na
haifa, saboda haka kada ki kuma yimin haka.
Momy ta 6ata rai tace "to wallahi Alhj yau duk
abinda ze faru saidai yafaru Amma wallahi ilham
bata isa ta d'auko 20k takaima wata banzar
'kawaba wacce batada tarbiya, ni wallahi wannan
makarantarma ko kad'an yanzu bani 'kaunarta.
Dady ya kalli ilham yace "jeki d'auko ninace ki
d'auka kuma kud'inane bana momynkiba, ilham ta
matsa da niyyar shiga d'akin Momy ta daka mata
tsawa "kada ki d'auko.... Dady yace jeki
d'auko..... Ilham tawuce tasa kai d'akin Momy na
kada tayi amma bata sauretaba ta kutsa kai cikin
d'akin aiko a fusace Momy tabita d'akin ta
ficikota ta falla mata wani lafiyayyen mari, tace
wuce dan ubanki. Ilham ta dafe kunci tafasa
'Kara saboda tsananin zafin marin da momy
tayimata, jin haka yasa dady shigowa d'akin yana
tambayarta abinda yafaru. Su Hassan da
Hussaina kuwa sungaji da jira saboda haka
sukaje driver ya kaisu school, dan dama kullum
shine ke kaisu idan kaji dady yace ze kaisu to
tare da ilham za'ayi tafiyar to itakuma ba kullum
take zuwa school d'inba. Ranar dai hatsaniya
akayi sosai tsakanin Momy da daddy, Momy
kuma ta dage akan baza'a d'auki kud'inba
'karshema kulle d'akin tayi ta tafi d'akinta da key
d'in. Cikin 6acin rai daddy Yakama hannun ilham
suka nufi mota, suna tafiya yana rarraahinta
itakuma sai kuka take, har cikin ransa yakejin
kukan nata, Bank suka biya yasaka ATM yaciro
kud'i yabata 30thausand sannan ya wuce. Haka
ilham tashiga school d'in ranta 6ace. A class ne
bayan anyimasu break fast duk Kowa yafita
amma ilham batada niyyar fita saboda har yanzu
zuciyarta zafi take, tunda tashigo Hakeem ya
kula da halin datake ciki saboda haka shima kasa
fita yayi ya tsaya yana tambayar ilham dalilin
6acin ranta. Nan ta kwashe kome tagayamshi,
cike da damuwa yace "ilham bakiyi abinda
Abigael tace kiyiba da kinyi da Momy bata Isa ta
6atamaki raiba, ilham ta share hawayenta tace
kada ka damu Hakeem yau Dana koma zan
aiwatar da kome, Hakeem yayi murmushi yace
yauwa babyna saikin daure bekamata ace babbar
yarinya kamarki kullum kina cikin 6acin raiba......
Aranar dai haka Hakeem ya rinka 'karfafama
ilham gwiwa tare dayimata kalamai masu dad'i
harta saki ranta. Love u all Zee Elkaseem